← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 176

Sashe 153

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin tausayi mai nauyi ya cika zuciyar Akhnan.
Saboda ta gane,mutumin da duniya ke gani a matsayin untouchable… a wannan daren, yana neman gida ne kawai. Wannan gidan kuwa itace.....jikinta ne......kulawarta ce,batayi qasa a gwiwa ba ta soma bashi wannan gidan,tana mantar dashi komai da zafafan 'yan aike.

Sai daya tabbatar da baccinta yayi nisa sannan ya miqe ya koma ga wayarsa,yana budewa hoton wasiqar yana fadowa email dinsa. Ya zauna a hankali ta yadda motsinsa bazai tasheta ba ya soma karantawa.

Haisam

Na tsane ka.
Wataqila wannan shine abu na qarshe da zaka taba ji daga gareni,amma bana son tafiya ba tare da ka san cewa kai ne mutum na farko da ya sa na ji tsoron kaina.

Ka rushe komai.

Ba saboda ka qi sona ba…ko na kasa samun goyon bayanka ba, sai saboda ka kalli raina da burikana kamar basu da wani muhimmanci.

A rayuwata ban saba da rashin samun abin da nake so ba. Amma a kanka!.
Ka bani abu mafi muni fiye da wofantarwa da rashin nasara,wannan shine.
Wulakanci.
Ka sanya mutane suna kallona da tausayi.
Ka tozarta alfarmata,ka kashe mafarkin dana shekara sama da arba'in ina ginawa tun quruciyata.
Ni.
Mammina.
Ban iya rayuwa cikin wannan ba.
Ban juri qasqanci ko rayuwa qasan kowa ba
Daukaka na sani,jagoranci ne dabi'ata.
Tunda dukka na rasasu....na fi son na bace da in tsaya ina jiran a yanke min hukunci kamar wata mara daraja.
Ka ci nasara, Haisam.
Ka kare matarka. Ka kare sunanka. Ka kare duniyarka. Ka kare ahalin matarka.....tabbas na sara maka da wannan namijin qoqarin.....na yaba maka,na kuma taya akhnan murnar samun namijin duniya irinka
Amma kada ka taba tunanin baka lalata tawa rayuwar ba....kaine ka lalatata,kaine silar mutuwata.
Zan tafi barzahu qiyayyarka a raina.....data akhnan da dukkanin jinin safeena
Mammina.

"Subhanallah" Ya maimaita har sau uku yana lumshe idanunsa. A hankali ya motsa labbansa.

"Ba shakka abinda Allah ya fada a qur'ani gaskiya ne. Wanda Allah ya shiryar shine shiryayye.....duk wanda kuma Allah ya batar ba wanda zai shiryar dashi. Yaga wannan ayar a zahiri kan mammina,sai ya shiga ya goge saqon gaba daya,don baida wani amfani a gurinsa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 140*
________________________
*_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
________________________

A kwanakin da suka yi a Amangiri, Akhnan ta fara fahimtar wani bangare na Haisam da duniya bazata taba gani ba. Sai ita kadai,sai ita daya ita khadeeja muhammad hammud.

Hamadar wajen ta kasance da wata irin cikin nutsuwa da kuma wani irin yanayi me kwantar da hankali… a karon farko a rayuwarta,shiru bai tsoratar da ita ba. A karon farko ta fahimci ma'anar shiru.... A karon farko ta gane shiru wani abu ne dake bada alamu na nutsuwa cikakkiya tare da shi.

Ta kalli yadda yake lura da qananan abubuwa game da ita ba tare da tayi magana ba. Yadda yake rage muryarsa idan zai mata magana. Yadda yake cire duk wani abu da zai dame ta kafin ma ta furta,tare da cika mata komai da take so take muradi kafin ma takai ga furtawa.

Kuma duk da ikon da yake da shi… a wajen, bai yi kama da mutumin da duniya ke tsoro ba,sai wani mutum da duniya take girmamawa matuqar girmamawa.

A idanunsa take ganin mutum mai gajiya da yake neman wajen hutawa a tare da matar da yake so.

A wasu dararen,Akhnan kan tsaya tana kallon desert lights tana tunanin yadda rayuwarta ta sauya.

Cikin lokaci kadan daya wuce ta taba jin tsoron duniyar haisam.

Tsoron irin ikonsa.....tsoron izzarsa da irin girman da yake da shi a idanun duniya.....daga qarshe ta soma tsoron soyayyar da zata iya cinye mutum gaba daya,saboda girmanta da fadinta.

Amma a Amangiri… ta fara jin wani abu daban. SAFETY. Ba saboda wajen ba,sai saboda shi. Ya bata wani irin aminci cikin rayuwarta. Ya bata tabbaci.......sannan kuma ya bata yaqini na har abada.

Ko lokacin da jikinta ya fara canzawa, canzawar da ta sani da gaske ne yana sauyawar. Lokacin da tsoro ya fara shiga zuciyarta,haisam bai matsa mata ba. Bai tambayi abin da bata shirya furtawa ba. Bai tilasta mata fuskantar gaskiyar da take gudu daga gare ta ba.

Sai dai ya tsaya kusa da ita cikin nutsuwa… kamar yana gaya mata cewa ko menene zai zo, bazata dauke shi ita kadai ba.

Kuma a cikin shirun hamadar da babu kowa sai su biyu…Akhnan ta fara gane cewa wata soyayyar bata zuwa da hayaniya. Wata soyayyar tana zuwa ne da kulawa da nutsuwa, hannun da baya sakinka idan kina tsoro, da kuma mutumin da yake maida duniya gaba daya ta yi shiru saboda ke.

Private jet dinsu ya bar hamadar Amangiri ne da sassafe.

Idanun akhnan kafe daga qasa. A qasan golden desert din na qara nisa a hankali.

Amma duk da tafiyar,akhnan har yanzu tana kallon wajen ta window kamar bata son barin peace din da suka samu a can ita da haisam din.

Yana zaune kusa da ita. Suit dinsa dark charcoal. Ta kalli hannunsa a hankali,agogon hannunsa na kyalli under soft cabin lights. Wannan royal calm dinsa ya dawo yanzu.

Phones. Business calls. Security updates,kamar da zarar sun bar Amangiri duniya ta sake tunawa da shi. Wannan ya sake gaya mata da gaske ya manta da kowa dake duniya sanda suna Amangiri. Da gaske ya bar mata dukka duniyarsa ne da lokacinsa gaba daya. Ya sadaukar mata da komai da komai ita daya!.

Sai dai ta lura duk tsakiyar calls din,idanunsa na komawa kanta lokaci zuwa lokaci. Always checking. Always aware of her.

“You’re back to being busy.” ta fada softly cikin salon tsokana.

Wani lallausan murmushi ya saki yana sauke wayar dake riqe a hannunsa.

“I was always busy.”

“I just ignored the world for you.” wani laushi zuciyarta tayi, ta lumshe idanunta a hankali. Kowacce magana Idan zaiyi sake bata proof yakeyi na yadda yake qaunarta. Kowacce magana proof ne na yadda soyayyar ta take da zurfi a zuciyarsa.

Da wannan kallon yake dubanta, da wadannan idanun nasa masu matuqar kwarjini. Idanun nan da har yanzu nauyi suke mata.

"Zo nan" Ya fada softly yana miqa mata hannunsa. Ka fada ta maqale tana narke idanunta cikin nasa. Jikinsa ya mutu murus da kalar kallon da take masa.

"Ayimin izini ranki ya dade na qaraso idan ba zaki samu tasowa ba" ya sake fada yana karya wuya kamar wani marayan da ya rasa uwa da uba gaba daya.

Murmushi ne ya subuce mata, ta karyar da wuya itama tana kallonsa. Tana kallon mutumin da dukka rayuwarta da numfashinta suka dogara dashi. Sai ta miqe, da wata irin nutsuwa,da wani irin taku da tasan yana janye hankalinsa. Da wani irin yanayi da takejinta a sama. Tana jinta kamar tafi kowacce mace sa'ar miji da dacewa.

Kyakkyawan masauki ya mata cikin jikinsa,yana matseta da kyau a jikin nasa. Ya sauke wata sassanya kuma siririyarr ajiyar zuciya yana cewa.

"duk sanda nake neman gida......ba wani gida sama da nan" ya fada yana nuna saman qirjinta,inda mafi yawan lokuta a nan yake kwantar da kansa idan zai mata runguma irin wannan. Hannuwanta duka biyun ta saka itama tana zagayeshi gami da rungumeshi tsam cikin jikinta. T sauke itama ajiyar zuciyar tana bashi daman sakewa a jikinta. Lokuta da yawa bata iya magana,bata iya cewa komai idan ya soma dafa zuciyarta da lausasan kalamansa irin haka.

Lokacin da suka isa jimma sama ta fara duhu kadan da alamar samun saukan ruwan sama kowannw lokaci daga sannan.

Jimma ta yi green sosai saboda wadataccen ruwan sama da tsirrai suka samu. Gari ne da yake da wani irin yanayi me kyau tun asali,wadatar shuke shuke da qoramu dake sanya garin kasancewa cikin koren yanayi,sosai suke da yawaitar tsirrai,tsaunika masu kyau dake qarawa garin kyau,bishiyoyi dake dashe a tituna da Street na anguwanni. Wani iska mw sanyi garin yake bayarwa,ga qamshin qasa mai sanyi dake alamta saukar ruwa.

Convoy mai tsawo ne yake jiransu outside private airstrip.

Black luxury SUVs,royal security.

Mutanensu ne cikin girmamawa da Karramawa.

Zuwa yanzu ta gama fahimta ta kuma fara sabawa da ganin komai tattare dashi......amma kowanne lokaci tana sake fahimtar haisam ba ordinary bane.

Soyayyar mutanensa a kansa tana da girman data isa ka gane cewa,bawai.....sun sonsa bawai don yarimansu bane. Suna sonsa bawai don ya mallaki dukiya bane. Aah,kalar soyayyar da suke masa.....soyayya ce da zakasan cewa tausayi da kulawa da kyautatawa sune jigon ginata.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

A nutse giiftii akhnan ta sauka daga motar tana kallon surroundings din sans motocinsu ke daukan hanyar gida. Wannan bangaren Jimma din da suke nufa ba irin city din da ta sani bane. A hankali ta waiwayo gare shi tana dubanshi.

"ina zamu je?" ta furta kai tsaye,don ita nanay takeso ta gani,ta masu taje ta ganta. Har cikinranta da zuciyarta takejin tayi missing dattijuwar sosai. Sosai take jinta a ranta tamkar mahaifiyarta. Ko ba komai......ko ba alaqa ai ta haifa mata jarumin maza,daya tamkar da Million.

Siririn murmushi ya bayyana a lips dinsa. Wancan murmushin nasa nan da yake nuna ya san wani abu ita bata sani baa

“Home.” ya amsa mata a taqaice.
Chapter 153 · 0% Book details