← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 176

Sashe 35

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai ya fahimci abinda haisam ke magana akai,kishi.....kishi ne da bazai barshi ya shiga ciki ba,shima kuma bai yarda ya koma ba duk da matarsa tana ciki. Dole kuma yana buqatar wani,wanin da zai lallasar masa falaak din ya kuma bata taimako bayan wanda yayi iya yinsa.

Matsawa akhnan hanya maleek yayi yana fitowa,saidai bai yarda sun hada idanu ba,sai wani gaisuwar babbar yaya da yake mata.

"Barka da warhaka tanti.....ina fata kina lafiya" Ita bata ma fahimci wannan abun nasa ba,hankalinta dari bisa dari yana kan falaak,bata taba zaton ta damu da ita ba sai yau,yau din da taji batun kisa. Mamaki kuma ya kamata ganin maleek ya fito gabansu,ba alamun jini ko wani abu na kisa a tattare dashi,kawai tunda taji alamar haisam ya sake mata hannu saita zame da sauri ta wuce ciki.

"Fito munafuki" Haisam ya sake maimaitawa yana zubewa maleek idanu. Murmushi kawai maleek ya saki suna takawa zuwa lobby din dake daura da gurin,wanda aka qawatashi da kujerun zama daidai da yadda masu zama a gurin zasuji dadin zamansu.

Kai kawai maleek ke girgizawa,ya gaza amsawa haisam kalman munafukin daya kirashi.

"Kayyasa......wallahi mun dade a matsayin buhunhuna kuma bahuna......ashe naseeb ya fimu wayo?,me yasa duka shekarun nan muke zaune bamuyi aure ba?" Shuru kawai haisam yayi,da wannan kalar cikakkiyar nutsuwar tasa yake kallon maleek. Yanason gano abinda yaji ba'a kalamansa ba,a yanayinsa da yadda maganan ke fita daga can qasan zuciyarsa. Bazai qaryatashi ba,idan ya gwada da abinda ya faru dazu dashi baisan me ya sanya maleek wannan sambatun ba. Bayason jin komai,kamar yadda yasan maleek din shima ba fada zai ba,amma sambatun da yake masa yayi yawa,yana tsoron kuma amanar sultane a hannunsu,kada yaci gaba da tafi da falaak din a haka,shi yasan illar da irin hakan yake haifarwa a matakin farko tsakanin ma'aurata.

"Wanne irin rashin imani ka gwadawa d'iyar mutane?,kanason taci gaba da gudunka?" Sakin baki maleek yayi ya zubawa haisam ido.

"Captain......anya kuwa kaje inda naje?" Tambayar ta dan zowa haisam da nauyi,sai kawai ya lumshe idonsa ya budesu duka akan maleek,don ya sani,idan bai sauke masa nauyi me yawa ba daga cikin idanunsa ba yanzun sai ya sauka daga kan layi ko shi ya saukeshi.

"Ba wannan na tambayeka ko nace ka tambayeni ba.....ba huruminka bane" Idanun sunma maleek nauyi yadda aka saba,ya dauke kansa zuwa gefe saboda a yau dai yana jin bazai fasa yiwa haisam tsiya ba ko bata da yawa

"Allah ya sani ni bada niyya bane,bansan ma yadda akayi komai yazo a haka ba.....amma dai yadda kamin tambayar nan ne captain sai ake gayamin bakaje ko ina ba shi yasa ka tuhumeni,inda ka bude littafin kayi karatunsa da kyau Allah ba zaka tuhumeni ba,saboda kaima......" Saukar wani irin duka a gadon bayansa ya dakatar da jawabinsa,koda ya waiwayo sai yaga haisam ne,kuma sake mulmule hannunsa yakeyi,ba shiri ya matsa zuwa mazaunin gaba

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Fisabilillahi ina kan sharafina zaka tsugunnar dani....."

"Gwara ka tsugunna din ai......kaga sai kuyi jinyar,tare mara imani" Dariya maleek ya fashe sosai dashi

"Um....um fa captain.....kada lokaci yayi muzo muna wasan 'yar buya fa?".

"Wasan 'yar bacewa zamuyi" Ya fada yana danna masa harara,dole maleek ya sake sakin dariya sosai yana duban haisam.

Qafafunta har rawa suke sanda ta isa bakin gadon dake a yamutse kamar na 'yan dambe.

"Falaak" Ta kira sunanta muryarta tana rawa ta kuma haura gadon da sauri tana rarumar falaak din.

Rungumeta tayi sosai a jikinta,ita kuma falaak din ta saki kuka sosai tana riqe akhnan din itama.

"Me yayi miki falaak.....me yayi miki?" Tambayar kawai da akhnan din ke iya maimaitawa kenan a rude tana sake riqe falaak sosai cikin jikinta. Idanunta akan fuskarta da taga ta wani rame lokaci daya ta fada sosai.

"Ba komai" Amsar da falaak ta iya bata kenan. Batasan yadda zata mata bayani ba,batasan me zatace mata ba,saida tazo sannan takejin wata kunyarta tana danneta,damuwa da rudewar kuma data gani tattare da akhnan din saita qara mata qaunarta sosai.

Tambayar duniya amma amsar falaak itace ba komai,dole akhnan ta saketa a hankali tana fadin.

"Na baki ruwa?,bakinki kaman ya bushe....jikinki da zazzabi sosai".

"Wanka nakeso na sakeyi,ruwan dumi nakeso sosai" Kai akhnan ta daga mata jikinta har yanzu rawa yake,don bata gamsu da abinda falaak ta fadinba,bata taba ganinta cikin wannan yanayin ba duk da ba wata doguwar alaqa bace a tsakaninsu.

Hannunta ta dauke da dan sauri jin ta dorashi saman wani danshi danshi..

"Jini?!" Ta fada a rude tana duban falaak,saita sake maida idanunta akan bedsheet din. Nan gurinne kawai keda jinin,amma akwai wasu gurare da ya danyi staining kadan kadan.

"Falaak......ki fadamin ne yayi miki....jini fa nake gani,ki fadamin ko na kira sultane yanzun nan"

"Ba komai.....ba komai tanti" Falaak ta fadi idanunta suna rau rau da hawaye. Ido ta zubawa falaak ranta yana baci,da alama yarinyar soyayya ta rufe mata idanu ne har bata ganin laifinsa,ita kuwa ba zata bari ba.....ba zata bari kowa a cikin su ya cutar dasu ba don suna ganin ba qasarsu suke ba,kawai saita sauka daga saman gadon da hanzarinta,don ta tuna wayar haisam din ya zameta a hannunta sanda zasu shiga elevator.

A nutse ya daga idonsa daga kan waya ya maida kanta sanda take fitowa daga dakin,ya zuba mata idanu ganin tana waige waige. Miqewa yayi tsam,don shi kadai ne a gurin,maleek ya sauka can first reception zaya karbi saqo.

"Wayata zaka bani" Ta fada tana miqa masa hannunta. Hannun yabi da kallo,gefan hannun rigar tata ya danyi stain na jini kadan. A nutse ya sauke kallonsa cikin qwayar idanunta. Yana karantar wani fushi da zafi sosai cikin idanunta

"Kiyi me da ita?" Ya tambaya calmly.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 33*

"Na kira sultane.....na fada masa jini har a kwancinta amma taqi gayamin abinda yayi mata....bayan dazun zai kasheta tacemin" Tayi maganan tana sauke numfashi da alamun fushi sosai a fuska da muryarta.

Wani irin kyau tayi masa.....wani irin kyau daya sanyashi lumshe idonsa sannan ya budesu dukka akan fuskarta. Bai taba ganin fushinta na gasken gaske ba sai yau.....wani irin kyau fuskar tayi yadda ta tsuketa.

"Ba zata gaya miki ba.....kema ba zaki kira sultane ba....kije ki taimaka mata kawai ya isa".

"Jini fa a jikinta?,sannan kace kada na kirashi?" Ta qarashe fada tana kallon yadda yake takowa inda take yana rage tazarar dake tsakaninsu. Bata matsa baya ba,saboda ranta a bace yake da gaske,wannan ya basu daman tsaiwa sosai gab da junan da cikakken motsi dayansu yayi yana iya cike gap din.

"Sun cika aurensu ne.....zaki fallasa sirrin first night din wasu ne?" Dummm taji kanta yayi mata,hannunta dake pointing wani guri ya tsaya cak ya qame a gurin. Wani irin yanayi me nauyin gaske ya saukar mata,shin me yasa ma ta tsaya bata ja baya ba sanda yazo dab da ita,gashi yanzu ya fada mata wasu kalmomi da nauyinsu ya sanya takejin kamar ba zata iya daga qafanta ba.

"Uhmmm.....tell me....me zakice da sultane din idan kin kirashi,I’ll help you call him." Ya fada yana latsa wayarsa kamar me nema mata number sultane din.

Kaf energy dinta aka kwashe,idea dinta kuma ta bace. Shi baida kunya fisabilillahi?,meye na gaya mata haka kai tsaye?,saita samu kanta da kallonsa kawai bakinta ya gaza cewa komai.

Sanda ya dago idanunsa sai suka hadu da nata,ya dage giransa dukka biyun.

"You keep staring......uhmmm tell me me zaki gaya masa?" Idanunta ta sauke da wani irin sanyi,sai tayi taku uku baya cikin dabara,sannan ta juya da wani zafin nama tana arcewa cikin dakin.

Da kallo yabi bayanta,yadda take saurin kawai zai gaya maka akwai abinda ya tilastata,akwai abinda kuma take gujewa,amma sam saurin baiyi matching character dinta ba.

Baisan ya akayi murmushi ya subuce masa ba,ya ciji gefan lips dinsa na qasa,ya koma da baya a hankali ya zauna bayan ya ajiye wayar a gefansa.

Ta dade tsaye tana kallon falaak sannan ta tattaka tana mata sannu. Tsoro sosai ya dinga mamayarta sanda taga falaak din na takawa da dabara zuwa toilet. Abinda bata taba ba,yau itace da yaye bedsheet da kanta,bedsheet din data ji qwalla da tsoro sun kamata da taga ragowar jinin da yayi staining a jiki.

"Maza basu da imani" Ta samu kanta da fadi itakam ta yaya ma zata bari akai wannan abun bare har ayi mata irin wannan aika aikar?.

"Kina da tabbaci?" Zuciyarta tayi mata tambayar data kusa tsayar da bugun numfashinta saboda tsoro.

Ita ta taimaka mata da iya abinda zata iya ta gasa jikinta,saidai ko gurin gyara gurin falaak din ta lallaba tayi. Koda akhnan batayi mata komai ba zuwanta ya bata relief sosai. Kallon falaak kawai take jikinta a sanyaye tsoro yana kamata,to amma sai take samun sassauci idan ta tuna ba wani soyayya bane a tsakaninsu da zai kaisu ga wannan,uwa uba ma daki daban daban suke kwana,ba kaman falaak ba data lura suna sharing daki daya ne.

"Ke kinsan haka yake,me ya kaikai sharing daki dashi?" Tambayar ta bawa falaak mamaki da dariya can qasan ranta,da gaske akhnan batasan haka abun hake yake ba?,inde haka ne kuwa akwai qura,sai ta yanke tayi mata gwari gwari kawai.

"Haka abun yake tanti....haka kowacce mace takeyi"

"Take uban me falaak?,kinsan me kike fada kuwa?" Ta fadi har batasan tayi spark ba saboda wani tsoro da falaak din ta qara mata. Qasa tayi da kanta dariya nason qwace mata amma tana dannewa. Da gaske koda akhnan tasan da wannan abun amma sam bata taba kawoshi a lissafinta ba sam a cikin aure.

"Da gaske nake....ki kira tanti hairaaan kiji"
Chapter 35 · 0% Book details