← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 176

Sashe 111

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu aisa kawai ba.....hatta da akhnan kanta ya sake kwanceta fitar da sukayi. Guraren da suke kashe kudade masu yawa.....guraren da suke kula da shigarsu a yau sun shiga sun fito ba tare da sunsan sun kashe komai ba. Batasan girma da kimar da yake dasu haka ba cikin qasar.....wanda iya card dinta kawai ake kalla a duk inda sukaje din sai taga an ninka girmamawar da ake bata.

luxury malls.....rooftop lounges......waterfront restaurants......designer stores.....amma duk inda suka shiga da zarar Akhnan ta nuna card din. Staffs nasu suna sauya attitude instantly.....still kuma
ana kaisu VIP sections a kowanne guri da zasuje din.

Daidai da boutique din da sukaje private collection room aka kaisu.

"Wow" Kawai shehnaz ta fada. Kaman yau ta fara sani ko ganin luxury,sai takejin kanta yana sake girma da fadi.

"Sheikh dinnan....wannan sheikh din naki ya wuce duk zatonmu.....me yasa ya boye kansa haka?,anya ba yana sane bane kuwa?,anya ba wani babban dalili kuwa?" Shehnaz ta fada tana fidda idanunta waje sosai.

"Kudi ne da mutumin nan irin na films"

"......ba kudi kawai ba shehnaz....influence" Aisa ta fadi itama abun yana tsumata.

Tambayar qarshe da suka mata bayan sun koma gida. Shehnaz ta rutsata.

"Don Allah biftu mana.....wannan fa ba sheikh dinnan bane na agadez.....ki gaya mana waye haisam?" Tana daure zaren igiyar rigar baccinta ne sanda shehnaz take mata tambayar,kanta cunkushe da tunani,saita samu saman sofa bed ta zauna tana dubansu da blue eyes dinta.

"Mijina" Ta furta kai tsaye don bata da amsar data wuce wannan.

"Akhnan" Aisa ta fadi tana sake samu tabbacin wani abu game da abinda yake faruwa yanzun haka a sahel couture.

".....barta mana aisa.....bafa wannan muka tambaya ba" Ta fada tana fiddowa akhnan ido waje,abinda ya tilastawa akhnan din murmusawa. Idan wannan tambayar ce....itama har yanzu neman cikakkiyar amsarta takeyi

"Kinga yadda mutane suke rusuna masa kuwa?" Aisa ta fada fuskarta dauke da tarin tambayoyi da kuma murmushi.

"Ke bakiga yadda ake sauya komai saboda sunansa kawai ba?" Shehnaz ta fada tana rungume da hannayenta. Komai burgeta yake.....amma mamakin da suke shiga yafi qarfin kwatance.

"Ni kaina ban gama fahimtar hakan ba....ni kaina a rude nake har yanzu" Ta fadawa kanta da kanta ba tare data bari sunji ba.

Security alert na qofar suite dinne ya kada,alamun akwai wani kusa da qofar. Hirarsu ta katse da tarin tambayoyinsu,suka maida dubansu ga akhnan.

"Bari na duba" Ta fada softly tana miqewa gami da zura flip flops dinta.

"Dawo ki dauki wayarki,don idan mijinki ne babu lallai ya barki ki dawo" Aisa ta fada tana dariya shehnaz tana tayata.

Tsaiwa tayi cak,sannan ta waiwayo tana watsa musu harara.

"Banason sharri.....be dawo bama ballantana kuce shi dinne".

" Zamu gani.....idanuwan sheikh na rantse da Allah cike suke da giyar qaunarki....kowanne motsinki akan idanun security dinki,wanda na tabbatar suna aikinsu ne da qaqqarfan gargadinsa na su kula dake".

Bata waiwayowa ba ta biyewa zancan shehnaz,saidai har cikin ranta tana jin saukar kalamanta,ta kuma ga hakan itama,ta yarda dari bisa dari,amma idan tace zaya biyewa shehnaz ne to zasu kwana suna musu.

A hankali ta murda qofar tana budeta. Zuciya daya.....ruhi daya dake rayuwa cikin gangar jiki guda daya suka bayyanawa juna.

Yarima haisam ne......sanye cikin dark gray din silk pajamas masu gajeran hannu da dogon wando. Sassnyar iskar dake yawo cikin Atlantis the royal tana kada daddadan turaren nasa kamar yadda take kada sassalkar sumarsa dake kwance saman kansa. Da alama ya dawo tun dazun,kuma har yayi wanka sannan ya sauya kayanshi ba tare data sani ba.

Ta qifta idanunta har sau biyu a kansa saboda yadda ya mata wani irin sassanyan kyau cikin hasken fitilun alfarma da suka qawata ginin gaba daya.

Baiko barta tayi tunani na biyu ba,ya saka hannunsa dukka biyun ya dagata cak kamar ya samu baby doll,ya rungumeta sosai cikin qirjinsa sannan ya juya ba tare daya damu da rufe qofar suite din ba.

"Ka saukeni please,zan iya tafiya da qafafuna"

"No need.......indai ina tare dake ba buqatar sai qafafunki suna aiki,tawa ta ishemu" Ta motsa zata sake magana,sai bai bata wannan damar ba,ya hade bakinsu guri daya yana takawa da ita sannu a hankali har suka isa suite din nasu.

Ta dauka zai sauketa ne ta taka da qafafunta tunda sun shiga ciki....amma akasin hakan ci gaba yayi da tafiya da ita,bai kuma sauketa a ko ina ba sai cikin bedroom din da a yanzun suke sharing shi da ita. Ya kulle duka sauran bedroom din guda biyu ya hana mata maqullin.

Saman lallausan gadon ya direta sannan yayi mata rumfa. Da wani irin zafi zafi yake aike mata da saqo.....wasu irin saqonni da suka soma bin jininta cikin mintuna qalilan.

A yau....bar mata bakinta yayi a bude,baiyi yunqurin komai na rufe mata shi ba,saidai da kanta.....a karan kanta ta kasa kiran sunan kowa.....ta kuma kasa tabuka komai saboda yadda saqon ke shigarta da wani irin tasiri me gigita tunani.

Sai daya kaita wata duniya me nisan gaske.....sai daya kaita qololuwa sannan ya zame jikinsa a hankali yana sauke wani irin numfashi.

Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,wani irin shuruuuu daya shige har cikin kawunansu. Ya runtse idanunsa sosai yana riqe tsintsiyar hannunta da wani irin qarfi da sai da taji riqon har cikin qashinta,a kasalance ta furta.

"Wayyo Allah" Mirginawa yayi yana maidata cikin jikinsa da kyau yana matseta sosai wannan karan har sai data saki qarar me dan qarfi.

"I'm sorry....." Ya fada dukka jikinsa yana rawa.

"Me yasa zaki tafi ki barni?......me yasa zaki barni a kango?,me yasa zaki sanya na dauki alqawarin da zai wahalar dani?" Ya fadi yana kamo fuskarta ya hade da tasa yana sauke wani irin wahalallen numfashi,gumin da yake tsatsafowa daga kowanne sashe na jikinsa yana ratsa fatarta wadda tuni ya kauda komai da zai zame masa shamaki daga nutsewar fatarta cikin nasa.

"I'm sorry......kayi haquri" Ta fada softly tana motsa labbanta da wani yanayi daya tilasta masa kama lips din nata ya tsotsa da kyau. A hankali ya zame bakin nasa daga nata,ya sake riqe fuskarta sosai a tausashe

"Ke tawa ce......ni kadai giiftii.....ba zanyi sharing dinki da kowa ba" Ya fada yana zamewa daga jikinta. A karo na biyu ya sake saka hannu ya dauketa cak,ba tare daya damu daba komai a jikinta ba,ya kuma wuce kai tsaye da ita zuwa bathroom,tana qanqameshi saboda nauyin hakan da takeji,saidai batasan hakan da takeyi sake kunnoshi kawai tayi ba.💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 100*

*_THE REVEALS_*

Wani shiryayye kuma lafiyayyen grand opening ne da labarin yinsa ya zagaya duniya gaba daya. Wani bikin bude kamfani da yasha banban da saura......bikin daya tara manya manyan shuwagabannin larabawa masu yawan gaske. Al'umma daga kowanne sassa na duniya.....bikin kuma da aka shirya gabatar dashi da daddare sab'anin rana.

Da wannan amintaccen hasken na qasar dubai,wanda ya zame mata kamar wani ado daya sake banbantanta da kowacce qasa a duniya. Kamar duk duniya sunfi kowa sanin martabar haske da qyale qyale na rayuwa.

Qarfe bakwai na daren.....sanda wasu irin golden light suke walqiya cikin babban dakin taron sabo dal dake wata shiyya daban na kamfanin. Manyan glass windows da na building din gaba daya an qawatashi da wasu irin fitilu gold color.....flowers masu tsada cakude da daddadan qamshin turare mafi tsada da girman daraja daga gurin larabawa wato oud. Tako ina qamshin sa ne me dadi yake tashi,qamshin da zai gaya maka da gaske bikin bude kamfanin turare ne.

Daga gefansa take zaune....cikin Rolls Royce din da a yau da kansa yake driving dinta ba tare daya buqaci driver ba.

Wani irin kyau yayi mata,wani irin kyau dake fusgar idanu da hankulan kowanne mutum.

Kanta ta dauke a nutse tana maidowa kansa. Ya jima a waje yana gaya mata gashinan dawowa.....ya jima da fita yana gaya mata zaizo da kansa ya kaita,har ta fidda rai,tana kuma kallo su shehnaz da aisa sukabi su maleek da falaak da suma sukace mata sunzo ganin bikinne. Ta danyi mamaki,idan shehnaz da aisa fan din brand dinne.....batasan maleek da falaak a wannan harkar ba.

Tanata juya wayarta tana kallon yadda lokaci yaketa gudu,idanunta sunata tara hawaye tana hanasu xubowa sanda ya shigo. Wayace a kunnensa yaketa amsawa,yayi cak yana zuba mata idanu kafin ya ware mata hannuwansa,ta taso kaman hakan take jira ta fada ya rufeta a qirjinsa. Still bai daina amsa wayar ba wadda da larabci yake duk maganan da yake,wannan ya sanya bata iya gane abinda yake fada.

Wayar dai bata qare ba,don yana ajiyewa wani kiran zai shigo,a haka ya taimaka mata ta fara shirya kanta cikin wata baqar laffaya da aka yiwa adon gold stones.

Sai daya taimaka mata ta gama nade jikinta tsaf sannan ya saki wayar tayi gefe.

"Ya salammmm.....zan iya?" Ya fada yana motsa maqoshinsa a hankali. Idanu ta fidda waje tana dubansa,gabanta yana faduwa,kada dai yace an fasa zuwa....indai hakane batasan wanne irin kuka zatayi ba

"Ina kishinki.....na rantse da Allah,inajin kamar kishinki zai iya kasheni......" Ya fada idanunsa suna lumshewa can qasa da wani irin emotion cakude da kishi.

".....idan wani ya kalleki biftu.....koda sau daya ne......inajin kamar na shafeshi yabar duniya.....inajin kamar kowanne namiji yabar duniyar nan.....ya barmin duniyata dake kawai a ciki" Ya qarasa fada yana mata wani kyakkyawan riqo cikin jikinsa kamar zai hadiyeta.

Saidai taji nasa kishin baikai nata ba.....nasa kishin kaman salam ne akan nata sanda ya fito cikin shigar wata irin suite da hannunta bai taba kaiwa kan fabric irin nata ba.

Har ji tayi kaman bata iya shaqar numfashinta da kyau,duk yadda takeso suje gurin,sai taji kamar tace masa su fasa.

"Yadai?" Ya fada sanda yaga yanayin fuskarta yana sauyawa. Kanta ta kwantar a hankali hannun kujerar.

"Zasu kalleka......."

"......dukkansu maza ne.....maza suke komawa a idanuna......wallahil azeem biftu" Ya fada yana kama tafin hannunta yana murzawa a hankali.

"Mu tafi?" Ya fadi bayan ya dauke idanunsa daketa haske. Kirane yaketa shigowa ba qaqqautawa wani yana bin wani.

"Muje....kiranka akeyi" Ta fada tana sauke idanunta akan wayar da taqi daina haske.

"Zan iya dakatar da komai saboda ke.....har sai kin amince kin gamsu mu tafi din" Ya fada yana daukar wayar. Cikin idanunta yaga kaman tana suspecting wani abu.....don haka ya haska mata fuskar wayar da sunan OMAR keta yawo akan screen din.
Chapter 111 · 0% Book details