← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 176

Sashe 50

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta daga idanunta a nutse tana maidasu ga window ta cikin baqin gilashin da zai baka daman ganin na waje ba tare da shi ya ganka ba.

Shine....mr President na Ethiopia gaba daya Taye atske selassie,tare da prime minister abiy ahmed.

Dukkaninsu ta sansu,saboda tafiye tafiye na seminar data tana hadasu a gurare har biyu.

"Afwan......khansaa zata kasance da ke,zan sameku a gida in sha Allah......you are safe" Ya fada softly yana bata tabbaci da qwayar idanunsa.

Kamata yayi taji bata gamsu ba......kamata yayi taji ta qaryatashi da dukkan ruhinta da gangar jikinta,amma abun takaicin sai taji zuciyarta ba wani d'ar shakka ko kokwanto akan maganarshi.

Da idanu ta bishi sanda yake sauka a motar,da dukka nutsuwarsa yake takawa zuwa garesu,ba wani yanayi da zai nuna maka farin shigar haduwa dasu ne,dukkan takunsa da motsinsa yana nuna maka mutumin da aka haifa cikin mulki da iko ne.

Idanunta ta janye gabanta na bugawa da qarfin gaske sanda taga yana basu hannu kai tsaye suna musabaha,fuskar nan tasa da madaidaiciyar fara'ar dake qara fidda kyansa da kwarjininsa,daidai sanda khansaa ke shigowa cikin motar.

"Sai kinwa angonkin nan uzuri,jama'arsa yawa ne dasu,kowa zai buqaci ganinsa na sani a dawowar nan,zai iya zama busy na wasu lokuta.....amma idan komai ya daidaita....." Saita dakata tana sanin murmushi.

"Zaki bada shaidar ba macen data kaiki dacen miji" Ta qarasa fada sanda motar ta fara motsawa a hankali da sauran ayarin motocinsu da suka fita daga cikin nasu prime minister da mr President.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 46*

Sake gyara zamanta hasnaaa tayi,tana gyara lullubin tattausar laffayar jikinta.

"Allah yasa kada na dameki.....bana iya zama banyi hirara qanina ba" Ta fada da murmushi. Maganan daya dauke idanun akhnan daga kan hanya,ya maida kan hasnaa irin kallon da baya sauka kai tsaye cikin fuskar mutum.

"Ba don yana qanina bane.....amma shi din na dabanne. Inda Allah ya halatta aure tsakanin yaaya da qaninta,inajin da bazan bari ki samu Captain obbo ba" Ta fada da murmushi me sauti. Maganan ya sanya akhnan duban hasnaa kadan,fuskarta da idanuwanta dukka sun nuna mata da gaske take,abinda take fada daga zuciyarta ne. Saita gyada mata kai.

"Eh,bani kadai ba,na tabbata dukka qannen haisam idan da zaki tambayesu zasu gaya miki haka.....amma tsaya.....meye sirrin?,wannan zuciyar......ya akayi kika samu muqullin budeta?" Tayi tambayar da sigar tsokana da dariya sosai akan fuskarta. Murmushi kadan akhnan ta saki,haka kawai takejin wani nauyin khansaa ya saukar mata,tayi qasa da idanunta a hankali.

Tambayarta bata da amsa.....don bazata iya cewa komai ba. Har yanzu bata sani ba,ita ta saceshi ko shine ya saceta?,a cikin su batasan waye yayi wani aiki gagarumi ba. Kai tsaye ma tana iya cewa aikin na sultane ne.....sultane ne ya shirya komai,ba ita bace......kaman yadda zarginta na farko akan shine silar shirya komai tuni ya tsiyaye tas daga ranta.

"Kodai shine ya soma?.....nasan halinsa......yana da wani irin sirri da ban taba ganin gurin kowa ba sai qanina" Ta sake fada tana yin qasa da muryarta da wani salon tsokanar na daban.

Yadda take maganan kamar sirri sukeyi yaso bawa akhnan dariya. Wanne irin mutane ne wadannan?,tana hangen izzar sarauta sosai tare dasu da wani irin salo......amma kuma wani sassauqan hali da mu'amala garesu har haka?.

Idanunta ta lumshe tana sauraren yadda Khansaa ke bata taqaitattun bayanai akan haisam din. Bayanan data samu kunnuwanta da zurfafa gurin saurararsu,suka kuma dinga buda mata wata siririyar qofa game dashi,saidai qofar batayi fadi ba......bata kuma kaita zuwa inda takeson zuwa kai tsaye ba.

"Alhamdulillah mun qaraso" Taji hasnaa tana fadi,daidai sanda wayarta ta dauki qara. Kusan a tare suka maida dubansu kan wayar,ta dago fuskarta fal murmushi.

"Nanay ce.....anya nanay zata iya bacci yau?,matar sheikh a jimma kusa da ita?". Ta fadi wani kykkyawan murmushi yana mamaye fuskarta,sannan ta soma qoqarin daga wayar tana barin akhnan da zarcewa duniyar tunani.

"Nanay......khansaa.....hasnaaa......obbo......" Komai nasu wani iri yake mata,dukka sunayen baqi ne a kunnenta.

Cikakkiyar sallamar data burge akhnan taji hasnaaa din tayi cikin qaramar dariya.

"Nanay.....karki damu,matar captain tana cikin aminci......tana tare dani"

"Alhamdulillah.......alhamdulillah,karku barta cikin kadaici........abar mata duk wanda takeson kasancewa dashi,idan kun shiga ciki kun kammala komai ki kirani ki hadani da ita". Nanay dake tsaye gaban mirror dinta ta fada tana jin wani sanyi da nutsuwa yana saukar mata.

"Da wuri haka nanay?,babu kara ko kadan?" Qaramin murmushi Nanay din ta saki. Komai da takeyi kaara kawai take saboda dattijai dake cikin tafiyar,banda haka.....abinda zatafiso shine,taje da kanta ta tarbo matar muhammad dinta.....ta taka da kanta ta riqo hannunta,ta kaita palace learning residence. Itace mace ta farko da zata fara shiga gidan,wanda an ginashi ne kawai saboda ita. Suruka ta farko ga family din moti ibraheem aba jifar,amma tayi dukkan kawaici ta dauke kai ta barwa masu yi sukayi,hakan bai isa ba?.

"Hasnaaa....kiyi yadda yadda nace"

"An gama nanay" Ta fada da murmushi tana gimtse kiran,daidai sanda dukkanin motocin suka karkata akalarsu zuwa katafaren gate din me fadi da tsaho.

Wata irin qofa Dark carved hardwood me adon gold details,wata irin qofa ce da aka qerata da wani nau'in katako me duhu,katako ke daraja katako ba irin qofar qarfe da aka saba gani ba a dukka main entrance na gidaje. Da wani nau'in gold aka sassaqa zane a jikinta,zanen dake nuna symbol na sarauta da heritage dake nuna qarfin iko.

Lokacin da motocin ke qoqarin wucewa ta cikin qofar sai taji kamar sun qanqance saboda fadi da tsahon qofar. Idanunta ta sake saukewa a hankali akan murafun qofar guda biyu,tarihi take tunanawa da al'ada......amma ga duk wanda ya fita a gidan sarauta zai fahimci akwai alfahari wajen sassaqa qofar da kuma narkar da maquden kudade.

Zanen zaki ne a jiki,garkuwa da kuma wani irin crown da yasha banban da yanayin wanda ta taba gani. Idanunta ta maida kan mutum biyun da suka bude qofofin don bawa dukkanin motocin damar shigewa.

Wasu irin bayi ne manya,masu tsaho kauri da qiba,sama da yadda take ganin girma da cika idanun tamim da kusan yafi kowa cikin masarautar agadez irin wannan qirar. Sanye suke da wasu irin uniform dake nuna cikakakkun ma'aikatan da rayuwarsu ke cikin tsari.....uniform din da zai gaya maka an tsamosu ne daga wata masarauta me cikar izza da iko.

Wani irin parking lot ne dake tsare da wasu irin grass carpet na alfarma da wata irin rumfa dake bada yanayin ajiya me kyau,dukkanin motocin,duk yawansu a nan suka samu guri,kafin qofofinsu su fara budewa,saidai tasu motar bataga koda hasnaaa ta bude ba,sai murmushi data sauke mata.

"Wannan mutumin....kowa ma sai ya koya masa tsarinsa?,su waye mutanen nan?" Ta tambayi kanta da zuciyarta dake bugawa idanunta suna hangen hadimai da guards da sukayi sahu sahu kamar ba rai a jikinsu tsabar biyayya wa umarnin da bataji wanda yace musu ko kalma daya akan ga yadda zasu tsaya ko kuma ga yadda zasu tsara ba.....tsabar horo.....tsabar iyawa da tsananin qwarewa data zamewa kowanne hadimi ruwan jikinsa sakamakon jagorancin fasihin shugaba yarima me jiran gadon sheikh muhammad haisam. Sai ya zamana kamar kowa yasan kansa,kamar kowa yasan aikinsa.....kamar kowa yasan darajar kansa da muhimmancin lokaci,kamar kowa yasan abinda ya dace yayi a sanda ya dace ba tare da an bata lokacin yin magana da kowa ba.

A hankali qofofin motar suka bude da kansu ba tare da kowa ya budesu ba. Wani abu ya tsarga mata tare da sake nauyaya cikin kanta. Ta sani,akwai motocin dake da voice assistance.....akwai masu automatic doors.....amma bata taba tsammaninsu tattare da haisam ba.

Ta daya side din hasnaaa ta zagayo,ta miqawa akhnan hannunta tana fadin.

"Ki fito da addu'a....Rabbi anzilni munzalan mubarakan wa'anta khairul munzileen.....rabbi adkilni mudkala sidqeen,wa'akhrijni mukhraja sidqeen,waj'alni minladunka suld'anann naseera(addu'o'i ne masu kyau ga amaren da zasu sanya qafafunsu gidajensu na aure,sai a daure kuma a saka niyyar aiki da kykkyawan addu'a da fatan dake cikin ayoyin)". Lokaci daya dukkan ayoyin suka zauna mata a kai,ta maimaitasu kaman yadda taji hasnaaa tayi,sannan ta taimaka mata ta tattare mata rigar don kada ta taketa.

Maimakon grass carpet ko interlock ko marbles da take sanya ran gani a qasan,aah....wannan din wani shimfidadden velvet carpet ne me duhu da aka yiwa ado da zaren gold,iyakar ganinta.....ganin daya kai idanunta har hallway din.

Babban hallway take iya hanga daga gabansu.....wani irin hallway da aka tsarashi da wasu irin fitilu masu girma da tsaho da suke bada wadataccen hasken daya hana rana fitar da haskenta yadda ya kamata saboda hadarin dake kwance luf cikin sararin samaniyar jimma Ethiopia.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

A hankali hasnaaa ta saita mata qafafunta zuwa bakin hallway din,ta tsaya cak tana fuskantarsa,daidai sanda siririyar daddadar busar sarewar ta soma tashi,sai tsaiwar ta mata kama irin tsaiwar da wani babban mutum keyi don ayi masa parade na girmamawa.

Cikin kintsi da nutsuwa gurin yake,kowa yana tsaye a nutse,yawansu bai sanya komai ya hargitse ba,iya yanayin kawai zai gaya maka harka ce ta mutane masu cike da addini da nutsuwa,wadanda suka samu tarbiyya da horo daga hannun daya dace.
Chapter 50 · 0% Book details