← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 176

Sashe 65

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sha biyar ga wata.....wata daya kenan a gaba?" Ta tambayi kanta.

"Lallai ne a wannan lokacin bikin aure zai hade dana bude kamfani" Ta fadi can qasan ranta,saima ta fasa daukan ruwan,ta fito tana ficewa,wanda harta fice dimma basu kula da ita ba saboda hirarrakinsu da sukeyi,amma ta lura haisam din baya gurin da alama shi ya fice ne.

*_W A S H E G A R I_*

Cikin girma isa da qasaita jerin motocin masarautar aba jifar ke shigewa gate din palace learning residence wanda ke dauke da wata fakadediyar harabar da zata cinye dukka adadin motocin da zasu shigo cikinta ba tare da sun takura ba.

Wani abu me sanyi nanay keji yana ratsata tunda suka shigo farfajiyar gidan. Wani zumudi ne yake kamata da zaquwar data kwana da ita tun a daren jiya. Daga jiya zuwa yau ta rufe idanunta tayi addu'a cikin zuciyarta har batasan adadi ba. Tana roqon Allah yadda ya tanqwara zuciyarta ya bata ikon daidaita adalci tsakanin 'ya'yanta,soyayyar dayansu bai sanya ta fifitashi a gaban idanunsu ba.....Allah ya bata ikon yin adalci tsakanin surukanta da duk za'a auro mata..

Batasan me yasa ba.....ko don haisam din na dabanne a ranta shi yasa komai nasa.....komai daya shafeshi yake zama na daban a ranta?.

Tayi bismillah tana sako qafafunta waje sanda haisam ya bude mata motar da take ciki,hadiman da suke tare da ita suka matso don gyara mata rigarta ta baya,ya daga musu hannu yana dakatar dasu. Ba gwanar fita bace nanay sam,zai wahala ace maka yau bata nan,amma duk sanda zata fita din haisam ke hidimar rakata yana kula da lafiyarta da motsinta har su dawo. Shi ya matsa da kansa ta bayanta ya gyara mata komai,idanun samee dake cikinsu Aaanani yana kansa.

Wani sake burgeta yakeyi,tana ji har cikin zuciyarta ba zatayi asarar wannan ba,shi din mallakinta ne. Tana ji a ranta inama ace itace tsaye haka a gabansa yake hidima da ita?.

Jerawa sukayi shi da Nanay din suna takawa a hankali,su rumaisa na bayansu,hadimanta mata a bayansu rumaisa din,sai guards da dogaran da suke cikin fararen kaya da suka cika gida kaca kaca sama da yadda yake a baya.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 59*

Cikin kamalar nan tata,uwa mabada maama khadeeja yunnus jallata......baya goya marayu,tayi tata tayi ta saura,uwar tausayi da taimako,MAMA OROMO kaman yadda da dama jama'anta ke kiranta take takawa zuwa cikin gidan,hannunta cikin na haisam yana riqe da ita.

Wani kalan kwantaccen murmushi ne akan fuskarta,murmushin da iyashi kadai ya isa ya gaya maka labarin dake cikin zuciyarta. Sanye take da wani lallausan tufafi daya kasance ainihin suturar qabilar oromo,saidai dinkin da aka mata dinki ne dake nuna sarauta da kuma girma irin da dattijantaka.

Cikin parlor na biyu suka yada zango,yayi tsaye riqe da hannun nanay,daidai sanda hadiman gidan sarautar aba jifar sanye da fararen kaya suka fara shigowa da wasu akwatuna,wanda shi kansa baisan sanda suka taho dasu ba.

Wasu irin akwati ne,4corner me masifar daukar idanu,wanda baka da tabbacin da meye aka tsarashi,off white ne da aka yiwa adon royal gold a jiki. Idanunsa ya lumshe a hankali ya bude yana azasu kan nanay. Baisan wacce irin qauna takewa akhnan ba tun yanzu?. Wadannan akwatuna ne masu tsananin tsada da daraja,wadanda suka kusa guda ashirin da hudu,iya akwatin kawai baisan ma meye a ciki ba.

Murmushi ta sakar masa a tausashe,tasan abinda ke kai kawo a ransa,tasan meye a zuciyarsa. Iya hussam da yaga kayan sai daya fara qorafi.

"Iyyeee......matar d'an lele,anya zamu samu sauran space kuwa nanay?" Murmushi kawai tayi tana girgiza kanta. Ta sani bawai hussam ya fadi bane har zuciyarsa,yana da wasa da barkwanci,amma da gaske haisam daban yake a zuciyarta,dole ko meye yazo daga gareshi ya zama na daban.

"Zamuje ganin d'iyata goben....."

"Banda ni nanay,kinsan halinsa ko,zaice ne zamuje kalle masa mata,daidai sa Aareef Allah yasa ya barshi,idan ta fito zamu hadu a nan,Allah ya dawo daku lafiya,gobenma inajin zanje addis ababa jibi zan dawo" Dariya ya sake bata,yasan halin yayanshi kaf.....amma wani lokaci tsabar wasa da ya yiwa hussam yawa ne yasa basa shiri da haisam din.

Dukkaninsu kowa ya samu guri ya zauna,hakanan duk hadiman dake cikin gidan suka qaraso cikin matuqar ladabi da girmamawar nan da suka saba da ita suka diban gaisuwa.

Cikin mintina qalilan suka cika gabansu da abubuwan ciye ciye,zenabu taja baya kanta a qasa tace.

"Wannan aike ne daga uwargijiya,tana ciki yanzun nan zata fito,tace ayi mata afuwa da rashin kammala shirinta kafin isowarki mama oromo.....yanayin shigar ne yasha banban da tasu" Murmushi nanay tayi,tana sake dafe hannun haisam da har yanzu yake cikin nata,saidai kafin tace komai haisam din ya rigata magana.

"Ki gaya mata zamu shigo ciki nida nanay mu sameta"

"In sha Allah" Zenabu ta furta ta miqe tana shaidawa bara'atu,ta tattaka itama tana komawa ciki.

Tsaye kawai tayi gaban babbab madubin,tana kallon zaman doguwar rigar da aka dinkata daga asalin yadin alharir na asali me tsadar gaske. Ko ba'a gaya mata ba kayan ta sani sun nuna alaman kaya ne masu dadadden tarihi,bawai saboda tsufa ba.....aaha,hasalima kayan kaya ne masu madaukakiyar darajar da idan za'a kaisu kasuwa yanzu tabbas za'a bada kudade masu nauyi sa dimbin yawa a kansu kafin a karbesu. Kawai ta fahimci tsohon yadin alharir ne kasancewarta me mu'amala da yaduka zararruka auduga da dukkan wani yadi me tsada,fara gudanar da kamfaninta na sahel couture ya sanya take iya fahimtar abubuwa da dama dangane da suturu na alfarma masu daraja.

Abu na biyu kayan sai taga suna mata kama da wata sutura,wani tufafi da ta taba ganin kamar cikin kayan da momma ta bata.....a jikin wata kaman ranar aurenta data gaza tuna wacece?. Ta sake kallon sarqar wuyanta dama bracelet din hannunta,duka abu guda yake gwada mata.

"Ga wannan......itace kyautar da zaki miqa mata bayan kun gaisa" Birra ta fada tana miqawa akhnan wani nannadadden abu me qyalli,shiba paper ba shi ba leda ba. Juyashi take kawai cikin hannunta,kafin ta dago tana duban birra.

"Birra.....me yasa duka wannan......me yake faruwa?,zuciyata kamar tana fadamin akwai wani abu" Qasa birra tayi da kanta,tana jin zuciyarta na mata nauyi kadan.

"Babu komai.....babu komai ranki ya dade sai alkhairi" Kafin ta sake cewa komai bara'atu ta shigo,ta kuma isar da saqon haisam.

"Ki shiga dasu duk inda suka zabi shiga" Ta fadi tana sake maida dubanta kan madubi.

Kayan sun mata kyau,shigar ta mata kyau sosai ita kanta ta gani,hakanan kayan cif cif jikinta kamar don ita aka dinkasu. Ta lumshe idanunta sannan ta budesu a hankali,tana jin zuciyarta na wani irin motsawa kamar akwai wani abu daya tabata.

"Mu qarasa ciki nanay.....akwai kyautar da nakeso nayi miki,ina fata kuma ta zama kyauta mafi karbuwa a gurinki da bazaki manta da ita ba" Murmushi tayi a hankali ta soma takawa tare dashi,ta amsa masa a hankali saboda ita kanta tana jin wani yanayi a zuciyarta da gangar jikinta

"Bayan wannan kyautar da kayimin na suruka sukutum da guda?,harda wata kyautar ta daban muhammad?" Kai ya gyada mata a hankali

"Akwai nanay.....akwai saura" Jinjina kai itama tayi.

"To na gode,Allah yayi maka albarka"

"Ameen" Ya amsa yana jin wani sanyi cikin ransa. Addu'arta ta daban ce a gurinsa,ba wani abu a duniya ke masa dadi sama da yadda addu'arta ke masa.

Qawataccen parlor ne wanda yasha banban da sauran falukan gidan,tunda tazo gidanma ba'a taba budeshi ba bare a shiga,iyakaci a gyarashi a tsaftaceshi.

Bismillah nanay tayi ta zauna saman tattausan kujerar data lume a ciki. Dubansa tayi sanda taga yana shirin zama kusa da ita.

"Ya haka?"

"Nanay?" Ya furta a hankali.

"Jeka da kanka ka tahomin da ita,jeka da kanka ka taho da matarka" Murmusawa yayi,sannan ya miqe a hankali yana takawa. Hakan yakeso,zaiso hakan sosai,amma yake alkunyawa nanay.

Zuciyarsa a matse take da wani abu da yafi masa kama da zumudi. Daren jiya da qyar yayi wani wahalallen bacci da bai taba wahala irinsa ba. Ciwon mara sosai yayi shi kadai cikin sassansa. Yasha kanwa yasha lemon tsami har doze din yaso ya wuce,sai gab da asuba ya samu sassauci,don bai farka ba sai bayan an kammala sallar asuba da wasu mintuna,jikinsa sharkaf da gumi da janaba,yayi wanka a daddafe yayi sallar sannan ya koma ya kwanta yana jin marar har yanzu a daure,hakanan ba wani kuzari a jikinsa sam.

Ta bawa qofa baya,tana tsaye har yanzu gaban madubin,wannan ya bashi daman fara arba da wadannan blue eyes din nata da haskensu yake cika masa idanu.

Fes komai ya dawo kanta,abinda ya faru tsakaninsu jiya. Wata irin kunya ta kamata har taji kaman qafafunta sun soma rawa.

"Ya ilaheee......ya rahman" Ya furta can qasan maqoshinsa yana hadiyar wani abu,adam apple dinsa daya fito sosai kaman zaka sanya hannu ka ciroshi ya motsa sama da qasa.

Ta zare nata idanun daga kansa,don bata da juriyar kallonsa tun daga jiya da abinda ya mata ya zarta na wadancan kwanakin,tayi qasa da kanta kawai tana murza bracelet din hannunta tana jinta kamar tana nutsewa a qasa.

Idanunsa ya lumshe sanda ya iso gabanta,numfashinsa yana masa wani irin nauyi,yana jin kamar akwai wani abu dake fusgar zuciyarsa. Saidai duk yadda yakeji bugawar da tata zuciyar takeyi ta danne tashi. Wani irin salon dressing take gani a jikinsa karo ma farko tunda ta fara ganinsa,ya fito sak MATASHIN OROMO da shigar kayansu na al'ada da aka zamanantar dasu.
Chapter 65 · 0% Book details