← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 176

Sashe 45

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kark......" Ragowar kalaman dukka basu gama fita ba tsawa ta biyu ta biyo baya,wadda shi kansa ya jita,bai gama fahimtar komai ba kuma ya jita cikin jikinsa da wata irin kalar runguma me tsaurin gaske.

Kuka yake qasa qasa,kukan da yake iya jin qananun sautikansa a qirjinsa. Bappi take kira,kamar wata qaramar yarinya,yadda kuma take kukan zai fada maka daga can cikin zuciyarta ne.

A gurinta ne sautin yake kuka,amma a gurinsa tamkar sautin gayyata ne take aike masa zuwa wata duniyar ta daban. Yayi duk dabarar da zai qwace amma yadda ta riqeshin ma sake zare masa duk wani karsashi take sakeyi.

Tsaiwa yayi cak yana jin yadda kunnuwansa suke nisa da duniyar da yake ciki.....hankalinsa yake dada nisa dashi.....tunaninsa yake sake dauko masa wani yanayi na musamman........kaman yadda duk wani sake shige masa jiki da takeyi yakejin kamar tana tura masa komai da komai ne wanda direct yake isa ga fatarsa. Wani sabon salon skin to skin yakeji tana masa.....wani yanayi me firgita hankalin me hankali,da jirkita nutsuwar me nutsuwa duk kuwa kalan nutsuwar da yake tutiyar ya mallaka.

Bashi da wani zabi face bin abinda zuciyarsa take ayyana masa,a hankali ya dora hannuwansa guda daya akan bayanta,daya hannun nasa kuma ya riqe bayan kayanta da kyau,hannuwansa suna nutsewa cikin sassalkar sumarta.

Fuskokinsu ya hade guri daya,tsinin hancinsa ya sauka akan nata,sai ya soma gogawa a hankali yana fadin.

"Aakhnaaan" Da wani irin rarraunan sauti daya sanya tsigar jikinta tashi.

"Na'am" Ta amsa tana qoqarin dauko tunaninta ta dawo dashi gabanta. Sake kiranta yayi,ta sake amsawa,a karo na uku kuma daya sake kiran nata sai kiran ya fito a wani irin zafafe,ya hada kuma da saukar hannunsa saman wancan gurin da ta kawo masa da kanta ba tare data sani ba.

A nan duk wani lantarki na jikinta ta tsinke,a nan ne tunaninta da yayi nisa a dazu ya dawo,ya karanta mata cewa suna saman gado daya,bata da riga baida riga.....tunaninta ya sake karanta mata wani irin saqo me wahalar fassara data soma jin yana aike mata,tunaninta ya sake finciko mata saukar hannuwansa a gurare da dama na jikinta,bata kuma sake tuna komai ba sai taji ya game bakunansu guri daya yana aike mata da wani zazzafan kiss kai tsaye baki da baki.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Wani irin nauyi yake sauke mata,nauyin dake nuna mutumin daya dade yana riqe kansa. Wani baqon abune da bata taba jin irinsa ba tunda tazo duniya.....wani irin yanayi da bata taba kawoshi zai faru a kanta ba nan kusa. Ya yaye dukkan wani hijabi dake tsakaninsu,ya kai hannunsa dukkan wani sashe da yake cikin alfarmarta da alfaharinta na diya mace,ya ajiye fuskarsa a duk wani guri da takejin yana da tsananin girma da kima da tsaro a gurinta. Ta tureshin ta kirashi da mabanbantan suna amma bataci nasara ba.....daga qarshe kawai abinda ta yanke.....kiran sunan sultane da dukkan muryarta,wani abu daya sanyashi tsaiwa cak.......jikinsa yayi wani irin laushi,ya zame a hankali yana kwantawa a gefe rub da ciki yana runtse idanunsa da kyau,ya cije labbansa na qasa sosai yana jin wannan yanayin yana ratsashi,yana lalube cikin kwanyarsa yadda zai samu relief.

Dukkan qarfinta ta sanya tana tattaro duvet din duk da girman da yake dashi tana lullube jikinta gami da curewa guri daya. Wani irin tsoro ne yake ratsata,ta tabbatar banda Allah ya mata ludufi zazzabin ya sauka ba abinda zai hana tsoro ya sanya ta shide gaba daya.

Ya damqe bedsheet din sosai cikin hannunsa kaman zai tsagashi,ya sauke wani numfashi a hankali jikinsa yana qarasa saki gaba daya. Sai a sannan sautin kukanta ya soma dawo masa cikin kunne.

"Me nayi mata ma?" Ya tambayi kansa yana tuna a daidai gurin data sanya masa iyaka. A gurin daya tabbatar inda ya isa can din da yanxun wani sunan daban zai amsa haka ita dinma.

A hankali nutsuwarsa ta dawo jikinsa,yana kuma jin sautinta a hankali,saidai haka kawai yakejin baida energy din da zai iya cewa da ita komai.

Ya kusa mintuna talatin sannan ya iya miqewa,har wani jiri yakeji bayan nauyin da jikinsa yayi masa. Ta dauka zai fita ne zuwa dakinsa,amma ga mamakinta sai taga ya wuce zuwa bathroom dinta kai tsaye.

Tana jin saukar ruwa daga bathroom din wanda ya tabbatar mata wanka yake. Jin komai take kamar a mafarki,har yanzu a gigice take jinta,ta kasa gasgata abinda ya faru tsakaninsu koda na minti daya.

"Inda ya samu nasara fa?" Zuciyarta ta jefa mata tambayar data sake sakata fashewa da kuka. Da tuni shikenan,asirinta zai tonu kenan kamar yadda na falaak ya tonu a idanunta? Tun wancan ranar bata sake bari sun hada ido da falaak ba,haushi haushin falaak din takeji,ita kuma kunyar akhnan takeji.

Da sauri ta maida kanta gaba daya ta lullube a duvet din. Haisam ne......daure da towel a qugunsa,yanayin da yayi matuqar gigitata.....yanayin da bata taba zaton zai iya aikatawa ba. Fitowarsa a haka ba riga,duk wani siffar qarfi nashi ya bayyana ta qaramin hasken bedside lamp daya kunna. Wannan lallausar gargasar da takeji kamar tana ajiyar qamshi na musamman......wannan faffadan qirjin,santala santalan hannayensa duka a fili muraran.

"Kina buqatar wanka?....akwai ruwa a bathtub fresh" Ya fada da wani yanayi na kulawa a muryarsa.

Ba shakka inda akwai daman dan adam ya bace ba abinda zai hanata bacewa. Yana mata magana kanshi tsaye,dab da kanta yadda take iya jin damshin jikinsa ta hannunta daya da bata lullube ba. Wato tambayarta yake a fakaice shin takai inda yakai?,koshi kadai ta raka ta dawo?.

Wani kukan kunya ya qwace mata. Ta tabbatar a yanzu jikinta ba inda hannunsa bai kai ba,ba inda hannunsa bai taba ba,shikenan bata da wani sauran martaba da daraja?. Ya akayi ma ta barshi har saman gadonta?,ba'a kansa kadai ba,tasha ganin kallon sha'awa a kanta daga idanun maza masu tarin yawa,wannan dalilin ya sanya ta tsani kallo daga idanun kowanne d'a namiji.

Bata taba ganin ya mata wannan kallon ba,shi yasa ta sakankance,bata taba kuma kawo hakan a ranta game dashi ba,ashe zai bata mamaki.

Mamakin kuwa yaso bata sanda yake bata zabin taje tayi wanka ko ya dauketa da kansa ya kaita. Hakanan ta tattare duvet din tayi toilet dashi,tanata satar kallonsa,saidai shi idanunsa ma baya kanta,yayi tsaye ne a saitin qofar glass dinnan dake nuna masa Haram na madeena kai tsaye.

Sau ba adadi yana lumshe idonsa yana budewa cikin haram din,wata irin tarin nutsuwa yakeji tana saukar masa. Ambaton sunan Allah kawai yake cikin ransa yana motsa labbansa kuma a hankali,yana tsarkake ubangiji,yana sake miqawa Allah godiya.

Duk da bai isa inda ya dace ya isa ba,amma ko a iya nan ya fahimci abinda zai sanya duk namiji ko.macen da suka kuskura suka fara zina a rayuwarsu zai wahala su daina.

(Duk runtsi.....duk runtsi,duk yadda za'a je a dawo ka/ki yiwa kanki katanga da zina,karki kuskura karka kuskura ka yarda ka dandanata,ka jira halal time......in halal way kuma,Allah haula da zuri'armu duka ka nesantamu da ita).

"Alhamdulillah......alhamdulillah" Yake furtawa a hankali. Wani girma da tsoron Allah yana sake ratsa zuciyarsa......imani na gaske da yaqini,irin karamcin Allah daya yiwa bayinsa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 42*

Duk abun daya ne,amma saboda Allah ya karrama dan adam ya sanyashi ya zama ta halastacciyar hanya. Cikin girma mutunci da karamci da amincewar iyaye,bayan ka biya wani abu cikin kalmomin Allah da sunnar manzonsa S A W.

Yana jin sanda ta fito,ta dade tana lallabowa gami da takawa a hankali tanason saka kayanta. Bata lokaci yayi,yayi kaman bayan gurin,bai juyo ba ya barta ta shirya duk da tsorace take,sai daya tabbatar ta hau gadon sannan yabar bakin gurin,ya tako a hankali da wani irin sanyi da nutsuwa yaja duvet din ya lullubeta.

Samun kansa yayi da sunkuyawa daidai goshinta. Lite kiss ya ajiye mata,ya taka da baya da baya a hankali ya kashe duk wutar dakin,sannan ya juya yana barin dakin da wani abu daya soma nauyi da girma a qirjinsa,wani abu da baisan meye shi ba.

Duk da taji fitarsa amma ta kasa motsi tun bayan da kiss dinsa ya zauna mata daram a goshinta. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana tuna komai daki daki. Takai hannunta saman wuyanta... Kunnuwanta,qirjinta,cinyoyinta dama bayanta. Duk inda takai hannun saita tuna da wanne irin yanayi nasa hannun ya sauka a gurin,saita runtse ido sosai tana damqe pillow din da take kai. Sai a yanzun takejin wancan feeling din daya kamata ta jishi a dazu sosai tsoro ya hana.

"Biftuuuuuuu" Taji wani sashe na zuciyarta ya kirata da qarfi,saita cusa kanta cikin pillow tana rasa me zatayi?.

Anya bata fara hauka ba?.....bata fara samun matsalar kwanya ba?. Me yasa komai dake tattare da ita yake sauyawa?,me yasa komai nata yake sauya kanshi?. Ina wannan ra'ayin nata?....ina dukka dokokinta da tsarinta suka tafi? Wannan malaminne fa?,wannan malaminne fa kamar dai sauran malamai data sani.

"Ba kamar sauran malamai ba akhnan.....ba kamar sauran ba" Wani sashe na zuciyarta ya shiga gaya mata a hankali. Batayi saurin qaryatawa ba,samu kanta tayi da sake tariyo komai nasa. Ranar farko data fara ganinsa......yadda izzarsa bata bari a takashi. Yadda bai yarda da wulaqanci qansqanci ko tazarci ba. Girman muqami na mahaifinta da dukka kyanta bai sanya ko sau daya ya shiga sahun mazan dake nacin shiga Rayuwarta ba,sai yanzu.....sai yanzu da igiyar aure ta qullesu guri daya.

Saka dukkan qarfinta tayi tanason wancakali da tunanin ko zata samu bacci,saidai duk inda ta motsa.....duk yadda ta juya ba abinda hancinta yake shaqo mata sai wannan qamshin nasa. Wannna qamshin dai.....qamshin da tasake ji a ranta ko yaya ne zatayi ta mallaki wannan turaren.
Chapter 45 · 0% Book details