← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 176

Sashe 66

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kayan sun bala'in kwanta masa sunyi biyayya tamkar sunsan a jikin wanda suke. Hannunsa ya miqa zai riqe hannuwanta da bracelet din suka zauna mata tamkar dama can mallakinta ne,amma daya tuna nanay nacan zaune tana jiransu sai ya janye hannun nasa da sauri. Ya sani,zai wahala ya tabata ya iya jurewa wani abu bai biyo baya ba,bayason kuma yanayinsa ya sauya kwata kwata,don yasan tsaf nanay zata dago wani abu.

"Barka da warhaka" Ta samu kanta da fadi tana rusunar da kanta da alama ta girmamawa.

Idanu ya zuba mata,karon farko da yaji tayi wani irin burgeshi,yanayin gaisuwar ya mata kyau,cakude da izza da quruciyarta da yake gani muraran tun daga jiya..

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Gaisuwarta tayi,cikin yanayin dake nuna tarbiyyar masarauta da qabilar oromo ta fara shigarta. Saidai shi ko kadan baya ra'ayin irin wannan gaisuwar,ba irinta yakeso ba. Ya jima da tsara rayuwarsa da dukkan macen da Allah ya qaddara zai aura. Koda da gaisuwa yana fadin zata zama ta musamman ne.

"Kinyimin kyau sosai princess of agadez......na jawoki kusa ki kiramin bappi" Ya furta muryarsa a narke yana karya wuyansa idanunsa na narkewa a kanta,kamar ya manta gaban wa yake.

Har cikin b'argonta taji wannan muryar......wannan husky voice din nasa da yayi wani irin laushi da taushi,cikin nutsatsen sautin da kamar zabarsu yayi ya kuma jerasu kafin ya furta mata su.

Shi kansa baisan me yakeji ba....baisan me yake fusgarsa a kanta ba....baiji kuma yanason ya dauke kallonsa daga kanta ba. Wani yanayi ne me cakude da tausayi,tausayin batasan ainihin suturar wadda take sanye da ita ba.....suturar wata sashe na jikinta.....suturar halitta mafi qaunarta a duniya,suturar halitta mafi soyuwa a gareta a duniya.

Qasa ta sakeyi da kanta tana sake murza bracelet din. A hankali idanunta suka sauka kan qafarsa,wannan qafar dake mata wani irin kyau,wannan qafar dake burgeta cikin baqin takalmin daya fito da zara zaran yatsunsa ya kuma haska farar fatar qafar tasa dake kwance lumui kaman batasan wani abu wai qasa ko qura ba.

Batasan me yasa komai ta kalla yake burgeta a tattare dashi ba......batasan me yasa komai nasa yake jan hankalinta ba,komai nasa kaman ya zaba kaman ya tsara,har wani lokaci sai taji zuciyarta tana gaya mata,ya fiki kaza.....ya fiki kaza.

Tafin hannunsa ya sanya qarqashin idanunta yana bude mata su,ta dora idonta a nutse akai. Wani guri da a koyaushe take samun nutsuwa koda a rude take muddin zai cakuda zara zaran yatsun hannunsa da nata. Tana jin wani lokacin idan yayi hakan,kamar wani assurance yake bata na samun nutsuwa.

"Zamu iya tafiya?" Ya fada da French din nan nasa me cike da wani accent da take yawan gwadawa ko zata iya magana dashi.

"Inaso a sanda idanun nanay ke kallonmu......ta kallemu a matsayin cikakkun ma'aurata,wadanda basu da matsalan komai.....ma'auratan da sukayi auren qauna da soyayya......ba wadanda sukayi auren yarjejeniya ba" Yayi maganan ne cike da tarin nutsuwar nan dake masa ado,amma sai kalmarsa ta qarshe ta haifar mata da wani faduwar gaba.

"Auren yarjejeniya.....na manta" Ta fada can qasan ranta. Har yanzu yana riqe kenan da maganganun mammina?,har yanzu kenan yana kan alqawarin mammina?....hakan yana nufin?" Sai zaren tunanin nata ya tsinke tana jin wata fargaba.

"Hakan yana nufin wataran.....komai zai qare?" Tambayar da bata lalubo amsarta ba,ta tsinci wannan lallausan tafin hannun nasa cikin nata.

Wani space ya bata nayin shuru saboda heart rate dinta ya daidaita.

"Kin shirya?" Ya fadi a hankali. Bata ja da nisa ba kawai ta daga masa kai. Batason kowa yaga sun dade a cikin dakin da daga ita saishi ballanta a zargi wani abu,ya jinjina kansa a hankali ya soma takawa tana biye dashi.

Qarar taba qofar ya sanya nanay maido hankalinta ga hanya maimakon TV din daketa aiki ba wanda ke zama ya kalla,wanda suke hasko labaran qasa na yammaci a gidan tv mallakin gwamnatin qasar Ethiopia din.

Da farko haisam ta fara kalla,sannan a hankali ta aje idanunta akan fuskar akhnan.

Wani irin abu me qarfin gaske ne ya fusgeta,wani irin yanayi da yafi kama dana Mitumin da aka tasa a bacci ba tare daya shirya ba.

Idanu sosai ta zubawa akhnan din,wani irin abu take gani yana gilmawa akan fuskar ta,wasu kamanni na sak da sak......kamannin da suke cikin dukkanin baccinta na shekara da shekaru.

Da fari qafafunta da hannayenta ne sukayi wani irin sanyi,don kamannin da take gani yanzu a gabanta ta sani wani abune me wahalar kasancewa. To amma koda ta matso kusa da ita....koda ta zubawa shigarta idanu sai take ganin safeena a gabanta,safeena cikin shigar kayan aurenta Randa za'a kaita gidan ajani......safeena da quruciyarta ta sake dawowa baya kaman wadancan shekarun da suke lokacin 'yammatancinsu.

"Ki nutsu Khadija......wannan din surukarki ce,kada ki koma maganan badini zahiri ne a gabanki" Wannan tunasarwar da zuciyarta tayi mata shine abinda ya sanyata miqewa. Idanunta fes akan Fuskar akhnan data sunkuyar da ita qasa kadan. Wani irin nauyi taji tana ji daga kallon fuskar matar sau daya tak. Wani irin kwarjini taji tayi mata matuqa da gaske,kwarjinin da taji zuciyarta a take tana gaya mata.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 60*

"Ga asalin inda kwarjininsa ya samo asali da alama". Kallo daya tayi mata,amma sai take ganin wani yanayi tattare da matar. Nutsuwa kamala da cikakkiyar haiba,ga wata irin kunya da batasan abinda ya kawota ba,kalan kunya da bata taba jinta dangane da wani dan adam ba.

"Ma sha Allah,tabarakarrahman" Nanay ta gaza jurewa sai data furta. Duk da akwai wasu kamanni saman fuskar akhnan din da take hange yanzu haka......amma hakan bai gaza banbanta wannan kyan da wancan kyan ba,wasu banbance babance da tana sake qarasowa gabanta tana ganinsu.

Hannuwanta dukka biyun ta miqa akhnan din tana dubanta da wani irin tarin qauna da takeji ya saukar mata,qaunar da ta ninka wadda takeji kafin takai ga ganinta.

"Bismillahir rahmanir rahim......ina miki maraba da shigowa cikinmu,ina miki maraba da shigowa masarautar oromo.....ina miki kuma maraba da shigowa ahalin aba jifar" Tayi maganan dukka tana miqawa akhnan hannunta.

Ji tayi ba zata iya ci gaba da tsaiwa a gabanta ba,karon farko data rusunawa wani dan adam akan gwiwoyinta bayan sultane dinta,saita fara sulalewa zatakai qasa,abinda ya dauki hankalin haisam matuqa da gaske d wanin irin yanayi na burgewa da mamaki,saidai amma caraf nanay ta kama hannuwan nata tana fadin.

"A'ah.....ke a gareni diyace,tamkar dai Aanani noorah rumaisa balqees hasnaaa husssss......." Sai maganan Nanay ya datse daga sunayen da take jero mata sakamakon sauka da idanunta sukayi akan abun hannun akhnan din.

Cak komai ya tsaya mata.....kwanyarta ta kwasheta da wani irin gudu tana maidata shekarun baya. Shekarun da safeena ta kawo mata ajiyar wannan abun hannun.

"Ki ajiyemin,kinfi safiyya iya adani,Ahmad ne ya bani,haka kawai nakw tsoron ajiyarsa cikin gidan" Ta ajiyeshi da matuqar muhimmanci,saidai safeena ta karba daga baya tana shaida mata yanzun ta samu tabbacin zata iya ajiyarshi.

"A......a ina kika samoshi?" Ta furta idanunta a waje tana dan girgiza hannun akhnan da sauri.

Da hanzari akhnan ta daga kai gabanta yana faduwa,tanaso ta gane akan me dattijuwar ke magana,saita fuskanci idanunta da hankalinta suna kan abun hannun ta.

Da sauri ta daga kai tana kallon haisam,gabanta yana tsananta faduwa,tunani kala kala yana sarqa kanshi da kanshi a zuciyarta,ina ya samo ya bata?.

"Nine na bata" Ya fada calmly bayan ya zare idanunsa daga kan akhnan dake masa kallon da ya gama fassarashi,ya kuma tafi kai tsaye zuwa ga ma'anar kallon dake cikin zuciyarta.

Still nanay bata saki hannun akhnan ba,ta maida dubanata ga haisam a rikice.

"Nine na bata nanay,nace ta saka don ki sake gamsuwa da gaske ita din jinin SAFEENA ce". Maganan ya saukowa nanay da wani mugun nauyi,har sai da tayi taga taga kaman zata fadi,saidai kafin yakai ga qarasowa gurin tuni akhnan ta sanya siraran yatsunta ta taro bayanta sosai,yana qarasowa sai ya tallafeta ta hanyar tsaiwa ta bayan nata.

"Baka tabamin irin wannan wasan ba" Ta fada tana maida Fuskarta da dukka idanunta akan abun hannun akhnan.

"Baka qarya muhammad,baka tabamin qarya ba....kuma a yanzun ma nasan ba zaka fara ba,ba halinka bace" Ta qara fadi tana sakin hannayen akhnan.

Tafukan hannayenta dukka biyun ta sanya tsakanin gefe da gefe na fuskar akhnan,ta juya fuskar tata daga hagu zuwa dama,ta saketa,ta kama gefan mayafin dake lullube a kanta ta murza,sai ta sake saki tana sake kamo hannuwan akhnan din.

Yatsunta ta kalla dogaye wadanda har yanzu da sauran jan lallen da yayi dishi dishi,sai ta juya tafin hannunta tana qare musu kallo da kyau.

Ba wanda ya zata a cikin su shi da ita,sai wata wawar runguma kawai da sukaga ta kaiwa akhnan din tana fashewa da kuka mara sauti,saidai muryarta ta nuna kukan takeyi

"Allahu akhbar......Allah akhbar,Allahumma lakal hamdu kulluh,wa lakashshukr kulluh.... Lallai ba shakka ke din jinin SAFEENA ce,tsatson safeena ce ke" Ta qarasa fada dukka jikinta yana girgiza da alamar abune me zurfi da taba rai.

Bata gane komai ba har sanda haisam ya kama nanay ta tayashi suka zauna. Banda sunan safeena data fahimta a dukka maganganunta,safeena mahaifiyarta bata gane komai ba,ta zuba ma nanay dake riqe da hannunta har yanzu idanu,sannan ta maida idanun nata ga haisam dake matsa hannun nanay din a hankali cikin wani yanayi na tausar zuciya,hannunsa saman kafadar nanay din yana shafawa a hankali kamar me lallashin yaron goye dake rigima.

*_BAYAN MINTI TALATIN_*
Chapter 66 · 0% Book details