← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 176

Sashe 157

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka shigo muhammad" Ta furta,sai ya tsugunna ya zame takalman qafafuwansa sannan ya sanyo qafar tasa a hankali yana shigowa.

"Shikenan......tawa ta qare,Allah sarki ni" Ya fada da muryar tausayi wadda dukkansu sai data saka suka kusa fashewa da dariya,harsa akhnan da kadan kadan takejin yaren oromo,amma zamanta dashi tana fahimtar abubuwa sosai,maidawa ce saidai da qananun jimloli kuma.

Ga mamakinta kanshi tsaye ya wuce saman abun sallar nanay din,ya qarasa zuwa gabanta ya zauna sosai yana tanqwashe qafafu.

Hannunta ya kama cikin nasa,yana duban idanunta cikin kulawa da qauna ya fara gaidata.

"Fatan kun dawo lafiya....."

"Alhamdulillah nanay,ina fatan na same ki lafiya"

"Lafiya qalau muhammad...." Ta fadi daidai sanda ya riqe hannunta yayi kissing bayan hannun nata.

"Ma sha Allah" Ta fada itama tana dora hannunta saman nasa.

Satar kallonsa akhnan keyi,mamakinsa yana saukar mata. Mutumin da kullum yake tafiya da cikakken iko da nutsuwa... wanda ko manyan mutane ke gyara zamansu idan ya shigo waje...
yanzu yana zaune a gaban Nanay kamar qaramin yaro.

"Amma muhammad me yasa baku zauna ta huta ba?.....nace da kaina zan shigo ko?,dazun muka gama magana da motii" Nanay ta tambayeshi tana kallonsa cikin zallar kulawa.

Tunanin akhnan ya yanke sanda ya zame ya kwanta,yana dora kansa saman cinyar nanay din,ya gyara kwanciyarsa sosai fuskarsa tana nuna kalar nutsuwar daya samu.

"Gata nan nanay....ita ta takura lallai sai tazo ta ganki" Ya qarasa maganan yana sanya idanunsa cikin na akhnan wadda mamaki ya sanyata daskarewa a gurin.

Hannu nanay ta dora saman lallausan gashinsa

"Laifinka ne......me zaisa ka bari tayi wahala.....halanma kaine ka matsa sai kun fito" Ta fada tana duban akhnan.

"Wayyo ni" Ya fada a tausashe.

"Nanay.....giiftii ta fara shiga tsakanin mu" Ya fada a narke yana maida idanunsa ga akhnan,akhnan din data narke a gurin tana kallonsa.

Wannan ne haisam?. Wannan ne mutumin da idan ya shiga daki mutane ke gyara zamansu. Wannan ne mutumin da ko murmushi yake yi sai ya zama kamar ni'ima ga wasu. Amma yanzu...yana kwance kan cinyar Nanay kamar qaramin yaro da ya dawo gida bayan doguwar tafiya.

Ido daya ya kashe mata,saita janye idanunta a hankali tana kallon qasa.

A gurinta kawai da gurin nanay take iya ganin wannan siffar.....wannan kamannin.....da wannan haisam din. Mutum biyu ne kawai DUNIYARSA a rayuwa.....mutum biyu kawai ke iya ganin wannan side din nasa.....mutum biyu kadai,ita da nanay.

"Zo nan kinji" Nanay ta fada tana miqawa akhnan hannu.

A kunyace ta miqe tana matsowa gaban nanay din,wannan ya sake bata daman sake qarewa akhnan kallo sosai. Ta sauya....komai nata ya sauya,komai nata kuma yana bada wata alama ta daban. Amma ba wanda yace mata komai a cikinsu,wataqila kunya sukeji.....wataqila akwai sanda suka ajiye don sanar mata. Zata jira wannan lokacin,duk da bata da cikakken tabbaci.

Cikin jikin ta zaunar da akhnan din,sai ya daga kansa a hankali yana dubansu,a badini zuciyarsa na masa wani fari da haske,yana kallon duniyoyinsa guda buyu,yana kallon farincikinsa.....aljannarsa da kuma rayuwarsa a fuskokinsu.

Amma kuma a zahiri sai ya hade rai kadan.

"Nanay....."

"Haisam" Ta fada tana tsaidashi. Bayason kowa a gurin idan suna tare,ta sani,amma yanzun tana jin akhnan ta riga ta shiga wani bangare na rayuwarsu dukkaninsu.

Kafin tace komai rumaisa data fice ta basu guri ta turo qofar.

"Nanay.....an shirya table din"

"Gani nan" Ta amsa mata,sai rumaisa ta juya ta koma,don sun saba kebewar Captain din nasu da nanay dinsa ba wanda ya isa ya shiga,sai yanzu da akhnan ta zama ta ukunsu.

Tana riqe da hannunsu suka isa dining din. Katafaren dining din da aka shiryawa kalolin abinci,ba masu yawa sosai ba,daidai yadda zai nuna alfarmar wanda zai zauna cin abincin.

Yana shirin jawa nanay kujera don ta zauna akhnan ta rigashi. Yadan fiddo idanu cikin subutar baki ya furta.

"Easy mana....karki qara" Zuciyarsa nadan bugawa kadan. Gani yake kaman mistake qarami zai iya taba abinda akhnan din ke dauke dashi,abinda har yanzu akhnan din bata amince akwaishi ba.

Dukkaninsu ita da nanay din suka kalleshi,idanun akhnan fal da tambaya,yayin da nanay kuma abun ya sake sa mata gamsuwa da zarginta,amma saita dauke kai kaman bata fahimci komai ba. Shima basarwa yayi yana shafa sumar kansa,ya matsa a hankali ya jawa akhnan tata kujerar,ta zauna,sannan yaja tasa opposite tasu shima ya zauna.

Biyu daga cikin bayinta ne suka matso suka fara serving nasu,akhnan tana jin hirarsa da nanay din kadan kadan. Bata saka musu baki ba,duk da yadda nanay ke sakata a hirar. Yanayin mu'amalarsa da nanay na burgeta,har wani lokaci takan rasa tantancewa dawa yafi shaquwa?. Nanay din ko motii. Abu daya ta barwa ranta,shaquwa ce sosai tsakaninsa da nanay,da motii kuma wasu sirrikane yakeyi dashi wanda qirji da zuciyar uwa ba zasu iya dauka ba,dole lallai sai uban.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Fitowar noorah da Aareef ya sake sanyawa ta kuma jin dadin zaman. Tanason yarinyar sosai,tana da wani irin hankali me ban mamaki. Ta yarda ba banza ba haisam ke sonta shima. Tana murmushi take tsokanarta bayan ta gaidata.

"Hoton me dame aka dauko mana a wannan satin?" Murmushi ta saki tana ciro camera dinta da bata rabo da ita.

"Na sake siyan wasu sabbin tsuntsayen wajen halyjesheru ventures giiftii 704 666 5338....har da dawisu guda hudu.....kin gani" Ta fada tana miqa mata camera din. Daidai nan rumaisa da Aanani suka shigo,suka samu guri suka zauna suna jan plate suma,tana jin nanay tana mitar sai suqi cin abinci sai taxo cin nata,ta saki murmushi family din na sake burgeta.

Tana murmushi tana duba hotunan,sai ta sake girmama lamarin ubangiji. Wasu irin kyawawan tattabaru da kaji,ga wasu irin dawisu harda parrot ma,ita sun mata kyau sosai,ta daga ido tana duban haisam. Girarsa ya dage mata,sai itama ta dage masa tata girar,ya juya ga noorah a nutse.

"Auta,a saka mana order.....a zaba mata masu kyau" Murmushi noorah ta saki,wannan murmushin dake qarawa yarinyar kyau.

"Amma obbo.....zan dora ribata fa" Murmushi ya saki

"Riba halal ce auta,ki qara ko nawa kikeso" Suka saki dariya gaba daya.

Duk cikinsu bayan shi itace ta biyu dake da neman na kanta sosai,shi yasa yake qara qarfafa mata gwiwa,yanayin abubuwanta zaka dauka ba daga gidan sarauta me girma irin wannan ta fito ba. Ga qananun shekaru amma haka take koyon kasuwancin dabbobin.

Dauke da babban tray ta shigo gurin,ko sau daya akhnan bata yarda ta kalleta ba. Haka kawai batason koda ganin fuskar yarinyar. Ta qaraso tana tafiya a hankali zuciyarta tana wani irin matsewa a qirjinta.

Tsakiyarsu ta ajiye tray din coffee din,saidai,ta ware cup biyu kadai. Nanay ta zubawa ta ajiye a gabanta,sannan ta sake zubawa a dayan.

Sai data saci kallon akhnan din,sannan ta sanya qaramin tray a qasan mug din. Ta matsa daura dashi tana lanqwashe murya.

"Gashi obbo" Ta qarasa fada tana ajiye masa a gabanshi.

Hannu yasa ya janyeshi gefe idanunsa na sauka kan fuskar akhnan.

"Daukeshi daga kusa da nan.....na nanay is okay" Ya fadiwa saamee ba tare daya kalli fuskarta ba.

Ta lumshe idanunta a hankali tana budesu saboda tuni qamshin ya buwayi hancinta da wani irin yanayi me daga hankali. Kaf qamshin nan da yakeyi wani abu na daban yake zame mata yana sake hautsina mata ciki.

"Are you okay?" Ya fada muryarsa can qasa da wani irin kulawa. Kai ta daga masa a hankali tana qoqarin qaqaro murmushi,sai ya dora hannunsa a hankali saman bayan hannunta idanunsa cikin nata.

Gabanta yayi wani mummunan faduwa. Wani abu ya sauka a hankali yana mamayar zuciyarta. Kulawarsa.....kulawar da yake bata ta tsaye mata a rai da wani irin matsanancin kishi.

"Me yasa batason qamshin coffee.....me yasa?" Ta tambayi kanta. Tantancewa takeso tayi,tana son sanin dalili,sai ta dauki wani mug din ta cikashi taf ta tura gabanta.

"Ga naki" Ta furta idanunta akan akhnan.

Iskar data shaqa ta shiga sosai cikin cikinta,ta soma hautsina mata duk wata nutsuwarta da walwalarta,take ta tattara wani irin amai cikin qasa da second biyar ta soma yunqurin turo mata shi waje.

Yunqurin aman da sautinsa ya daga haisam daga mazauninsa cikin qiftawar idanun da baisan zai iya hakan ba sai yanzu. Sai akan akhnan din.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 144*

"Me ya faru?....giiftii....I'm sorry.....sorry please" Shine kalman da yaketa maimaitawa kawai da wani irin rudadden yanayi.

Kaman aman na jiransa ne ya isa gabanta,gaba daya ya soma fitowa ba tare da wani jiran komai ba. Kai tsaye ta soma wankeshi tana wanke kyakkyawan jubah din jikinsa. Dukkaninsu hankulansu yayo kanta,nanay ta tashi itama daga mazauninta ta iso gaban akhnan din tana qoqarin riqeta,saidai kuma me abun ya rigata,tuni haisam ya sanyata a jikinsa yana jin yadda jikinta dukka ke girgiza saboda qarfin aman.

Damuwarta na yadda zata kauce masa ne kada ta batashi. Tanata qoqarin kauce masa amma sake sakata yakeyi a jikinsa yana tare aman.

"Sannu.....I'm sorry" Shine kawai abinda yake fadi. Ya rikice gaba daya saboda ganin yadda farar fuskarta ta soma zama jajaja saboda azabar yunqurin.

Matsanancin bugawar da zuciyarta keyi,da tashin da hankalinta yayi na fahimtar abinda akhnan ke dauke dashi yafi komai daga mata hankali sama da irin hukuncin da zata fuskanta daga gareshi. Ta tattara dukkan wadannan yanayin,tashin hankali da bala'e'en kishin da takeji ta cinyesu gaba daya da wani irin yanayi me rad'adi tana takowa zuwa gefansu,tana kuma amfani da dukka wani sign na tashin hankali da takeji tana juyeshi akam dukka damuwa da yanayin akhnan ne.

Aareef noorah rumaisa da Aanani dukkaninsu sunyi carko carko daga gefanta. Har zuwa sanda ta kammala aman.
Chapter 157 · 0% Book details