← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 176

Sashe 174

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya miƙe tsaye gaba daya.

"Na ce ya isa!" Numfashinsa ya dan yi nauyi, idanunsa a kanta,har tsakiyar zuciyarsa yana jin quncin yadda ta tilastashi yayi abinda bai taba tunanin zaiyi ba.

"Kin tambaya, na amsa. Amma ba zan zauna kina jujjuya maganata yadda kika ga dama ba......ba tsoronki nake ba....ko kadan,idan inason ganinta....ko inason gayyatarta kai tsaye....kai tsayen zan aikata hakan" Ji tayi kamar jiri zai kayar da ita,hawaye take suka cika mata idanu.

Ita haisam yake gayawa haka?. Kansa tsaye?,yana kallon cikin idanunta?. Kawai saita sauke masa wayar ta doshi qofa da sassarfa tana ficewa.

Komawa yayi ya zauna,yana jin wani abu mara dadi yana mamayarsa. Karon farko....karon farko kenan da wani abu mara dadi ya taba shiga tsakanin su.

"Me yasa baka jure ba....me yasa baka sake kai zuciyarka nesa ba?" Zuciyarsa da ta kasa ganin laifin Akhnan ke tuhumarsa. Tunda ya kwanta bacci ya kasa zuwar masa. Fuskarta kawai yake gani cikin idanunsa da suka cika da qwalla. Amma me yasa?,me yasa zata tursasashi yayi abinda baiyu niyya ba?,abinda ba halinsa ba?.

Da qyar ya taushi zuciyarsa.....ya hana kansa binta. Yanaso ta gane tayi kuskure.....yanaso ta fahimci duk girman son da yake mata idan tayi kuskure dole zai gyara mata.

Da asuba yabi duka yaran mazan ya hada kansu suka wuce sallar asuba,saidai kafin su wuce din ya biya dakinta,yana kulle bata bude ba,ta cire kuma security check na qofan bare ta bude masa automatically,amma still ya mata knocking ya kuma kira sunanta. Ya tabbatar taji,don ko bacci take muddin ya kirata da sunan nan nata zata farka ta kuma amsa.

Da gaske ta jishi.....don bayan ta dawo dakin tayi kuka sosai,zuciyarsa tayi sanyi sai ta soma hasaso abinda ta aikata. Itama batasan dalili ba....batasan meye yahau kanta ba.....saidai tana danganka hakan da zallar sonshi daya mata yawa....da kuma sauyin da takeji a jikinta da yake sake gaya mata anya ba ciki bane?. Kusan shigen yanayin irin na cikinsu ashraf ne,ta kasa gwadawa koda da pt stripes ne.

Wani kunyarsa data rugo ta lullubeta ita ta hanata amsa masa. Kuma ko yanzu bayan ta idar da sallar asuba,a gurguje ta fita ta bada umarnin duka abinda zaayi sannan tace musu kada subar yaro ko daya ya tasheta har su wuce gurin hawan,idan ta gama abinda takeyi zata fito da kanta.

Saqon da haisam yaji suna gayawa su ashraf kena da suka nufi dakin da zummar shida gaidata. Ba dashi suke ba....amma sai shima yayi amfani da wannan ya qyaleta bai sake komawa ba.

Shi ya kula da komai,da taimakawar hadiman.

Gidan ya cika da annuri. Tana daga daki amma tana jin hayaniyarsu. Ranta ya sake baci ganin haisam bai biyota ba,kamar ma ta manta ita ta buqaci kada wanda ya dameta.

Dole ta tashi tayi wanka,ta shirya cikin wasu kaya daban ba wanda sukayi zata saka ba. Don gaba daya abun ya fice mata a rai,jin laifi da haushi kawai takeyi tattare da ita.

Jin hayaniyarsu kamar kusa da dakinta yasa ta gaza ci gaba da jurewa. Da alama sun gama shiryawa. Shirin data ciwa buri,shirin data tsara ita zata shirya mijinta da kanta,sai kawai ta karya billenta,ta bude security na qofar ta fito.

Sai ta tsaya cak.
A falon...sanda ta qarasa fitowa.

A parlour din nata.....haisam da yaransa takwas ne tsaye. Bayan yaran nasa da sauran yaran 'yan uwansa da nata 'yan uwan.

Dukkansu cikin fararen shaddoji sukayi,saidai nasa da na garansa yasha banban dana sauran.

Babbar riga iri daya,fara qal sai maiqo take da wani qwataccen qamshi. Dinkin anko da mahaifinsu.
Kamar an zare su daga juna,kamar daga jikinsa aka dinga tsagosu,don hatta da takalmi da agogon hannunsu iri daya ne.

Ashraf......asif......afeef.....ahlam.....ahsan....da ajmal. sauran 'yan matan kuma su biyu wata farar Royal abaya ce a jikinsu da yasa aka saqa musu qwaya biyu kacal saboda wannan ranar.

Dukkansu suna kama da Haisam ta wata fuska. Duk da wani lokaci su yumna da ita ake cewa suna kama sak da sak.

Haisam yana tsaye a tsakiyarsu,yana gyara hular Ashraf,yaron dake da wani irin tsaho kamar yanason taddo mahaifinsa ne.

A jkinsa yaji fitowaeta,sai ya dago kai,idanunsu suka hadu,wani irin chemistry ya ratsa tsakaninsu me qarfin gaske. Shiru na wasu dakikoki,karon farko da suka kwana gida daya amma a mabanbantan dakuna. Ciwo ko lalura lafiya ko rashinta bata taba rabasu haka ba.

"Ammeee" Yumna ta fada,t ruga gurinta da gudu,abinda ya jawo hankalin sauran suka biyo baya.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Nan take yaran suka kewaye ta,wani ya rungume qafarta.
Wani yana gyara mayafinta. Wani yana gaya mata ya fi kowa kyau yau,duk sai taji kewarsu ta cikata.

Haisam kuwa yana kallonta ne kawai.
Da wannan murmushin nasa. Yana jin wani tausayinta yana ratsashi. A jiyan baiyi baccin kirki ba. Ya kwana ne kawai yana tuhumar kansa,inda daga qarshe ya kwana yana sallah kawai. Sanda ya tuna wani zargi daya darsu a ransa tun rannan,sai yaji kaman ya tashi cikin daren ya bita,amma bayason tayar da ita.

"Anya ba ciki bane?" Tambayar data sanyashi yayita nanatata daga qarshe ya aminta da hakan. Saboda ya sani....wannan akhnan din wata akhnan ce daban,ba a banza tayi masa haka ba,yayi imani da wannan ya sani sosai. Shine na farko da zai shaidi matarsa. Bashi kawai ba....koda takalminsa da yake sanyawa girmamashi take ballantana shi.

Ruqayya ce ta shigo ta tattara kansu suka fice,a mota zasu isa jimma palace kafin a nadawa kowa rawaninsa,a bashi dokinsa,dawakan sa already suna dasu kusan uku uku kowa ke dashi.

Bayan yara sun fita zuwa motocinsu...sai ya rage su biyu. Tare suka miqe zuwa ga juna,amma sai ya tsaya ganin ta nufoshi.

A hankali Haisam ya soma takowa shima,yayi saurin kamota sanda ta zame zata zube gwiwarta a qasa. Dagata yayi zuwa jikinsa yana qoqarin lalubo qwayar idanunta amma kunyarsa tasa ta kasa bashi dama. So take ya qyaleya ta tsugunna gabansa ta bashi haquri.

"Har yanzu kina fushi?" Akhnan ta gyara mayafinta a kunyace.

"Ban ce haka ba." Ta fada a shagwabe tana cikin jikinsa,wannan lallausan qamshin nasa yana shige mata hanci.

"Akhnan." Ta qi kallonsa. Sai ya dan sunkuyo kadan yana murmushi me sauti.

"Habibti."Har yanzu ta qi kallonsa. Kunya takeji......amma da alama baima gane ba.

Sai ya yi dariya qasa-qasa.

"She called."Shiru.

"I didn't."Har yanzu babu amsa.

Sai ya matso da ita yana manneta da jikinsa,qamshin shaddarsa.....da qamshin turarensa suna bada wani kalar qamshi me taushi.

"After all these years..."Muryarsa ta yi qasa.

"...you still don't know who owns my heart?" A wannan karon ta kasa hana kanta kallonsa,ta ware blue eyes dinta sosai a kansa.

Sai ya nuna yaran da suka riga suka fita.

"Eight children."
Sannan ya nuna kanta.

"And still jealous." Murmushi ya subuce mata duk da qoqarinta na hana kanta tayi murmushin.

Nan take ya gane ya yi nasara,tasa hannu ta daki qirjinsa a tausashe.

"Kayi haquri please" Bakinta ya toshe da nasa kadan,yadan tsotsi lips dinta sannan ya janye.

"Karki wani nema afuwa.....menelik ce.....tun daren jiya na miki maganinta." Idanu ta waro waje.

"Yes.....ya zan zauna ta jawomin jagwal. Ashe ba haisam dinki tazo turawa ba.....itama ta samu nata haisam din. Tayi saving same name ni dashi,zai kuma zo Durban din,ta ban haquri,tace zata hadamu don na tabbatar,ta kumayi deleting number mijinki,shikenan?" Ya fada yana jan hancinta kadan.

Sosai ta sakejin kunya,tayi qasa da kanta tana boyewa,ya saki murmushi me laushi

"......the game is over.....chapter closed..... Khadeeja ta mallake Muhammad haisam....."

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 161*
_________________________
https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa ameen*
__________________________

".....abbee"

"Don't.....karki musa" Ya fada yana daga hannuwansa sama duka biyun.

"....coz ni na yarda....saboda...." Sai yadan tsaya.

"......dama a mallake nazo wallahi" Dariya suka saki shi da ita,sai ya jata jikinsa a karo na biyu yana manna mata tattausan kiss.

"Khadeeja zaki haifo in sha Allah....da alama kuma rigimarki zatayi,so stay at home,banaso kiyi stressing kanki,zan saka a saka miki device,zakiga komai kamar kina gurin....after an gama,zan tattaro duk wanda kikeson gani na kawo miki shi nan......ko waye....." Kai kawai take girgizawa. Yana fasa mata kai da yawa. Tana jin kamar gatan ya mata yawa.

"Abbee" Ta kirashi sanda yakai bakin qofa tana qare masa kallo. Ya waiwayo yana dubanta da manyan fararen idanunsa.

"Kayi kyau......" Murmushi ya subuce masa.

"Kuma haka zasu gani su haqura su barwa khadeeja ni ba" Dariya sosai ya sanyata harda hawaye.

"Ka yafemin" Ta sake fada.

"Don Allah....bazan sake ba" Juyowa yayi gaba daya yana dubanta.
Chapter 174 · 0% Book details