← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 176

Sashe 154

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"wanne gida......banga nanay ba.....haisam mana" ta furta a shagwabe tana kyabe fuska. Murmushi ya kuma saki,yana lumshe idanunsa gami da budesu duka lokaci guda. Har jijiyoyinsa yake jinta idan ta kirayi sunanshin nan. Baisan sai yaushe ba,bausan sai yushe zai daina jin dadin sunanshi idan ta kira ba.... Ba lokaci,baya jin akwai zuwan wannan lokacin.

Sai ya gyada kai kawai yace.

“Mhm.”

“The one I built for you....Ba wani guda bayanshi akhnan" Ya fada yana lumshe idanunsa Akan fuskarta. Zuciyarta ta motsa a hankali. Yau itama zata shiga gidanta kenan Kamar kowacce cikakkiyar mace?.

Idanunta ta maida a hankali kan hanya sanda motocinsu suka fara hawa wani private mountain road. Fog mai laushi na zagaye da bishiyoyin gurin.

Tun daga tsarin hanyar da titin tasan cewa wata unguwa ce...... Wani guri ne na musamman da yasha banban da kowacce hanya.... Kowanne titi da kowacce unguwa. Tsarinsa na dabanne kuma na musamman. Tun daga nutsuwa da shirun titunan. Kwaltar da aka malale titin dashi,dama fitilun dake jere tare da shukokin da suka yiwa titin rumfa.

A hankali suka fada wani street daban na cikin unguwa, Wanda duka duka tafiyarsu bata haura mintuna goma ba zuwa sha biyar suka soma qoqarin tsaiwa gaban wata villa.

Idanunta ta daga a hankali,kyawawan idanunta nan da suka qara girma da haske tana saukesu saman Villa din da yake a gaban ta din,daidai sanda motocinsu suka fara motsawa a hankali suna shigewa ciki bayan tafkeken gate din gidan ya bude Kansa da kansa automatically ba tare da kowa ya isa gabanshi ko ya tabashi ba.

Ba kawai gida bane. Masterpiece ne.
Modern royal architecture. Huge glass walls. Dark stone exterior. Soft warm lights.
Gidan ya zauna cikin mountains kamar wata boyayyar masarauta da aka killaceta daga ganin idanuwa.

Water features na gudu softly a gefe. Dogayen bishiyoyi sun kewaye compound din. Everything private. Everything expensive.

Wani irin laushi jikinta yayi,taji wani irin nauyi yana ratsata. Wanna irin gida ne wannan kenan?. Wacce irin ginanniyar masarauta ce?. Me yasa komai nata yakan sanyashi ya zama na daban?,me yasa ko yaushe yake zabar mata surprise akan komai?.

Da wannan halin nasa na basarwa.... Yayi abinda ya kamata ya kalleka..... Yayi abinda ya dace ya tsaya ya tayaka dauka girman mamakin abun,Amma sai yayi burus Kamar baisan komai akai ba.

Tafin hannunsa ya bata sanda kowanne guard da security na gidan suka janye suka kuma juya baya don bawa matar oga daman fitowa. Idanunshi ta sake kalla,har yanzu bai yarda ya kalleta ba, Amma tana iya ganin kyakkyawan murmushi can qasa boye qasan idanunsa. Ta janye nata idanun tana dora masa nata hannun kawai saman nasa ba tare da tace komai ba.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 141*
___________________________
*_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________

Cikin girmamawa ma'aikata da hadimai na gidan ke miqa musu gaisuwa,cikin girmamawa da sunkuyar da Kai. Wani irin ban girma da har yanzu yake saukar da mamaki a zuciyar akhnan. Da kulawa Kamar ba wannan hamshaqin yariman billionaire din ba yake amsawa. Yana riqe da hannunsa cikin nata Kamar wanda za'a qwacewa ita Idan baiyi hakan ba.

Tare suka ratsa cikin gidan,har suka kai deluxe entrance na gidan. Wata irin qofa da akhnan ta kasa gane kanta kwata kwata,sai idanu da take binta dashi. Yadan sunkuyo kadan zuwa fuskarta.

"Kiyi addu'a" Ya fada a nutse,ta lumshe idonta tana sauke ajiyar zuciya. Komai matsayinka a rayuwa akwai na gaba dakai. Da gaske ne baba ma da babansa, tabbas rayuwa ta gaji irin wannan abubuwan.

A nutse yake Karan to mata addu'o'in tana maimaitawa, ya sake riqe hannunta cikin nasa suka sanya qafafuwansu bakunansu dauke da bismillah.

A cikin jikinsa ya sanyata, suka fara zagaya gidan ita dashi yana mata bayanin kowanne sashe dalla dalla.

Ta kasa magana,sai bin ko Ina kawai da takeyi da kallo. Duka yadda taga ginin daga waje, ta ciki ya zarta hakan. Wata aljanna ce kawai ya Samar da ita tun daga nan gidan duniya.

“Haisam…” ta kirashi tana dubansa bayan daya Kira sunanta tana tsaye cikin dakin Yara. Wani irin daki da aka masa wani tsari na musamman, tsari me daukan hankalin da duk uwa zataso ace mallakin abinda zata Haifa ne. Komai an saka a dakin, ba wani abu da za'a buqata sai sanda za'a haifi abinda aka tanadi gurin saboda shi.

“You like it?” ya tambayeta, yana tsaye da wannan tsaiwar tasa irin ta giant din maza. Hannunsa zube cikin aljihun wandonsa ya rusunar da narkakkun idanuwa nan nasa a kanta.

Ta kasa magana ma kwata kwata, Idan ta bude baki zatayi magana sai taji muryarta tana rawa. A hankali ta fusgo kalmar

“You built this?”Sai ya gyada kai.

“For year” Ta kasa magana kawai tana lissafa kwanakin zuwansa agadez. Shekara ta farko daya fara saninta. Shekarar daya fara hada idanu da ita. Shekarar daya fara jin cewa yana sonta a rayuwarsa.

"A wannan shekarar kenan ya fara gina gidan saboda ita? " Ta yiwa kanta tambayar tana daga idanunta tana zubesu a kansa.

Yanzu take sake realizing.....tun kafin abubuwa su kai yadda zasu fara magana da juna.....tun kafin ta fahimci yadda yake sonta.....already yana gina mata future cikin wannan shirun daya zama tambarinsa.

"Amma wannan dakin...... Bani da ciki haisam" Tayi maganan tana narke murya. Murmushi ya saki,wani qaramin murmushi me dauke da tarin ma'anoni. Baisan ya mata suke idan suka samu ciki ba, Amma shikam lamarin akhnan dariya yake bashi. Har yau har gobe taqi believing abinda takeji,bayan ita kanta shaida ce da yadda abubuwanta keta canzawa. Ita kanta shaida ce Akan yadda komai nata yake tafiya ba'a daidai ba, ba'a kuma yadda ta sanshi ba.

"I know" Kawai yace mata, yana qoqarin adana dariyarsa.

Taku biyu ya iso gabanta,ya sake sanya hannunsa yana lalubo hannunta cikin nasa, ya hade tafin hannunsa da nata, sannan ya fara takawa da ita a hankali suna fita a dakin.

Juyawa take tana kallon komai cikin disbelief.

Ta tsaya tsakiyar living area din da suka sake bullowa. akwai elegant staircase,saidi amma ba sama yake hawa ba. Qasa yake sauka,underground. Ta sake maida idanunta kansa da mamaki.

“What’s down there?” ta zabi ta bayyana qauyancinta kawai akan tayi shurun.

Haisam ya zuba mata ido,siririn murmushi yana subucewa daga labbansa. Tana burgeshi, bata da girma kan nuna batasan abu ko bata ganeshi ba. Zata tambaya ne Kai tsaye kawai, ya danganta da yadda ka dauki abun.

“Come see.” ya kamo hannunta gently.

Sauka suka fara yi tare,step by step.

Wasu irin soft hidden lights na cikin stairs din na haska ko Ina, har saman qafafunsu da suke takawa da wata irin cikakkiyar nutsuwa.

Akhnan na jin zuciyarta na bugawa saboda gidan already ya wuce imagination dinta.

"To me zai sake boyewa a qasa?" Ta tambayi kanta da kanta can qasan zuciyarta.

Ko ba'a fada mata ba stair case din ta musamman ce. Kana takawa kana jin wani sanyi da taushi qasan tafin qafarka. Suna sauka suna nutsawa zuwa qasan wani yanayi me dadi yana lullube gangar jikinka. Wani haske.... Wani tattausan oud scent me dadin shaqa.

Da suka isa qarshe sai ta tsaya cak.

Gaba daya underground level din kamar secret luxury world ne.

Private indoor lounge,glass ceiling sections,soft waterfall wall,library,cinema room ga kuma hidden relaxation spaces haka suka dinga zagayawa daki daki.

Kamar wajen da mutum zai boye daga duniya ya samu sukuni ya manta da komai. Sai a sannan ta sake gasgatawa,ta sake yadda dashi. Da gaske bayason hayaniya. Da gaske shi din mutum ne da baison dogon zance ko kuma hayaniya ko kadan. Tasha jin su rumaisa suna gulmarsa,amma yau ta samu tabbaci da kalan ginin gidan qasan da yayi.

Ta juya gare shi cikin mamaki sosai,sai ya sake bata hannunsa suna sake takawa ciki.

Da suka shiga ciki,even the silence felt luxurious.

Huge open spaces. Warm lighting,minimalist elegance....Oud scent mai laushi.

Kowane detail din wajen carefully planned ne. Da wannan nutsuwar tasa..... Tsarin nasa da ita aka gina wajen..... Da ita aka gina komai na gurin.

“This doesn’t even look real. " Kaman bazai magana ba, kaman bazai motsa ba kafin ya tako a tausashe ya qaraso kusa da ita sosai. Kusan da take iya jin saukar numfashinsa a hankali.

“It’s real.” yadan dakata da tarin nutsuwarnan tasa.

“And it’s yours too.” wani irin shuru ya gilma,akhnan ta ji zuciyarta na yin wani irin laushi,saboda duk inda yake kai ta.....bawai wajen nuna kudi kawai yake kai ta ba,a'ah...

Yana gina mata tsaro da wani irin aminci ne,da rayuwar da bata taba mafarkin zata samu ba.

Ta bude baki zatayi magana,Amma sai ya hana mata wannan damar, ya sanya hannuwansa gaba daya ya daga ta cak ya rungumeta a qirjinsa yana cewa.

"Ki huta haka nan,zan amsa kowacce tambaya taki bayan kin huta" Wani guri taga yana nufa da ita, sun wuce wani dogon guri me kama da hallway wanda ya qunshi wasu irin luxury bedrooms ba daya ba ba biyu ba. Ya zabi daya daga ciki ya tsaya a gaban qofar, tayi magana cikin harshen turanci tana nuna fahimtar waye tsaye a wajen, ta kammala scanning nasa ta bude musu suka shige.

"Welcome to my world" Ya furta yana direta tsakiyar bedroom din data jita tun bayan shigowarta tana fita daga duniyarta zuwa wata duniyar ta daban.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Chapter 154 · 0% Book details