Sashe 127
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee*
________________________
Cikin kunnuwanta yake rad'a mata wasu abubuwa,wasu irin kalamai masu saukar da wani irin sanyi ga zuciya. Kalaman da suka sassauta mata zuciya ta dinga sauke ajiyar zuciya shi kuma yana sanya yatsunsa yana dauke mata hawayen.
"Kina sonsu ne gaba daya?" Ya mata tambayar ba tare data zaci haka daga gareshi ba. Jiqaqqun idanunta ta daga ta kalleshi.
"You're buying them back?" Ta fada da dusashiyar murya. Wannan murmushin dake da hatsari yayi.
"Would you rather strangers keep pieces of your father?” wani lafiyayyen murmushi ne ya qwace mata,ta riqeshi qam qam cikin jikinta idanunta suna tara sabbin hawaye. Godiya takeson masa amma batasan ta wacce hanya ba.....ta kasa magana gaba daya,sautin mammina ya sake ratsasu.
"Da wanne arziqin zaka iya siyan dawakai masu tarin daraja irin wannan?,da albashin kudin bincike?,zamu gani" Saita taka tana daga murya.
"Kowanne d'aya inaso a ninka farashinsa ga duk wanda zai siya". Idanu suka hada da akhnan,abinda ya gani a idanunta suka sanya tausayinta ya kusa narkar dashi. Kamar tana tuhumar kanta.....me yasa ta zama uwa a gareta?,kamar tana tambayar kanta ya akayi ta shigo ahalinsu?,kaman kuma tana tuhumar me yasa sultane ya aureta?. Kai ya jinjina mata yana mata wani kyakkyawan riqo,kafin ya dagata cak ya rabata da qasa yana rungumeta a jikinsa. Murya can qasa.....ya kuma kulle idanunta cikin nasa yana hanata kallon kowa ya soma mata wata magana qasa qasa,wadda ta sanyata kwantar da kanta cikin qirjinsa tayi luf.
Wani mugun tsaki mammina taja tana binsu da mummunan kallo. Ba abinda zai hanata tsinke wannan igiyar soyayyar. Tasan ibraheem.....kome akace yaronsa zaiyi akan matarsa na sadaukarwa ba zatayi mamaki ba.
"Aikin banza.....ka dauka kudin wadannan dokunan kamar kudin siyan littafi ne?". Sautin ya isa kunnensa,amma ya hana akhnan taji da zaqaqan kalaman da yake karanto mata har tana jin duk wani bacin ranta yana kwaranyewa.
★★★
A cikin kwanaki kad'an ta soma wargaza masarautar da tarin sauye sauye na fili dana boye. Kadarorin sultane......tsarukansa da komai nasa ya zama a hannunta da sarrafawarta.
Cikin wani irin qwarewa da take tunanin tana da ita....cikin qwarewar da take ganin ta kai mata take karban komai d'aya bayan d'aya. Manyan kadarorin sultane tana gwanjonsu cikin kwanciyar hankali da yaqinin ba wanda yake da kaurin wuyan qalubalantarta. Dawakan da yafiso....,manyan muqullai suna hannunta,takardu masu daraja....zinare......azurfa.....dama dukkan wani abu da tasan me kima ne. Babu me qoqarin yayi magana.....saboda abune me sauqi yanzun nan ace an rasa wane....ko an koreshi kwata kwata daga agadez din. Mutane da yawa ta siya.....kama daga mañyan fada da jami'an tsaro na cikin garin,wannan ya sake bata daman sakewa da ci gaba da aiwatar da komai yadda takeso. Masu tsaro da amintattun da suka fara canza bangare. Wasu saboda tsoro.....wasu saboda kwadayi da neman mafita irin ta son zuciya da butulcewa halacci irin na d'an adam.
A cikin kwanaki kad'an…..masarautar Agadez ta fara sauyawa zuwa wani abu daban da mutane da yawa basu tab'a tunanin zasu gani ba. Ba kuma saboda an rasa sultane kawai ba...aah. saboda mutanen da suka dad'e suna fakewa da inuwa da tsoronsa… sun fara fitowa fili.
Fadar agadez ta fara rasa tsohon numfashinta na asali,dokokin da sultane ya kafa shekaru masu yawa an rushe wasu,an sauya wasu. Sabbin fuska suka fara bayyana cikin fadar.....sabbin umarni da sabbin tsare tsare da sabbin dokoki. Komai yana sauyawa cikin sauri me ban tsoro da d'aure kai.
Mutum daya.....mace daya data zame mata qarfen qafa.....macen dake tsaye wajen qalubalantarta da dukka tsarinta MORSA SAFIYYA sai lafiyarta ta fara rauni,wannan ya sanya hairaan yanke shawarar hanata jin komai. Ba morsa SAFIYYA kadai ba.....harda akhnan dinma da falaak da suke kyautata zaton laulayi takeyi. Don sam taqi yarda taje asibiti bare a gwadata. Morsa SAFIYYA tayi tayi kuma tabi mijinta su wuce tunda anyi bakwai.....amma tace sai anyi arba'in tukunna.
A hankali tsoro ya shiga zuciyar kowa,tsakanin masu aiki sam ba sakewa.....babu aminci saboda kowa ji yake bai tsira ba. Cikin kowanne second....cikin kowanne minti kowa yana iya shiga TARKO na giwa mammina. Uwa uba a yanzun ba kowa ke yarda da kowa ba cikin masarautar. Kana zaune da mutum yanzu,anjima zaka tsinceshi ya koma dan bayan mammina dari bisa dari.
Masarautar ta fara zama wajen zargi,tsoro da siyasa,da kuma murmushi na jabu,murmushin da zai iya hallaka wanda ya rud'u da ganinsa saman fuskar mammina din.
Sauyi ne daya fara tun daga manyan corridors har dakunan masu aiki na gidan,bayi dama hadimai. Anajin wannan sauyin. Ana ganinsa. Kuma kowa na tsoronsa.
Tutar masarautar tana nan a tsaye.....masu tsaro suna tsaye a bakin dukkanin qofofin.....dattawa suna nan a majalisar zartarwa ta fadar agadez,amma RUHINTA ya fara canzawa.
A hankali sunan SULTANE ya fara zama kamar wani abu da ake qoqarin turawa baya. Aka fara cire manyan hotunansa daga dogayen private halls na gidan.
Ambatar sunan SAFEENA ko 'DA SULTANE YA RAYE' ya fara zama babban zunubin da ba za'a gafartawa wanda ya aikatashi ba. Kalmomi suka fara zama abubuwa masu hatsari cikin masarautar AGADEZ.
A hankali akhnan ta fara jin kamar tana kallon gidansu yana zubewa a idanunta.
Mammina ta fara zagayawa cikin fada da wani irin nutsuwa da jin gamsuwar nasara ta tabbata a hannunta!.....nasara a hannunta tayi nisan da ba wanda zai iga qalubalantarta. Ba gudu take yi ba....Ba rikici kawai take tayarwa ba. A’a. Ta fi amfani da:
umarni masu laushi......murmushin karya,dokoki,tsoratarwa.....da kuma rashin tabbas data saka a zukatan kowa da rayuwarsa.
Wani lokaci zata yi magana cikin taushin murya…..amma bayan awa guda wani hadimai ko bawa ya rasa aikinsa. Ko wani cikin masu tsaro ya b'ace.
A hankali sai mutane suka fara fahimtar mulkinnan na mammina......sannan mulkin mammina ba ihu bane. Mulkin Mammina… shi ne ka kwanta lafiya,ka tashi ka tarar an canza rayuwarka.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Jama’ar Agadez sun fara shiga rud'ani. Wasu suna kuka da gaske saboda rashin Sultane. Wasu suna tsoron future ɗin masarautar. Amma kuma.....ba wanda ya isa ya fada da qarfi.
Fadar agadez ta fara zama wajen sirruka. Qananan qungiyoyi suna had'uwa cikin boyewa. Ana kai takardu cikin duhu. Ana canza masu gadi a tsakar dare. Ana jin jita-jita marasa dad'in ji kala mala.
Wasu daga cikin tsoffin masu biyayya ga sultane sun fara ja da baya cikin tsoro. Saboda sun kasa gane.....wa za’a yarda dashi?......wa yake siyar da bayanai.......wa zai biyo bayanka idan kayi kuskure???.
Duk sanda wani zai magana amsa daya ce.
"Ina tattalin masarauta.....ina tattalin mutuncinta.....ba abinda zai sake gudanawa sai an tabbatar da wanda ya kashe sultane.....sai bayan bincike ya kammala tare da kama duk wanda ke da hannu cikin mutuwarsa". Wanda yayi wannan maganar har ya samu amsa.....ba lallai bane gobe a sakejin motsinsa ko a sake ganinsa ba. Wannan ya zama wani abun tsoro da kowa ke shakkar magantuwa akai.
A wannan lokacin ne akhnan ta fara jin cewa.....ba fadarsu bace wannan kwata kwata.... Ba masarautar mahaifinta bace......duk inda ta juya sai ta ga canji
Wani sabon tsari. Wani sabon umarni. Wani sabon tsoro a idanun kowa.
Sai dai abu d'aya bai sauya ba. Kallon Haisam!. Duk lokacin da idanunta suka had'u da nasa.....tana jin kamar. Akwai wani abu daya sani da kowa bai sani ba!. Kuma wannan abu… shi ne kad'ai yake hana masarautar rushewa gaba ɗaya.
*HAISAM* mutum d'ayan da ya ci gaba da kasancewa cikin nutsuwa mai tada hankali da sanya mamaki. Haisam....yana gani.....yana sani. Amma bai hana komai ba. A kallo… ba a fili ba......a filin kuma KAWAI bawai a bad'ininsa ba. Badinin da ba wanda ya sani sai Allah saishi.....sai team dinsa dake qoqarin tattara dukka wata hujja data motsin mammina!.
Wannan shurun nasa......wannan nutsuwar tasa....shine ya fi tsoratar da wasu daga cikin dattawan fada. Saboda sun kasa gane?......shin yana jiran komai ya rushe ne?......ko kuwa yana jiran wani lokaci ne da zai maida komai hannu d'aya?.
Mammina naci gaba da jin d'and'anon nasara. Karo na farko cikin shekaru,ta fara tafiya cikin masarautar kamar ita ce ke da ikon qarshe a duniya gaba daya. Ba tare da idon sultane a kanta ba.......Ba tare da wani dake iya tsayar da ita ba.
Ko a zuciyarta da a farko take shakka da kokwanto......ta fara gaskata cewa...... A iya yanzu kadai TACI YAQIN DATA SHEKARA DA SHEKARU TANA JIRA!!!.
★★★
Babban zauren majalisar masarautar Agadez cike yake da manyan mutane,dattawa da masu riqe da dokokin fada. Masu kula da kadarorin masarauta. Hakimai da manyan masu fada aji.
Zaman an yishi ne don a tattauna rabon gadon Sultane,karo na farko tun bayan mutuwarsa,ganin yadda kwanaki ke dada nisa. Cikin manyan malamai aka samu wani ya fidda tsoro ya kuma shirya zaman saboda qaunar da yakewa sultane din da kuma fatan sauke masa nauyi koda hakan zai zama silar faruwar wani abu a kanshi.
Wurin ya yi shiru mai nauyi,irin shirun da yake nuna kowa na taka-tsantsan da kalamansa,sannan kowa na kallon kowa da zargi da rashin aminci.
Mammina na zaune cikin baqar alkyabba mai nuna iko da isa. Fuskarta babu alamar wata damuwa irin ta macen data rasa mijinta masoyinta kuma jigonta.
A gefe guda kuma morsa safiyya ce,zaune cikin nutsuwa duk da alhini da gajiyar da suka bayyana a idanunta dama gangar jikinta data nuna rama sosai.
Kusa da ita kuma akhnan ce zaune,tashin hankali ne kwance saman Fuskarta yana nuna kansa muraran.
Tun bayan mutuwar sultane ta fara jin kamar masarautar tana zamewa daga hannunsu. Tun biyowar bayan sabon takun mammina da har yanxu yake daure mata kai takejin komai yana dagulewa cikin rayuwarta.