← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 176

Sashe 84

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanunta ta lumshe saiga ruwan hawaye yana gangarowa,ya sake matsawa da kujerarsa jikinta sosai har gwiwoyinta suna shigewa cikin qirjinsa.

"Karkiyi kuka.....na gwammace na mutu d......."

"Ba zaka mutu ba!" Kalmar ta fita tana fusgarta da qarfi daga bakinta. Kalmar MUTUWA na daya daga cikin abinda ta tsana,tun daga sanda ta fahimci ita ta rabata da mamminta bayan kowan data sani tare da tashi mahaifiyar yake raye.

"Zan mutu mana khadeejaaaaaaaa......" Yaja sunan numfashinsa yana yin Kamar zai dauke saboda mararsa data sake dunqulewa ta cure guri daya da wani irin ciwo.

"Ba zaka mutu ba!." Ta sake fadi a wannan karon muryarta tana fita da sautin kuka. Miqewa yayi tsam a gabanta,ya bude tafukan hannunsa yana sanya nata a ciki ya mayar ya kulle,ya sake matsowa sosai yana cike gap din dake tsakaninsu ta hanyar kusanta fuskarsa da tata. Da wata irin murya.....wata narkakkiyar murya da sam batayi kama da tasa ba,wata kalan murya dake fita daga can qasan maqoshinsa gauraye da wani irin sauti me nauyi taushi da sanyi ya furta.

"Kina sona biftuuuu" A dan razane ta daga idanunta tana kallonsa. Wannan tsoron ya gauraya da wata matsananciyar kunya. Ya akayi?,abinda take tsoro?,abinda take kunya?,abinda take boyo ya sani gashi a tsaye gabanta da mafi girman kusanci yana gaya Mata shi kai tsaye.

"Kamar yadda nake MUTUWAR QAUNARKI!!" Ya furta yana motsa labban nan nasa da suka sake zama wani pink color sosai yana dage mata dukkanin girarta,lumsassun manyan idanunsa suna sake nuna girmansu.

Wani irin mamaki ya finciketa yana barazanar tsayar mata da numfashinta. Idanunsa take kalla kai tsaye kamar yadda shima nata idanun yake kalla,yana jin kamar ya shige ta cikin idanun ya saje da ita,su kuma narke su zama abu daya ita dashi.

"Yes......ina mutuwar sonki gimbiyata.........ina sonki.....ina sonki.....ina sonki.....ina sonki......ina sonki....ina sonki......" Ya maimaita sau ba adadin da sai data ji kowacce wuta ta jikinta taka tsinkewa......ya maimaita kalmar da dukka zuciyarsa da fitar numfashinsa......ya maimaita fada da yanayin da a cikin muryarsa ta dinga jin kamar numfashinsa zai dakata daga fita daga hunhunsa,ya sauke kalmar yana kuma sake dorawa da fadin.

"......ba don wannan lokacin ba......ba don wannan ranar ba.....ba kuma don ina neman komai ba........biftuuuu........ina sonki tun daga ranar dana fara gane wacece ke!......tun daga wancan ranar,.....tun daga wancan lokacin,ban sake bacci da idanu biyu ba......ina sonki.......ina qaunarki irin yadda baki da dukkan kalamai sunyi kadan su bayyanata a asalin yadda take a zuciyata".

Wani irin sheshsheqa ta saki......irin sheshsheqar yaron da yasha kuka me yawa da tsaho ya kuma samu lallashi. Nauyi taji kalaman sun manta,tamkar wannan jaririyar zuciyar tata ba zata iya daukarsu ba. Yana mata magana da wani irin yanayi daya qarasa illata zuciyarta ya kuma kassarata gaba daya.

A cikin kunnenta......cikin tsakiyar kunnenta bayan ya dora labbansa ya furta kalaman. Tamkar dai kalamai ne da sukafi komai daya taba furtawa a duniya daraja da tsada.....irin kalaman da ake bada ajiyarsu da wani irin girma martabawa da darajtawa zuwa ga kalaman.......wadansu kalamai da suka zama zababbu na musamman da ba kowanne kunne ya cancanci yaji irinsu ba. Kalaman da akeso kuma su isa kai tsaye zuwa ga ZUCIYA inda ke fafutukar kafa kai a can.

Ya saukesu a muhallinsu,ya kuma saukesu a inda ya dace,sun kuma yi wata irin sauka da cikin qasa da second goma suka kafa wasu irin rassa masu matuqar qarfi da tunbukesu zai zama wani abu mafi girman aiki da dan adam zai tunkari yinsa.

"Ki yarda ki zama MALLAKINA.......kiyimin alfarma gimbiyata" Ya qara fadi yana narkewa cikin jikinsa kamar yadda yaro me qyuya yakeyi sanda wani ke yunqurin karbarshi daga hannun mamarshi,yana sake matse tafukan hannayenta cikin nasa.

"Nnnnnnnn.......na amince.....amma don Allah.....kada ka kasheni......kad......kada ka cutar dani....mmmn" Bata qarasa fadin maganarta saman dressing table din ba sai bisa hannuwansa. Ya dagata cak kamar yadda uwa ke daukan jaririnta da tafukan hannayenta gaba daya. Ya hadeta da qirjinsa,yana sunkuyo da fuskarsa daidai tata,wani abu da batasan meye ba yana taruwa cikin idanunsa.

"Kinyi hannun riga da cutarwa daga kowacce irin halitta tun daga wancan lokacin......koda kuwa aljani ne komai girman sharrinsa ballantana dan adam.......dan adam dinma yaron nanay da motii?.....ZUCIYARKI nakeso ki mallakamin ba iya gangar jikinki ba......kin shirya mallakamin gaba daya?".

Wannan yanayin yafi qarfinta.....wannan kallon.....wannan kalaman......wannan idanun duka sake kasheta suke sakeyi bayan kowacce daqiqa.

"Ki mallakamin......don Allah......na roqeki" Ya fada muryarsa tana rawa sosai yana kuma manne fuskarsa da tata.

"......Na mallaka maka.......na baka"

"......har abada?"

".......har abada" Ta maimaita tana gyada kanta a hankali.

"Idan nace na gode......tabbas na rage martabar kyautar da kika yimin......zan maidake mallakina da gaske ba'a baki ba......zan tabbatar kin zama tawan......sannan nasan wadanne zababbun abubuwa ya kamata a gode miki dasu.......amma saidai......" Ya fadi da wani salo na rad'a,irin radar nan da murya ke fita a dakushe bada cikakken sauti ba.

"......ki zama jaruma.......don Allah biftuuuu.......bazan cutar dake ba........amma banyi alqawarin iya riqe kaina gaba daya ba". Daga haka yaci gaba da takawa yana riqe da ita a hankali kai tsaye zuwa bathroom.

Ajiyeta yayi saman wata waterproof chair,wadda kusan amfaninta cikin bandakin kawai shine zama.

Zaman tayi kawai,tana kallon yadda ya daura alwala,alwalar da duk bayan wasu sakanni sai ya waiwayo ya dubeta kamar zata bace masa. Gabanta ya tako a hankali da wani abun diban ruwa. Cikin salo na girmamawa ya dawo gabanta ya tsugunna saman qafafunsa

"Kiyi alwala" Ya furta da wata irin kasala yana duban qwayar idanunta.

Ruwa ya dinga zuba mata a hankali tana daura alwalar harta kammala. Ya maida abun,ya kuma ciro qaramin lallausan towel ya dawo gaban nata ya sake tsugunnawa.

Qafafunta ya kama ya dora saman cinyoyinsa,ya saka towel din yana tsane mata ruwan cikin kulawa da wani irin taushi,toilet din ya dauki wani irin shuru sai zuciyoyinsu dake bugawa cikin qirjinsu da wani irin yanayi.

"Ina fatan wannan rana ta zama mabudin alkhairi tsakaninmu......alkhairi na har abada" Ya fadi yana sanya mata towel din cikin tafin hannunta don ta qarasa tsane damshin,saboda baya jin zai iya tsane mata na sauran sassan jikinta ba tare daya rasa alwalarsa ba.

Shi ya zura mata after dress....sannnan ya mata rolling da mayafin abayar. Fuskarnan ta fito tas da wani irin kyau haske da sheqi kamar farin wata.

Ya zare idanunsa yana sake qoqarin tattalin alwalarsa,ya matsa zuwa gaba ya tayar da kabbarar sallah.

Raka'a biyu sukayi,bai tsawaitasu ba,kaman yadda bai tsawaita addu'o'in ba,ya juyo yana dubanta yana zube mata idanunsa da suka sake wani laushi. Hannunsa ya aza saman goshinta,a hankali cikin nutsuwa labbansa suka fara motsawa.

"Allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi......wa'a'uzubika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi". Yana qare addu'ar wata irin nutsuwa tana saukar mata. Wata nutsuwa me cakude da aminci tana sassauta wannan tarin fargabar dake maqare cikin zuciyarta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Ya cire hannunsa daga saman kanta,dukkanin jikinsa yana amsawa da wani irin yanayi,saidai duk da hakan.....zaiso ya gina dare me albarka.....zaiso ya bude maqullin gina nashi iyalin na qashin kansa da dukkan wani abu na koyi da sunnar manzon Allah S A W,domin neman albarka a cikin rayuwarsu gaba daya.

Tana kallonsa ya fita......ba jimawa kuma ya dawo daki dauke da wani dogon glass cup. Dab da ita ya zauna,yana aike mata da saqon wannan lallausan qamshin nasa da a duniya a yanzu ba wani kalan qamshi da take mutuwar so da marari irinsa.

Da tattausan murmushi akan fuskarsa ya miqa mata cup din,wanda sai a sannan ta lura madara ce a ciki. Tatacciyar madarar data lura qabilar oromo na matuqar ji da ita. Madarar da sha daya ta mata ta samu kyakkyawan mazauni a cikin zuciyarta.....sannan kuma ta fahimci tarin banbance babancen dake tsakaninta da tasu ta agadez.

"Bismillah......kada kice a'ah.....late comer ne ban shigo da komai ba" Ya fadi dukkanin idanunsa da jikinsa na sake masa nauyi. Saidai akwai abinda yakeso.....wannan TSORON.....wannan tsoron yakeso ya cire daga ranta,nutsuwa yakeso ya samar mata. Ba gangar jikinta kawai yake buqata ba.....a'ah.....harda wannan zuciyar dake adane cikin gangar jikin.

Yanaso ya gina darensa da wani memory me kyau......yanaso ya fara da qauna soyayya da kulawa,ta yadda ba zata sake gudunsa ba,daga wannan ranar.....daga wannan lokacin,zasu narke ita dashi,su zama abu daya wanda ba za'a iya banbance ina HAISAM ba ina kuma AKHNAN?.

Bata musa ba,ta saka hannunta zata karba,saidai ya mata dabaran hade yatsunta cikin nasa,bai kuma sakar mata hannun ba ya tayata kai cup din bakinta.

Kurba daya,biyu uku tace alhmdlh,bai matsa ba sanda ta zare hannunta,sai shima yakai cup din bakinsa saitin inda ta cire nata bakin. Kurba ukun kawai shima yayi,ya miqe dashi a hannunsa ya sake fita.

Ta sauke ajiyar zuciya me nauyi tana jin nutsuwa na sake saukar mata. Wannan tsoron firgicin da razanar da tayi a dazu yana raguwa a hankali.

"Ashe ba haka bane....ba kaman yadda na zata bane" Ta fada can qasan ranta.

Da cikakkiyar sallamar data sake wanzar da nutsuwarta ya dawo dakin. Yadan jima kadan ba kaman fitar da yayi dazu ba. Ta daga kanta da nufin amsa sallamar saidai kallonsa a yanzu ya gagareta,bugun zuciyarta kuma ya nemi komawa da gudunsa kamar dazun.

Ba komai a tare dashi dai gajeran wandon daya tsaya iya cinyoyinsa. Wannan faffadan qirjin.....wannan ginannen jikin.....wadannan fararen cinyoyin dake lullube da baqar gargasa gaba daya sun bayyana.

A nutse ya dinga bin kowanne haske na dakin yana kasheshi,kafin ya tako zuwa inda take a hankali.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 76*
___________________________

*_INA MASU SON KOYON SANA'AR DATA SHAFI ZAMANI KAI TSAYE?_*

*_SANA'AR DA A YANZU DA ITA AKE DAMAWA?,ITACE TAKE KAI DUBBAN MATA GA GACI?....MAZA ZO KIYI JOINING WANNAN CLASS DIN DA GUDU_*
Chapter 84 · 0% Book details