← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 176

Sashe 25

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanda take rubuta gajeran saqon tana aikewa,ta dauka zataji tsoro......ta dauka zataji tsoro game dashi ya kamata......amma maimakon wannan wani aminci da nutsuwa takeji. Ta tabbatar sultane bazai aminta har haka da mutumin da ba gaskiya a tare dashi ba,amma duk da haka......tanaso ta sani......tana buqatar sanin koshi waye.......koda ba dogon zama zasuyi ba......amma tana buqatar ta sani.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽LU'U LU'U
(The diamond)💎
HUGUMA
BOOK 03///PAGE 23
Cikin awa daya da mintunan qalilan suka qaraso. Babban hotel dake dab da harami wato raffle makka palace.Ta sake daga idanunta tana daban hotel din. Daya daga cikin hotel din data saba sauka duk sanda zataje umara. Yana mata dadi,yanayin tsari tsaro kulawa dama komai nashi dabanne. Hotel ne na masu iko.....sarauta sama hannu da shuni a kowanne bangare na duniya."Raffle?" Ta sake nanatawa wani mamaki me girma da nauyi yana danne zuciyarta,zatonta da zarginta kuma a kansa yana sake ninkuwa.

Fuskarsu cike da alamu na sanayya, tashi fuskar kuma a sake da wani irin yanayi dake nuna nutsuwar da Allah ya yiwa ruhinsa baiwa da ita.Direct suka zarce zuwa elevator da zai rage musu tsahon tafiyar. Ko a ciki numfashi take ja kadan kadan tana sake satar kallonsa. So take taga wani abu daya sauya a tattare dashi amma babu. Shidinne dai......sheikh muhammad haisam din da suka taho tare daga agadez har zuwa makka din. Ba wani reaction nasa daya sauya, kamar komai yana kan muhallinsa ne, kamar ba wani baqon abu cikin lamarinsa, kamar dai normal daily life style dinsa kenan.A hankali elevator din ya tsaya, still bai kalleta ba, ya taka a hankali yana miqa mata hannunsa. Tsaiwa cak tayi tana duban lallausan tafin hannunsa daya miqa mata, idanunsa kuma suna kan wayarsa, da alama koda hannu daya koda hannayensa biyu dukka ya qware wajen sarrafa waya. Tafin hannun take kalla sosai, a karon farko taji wani tafi jinsa cikin nata hannun maimakon...

Wannan rayuwar.....ba irin ta talaka bace" Ta fada a zuciyarta,saidai har a fili ta gaza mallakar kanta. Tsoro ne yake kamata zuwa yanzu,tsoron da yafi na dazu qarfi.Shurun da yaji ya sanyashi daga idanunsa ya zube a kanta,take idanuwansu suka gauraye da juna. Ya dan zuba mata ido yanason karantar abinda yake cikin ranta,amma saita kawar da kanta tana jin tsoro da shakkarta suna qaruwa."Muje?" Ya fadi a tausashe yana maida hannun nasa cikin aljihun jubah dinsa maimakon ci gaba da miqa mata shi.A nutse take biye dashi tana sake karantar sa takunsa. QASAITA kowanne motsi nasa nunawa zallarta. Hankalinta ya sake rarrabu Sashen da suke nufa.....bata taba sauka a wani bangaren ba,wannan block din ma bata taba hauroshi ba.Bullowar wani balaraben matashi ya sanyata janye hankalinta kadan. Kaman sauran ma'a...

kammala ibadarta ta wuce.Bakin qawatacciyar qofar ya taka,ya matso da executive access card dinshi jikin qofar,tayi 'yar qaramar qara ta bude kanta da kantaIdanu akhnan ta sauke a hankali akan card din,adon gold din dake jikinsa na dabanne. Wani irin minimal design me daukan hankali. Ta aza idanunta akan embossed name din dake jikiAlsaamit shine sunan dake rubuce a jiki,akwai wani tiny emblem a jiki. Qawataccen crown me jan hankali sosai da daukan idanu.Tura qofar yayi,ya soma takawa zuwa ciki.Saita tsaya cak, qafafunta kamar sun qi motsi Cikin iikinsa yaji bata biye dashi,ya tsaya da tawa ya waiwayo da manyan fararen idanun sa yana dubanta.In salon bada sassauqan umarni.

Shima nasa fararen idanun ya zuba mata,sannan ya sauke numfashi a hankali yana maida wayarsa aljihu still bai dauke idanunsa daga kanta ba."Ki shigo" Ya fada da wani irin coolness yanayinsa yana nuna hankalinsa kwance yayi maganar.Ci gaba tayi da duban labbansa ba tare data iya kallon qwayar idanunsa ba. Haka kawai taji qwalla tana cika mata idanu,saita motsa labbanta a hankali."Ban tambayeka shiga ba.....waye kai?" Ta sake fada har ga Allah tana jin tsoro duk da ta sani tana amintaccen muhallin da ba kamarsa duk duniya. Amma ta sani,duka wannan.......dan wadannan,tsarin tafiyarsu.....private jet......wannan suit din duka ba aikin sultane bane. Tasan kudin da zasu sauka da farko,tasan jirgin da zasu bi duka ta bakin shehnaz......amma a yanzu sabanin komai take gani.Idanma sultane ne.....tun daga private jet zuwa wajen girmamawa tarba da karramawa

ma'aikatan hotel fa?."Ba gurin tsaiwa kiyimin tambayoyi bane nan" Sai ya daga hannunsa yana mata nuni da ciki kamar yana mata magana ne cikin ikon dake cakude da nutsuwa."Ki shigo" Ya rufe da fadin hakan cikin nutsuwar nan tasa.A hankali taji qafafunta suna saki,ta soma motsawa tana takowa zuwa ciki.A nutse ya saka hannu ya maida qofar ya rufe,sannan ya soma bin bayanta a hankali. Cak ta tsaya sanda yake tsaiwa Shima"Me yasa na yarda na shigo?,me yasa bance ba?" Ta tuhumi kanta. Saita daga blue eyes da sauri ta waiwaya tana sake dubansa."Ka fara bani amsa.....waye kai?". Idanu ya sake zube mata kawai yana karantarta ta cikin nutsuwa,tsoro,karaya duka yau yake...

da sauri ta waiwaya tana sake dubansa."Ka fara bani amsa.....waye kai?". Idanu ya sake zube mata kawai yana karantarta ta cikin idanunta. Rauni, tsoro, karaya duka yau yake gani cakude cikin shudin idanun gimbiyar agadez din a yau. Kafaffiyar gimbiyar nan wadda ta bawa maza da yawa kashi......kafaffiyar gimbiyar nan wadda bata sauka daga kan ra'ayinta......kafaffiyar gimbiyar nan da batasan tsoro ko sauya tsari ba.Lumshe mata idanun yayi yana budesu a lokaci guda, wani abu daya sake bayyanar da zanuun kyanshi."Zan baki amsa" Sai ya dakata."Amma ba yanzu ba" Ya cikashe maganarsa."Sai yaushe?" Ta sake fadi da alamu wannan dabi'ar tata ta kafiya ta motsa.

kanta,ya tara takawa a nankali yana nufar daya daga cikin qofofin dake cikin luxury living room din,ya budeta a nutse,ba tare daya kalleta ba yace."Ga dakinki.....ki shiga ki huta,ki kuma shirya nan da awa daya zamu shiga haram". Daga haka ya juya a nutse yana sake bude daya qofar dakin,ya taka a nutse yana shigewa ciki.Wannan mutumin?... meye ainihinsa?,Sheikh? businessman?,royalty?,Ko dukka?toh fa......masu karatu.....a samu wani ya taimaki akhnan ya bata satar amsa......ya gaya prince ne.....dan sarkin Ethiopia da kansa k tunani da canki canki ya qarasa zautata 😂😂😂muje zuwa mutane na💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 24*

Sai taji kaman tana neman zama wani abu na daban. Yawan magana da kan kanta ita daya......yiwa kanta da kanta tambaya.......da yawan tuhume tuhumen da takeyi yiwa kanta duk ita daya,nema yake ya zame mata al'ada ko kuma dabi'a.

Qafafunta a sanyaye ta taka zuwa qofar daya bude matan,ta tura a hankali tana saka qafafunta saman lallausan luxury carpet din dake malale cikin dakin.

Idanunta ta ware tana kallon dakin da kyau. Wani irin tsari ne me daukan hankali sosai,wani irin yanayi me sanyi da saukarwa zuciya dama gangar jiki nutsuwa. Idanunta suka sauka a bangon gabas na dakin. Glass ne gaba daya ta gurin,glass din da aka qawata da manyan curtains na alfarma masu kyau. Samu kanta tayi da takawa zuwa gurin,tana jin kamar ana jan zuciyarta. Tana jin kamar akwai abinda yake fusgarta zuwa gurin cikin wani irin yanayi.

Tayi tsaye gaban labulen,zuciyarta da qirjinta suna bugawa da wani yanayi na daban. Yau zataga wannan view din......wannan ganin da take kwadayi kai tsaye daga masaukinka cikin raffles makkah palace din. Ta miqa hannunta a hankali,ta yaye curtain din,take cikakken gani daga harabar harami dukkaninta ta bayyana kamar tana tsaye cikin gurin.

Wani bugun zuciya me cike da nutsuwa ya sakata lumshe idanunta sannan ta budesu. Wani irin yanayi me nutsuwa ya saukar mata,daidai lokacin,kamar ladanin masallacin haramin sheikh Ali Ahmad mulla yasan tana tsaye ne.....a daidai lokacin zuciyarta tana lilo da wani irin yanayi ya fara kwararo kiran sallan isha'i.....kiran sallar da taushinsa da yanayin sautinsa mai ratsa gabbai ya sanyata zamewa a hankali saman gwiwoyinta ta zauna sosai saman abun sallar tana sauraren kiran har zuwa sanda ya kammala.

Haka kawai bawai don ta sani ba ta samu kanta da daga hannuwanta tana addu'a. Tana addu'a wa sultane.....tana addu'a masa ingantacciyar rayuwa me tsaho,sai data qarar da dukka addu'arta a kansa ba tare da tasan ita me zata roqarwa kanta ba.

"Ki shirya.....zamu shiga haram" Ta tuna maganarsa. Dan turus tayi bayan data laluba,ta tuna bataga birra ba tunda suka taso,bataga falaak bama. To bama falaak ne damuwarta ba,birran ce. Ta yaya zata iya hadawa kanta ruwan wanka?,ta fidda kayan da zata sanya ta kuma shirya kanta da kanta?.

Tayi turus tana qiyasta yadda zatayi komai din da kanta,karo na farko a rayuwarta kenan. Har cikin ranta taji ta takura,har cikin zuciyarta taji kaman ba zata iya ba,amma data tabbatar ba birra a kusa.....babu kuma wani sauran hadima daya rage da zata taimaka mata,dole ta soma rage kayan jikin nata,sannan ta daura towel babba ta wuce zuwa toilet din.

Banda tazara da suke dan bayarwa tsakanin kiran sallah da iqama ta sani tabbas saita makara. Tun a iya gurin hada ruwan wanka kawai ta fahimci batasan komai ba,bata kuma iya komai don taimakawa kanta ba. Da farko ta hada ruwan da zafi,sai data fita ta sake gyarawa,sai kuma ta salamtar da ruwan gaba daya. Tayi wankanne kawai ba tare da ruwan ya mata daidai da yadda birra ke hada mata ba,sannan ta fito ta fara kici kicin tsane jikinta da shafa mai. Wannan bata dauki lokaci ba tunda ta saba,saidai gurin gyara gashinta wanda daga qarshe sakin gashin kawai tayi ta soma neman wanne kaya zata saka.

Turus tayi tana duban ma'ajiyar kayan da kafin su haura saman har cikin ma'aikatan dake tiri tiri da baqi ta gama shirya mata su tsaf a cikin gurin.
Chapter 25 · 0% Book details