← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 173 OF 176

Sashe 173

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Talakawa kuwa suna dokin ganin sarkinsu a cikin irin wannan biki da ba a taba yin irinsa ba a qasar baki daya.

A wannan lokacin kuwa, gidan Haisam da Akhnan ya cika da baqi fiye da yadda aka saba.

Babbar villar da Haisam ya gina shekara daya baya. Ya fidda sassanni daban daban masu daukan hankali da sabon salo,musamman bangaren underground villa wanda ya kasance mafi soyuwa a wurinsa.

Tun bayan ya lura da irin nutsuwa da farin cikin da Akhnan take samu a can, sai ya sake sanyawa akayi ginin gidan qasan ta hanyar amfani da sabbin fasahohi da kayan alatu na zamani.

Komai a gidan yana aiki ne ta hanyar fasaha. Daga ƙofofi masu gane fuska,tsarin tsaro mai amfani da basirar na'ura, har zuwa fitilu da tsarin kula da yanayin zafi da sanyi automatically kawai gidan zai sauya duka,idan dumi ko sanyi ake buqata.

Ginin kuwa yana da wani irin shimfidadden tsari mai daukar ido.
Kafin mutum ya ankara, kansa zai dauke shi daga abin da yake yi ya tsaya yana kallon qawatuwar wurin.

Da daddare idan fitilu suka haska lambunan gidan, ruwa yana kwaranya a cikin mabubbugan da aka tsara da fasaha, yayin da iska mai sanyi daga tsaunukan Jimma ke ratsawa cikin bishiyoyi....wurin yakan yi kama da wani sashe na aljanna da aka saukar a doron qasa.

Kuma a tsakiyar duk wannan ni'ima da yalwa....abin da ya fi daraja a wurin ba gine-ginen ba ne.
Ba dukiya ba ce.
Sai dariyar yara da ke cike da gidan,iyali daya fara tarawa me yawa,da kuma zaman lafiya da qaunar da Allah ya albarkaci iyalin haisam da Akhnan da ita.

Dukka yaran falaak guda hudu....yaran shehnaz guda uku.....saina aisa guda biyu suna gidan. Haka yaran rumaisa da takanas suka taho da rumaisa sunqi zama a aba jifar palace sai nan gidan. Itama ta samu albarkar haihuwa,duka yaranta maza guda biyar,sai Anaani dake da yammata biyu qaramin namaji ne da yaci sunan ahmad sultane of agadez,yaci sunan kakansa ahmad ajani.

Da taimakon sultana data fara zama 'yammata shekara goma sha biyu data hadiman gidan ta samu suka saita yaran. Kowa yaci ya qoshi,sukayi wanka suka shirya cikin kayan bacci,suka kwanta sannan ta dawo nata sashen.

Ta manta rabonta data kwana a dakinta,don tuni haisam ya rabata da dukka dakunanta. Tana nan underground villa dinsa da idan ka shiga bakasan ma me yake faruwa a duniyar ba. Daga ita saishi kawai.

Amma ayau din sai data ratse dakinta,ta sake wanka,ta fito fuskarta tana qyalli da sheqi da sabulun Mg's soap,wanda duk dare dashi take wanka. Wannan ya sanya fatarta ta sake gogewa da wani irin glowing da kullum sai haisam ya tanka.(0806 299 1549).

Sabbin kayan bacci ta bare,wanda kusan kullum cikin sanya sabbin design take. Ba kasafai ta fita maimaice ba a dukka suturarta,ba ita kadai ba hatta da haisam dinma,har gwara yaran idan wani ya musu suna nacewa shi zasu maimaita.

Idanu ta lumshe saboda qamshin turaren shuwa incense and more da yake fita a jiki,kabbasar da aka musu tun shekaran jiya ke tashi kamar yanzu aka turarasa.(+234 704 229 3387,ina sake maimaita muku,tasted and trusted ne🙌🏽🙌🏽🙌🏽).

A nutse ta dauki hijab dinta kawai don sallar dare,wanda ta saba zuwa yanzu,kota tasheshi ko shi ya tasheta,ta zura lausasan slippers dinta ta soma sauka zuwa gidan qasan.

Daka shiga zakasan gurin yana da banbanci da kowanne sashe na gidan. Kulawa da gyara na musamman take bashi da kanta,bata bari kowa ya shiga gurin.

Har zata wuce bedroom dinsa ta fasa,ta wuce zuwa kitchen ta hada masa special tea din da yakesha duk dare don warware gajiya.

Ta shirya komai da wani irin tsarin saman wani royal tray,sannan ta taka a nutse taka wucewa dakinsa.

Qofar na scanning face dinta ta bude kanta da kanta cikin abinda baikai second biyar ba,ta qara turata tana shiga bakinta dauke da sallama.

Yana tsaye daure da fari qal din towel me laushin gaske. Iyakarsa qugunsa,don haka wannan gymnastic body din nasa na waje a bayyane.

A wannan lokacin.....ba shine ya dauki hankalinta ba. Aah....wayar dake hannunsa wanda tana sallama ya ajjiyeta saman sofa bed yana aza idanunsa a kanta.

Murmushi ya sakar mata yana takowa inda take tsaye,haka kawai yau saita samu kanta da gaza jin murmushin nasa har cikin zuciyarta. Ta sakar masa tray din ta taka a nutse tana wuceshi zuwa saman sofa din.

Wayar ta kalla ta dauke kai,ba abinda yake dawo mata sai kiran daya dinga shigowar wayar tasa a dazu. Ba suna a number din......amma kuma duk wanda zai kirashi wayar zata sanar masa ko waye koda bai sani ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Menelik ta gani a rubuce a jiki. Wani suna guda daya da bazai dusashe daga kanta ba. Idanunta ta dauke a hankali daga kan wayar ta maida kansa. Saita sameshi shima ita yake kalla yana sipping tea dinsa a hankali.

Saqo ne ya sake shigowa,sai ya miqa mata hannu kai tsaye. Mamaki ya daskarar da ita ganin yadda yake dubanta kai tsaye.

"Omar ne.....muna magana dashi network ya dauke,inda yake ba network me kyau......" Bata tsaya qarasa ji ba kawai ta bude saqon kai tsaye,kasancewar komai na wayarsa ta sani. Pin da komai....ba iya na waya ba,komai nasa dake da password ko pin ta sani.

*_Muna hanyar zuwa kallon hawan Durban,koda ban samu ganinka a kusa ba....a nesa kawai ya wadatar....menelik_*

".....suna son zuwa da saamee,to amma yace batajin dadi....zai taho kawai shida yaran" Ya qarasa fada yana ajiye mug din saman table din.

"Saamee?" Ta fada da sigar tambaya,kansa ya daga yana dubanta jin sound dinta ya sauya.

"Ko ba saame ba?,saamee ta tafi.....amma ga wata saame dinnan" Ta fada tana wurgar da wayar gefe wani irin bacin rai yana mata tasiri.

Wayar yabi da kallo yadda ta kangarar da ita,saura kadan takai qasa,kuma tabbas data fadi fashewa zatayi.

"Eh saamee" Ya maimaita yana dubanta kai tsaye wani abu me kama da fushi yanason masa tasiri.

"A baya saamee.....yanzu kuma menelik?,menelik dai?,wa yasan sauran dauke boye da ban gansu ba?" Ta fada wani wutar kishi tana tasiri a ranta.

"Akhnan" Ya kirata a nutse yana ajiye turaren da yayi niyyar fesawa.

"Ki kula da yadda kike magana" Ya fada calmly saidai ransa yana sake baci.

Wata dariya ta saki wadda tafi kama da kukan bacin rai.

"In kula?,wai nice ma zan kula?,Na bude saqo da idona na gani. 'Ko da ban samu ganinka a kusa ba, a nesa kawai ya wadatar...' Wannan ma ba komai bane kenan?"

Ya sauke numfashi a hankali, yana qoqarin danne haushinsa.

"Kin gama?"

"A'a, ban gama ba." Ta miqe tsaye.

"Abinda nake son sani shine, me yasa har yanzu take turo maka irin wadannan saqonnin?"

"Saboda bansan da zamanta bama,don haka ban hana ta ba."

Kalmar ta fito daga bakinsa cikin sauqi,da kuma dukka gaskiyarshi.....amma ta sauka a kunnenta kamar dutse.

"Ban hana ta ba?" Ta maimaita cikin rashin yarda.

"Eh" Ya amsa mata kansa tsaye da gaskiyar nan tasa.

"To ni kuma na ga laifin saqon." Ya miƙe daga kujerarsa a hankali.

"Saboda kina kallon sa da wata ma'ana daban."

"To ka gaya min wace ma'ana yake da ita?" Ta jefa masa tambayar kai tsaye.
Shiru ya dan ratsa tsakaninsu,ya fuskanci shaidan keson tasiri a ranta akan abinda shi baida muhimmanci ko kadan a tare dashi.

Sai ya dauki wayar daga inda ta jefar, ya ajiye ta a gabanta.

"Kin san password dina. Kin san komai nawa. Ban taba boye miki komai ba. Amma idan har za ki riqa neman abin da zai bata miki rai a cikin komai, ko ni kaina ba zan iya taimaka miki ba.....wannan ba komai ban....."

"Mace tana cewa ko daga nesa ta ganka ya wadatar mata. Kai kuma kana zaune kana bani labarin wai ba komai bane." Ta fada da daga muryar da ya jita har tsakiyar kansa. Ya runtse idanunsa a hankali yana qoqarin controlling kansa.

*_INGANTACCEN MAGANIN SANYI NE SADIDAN,WANDA BA'A CAKUDASHI DA KOMAI BA SAI ZALLAR SASSAQE DA ITATUWA MASU AMINCI_*

*_KAYAN GYARA MASU INGANCI DA WARWARE MATSALAR MATA TA FUSKAR CIWON SANYI WANDA YA KASA JIN MAGANI_*

*_GARZAYA A SIRRANCE KI WARWARE MATSALARKI,KI TUNTUBETA TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE_*

+234 810 914 9876

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 160*
_________________________
*_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________

"Wannan ba maganar da ya kamata ki rikide ta zuwa wani abu daban ba ce."

"To ka gaya min me ya kamata in dauka?" Ta matsa.

"Ko kuwa zan jira ta zo ta tsaya a gabanka ne kafin in fahimta?" Wani irin shiru ya ratsa falon. Ya dube ta na wasu dakiku.

"Ki mayar min da wayar."

"Ba zan mayar ba."ta fada kai tsaye,mamaki sosai ya kamashi,abinda bata taba gwadawa ba.

"Akhnan."

"A'a,ba wata Akhnan,yau sai ka gaya min gaskiya."

Ta ga yadda yanayin fuskarsa ya fara sauyawa, amma hakan bai sa ta ja baya ba.

"Ko ita ce dalilin da yasa ka shirya Durban din?"

"Ya isa."

"Ko kuma kana fatan ganinta ne? Tunda ita ma ai zata zo." Ya rufe idanunsa na dan lokaci kamar mai qoqarin danne wani abu. Amma Akhnan ta ci gaba.

"Ko me yasa ma ba zaka gayyace ta kai tsaye ba? Tunda dai....."

"AKHNAN!" Muryarsa ta daki falon da qarfi har ta yi shiru nan take.
Chapter 173 · 0% Book details