← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 176

Sashe 105

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kinga gymnastic guy ko?" Ta fadiwa kanta da kanta can qasan maqoshinta. Dariya kadan ta subuce mata,ta juya idanunta a hankali tana qarewa dakin kallo.

Wani irin tsari da yanayi da dakin ke dashi,kamar kafin a ginashi sun shiga zuciyarta sunga tsarinta da zabinta a kaloli da tsarin daki. Ta fidda iska me sanyi a bakinta,abubuwa da yawa suna mata yawo akai.

Duk inda wayewarta.....ilimi da yawan dukiyarta yakai,a yanzun tana jinta wata maqasqanciya kuma baqauyiya idan har tana tsaye a gabansa,idan har tana cikin duniyarsa......idan har tana cikin da'irarsa sai taji komai nata yana zagwanyewa.

Wannan tunanin ta watsar,don ta tabbatar bata da riba a ciki sai sake dilmiya cikin qaunarsa,sannan ba abinda zai amfanar da ita face ta zama baqauyiya zam kamar yadda hotel din yake shirin maidata cikin qasa da minti arba'in kawai. Komai na musamman ne....komai na dabanne,komai kuma da nasa tsarin cikin hotel din. Especially mr aba jifar residence din. Karon farko kenan data gani da idanunta,bawai a labari ba. Residence guda cikin hotel din da yafi kowanne hotel tsada a duniya?.

"Wanne irin arxiqi ya mallaka?,me yasa baya qoqarin nunawa duniya kanshi?,me yasa silently power dinsa take magana?" Ta yiwa kanta dukka tambayar yana qoqarin lalubar number shehnaz ta kira kota WhatsApp,duk wadda ta samu.

Shuru dakin ya dauka,sai qarar zubar ruwa a hankali daga bathroom din.

"Akhnaaaannn" Kalmar ta fito da wani irin sauti tana sauka a kunnenta ta gauraya da shurun da dakin yayi. Haisam ne.....sautin ya fito can qasa amma ya mata wani irin tasiri a gangar jikinta.

Kanta ta daga a hankali tana duban qofar bathroom din. Bashi ya bayyana ba,muryarsa ce kawai.

"Hmmmm?" Ta fada a hankali.

"Can you bring me the towel?" Ya fada da tattausan French dinsa dake dake tsumata. A duk sanda zai magana dashi sai taji wani abu cikin zuciyarta da kanta ya motsa. Girarta tadan tsuke kadan,me ya hada da bashi towel indai ba neman tsokana ba?. Idanunta ya sauka cikin nasa sanda yadan leqo da idanun nasa,wataqila yanason yaga yanayinta ne.

"Mantawa kayi baka dauka ba?" Ta fadi a shagwabe,tana son dauke idanunta daga lallausan gashinsa dake digar ruwa,ya kuma kwanta sosai a gefan fuskarsa,hakan sai ya zama kamar wani ado na musamman ga kyawunsa.

"Apparently" Ya fada idanunsa suna lumshewa suna bude kansu kusan lokaci guda,akwai wani siririn abu cikin muryar tasa,kaman yana amsa mata ne da nishadi,irin nishadin da mutum keji a duk sanda zai tsokani wani.

"this French man....."

".......and his endless tricks" Ta fada can qasan maqoshinta tana kyabe fuska a shagwabe. Idanunsa ya sake lumshewa,ta masa kyau.....wani irin kyau da shagwabar tayi mata,yana jin kamar ya hadiyeta ya huta.....ko ya zauna ya lashe kayarsa tas.....saidai yanzun ba irin wanna kusancin yake nema ba. SABO yakeso.....sabon da zata nemeshi cikin kowanne motsi na rayuwarta. Kusanci zukata first kafin na gangar jiki.

Miqewa tayi a hankali ta dauki towel din dake ajiye hannun kujerar daya cire kayan nasa. Da alama ya daukoshi dinne ya manta,sai wannan ya bata nutsuwa kadan,ta kuma sakejin nutsuwa sanda ta isa bakin toilet din taga kanshi baya nan kamar dazun.

"Ga towel din" Ta fada tana dan daga murya kadan.

Hannunsa taga ya zuro,tabi fararen dogayen yatsunsa da kallo wadanda ke digar da ruwa. Miqa masa towel din tayi saitin hannunsa,sai ya matsar da hannun gefe.

"Gashi fa a ta nan" Ta fada tana sake cuna masa,saidai ya sake kaucewa gefe,kawai saita yanke shawarar kama hannun nasa ta saka cikin towel din.

Wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,sanda ta kama hannun,sai yayi amfani da wannan damar ya damqe yatsunta cikin nasa,ya kuma hade da ita da towel din ya jawosu cikin softly gaba daya ya maida qofar ya b'ameta b'am da lock.

"Haisam!" Ta kira sunansa a rude tana ware blue eyes dinta a kanshi.

"Oh my god.....say it again?!" Ya furta yana cusa yatsunsa cikin jiqaqqen sumarsa yana maidata baya saboda hana mishi kallonta sosai da takeyi.

Idanunta ta janye da sauri tana duban qofar yadda ta rufe,gaba daya bathroom din ya cika da warm steam da qamshin turarensa. Bugawa zuciyarta kawai takeyi,ta kasa kallonsa.....ta kasa daga idanunta ta kalleshi,baida maraba da mutumin daba komai a jikinsa.

Da wani irin shauqi dake fusgarsa ya tsaya a gabanta idanunsa a kanta,sanye cikin relaxed black swim pant da gurare kadan ya lullube a jikinsa,gashinsa dukka a jiqe yake daga na jikinsa har na kansa,yana digar ruwa a hankali.

"You were leaving too quickly" Ya fada da wata kasalalliyar murya yana sake samun kusanci da ita,

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 94*
_________________________
DEA’S MODEST ARTISTRY ✨
Aminataccen wajen samun
✔️ Abaya masu kyau
✔️ Lifaya & Veils masu tsari
✔️ Handmade paint work
✔️ Shadda designs
✔️ Elegant modest wears
✔️ Accessories masu kyau da inganci
Muna kawo muku kaya masu kyau, tsafta da araha domin kowane irin event 💫
Ko na daily wear, outing, wedding ko special occasions —
DEA’S MODEST ARTISTRY na tare da ke 🖤
📍Quality first
📍Affordable prices
📍Neat finishing
📍Classy & Modest styles
Ki kasance cikin kyau da nutsuwa ba tare da tsada ba ✨

https://chat.whatsapp.com/IZGMwJXP8Oa5qUc4sDSKZv?s=cl&p=a&mlu=3
__________________________

Hararsa tayi wannan karon,hararar data dauki hankalinsa matuqa. Bai taba sanin harara na yiwa idanu kyau ba.....mugun kyau me fusgar hankali ba sai yanzu.

"Ka yimin wayo ne kawai....dama ka shirya hakan" Ta qarasa maganan a shagwabe tana narke masa.

Dan tattausan murmushi ya saki yana duban wadannan unique blue eyes din nata.

"Yes" Ya furta kansa tsaye

"And I’d probably do it again.”

Kanta ta girgiza,saita rabashi tana niyyar wucewa zuwa bakin qofar fita. Softly ya tare hanyar,bada qarfi ko nuna iko ba,sai wani irin teasing closeness yana lalubar qwayar idanunta

"One minute mana" Ya furta yana karyar da kanshi.

"Haisam" Ta sake fadi cikin subutar baki ganin ya fara narke mata irin yadda ya saba. Wannan narkewar da take tuna mata amanar nanay ce shi a hannunta.....wannan narkewar da take sanyata jin kamar ta gaza kula dashi yadda nanay tace tayi.

Sunkuyawa yayi kanta kadan,ya lalubi kunnenta,sannan a hankali kamar me rad'a yace.

"You called me a gymnastic guy earlier" Dam zuciyarta ta buga,ta zaro dukka idanuwanta waje,wata irin kunya tana qoqarin narkar da ita.

"Ban fada a gabanka ba!" Tayi furucin cikin mamakin yadda akayi yaji. Dariya taso qwace masa,a komai yarintarta ke bayyana. Maimakon ta qaryata ko tayi qoqarin kare kanta...amma sai ta bashi wani hint daya tabbatar masa ta fada din. Sautin dariyarsa kadan ya bayyana,still muryarsa cool yace.

"Your face did" Bata da sauran zabi,sai kawai ta saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta cikin wani nauyi da kunya.

Da murmushi yake kallonta tana dada burgeshi,sai ya sanya hannunsa ya cire hannayen nata daga fuskarta gently

"Relax" Ya fadi a nutse.

"I just wanted a little more time with you". Ya fadi kaman yana bata daman zabi.

Wani irin shuru ya sake ratsa tsakaninsu,tana iya jin yadda zuciyarta ke zillo a qirjinta,kamar tana gaya mata cewa.

"Please.....stay with himmmm" . Shurun yaci gaba da wanzuwa,bai sakar mata hannuwa ba suna cikin nasa softly,hakanan steam din bathroom din yaci gaba da zagayasu yana ratsasu dukkaninsu.

Bayaso tace NO don haka ya mata riga malam masallaci,towel din ya miqa mata sannan yace.

"Before Nanay somehow appears in my imagination again and ruins the moment.” sai ya hade da hannunta ya dagata sama cak yana nufar bathtub da ita. Duk da a dan tsorace take amma magananshi na qarshe ya bawa akhnan dariya.

"Ka tsorata da mommy na ne?"

"I’m simply protecting my peace" Ya fada sanda dukkaninsu suka tsunduma cikin bathtub din ba tare daya damu da kayan dake jikinta ba.

Minti goma sha biyar ashirin talatin har arba'in kafin yakai zuciyarsa nesa su fito daga wankan. Bai mata komai ba......amma yayi warming up nata sosai,har bata iya hada idanu dashi. Yaja mata stool ta zauna,tana jin towel din da take daure dashi yayi qanqanta da yawa,sai mutsu mutsu take tana qoqarin rufe cinyoyinta. Inda Allah ya taimaketa towel din daya dora mata saman kanta don goge danshin gashinta dashi ta rufe kafadunta zuwa saman qirjinta,duk da bai rufu ba gaba daya amma yafi babu.

Ta dauka zai maza ya shirya ne,amma sai taga ya jawo daya stool din ya dasa a gabanta,ya kuma hau kai ya zauna da nasa towel din da iya gwiwarsa kawai ya tsaya.

Ya zuba mata wadannan shanyayyun idanun nasa da suka sake tsumuwa,cike fal da shauqin soyayyarta da sha'awar kasancewa da ita.

Kasa jurewa tayi,kashe mata jiki itama yakeyi,ga wani warm light da dakin yake bayarwa yana sauka a jikinsu softly. Ko blinking idanunsa bayayi sosai,kaman ya manta da komai dake cikin duniya. Ta motsa kadan tana tattara kalaman bakinta.

"Me kake kalla haka?." Shuru kaman bazai amsata ba,sai idanunsa still dake biye da ita da wata irin nutsuwa me nauyi.

"You"ya furta softly. Zuciyarta taji ta harba,saita dauke idanunta da sauri yanayin yana mata nauyi,ta kasa jurewa still,yana sake narkata tare da kaita wani gejin da bata zata zatakai akan kowanne dan adam ba

"Karkamin irin wannan kallon...." Tattausan murmushi ya subuce masa,ya sake rage tazarar dake tsakaninsu ta hanyar qara matsowa.

"Wanne irin kallo?" Ya tambaya kaman baisan komai akai ba. Kanta ta girgiza a tausashe.

"Kamar zaka karanta duk abinda ke raina" Ta furta masa tsoronta.....tsoron daya dade da karantarsa ta cikin qwayar idanunta.

"Maybe I'm trying to" Ya motsa lips dinnan nasa masu sulbi yana furta kowacce kalma a nutse kaman mai lissafa adadinsu. Da tsoronsa kadan da mamaki ta waiwayo,suka hada idanu,murmushin da bata shiryawa ba ya kufce mata a tausashe,abinda yasa ya qara jin kallonta kawai shine abinda yafi buqata a duk duniya a yanzu.
Chapter 105 · 0% Book details