← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 176

Sashe 80

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

".....ina fashin sallah" Ta fadi tana katse maganarsa gami da juyar da fuskarta gefe daya,don a yanzun ta bashi wannan taimakon da yace itace zata iya shine kawai a gabanta ba tare da tasan ainihin abinda yake buqata daga garetan ba.

Dif yayi.....kamar kawowa wuta da daukewarta. A hankali yaji jikinsa yana sanyi......komai kuma ya soma narkewa yana fita daga kansa.....ya barshi da wannan daurewar marar da kuma wani zazzabi da yaji yana fara kamashi. Hannunsa ya sanya ya kamo fuskarta a hankali yana dawowa da ita saitin inda yake tsaye.

"Har kwana nawa kikeyi?"

"Mene haka?" Ta tuhumeshi can qasan ranta ba tare data iya furtawa ba. Zai titsiyeta ta gaya masa abinda ita kadai ya shafa?.

"A addinance......ya kamata na sani" Ya fadi yana aza tafin hannunsa gefan fuskarta yana sake tsareta da ido.

"Gobe" Ta samu kanta da fadin hakan bawai don ta shirya fadar haka din bane. Ba yau ba ba gobe.....kwanaki da yawa takeso ta cika masa......amma batasan meye a cikin idanunnnan nasa da bata iya masa qarya ba.

Zare hannun nasa yayi a hankali yana sauke sassanyar ajiyar zuciya.

"Zaki bani magananin?,ba gurin na nanay ba" Ya sake fada a hankali yana takawa da baya da baya zuwa toilet din yana jin gaba daya duniyarsa ta tattara cikin tafin hannunta.

"Nayi alqawari.....na yiwa nanay alqawarin zan kula dakai,bada magani bazai zame min abu me wahala ba......idan na dauki alqawari,inaso naga na cika.....kaman yadda idan aka daukarmin nakeso naga an cikamin" Ta fadi a nutse tana bayyanar da wani sashe na dabi'arta da ta taba furta masa karon farko.

Ya sani,ya kuma karanci hakan cikin dabi'arta yake.....ko bata fada ba......amma a yau data fada da kanta da bakinta......sai yaji abun ya sake zama cikin kansa.

"Dabi'a ce me kyau.....haline me kyau,domin Allah ya fada......alqawari abun tambaya ne" Ya qarashe maganar yana isa bakin toilet din,sai ya juya yana karanta addu'ar shiga bandaki ya saka qafarsa a nutse.

Tana da wasu qualities.......tana da wasu dabi'u da ita kanta batasan tana dasu ba. Komai zaiyi baya yinsa kansa tsaye,....komai zaiyi yana binciken ingancinsa. Cikin dabi'unta akwai CIKA ALQAWARI. Bata iya qarya ba,kaman yadda bata iya boye abinda yake cikin ranta ba. Tana bayyana zuciyarta ne saman fuskarta koda hakan baiyi daidai da abinda mutum yakeso yaji ko ya gani ba.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 72*
____________________________
*_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________

Izzarta.....wani abu da yayi masa dari bisa dari. Mace me izza a gurin 'ya'ya maza DUNIYA CE. Zai wahala a yaudareta ko a cutar mata ta wasu hanyoyi da basu kamata ba. Zata kamewa miji kanta.....ba namijin daya isa sai MIJINTA KAWAI mallakinta. Zata bashi dukkan soyayyarta saboda shi daya ne ya cancanta ya mallaketa ba tare da wani ba.........uwa uba.........bayan izzarta,ya karanci abinda ya sake fusgarsa shine.......BA'A SAMUN ZUCIYARTA......BA'A SAMUN SOYAYYARTA.....BA'A SAMUN YARDARTA TA SAUQI.

Ya tsarawa kansa zama namijin da zai qwace daga hannun Tarin mazaje.....ba wanda za'a kawo masa ko ya samu yana daga kwance ba.... Ya zabi yayi farautar zuciya,....bawai zuciyar tazo ta sameshi a inda yake ba. A nan maganganun omar suka dawo masa.

Da gaske ne.....itace kalar macen da yakeso......ba'a halitta kawai ba ko zallar ilimin addini.....aah dabi'u. Wasu kebantattun dabi'u da ba jikin kowacce d'iya mace zaka sameshi ba.

Ya kasa son Menelik......ya kasa son saamee duk da tarin qualities da suka hada da kusanci da alaqa dake tsakani.....baisan dalilin hakan ba sai a yanxu. Saboda ya samesu ta sassauqar hanya,qila inda bayan gwagwarmaya ne kamar akhnan.....daya fada masarautarsu cikin tsakiyar yaqi ya zaqulota a tsakiyar sarqaqiyar da batasan tana ciki ba.....a hakan ma tana taurin kai da qi fadin yarda ta zama mallakinsa har sai daya cita da yaqi.....qila ya sosu suma.

Da tarin saqe saqe ya daura alwala ya baro toilet din. Tana zaune tana murza yatsun hannunta,tarin saqe saqe ne fal cikin zuciyarta. Ganin fitowarsa ya sanya ta miqe,bai kalleta ba saboda tattalin alwalarsa yakeyi yace da wata dakakkiyar murya.

"Karkije ko ina....nanay tace ki kula dani,kin manta?" Komawa kawai tayi ta zauna,shi kuma ya taka zuwa wannan corner din data gani ya sauke hannun rigarsa,ya jawo wata qaramar drawer sai taga ya fidda wata kyakkyawar farar hula irin ta larabawa ya dora saman kansa,ya tattara dukkan nutsuwarsa kamar yana fita daga wannan duniyar zuwa wata sannan ya kabbara sallar.

Yadda yake sallar a nutse haka take qare masa kallo a nutse. Karon farko data ganshi cikin qananun kaya,amma sai takeji a duniya ba wani d'a namiji data taba ganin qananun kaya sunwa kyau kamarsa. Ta rasa tsakanin jubah da cloak thobe dinsa da qananun kayansa wanne ne yafi masa kyau?.

Abu na biyu yadda yake sallarsa. Yadda yake sallarsa yana sanyata tana jin kamar tata sallar bata karbuwa.....kamar ba daidai take sallar ba,kamar akwai tarin kurakurai a cikin sallartata da abubuwan da ba'a kan daidai take yinsu ba.

Ta dauke idanunta tana sauke ajiyar zuciya sanda ya kammala sallar. Tana kallonsa,ya jima saman abun sallar yana azkar da addu'o'i. Karon farko da taji ya sake burgeta,wani iri haske da kwarjini ke fita saman fuskar tasa.

Da wannan damar tayi amfani don tasan ba lallai yayi magana ta miqe a hankali zuwa parlor.

Tana zaune ita daya daga gefe guda tana lissafin mintunan da suka kwashe cikin dakin ba motsin ko daya a cikinsu. Fitowartata ya sanyata zabura saboda wani abune da bata zata ba.

Kallo daya tak tayi mata ta dauke kai tana ci gaba da takawa zuwa saman dining. Kamar itama ta shareta.....kamar kada tace mata komai amma saita tuna bata haka ya cancanci ita ta bullo ba.

"Akwai abinda ake buqata?" Ta fadi a taqaice sanda akhnan ke buda warmers din.

Cikin ginshira da jan aji irin wanda ya zame mata jiki ta amsa mata bayan shudewar daqiqu kamar ba zata amsa din ba.

"Ba aikinki bane wannan" Ta fadi itama a taqaice ba tare data kalleta ba. Tadan jinjina kai,kamar zata sake magana amma ta kasa,saboda yadda ta amsata din da wani yanayi ne na kedin baki da muhimmanci.

"Ki danyi nesa kadan da nan,idan da buqatar za'a kiraki......." Maganar akhnan ta biyu ta saukar mata da wani irin nauyi da saida ta waiwaya ta kalleta sannan ta amsa da to. Kalmar to din data fita da qyar daga qasan maqoshinta.

Tayi matuqar qoqari wajen zuba komai a qananun bowl,cikin takatsantsan ta zuba a wani qaramin kwando,ta debi magungunan ta zuba akai sannan ta fara takawa tana komawa dakin.

Mamaki.......shine abinda ya saukar masa sanda take tura qofar dakin da kwandon a hannunta. Ya miqe a tausashe yana takawa zuwa gareta idanunsa a kanta. Wani irin kimarta tana ninkuwa a ransa.

A nan kusa,......bai taba zaton zatayi hidima haka dashi ba. Ya sani bata komai.....komai saidai ayi mata,daidai da zuba abincin,kaiwa bakinta kawai ta sani,amma a yau ta zabi ta kwatanta dafa masa shayi,sannan ta kusanto da abincinsa har daki.

"Me zata zama a nan gaba idan ta samu rainon daya dace?" Maganan data sauka a kansa kenan sanda ya isa dab da ita. Hannu yasa ya amshi kwandon idanunsa cikin nata.

"Na gode" Ya furta kalmar da wata zababbiyar murya da kuma zababbbun haruffa.

Har cikin jininta taji kalmar.

"Na gode" To me tayi masa?. Bata manta yadda yake hidima da kai kawon duba lafiyarta ba a duk sanda bata da lafiyar.

Idanunsa lumshewa kawai suke suna budewa sanda tayi zaune a gabansa tana zuba masa abincin. Daga yadda yake komai zakasan bawai ta iya bane.....amma ta burgeshi yadda bata sare ba,bata kuma gayawa kanta bata iyaba bazatayi ba. Komai tana qoqarin zubashi yadda taga nayi,tanayi kuma tana gyarawa.

Ta ballo magungunan ta miqa masa hade da cup din ruwa. Yafi fari qal din tafin hannunta da kallon wanda har kwanciyar jini sukayi saboda tsananin haske da hutu,sannan ya kalli maganin daya tabbatar ance mata yasha ne kafin abinci.

"Bazan sha ba.....banason magani" Ya fadi harda maqale kafada daya.

Karon farko da murmushi ya qwace mata,fararen jerarrun haqoranta qal qal kamar qanqara suka bayyana,abinda ya sake jan hankalinsa kenan.

Kaman shi?,da girmansa amma yace bayason magani?,kai tana tantama ma.

Murmushin daya burgeshi,ya kuma daukeshi ya kaishi wata duniya ta daban. Sai yaji kamar zazzabinsa yana sake ninkuwa,wani abu yana sake kwance masa.

Tafin hannun ta maida ta kulle batace komai ba,ta jawo wayarta tahau kiran da baisan wa ta kira ba,har sai da muryar rumaisa ta bayyana.

"Da gaske ne......bayason magani?" Iya abinda tace kenan,rumaisa kuma ta gane inda zancan ya dosa. Dariya sosai rumaisa ta saki.

"Giiftii.....sai kinyi haquri da obbo.....jinjiri yake komawa nanay idan baida lafiya......bayason magani,gwara a masa allura ko nawa ne da ki bashi tablet yasha. A kan cinyar nanay yake bacci......a nan kusa da ita,itama haka take jinyarsa kamar wata noorah......shagwababben nanay ne".

"Na gode" Akhnan ta fada gudun kada rumaisa ta b'aro wani maganan,don tana kallonsa sanda ya sauko ya dawo dab da ita ya zauna,zai kuma iyajin komai da rumaisa din zata fada.

Tana kashe wayar suna hada ido.

"Tunda an tona miki asiri na.....dole ki zama copy din nanany" Ta fada a tausashe,kafin kuma tayi kowanne yunquri yayi male male saman cinyarta.

Kwanciya yayi rigingine,idanunsa akan fuskarta,tadan shagwabe fuska

"Idan ba zakasha magani ba....."
Chapter 80 · 0% Book details