← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 176

Sashe 28

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin kariya takeji tako ina.....wani irin aminci da tsaro irin wanda bata taba jinsa ba tunda take zuwa umara,koda kuwa da hadimai guda nawa zatazo. Bata sake jin an matseta ba tun matsewar farko,bata sake maimaita kowacce addu'a ba sai addu'o'in da suke fita daga bakinsa cike da wata irin nutsuwa,addu'o'in da koda batasan ma'anarsu ba......amma tana jin wani gamsuwa da aminci a cikin maimaitasu.

Zagaye bakwai me cike da wani irin yanayi.....zagaye bakwai me cike da wani sirrin aminci da nutsuwa da bata taba sanin akwai irinsa ba.

Suka tsaya cak,tsill hannunsa cikin nata. Akwai rangwamen cunkos zuwa sannan,saidai hakan bai hana cunkuson masu son zuwa gaban ka'aba. Hannunta ya saki a hankali,sai ya riqe tsintsiyar hannunta yana zagayo da ita gabansa.

Qugunta ya riqe da hannunsa guda daya,a hankali ya sanya idanunsa cikin nata,sai itama ta daga blue eyes dinta tana ajesu a nasa. Wani irin abu ya sauka saman zuciyar kowannensu,wani abu me nauyi taji yana taba zuciyarta da wani irin yanayi data gaza fassarashi. Kallon ido cikin ido da qaramar tazara irin wannan.....tazarar da hatta da numfashin junansu musayarsa sukeyi,tazarar da take iyajin yadda jikinsa yake gogar nata,tazarar da ta fara gaban babban daki.....babban gurin da babu irinsa,tazarar da ta sanya wata nutsuwa a ruhinta....wannan tazarar da taji a karo na farko ba wata tazara mai qaranci da muhimmanci irinta.

"Es-tu prête?(kin shirya?)" Ya furta yana motsa labbansa da suka janye hankalin Akhnan sosai,sannan cikakkiyar girarsa guda daya tana dagewa sama. Sai data lumshe idanunta a hankali,tana jin wani yanayi na daban yana ratsata. Tayi qoqarin motsa labbanta amma ta gaza cewa komai,sai kai ta daga masa a hankali.

Shima da idanu ya amsa mata,kallon daya sanya taji wani abu yana narkewa tun daga zuciyarta yana kwaranya a gangar jikinta gaba daya.

Ba zato taji yasa hannuwansa biyu ya rabata da qasa. Tadan tsorata har batasan sanda ta riqe faffadar kafadarsa ba. Hannunta ya sauka saman lallausar fatar kafadarsa......laushinta ya hadu da taushin nata tafin hannun. Saman qafafunsa taji ya dora tafukan qafafunta bayan ya juyata,bayanta yana cikin qirjinsa,ya saka hannuwansa ya zagayesu saman cikinta,ya mata kyakkyawar garkuwa da dukkan jikinsa. Ta yadda ba wani abu da ya isa ya tabata.......a yanayin da ba wani abu da zai kusanceta muddin ba gangar jikinsa ba. Habarsa ya dora saman kafadarta,da wani kusanci sosai cikin muryarsa a tausashe yake fadin.

"Zaki tafiya saman qafafuna....zamu qarasa gaban ka'aba kiyi addu'a.....gurine me muhimmanci sosai.....gurine na amsa addu'a da dukkan buqatu.......zakiyi alqawari?". Sauka kowacce kalma take daga bakinsa kai tsaye zuwa kowane sashe na jikinta,saqon da dukka maganar suna ratsata. Alqawari daya fada ya sanyata bude idanunta dake lumshe tunda ya fara maganan,bata motsa ba,amma yaga alamun bude idanun nata.

"Zaki sakani cikin addu'arki?" Ya fadi maganan yana kaiwa qarshenta da wani irin numfashi me nauyi. Shuru kawai tayi.....tana jin sautin bugun zuciyarta ta cikin kunnuwanta. Zata sashi a addu'o'inta kamar yaya?,bata fahimta ba,ba kuma zata iya tambaya ba. Abu daya ta sani.....zai mata wani abu da zai shiga sahun tarihinta.

"Kinyi alqawari?" Ya fada yana dan matsa qashin qugunta kadan ba tare da yasan yayi hakan ba. Kai ta daga a hankali ba tare data shiryawa hakan ba.

Qafarsa ta farko ya cira,wani tsoro ya kamata taji kaman zata fadi,saita manne bayanta sosai da jikinsa tana riqe hannuwansa dake qugunta.

"Ki tsaya" Ya sake fadi kaman me rada a hankali muryarsa na sauka da wani irin sanyi.

"You're safe.......kina tare dani" Ya sake maimaitawa. Sai taji ta aminta dashi din.....ta aminta da maganarsa,sai taji ta saki jikinta hankali kwance. Yana takawa a hankali da ita,mutane na wucewa ta gefansu amma tana jin kamar komai ya tsaya. Da dukka jikinsa ya bata kariya,yana kutsawa da ita da wani irin qarfi na zuciya da hikima ba tare da cutar da kowa ba har suka isa gaban ka'abar.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Sauketa yayi a hankali daga saman qafafunsa,ta sake takawa ta matsa zuwa gaba,bai matsa daga bayanta ba,sai ya sanya hannuwansa ta gefe da gefan kafadunta yana dafe bangon ka'aba dashi,yayi mata wata ingarman rumfa da gangar jikinsa,ya lullube bayanta da kyau da jikinsa,ya kuma samar mata da space din da zai wadaceta tayi addu'a.

Hannunta ta dora itama saitin nasa tana dafe ka'aban. A karon farko kenan,duk da shekarun data dauka tana zuwa. A karom farko ta sanadinsa,da dukka wata kariya da zai iya bata ya sadata da dakin. Sai taji wani hawaye me dumi yana saukar mata,ta masa a hankali ta sumbaci hajarul aswad,ya sake matsawa da ita gefe kadan,ta saka bakinta fa sumbaci ka'aban,kafin ta dauke kanta ya sake manneta cikin jikinsa,ya kuma zuro kansa ta kafadarta,abinda ya hanata iya dagowa kenan,sai tabar fuskarta a jikin dakin tana sauraren fitar numfashinsa,dumin jikinsa,da sautin addu'o'in da ba zata iya tantance abinda yake roqa ba.

Wani yanayi ta jita a ciki,irin yanayin da yafi kowanne yanayi yi mata dadi cikin duniya. Ya zareta a hankali ya riqe qyam cikin jikinsa yana sake zareta daga turmutsitsin.

Sallah sukayi raka'a biyu daga nesa kadan da ka'aba din. Saita samu kanta da cikar hawaye a idanunta. Ta daga hannuwanta ta rasa me zata roqa?. Bayan addu'a data sakewa sultane,a yau saita samu kanta da yiwa mamarta addu'a.

"Ya Allah,kayi mata rahama.....ka shafe kurakuranta......ka yafe mata zunubanta Allah" Saita dakata,tana tuna me zata roqawa kanta.

"Allah......ka......" Kasa qarasawa tayi,tana juya abinda zuciyarta ta raya mata ta roqa din,ya cancanta?,ya kamata ta roqi wannan kuwa?. Wannw tabbaci take dashi?,wanne yaqini take dashi?. Bata da dukkan wata makama......bata da dukkan wani qwarin gwiwa nayin addu'a akan wannan.

Daga inda take zaune tana iya ganinsa. Tsaiwarsa a sallah......ruku'unsa dama sujjadarsa. Komai nasa sai take ganin yana da wani irin banbanci da wanda ta sani da kuma wanda ta saba gani.

Yadda ya zauna saman qafafunsa,cikin wani tawali'u da qanqan dakai,ya hade dukka tafukan hannayensa,ba wani sauran izza a tare dashi.....ba wata qasaita....sai zallar nuna miqa wuya ga ubangiji,sai taji itama tata zuciyar tana karyewa. Kuka kawai taji tana son tayi,ba tare da tasan dalili ba,sai kawai ta cure guri daya,ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tana bawa hawayenta daman sauka yadda sukeso.

Ta dauki mintuna aqalla ashirin a haka......a hankali taji kaman qamshinsa a kusa da ita.....a hankali takejin kamar akwai wani kusanci na daban a tare da ita,sai ta soma qoqarin daidaita kanta da sassauta kukan,kafin a hankali ta soma qoqarin daga kanta.

Shine a zaune a gabanta,da wani irin coolness ya zuba mata manyan idanun nan nasa. Kallon ya mata nauyin da ba zata iya jura ba.

"Kiyi addu'a......guri ne na bayyana dukkan damuwa da samun waraka". Sai ya miqe a hankali ba tare da yace komai ba. Maganar ta tsaya mata a rai,tayi qasa da kanta a hankali tana bawa zuciyarta daman ambatar dukkan abinda take buri da muradi.

Karo na biyu ta sake ganin an miqa mata cup,ta daga idanunta a hankali. Shine ya dawo,yana tsugunne saman qafafunsa da cups guda biyu masu cike da zamzam mai sanyi.

Batayi musu ba ta miqa masa hannun,yatsunsu suka hadu da juna,sai ya zare hannunsa a hankali. Kauda kanta tayi tana juya yadda zata sha ruwa a gabansa,yana zaune dab da ita,idanunsa ta tabbatar kuma suna cikin nasa. Kamar yasan me take tunani,kamar yasan abinda yake ranta,sai ya matsa gefe kadan yana zama sosai saman tiles din masallacin.

A nutse ta shanye gaba daya,sai taji wata nutsuwa tana saukar mata a hankali. Ta sake satar kallonsa,baya komai don ya nuna kansa.....amma komai qoqari yake ya nuna wayeshi. A yanzun tana jin kawai kamar binne kansa yakeyi......tana jin wani binnnan mutum ne kawai suke rayuwa dashi,ba ainihin haqiqanin sheikh haisam na agadez ba.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 27*

Ba a nan kawai ba.....sanda suke takawa a hankali ita dashi,tana daga gefansa.....iskar dare me tarin nutsuwa da wani irin sanyi tana kadasu. Kusan dukka inda sukebi kamar abun shiri,ma'aurata ne guri guri cikin yanayi na soyayya da zai dauki hankalin duk wanda ya gansu.

Wasu a kwance daya yayi pillow da cinyar daya......wasu a zaune suna hira......wasu karatun qur'ani.....wasu kuma dukkansu bacci suke kusa da kusa da juna,yayin da wasunsu kuma suke maqale da hannun juna suna tafiya zuwa gurarensu.

Idanunta yawo kawai yakeyi a kansu,haka kawai takejin komai yana burgeta,haka kawai takejin yanayin duk da take kalla yana burgeta.

Ba soyayya sam cikin tsarinta.....saboda ba kalan namijin da takejin yakai ya mallaketa......amma a yanzun batasan me yasa couples din suke burgeta ba.

Qarar da yaji wayarsa tayi ta Bluetooth din dake kunnensa shi ya sanyashi cirota daga qaramin wallet din hannunsa.

Beeno ne ya ajiye masa saqo,wanda ya tsara saqo kawai dama banda kira har sai sun kammala umara.

_muhammad ya damu.....yanason yaga 'yaruwarshi tunda ya rasa mamarsa_ shine kawai saqon. Wani nauyi yaji ya sauka a ransa,tausayin yaron ya kamashi,sai ya maidawa beeno din amsa a taqaice.

_ka bashi haquri,zasu hadu a Ethiopia_

Daga can wani sashe na daban take kallonsu,yana kwance saman cinyarta da alqur'ani a hannunsa,ita kuma ta tura yatsunta cikin sumarsa tana hargitsata a hankali tana kuma biye da sautin karatun nasa. Sautinsa ne sama da natan,amma dukka sound dinsu ya cakude ya bada wani launin qira'a me dadi.

Batasan me ya saukar da murmushi saman fuskarta ba......sannan ya fusgi hankalinta zuwa ga kallonsa don taga ko shima ya gani?. Still idonsa nakan waya,wani abu taji mara dadi ya tsaye mata,saita janye dubanta a kansa ta maida kansu,daidai sanda shi kuma ya juya a hankali yana dubanta da wani yanayi da zai wahala ka gane ita yake kalla.
Chapter 28 · 0% Book details