← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 176

Sashe 152

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga ranar yake wani kaffa kaffa da ita,kaffa kaffan da batasan dalili ba. Ya qara ninka yawan kulawarsa a kanta,Komai bayaso tayi. Ko fita sukayi tattaki cikin saharar....tafiya kadan take gajiya,sai ya zamana yana lissafe da sanda take gajiya din. Da sunkai wannan gejin zai tsaya ta huta.

Abinda kawai ta yarda dashi bata da lafiya,normal rashin lafiya. Inda zaka tambayeta kawai zatace rashin kuzari ne yake damunta. Sannan kuma tana yawan gajiya,uwa uba yanzun ba Komai takeso ba.... Ta zama me zabe zaben abinci,da launikan qamshi daban daban. Amma wannan qamshin nasa.....har yanzu ba abinda ya girgizashi a zuciyarta.

Yaso ma suyi using the sam perfume,amma ta girgiza kai tana lumshe idanunta.

"A jikinka kadai nake buqatar jinsa......zanci gaba da jinsa a gurinka kai kadai" Ya saki lallausan murmushi yana yin qasa da idanunsa.

★★★Kwanakinsu a amangiri resort wasu irin kwanaki ne da bazasu taba gogewa daga memories dinta ba. Bata taba ganin guri me tarin nutsuwa a duniya irin gurin ba. Zaka rantse da Allah ku kadai kuke rayuwa,don duk kwanakinsu a gurin sau biyu kawai ta taba ganin wasu couples. Kowa rayuwarsa yakeyi cikin suit dinsa.

*MORNING POOL*

Waya dasu rumaisa ne ya kaita gurin a safiyar.....mutanen da kulli yaumin saisun kirata sun tambayeta yaushe zata dawo jimma,don already sun baro agadez. Agadez din data musu dadi kaman ba zasu koma gida ba,saidai kuma an qulla babbar alaqa tsakanin sarki ahmad da rumaisa. Don tana kyautata zaton abune da bazai dauki dogon lokaci bama. Hakanan Aanani,sun dinke da muhammad. Da farko dabara ya mata akan ta zama malamarsa,yana zuwa daukan karatu,sannu a hankali sai taga karatun da yake zuwa dauka nasa ya zarta nata,ashe zuwa karatun nasa akwai manufa.

Ba ya wannan abun ya tsaya ba......Aisa da shehnaz........duka rumaisa ta fara qyasa mata. Khadeem dama da tuni ya nuna ra'ayinsa akan aisa. An riga an gama magana. Hakanan shehnaz,wadda dama anata kai ruwa rana tsakanin mahaifansa. Mamarsa shehnaz takeso,babansa kuma ya zaba mata wata,daga qarshe sultane ya yanke ya haqura gaba daya kawai zaifi kwanciyar hankali. Ana yin hakan mutallab ya sako kai..... Ba sabo ko shaquwa tsakaninsu.......amma kunya da nauyin haisam ya sanya ta bashi dama. Sai a sannan ta gane ashe sakiyar da ba ruwa takeso ta yiwa kanta.

Sunata mata nuqu nuqu,ita kuma tace ba zatace komai ba sai sun fito sun gaya mata da kansu. Sannan zata wankesu tass ta rama tsiyar da suka mata,duk da tuni taji zancan har a bakin haisam. Kar tasan kar ne,sunsan halinta,saita rama duk wata tsiya da suka tabayi mata.

A nutse take takawa a gurin,desert sunlight na shiga glass walls da infinity privaate pool din villa din nasu dake gabanta suna haske mata idanu.

Koda ta gama wayan zama tayi a nan,a bakin ruwan tana shaqar daddadar iskar saharar dake tuna mata da agadez. Ta baro haisam a ciki yana amsa waya shima.

Ta danyi nisa kadan cikin tunanin rayuwa. A hankali taga inuwarsa tsaye a bayanta daga poolside.

Takowa yayi yana dawowa ta gefanta,inda zaifi ganinta sosai. Ya zube lumsassun idanunsa da kullum ta kallesu abu daya suke gaya mata.

"Ina buqatarki.....na har abada a cikin rayuwata" Yana sanye da baqin trouser da tshirt me laushi me gajeran hannu,itama baqa. Ta zauna masa sosai a jiki da wani kwantaccen kyau. Tunda sukazo gurin bashi da wata sutura sai irin wadannan kayan. Three quarter short ko long trouser da sauransu.

Kallonta yake tana sake kwanciya saman ransa. A kwaakin wani glowing take qara yi,abinda ke qarfafa zarginsa a kanta kenan. Duk da har yanzu taqi bada hankalinta da gangan bare ta fahimci abinda ke gabanta. Zai qyaleta,har sai sanda komai ya mata ba zata. Dariya me laushi takan qwace masa a duk sanda ya hango ranar.....ranar da zatayi realising tana dauke da baby. Yana iya nasa qoqarin gurin bata kulawa da kariyar daya dace ace ta samu.

“You keep staring.” ta fada tana tura baki gaba kadan.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 139*
__________________________
*_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________

“You keep giving me reasons to." Ya amsa mata calmly yana sunkuyowa kanta kadan.

Hannu ta saka a cikin ruwan wanda ta tsoma qafafunta a ciki,ta debo kadan a hannunta ta dan watsa masa.

Sai ya tsaya still,then slowly ya cire agogon hannunsa.

Akhnan ta zaro ido da sauri

“Haisamm" Da wannan muryatata da kullum zata kirashin kashe masa jiki takeyi.

Saidai it's too late daga sanda ta kirashin,don tuni ya shiga pool din straight toward her. Calm.....focused.....dangerously.....attractive

Ta soma ja da baya tana dariya da wannan sautin nata dake shagaltar dashi.

“No.....don’t start.” ta fada tana qoqarin zame qafafunta don ta samu ta gudu.

“You started it.” ya fada da low voice dinnan nashi me zurfi.

Ya samu nasarar kamo hannunta gently,ya kuma jawota cikin ruwan,sannan ya sake matso da ita cikin jikinsa. Close enough da zataji numfashinsa.

“You’re happy here.” ya fada yana kallon blue eyes dinta daya cika da tsoro,da digo digon ruwa daya barbazu saman fatarta me santsi da sheqi,wadda sabulun Mg's skin product ya sake karbarta sosai.(806 299 1549).

Ta kalleshi da wani zuzzurfan kallo sannan ta gyada kanta.

“I’m happy anywhere…”

“…you let me rest.”. Wani irin softness ya bayyana a idanunsa,sai ya dora goshinsa a nata.

“Then rest with me forever.”

Kai tsaye bedroom suka koma bayan gama wankan,saidai suna shiga wayarsa nata ruri tana maimaitawa,sai ya taka zuwa gaban madubi ya dauki wayar.

"Omar" Ya furta a fili yana zama saman sofa ya daga kiran ya sakata a hands free gami da yin cikakkiyar sallamar nan tasa.

“Omar.” ya kira ssunansa Shiru,sai muryar Omar ta fito qasa qasa da wani canji a cikin ta

“Haisam…”ya kirashi da wani yanayi,nan take idanun Haisam suka dan sauya. Dukkaninsu suna iya gane yanayin junansu su shidan daga muryar 'yan uwansu.

“What happened?” daga daya bangaren......numfashin Omar ya fito a hankali kafin ya amsa.

“Mammina ta mutu.” maganan ya maqale cikin iska yana yawo.
Akhnan da ke gefen gadon ta d'aga kanta kamar me ciwon wuya.

Haisam bai motsa ba. Ko qyafta idanunsa baiyu ba na wasu seconds.

“Sun same ta a daki ta rataye kanta.”

“Ta bar letter.” omar ya sake fada

"Ta rubutata da manja na abincinta da tsinke."

Wani irin shiru ya cika suite din har Akhnan ta fara jin zuciyarta na bugawa.

A hankali Haisam ya juya baya ga glass wall din.

“Omar.” kafin yace komai omar yaci gaba da bayani.

“She didn’t wait for trial.”

“Ta ce bazata jure humiliation ba,ba zata juri qasqanci a idanun maqiya ba"

Haisam ya rufe idonsa na second guda. Ba wai saboda shock kadai ba......sai saboda ya san Mammina......ya san pride dinta. Ya san yadda take kallon duniya. Baya ga haka.....girman nauyin data daukawa kanta,bata tsaya an sauke mata shi ba tun a duniya.....bata tsaya an rage mata nauyinsa ba.....ta sake daukar wani gangamemen nauyin,nauyinma cikin haqqin Allah me gaba daya.

Har yanzu haisam ya gaza cewa komai,tsigar jikinsa kawai ke tashi. Ba don komai ba.....sai don hasaso nauye nauye daki daki dake rataye a wuyan mammina. An yankewa tamim dama dukkan wanda aka kama da laifin kisa hukuncin kisa. Masu cin amanar qasa kuma an musu nasu hukuncin daidai dasu. An saki yalwa bayan an horata,an kuma koreta kwata kwata daga masarautar agadez ba ita ba rayuwa a cikin ta har abada.

Omar ya sake magana cikin gajiya.

“The letter is mostly for you.” A hankali yatsun Haisam suka matse kan wayar,ya sani....zata rina....zata aikata. Ya sani duk duniya haushinta a kansa ne,koda ta mutu salin alin....zuciyarta zata tafi lahira ne da burin daukan fansa a kansa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Akhnan ta mike tsaye ta kasa zama jin zancan letter da kuma sunan haisam. Tana kallonsa. Something about his face changed.
Ba tsoro ba.......ba tashin hankali ba.
Sai wani heavy stillness.

“I’ll call you back.”Ya kashe wayar a hankali,sai ya rubuta masa gajeran saqo akan yayi scanning paper din ya aiko masa da saqon.

A yanzu bayason duk abinda akhnan zataji da zai sanya ko yaya ta kwana ba cikin farinciki ba. Ya gaji hakanan,bayaso taji komai idan ba alkhairi ba. Sunan mammina da case dinta wani abune daya kamata ace an rufe babinsa har abada. Zai roqa mata rahama da sassauci gurin Allah,amma baya ga haka,baida wani power akan lamarinta,wannan tsakaninta da ubangijinta ne.

“Haisam…” Bai amsa ba nan take.
Sai ya ajiye wayar a hankali kan table.

Ta matso kusa da shi,a hankali ta kamo hannunsa cikin nata.
Ba wai saboda ta san abin da zata ce ba.
Sai saboda suddenly… bata son ya tsaya shi kadai cikin wannan silence din.

"Shikenan.” ta furta tana lumshe ido kad'an

“Komai ya wuce…” sanda ya rigata sake magana muryarsa ta yi qasa sosai.

“Komai ya qare.” ta sake fadi itama.

Kalmar ta tsaya a tsakaninsu cikin nauyi....ba wai yana magana akan Mammina kadai ba. Yana magana akan rikice-rikicen da suka bi su a bayan rayuwarsu.

Akhnan ta kalleshi cikin nutsuwa,sai ta ga abin da bai taba furtawa ba.

Ya gaji.....ba da komai ba,sai da abinda dukka ya shafi mammina.

A hankali ta matso kusa da shi.

“Haisam…” kama fuskarta yayi cikin tafukan hannayensa ya sauke goshinsa a kanta na second guda. Sai ya rufe idonsa yana furta

“I just want peace now.”
Chapter 152 · 0% Book details