Sashe 89
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karon farko da yaji wani nauyi na kallon idanun nanay.....a yau din sai yaji kallo dama idanuwan nanay din kamar daban suke da kallonta na baya. Tunda ta qarashe maganan idanun cikin nasa.....hakan yana gaya masa shi takeso ya amsa mata tambayar bawai diyartata ba.
Shidai wayarsa baisan inda ya jefata ba,tun daga sanda suke magana da omar maganar da har yanzu ba'a kammalata ba,har zuwa yanzu bazaice ga inda take ba. Tata wayar ma bai ganta ba ballantana ya fadi inda take.
Samun kansa ya kawai da aza hannunsa saman sumarsa yana shafawa,ya sake taku biyu yana qarasowa gaban nanay din,da wani yanayi daya sanya Akhnan satar kallonsa ta qasan idanu sanda yake gaida nanay din.
"Da gaske ne" Ta fadi a ranta,da gaske shi din shagwababben nanay dinne......da gaske ne shalelenta ne,kusanci qauna da shaquwar da take gani a tsakaninsu yana sanya mata wani shauqi.....yana sanya mata burin cewa Dama tata MAHAIFIYAR tana raye,yana saka mata jin dama haka rayuwa tsakanin uwa da d'a take?......me yasa wannan qaunar me zurfi......wannan yanayin gaba daya bata ganinsa tattare da MAMMINA?.
Ta nuna mata kulawa a komai nata.....amma wannan kallon....wannan shauqin da take gani cikin idanun nanay zuwa ga haisam ita bata taba ganinsa tattare da mammina ba.
"Me yasa?" Ta yiwa kanta tambayar da kafin ta tsaya laluben sharhi ko amsarta muryar nanay ta ratsa kunnenta.
"Zuna diyata". Idanunta ta dawo dashi kansu,sai taga ya zauna shi. Ya zauna kusa da nanay kamar qaramin yaro,saitin qafafuwanta irin zaman da hadimai keyi gabam shugabansu.
A hankali ta zauna,yanayi daya sanya Nanay sake kallonta sosai tana qara jin zargi cikin ranta. Dauke kanta tayi a hankali,tana jin wani abu cikin ranta,wani abu me kama da nauyi. Inde abinda take zato ne yayi.....indai zarginta ya tabbata da gaske.....lallai ya shayar da ita mamaki kaman yadda motii keta mata dariya tun jiya.
"Balqees taso kuyi sallama.....komawar gaggawa ta sameta....amma bata sameku ba" Ta qara magana taka duban Akhnan.
To me zatace?,bata data cewa,hasalima yadda nanay ke kallonta a yanzun gani take kawai ta dago komai. Sam batasan ya hana shiga da fita ba kwata kwata a sassan.
"Barka da warhaka obbo" Saamee tayi namijin qoqarin fada tana danne abinda yake taso mata.
"Barka kade" Ya amsa mata saidai idanunsa akan Akhnan wadda ke murza yatsunta da wani irin yanayi na rashin sakewa. Yawu ta hadiye da qyar,karon farko data taba ganin tozarci irin wannan. Me gaisuwa daban,wanda ake kalla a amsa gaisuwa daban.
"Ya jikin naka?,nayita zuwa don na duba lafiyarku da abincinka......amma sun sanarmin,....."
"Ba maijin yunwa a cikinmu.....banason dogon hayaniya saboda zazzabi na tashi,shi yasa na bada wannan umarnin" Ya bata amsa wannan karon yana maida dubansa kanta. Maganganunta kawai ji yake suna katse masa jin dadinsa,yana jin kamar suna masa shishshigi ne dason hanashi morewa satar kallon Akhnan,wadda suke magana qasa qasa ita da nanay ba tare kuma da yasan me suke cewa ba.
A yanayinsa.....taga amsawar tasa batayi daidai da maganarta ba. Kamar dai wanda akewa dole. Anya zata iya?,anya ba zata canza salo ba?.
Ta dan lumshe idanunta tana tuna wani abu guda daya da yake tattark hankalinsu a kanta. Rashin lafiya.....inde zata kwanta bata da lafiya zata samu dukkan tattali da kulawa.......inde tana jinya cikinsu ba wanda hankalinsa baya kaiwa kanta. Ba zata kwanta ba kuwa?. Cak tunaninta ya tsaya akan wannan shawarar,saita zame kyakkyawan jakar ledar turaren daga cinyarta tana ajiyewa gefe,abinda yadan dauki hankalin nanay kenan.
"Lafiya?" Ta tambayeta ganin tana shirin tashi.
"Kaina yake dan ciwo kadan kadan,zanje nasha maganina ne" Shuru nanay tayi tana dan dubanta.
"Amma kin shanye wadancan magungunan kuwa?" Qasa tayi da kanta tana murza yatsunta,irin wannan kulawar take buqata daga gurin kowa,wannan kulawar takeso ta yiwa nanay jagora wajen sanyashi fuskantarta da nufi na aure.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 80*
_________________________
https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee*
___________________________
"Saura kadan" Kai ta gyada.
"Ki kammala shanyeshi,indai har jikin bai sauqi ba wannan karon asibiti kawai ya kamata ki fita gaba daya" Ta fada kulawa.
"To in sha Allah.....na gode" Ta fadi tana rusunawa sannan ta fara takawa tana fita a gurin. Kunnuwanta da zuciyarta cike da burin ko sau daya yace.
"Allah ya baki lafiya.....sannu.....ki kula da kanki....kisha maganinki.....ki.kwanta ki huta.....ki rage damuwa" Saidai a maimakon hakan ma,a daidai wannan lokacin idanunsa suna kan Akhnan din.
Maido idanunta nanay tayi kansu,sukayi kyakkyawan gani,yadda ya nutsu ya tattara hankalinsa dukka akan motsinta. Yakai hannunsa don gyara mata gashinta daya sauka gefen fuskanta,sai ya janye da sauri jin motsin nanay din.
Itama basarwa tayi,tayi kamar bata gani ba.....tayi gyaran murya tana cewa.
"Ga turare daga balqees,satin gaba zata dawo.....nima wucewa zanyi yau din ina da baqi......" Ta furta tana miqewa.
A hankali Akhnan din ta miqe,cikin ranta tana jin Kamar ta bita.
"Jikin naka kamar yayi kyau......" Ta fada tana dubansa cikin tsakiyar idanunsa. Ya sani.....yasan nanay dinsa,ya santa sarai wajen saurin gano abubuwa,yana jin nauyin kallon da take masa sosai,to amma bazai bari ta sake rabashi da ita ba sam,bazai dauka ba. A yanzun bayajin akwai wani abu da zai bari ya shiga tsakaninsa da ita har abada.
"Da sauran zazzabin nanay" Ya fada da wannan yanayin da zuwa yanzu Akhnan ta saba ganinsa tattare dashi. Yanayin nan na narkewa.....sangarta da shagwabewa nanay din. Da gaske kaman yadda ta gaya mata ne.....yana komawa tamkar wani qaramin yaro ne wanda baida kowa sai mahaifiyarsa.
Idanunta ta janye.....can qasan ranta tanaso ta tafi da Akhnan ne.....tanason ta cika kwanakin da sauran abinda ta tanadar mata,tana tsoron wannan kallon da take gani akan yarinyar cikin idanunsa,amma haka kawai saita kasa cewa komai,ta rufe da fadin
"Allah ya qara lafiya" Dan qaramin qayataccen murmushi ya subuce masa.
"Babu kamar nanay" Ya fada can qasan ransa yana jin wani abu yana ratsashi,amma a fili sai yace.
"Ameen,na gode,Allah ya qara girma,zan kawota da kaina zuwa goben idan na samu sauqi". Dan tsaiwa nanay din tayi,tana jin maganan nasa kamar ba asalin saqon dake cikin maganar take isarwa ba. Shima ya lura da hakan,da sauri ya koma zuwa ga kalaman daya furzar a yanzun,sai ya tsinci wani dan nauyi kadan a cikinsu.
Tattaki suka fara mata shi da Akhnan din,saidai suna zuwa qofar qarshe yasa hannu ya jawo Akhnan din baya a tausashe nanay ta qarasa fita.
Hannu ya sanya ya maida key din qofar ya murza idanunsa cikin na Akhnan din dake tsaye suna facing juna,har ya kammala saka key din sannan ya riqe qugunta dukka biyun still yana duban wadannan blue eyes din da shima a yau yaga sun qara haske.
"Bakiji kunyar cin amanar data bar maka ba?" Ta fada da wani tausashen harshe da lafuzzan nata suka zame masa kamar wata susa a inda yake masa qaiqayi.
"That may be my favorite sound.” ya furta muryarsa tana narkewa da salo na rada da wani sauti can qasa da kunnuwanta kawai ya lamuncewa taji,yana maganan idanunsa suna lumshewa tare da budewa gaba daya.
"Inda na fada mata zaka iya kare kanka ne?" Ta sake fada idanunta suna sake hada qwalla,tana kallon yadda yake qare mata kallo tsakanin idanunta da lips dinta dake juyawa a hankali.
"…what a beautiful sound.” ya sake fada cikin harshen faransanci yana jin yadda muryarta tayi too soft. Maganan da yakeso ta masa.....a yanzun ya sameta,sai yakejin kamar ya riqe lokaci su tabbata a haka ita dashi.
"Hais......" Dakatawa tayi ta kasa qarasa fada. Daren jiya.......daren jiya ne ya dawo cikin kanta,daren jiya daya buqaci ta maimaita sunan,kuma tayita maimaitawar cikin rashin sani.....daren jiya da furta sunan ya ajiye mata wani rubutaccen tarihi.
Bugu da qari a yammacin yau sai taji sunan ya mata nauyi,sunan ya mata nauyi a harshenta.....sunan ya mata wani daraja da bata taba jinta kusa da ruhinta ba.
Ya sani.....ya fahimta sunansa takeson fadi amma ta katse,tun kafin ta qarasa idanunsa suka fara sauyawa. Tun daga jiya yafara qaunar jin sunan daga bakinta. Tun daga jiya yakeji duk duniya a bakinta kawai yakeso yaji sunan.
Jawo qugunta ya sakeyi zuwa jikin nasa da wani irin kusanci me barazana ga bugun zuciya dama na qwaqalwa.
Tana jin yadda idanunsa suke kanta,tana jin yadda suke musayar numfashi da wani kalar qamshi da hatta a numfashinsa shine cakude a cikinsa.
"Say it" Ya sake fada da wannan coolness din,idanunsa suna lumshewa sosai yana kallonta ta qasan idanun nasa.