Sashe 116
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana zaune daga bakin skyline view din,sanye da wata cotton gown me dogon hannu,budaddiya me zuwa hade da wani irin tattasau mayafi. Gabanta cup ne dake dauke da coffee wanda ke fidda tururi a hankali. Fuskarta tayi wani irin fresh,tayi kyau,tana jin gajiyar taron da wadda haisam din ya hada mata daren jiya tana sauka daga jikinta a hankali.
Saidai kuma can qasan zuciyarta.....can cikin ruhinta sam ta rasa walwalar data dauka zata tashi da ita.
A cikin jikinsa jiya tayi mafarki,mafarkin daya razanata matuqa. Taron jama'a anata kuka,sultane yana tsaye a tsakiyarsu sanye da fararen kaya yana lallashin kowa.
Shi ya riqeta a jikinsa sosai harta samu nutsuwa,ya karanta mata addu'ar da akeyi idan akayi mummunan mafarki ta maimaita,ya hanata ta gaya masa me ta gani saboda haka sunna ta koyar,saidai ya sanyata ta shiga toilet ta sake alwala ta dawo ta canza side din data kwanta dazun kamar yadda annabi ya koyar.
Yanzun mafarkinne ke mata yawo cikin kai. Ya lura da yanayinta,shi yasa yau ko suite din nasu bai bude ba. Ya hana kowa ganinta,shiketa hidima da ita har mamaki da nauyinsa yana kamata.
"Kaman ba wannan sheikh muhammad haisam din na duk duniya ba". Ko coffee din dake gabanta yanzu shi ya hada mata,ya kawota nan wani guri na musamman me kama da farfajiya daga gaban benan nasu ta zauna tana hangen gine gine qananu daga qasa. Taga saqon falaak kan sun wuce ita da maleek,bata zaton su shehnaz sun wuce don jirgin yamma kamar zasu bi.
"Hello princess" Taji ya fada da muryar nan tasa da take mutuwar so. Idanunta ta dauke daga inda take kalla da zummar dubansa,amma kunyar daren jiya ta hanata,saita buge da sauke idanunta akan wayarta,sanda yaja kujerar dake opposite din tata ya zauna.
Girarsa ya dage mata dukka biyun dake nuna alamun tambaya. Kai ta girgiza masa a hankali tana sauke qwayar idanunta,
"Ina zuwa" Yace yana miqewa a nutse.
Cikin nutsuwa ya shiga dakin,ya jawo locker din da yayi ajiyar tun a jiya,yana jiran lokacin daya dace ya sake mallaka mata ita a matsayin kyauta. Saidai kuma yana kai hannunsa wayarsa ta dauki qara. Fasawa dauko qaramin akwatin yayi.....yayi taku biyu baya yana kallon wayar dake saman bedside.
"Ahmad?" Ya furta sunan kamar wanda yake mamakin ganin kiran nasa. A nutse ya taka ya koma ya dauki wayar,sannan ya zauna saman sofa bed din,idanunsa akan wayar tana nuna masa lokaci na qarshe da sukayi waya da ahmad din. Ajiya ne,sanda yake kan hanyar dawowa ya dauki akhnan zuwa taron.
Sunyi maganan jikin sultane da yake sake tsanani,ya kuma aike da likita na musamman qwararre da zaici gaba da bashi kulawa,yace da ahmad din.
"Idan sati daya ya wuce babu sauyi.....inajin zan laluba qasar da zata iya kula dashi a fita dashi can" Wannan shine plan dinsu na qarshe kuma maganarsu ta qarshe da ahmad din.
Sallama ita yake fara yi a duk wayar da zai amsa....saidai a yau sallamar tasa ta tsaya cak ba tare daya iya qarasata ba sanda muryar ahmad ta mamaye kunnensa.
Muryar dake cike da wani irin nauyi da rauni dake nuna tazararsa da sakin kuka kadanne.
"Sultane ya rasu.....sultane ya mutu" Shine saqon da ahmad ke fada masa da wata irin muryar dake cike da kakkarwa da saarewa.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine kalmar data fita daga bakinsa yana jin wani abu yana hargitsewa cikin kansa. Baisan waye ya kashe kiran ba.....shi ko ahmad din,yadai kalli wayar yaga ahmad baya kan layi.
A hankali wayarta dake gabanta ta dauki ruri,abinda ya maido da hankalinta kenan kan wayar. Idanunta suka sauka akan sunan dake yawo saman screen din.
"Mammina?" Ta furta sunan kamar wadda bata taba ganin sunan a rayuwarta ba sai yau,
Tasha kiranta.....amma sanda suka isa Ethiopia,tarin miscal dinta na kwana da kwanaki wanda bata tana biba. Amma a yau,hakanan taji tana muradin daga kiran.
Ta daga kiran sanda take hango haisam daga can qarshen balcony din yana takowa da dan nisa kadan a tsakaninsu,duk da a nesa yake amma hankalinsa yana kanta. Ta danna kore.....koren da dannashi ya juye mata zuwa jaa.
"Yanzu kinji dadin rayuwarki akhnan?......" Kalmar data fara fitowa kenam daga muryar mammina.....kalmar da akhnan din ta jita da wani irin nauyi ba tare da taji komai daga bakinta ba.
"Me?" Ta jefawa mammina tambayar haka kawai tana jin zuciyarta na wani irin bugawa kamar zata rikito daga qirjinta. Shuru ne na second daya....shuru na second dayan da akhnan ta jishi kamar yana daidai da shirun shekara dubu.
"Babanki ya mutu akhnan.....sultane ya mutu!" Ta fadi da wani irin qarfi a muryar ta,qarfin da zai gaya maka da anihin zuciyarta yake fita.
A karon farko da maganan ta dinga gutsirewa tana shiga kanta a hankali......tana samun mazaunai iri daban daban cikin kanta tanason zama tare da son isar da saqon inda ya dace yaje.
"Karya ne" Amsar data samu kenan daga zuciyarta,amsar da taji tafi gamsuwa da ita,ta kuma zabi tayi aiki da ita.
"Me kika ce?"
"Nace gatanki ya fadi.....ba sultane....sultane ya mutu!" Ta sake maimaita mata kai tsaye.
"....sultane ya mutu a sanda kike can yawo a dubai,kina shaqatawa da more rayuwarki ba tare da kin damu kizo kiga jikinsa da lafiyarsa ba.....sultane ya mutu sanda kika zabi miji....kika zabi yawon duniya akan ganinsa....qasa qasa"
"Aah mammina!" Akhnan ta fada a tsawace tana jin yadda zuciyarta ke bugawa kwanyarta kamar zata haukace.
Wata siririyar dariyar raini ce ta fito daga gefan mammina.
"Yanzu kika tuna kina da uba?.....ki dawo kiga gawarsa idan har kina da sauran mutunci da qauna tsakaninku" Sai mammina din ta fashe da kukan da yabar sautin cikin kunnuwan akhnan.
Zare wayar tayi a kunnenta,dukkanin ilahirin jikinta yana bari. Number ahmad take nema,shi kadai takeson kira don taji ta bakinsa.....ta bakinsa takeson tabbatarwa,sai taji kawai an zare wayar daga hannunta.
Haisam ne tsaye a gabanta,wanda batasan yaushe ya iso ba,batasan yaushe ya qaraso ba,amma tana hada idanu dashi abinda ta gani cikin qwayar idanunsa sai taji kamar yana ce mata.
"Da gaske sultane ya mutu"
"Haisam.....abbana......abbana ko?" Ta fada tanason samun amsarta ta idanunsa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Bayaso taji ko taga komai daga gareshi. Bai taba rasa iyayensa ba.....amma ya sani duk wanda zai gaya maka wannan labarin ba zaka taba manta fuskarsa sunansa da muryarsa ba.
Da gaske mammina ta isa ta amsa sunan MAQIYIYAR SAFEENA.....tunda ta zabi kaf fadin agadez ta zama ta farko da zata gayawa akhnan din babban rashi da faduwar babbban bango daga rayuwarta?.
"Bappi na....haisam bappi na" Ta sake fada tana jijjiga hannun haisam dake tsaye kamar wanda tunaninsa ya tsaya gaba daya da aiki.
"Bappi...." Ta fada da wata murya data tsayewa haisam cak a zuciya da kunnuwansa.
Qarfafar kansa yayi ya taka a nutse yana hade tazarar dake tsakaninsu,ya rungumeta sosai cikin jikinsa zuciyarsa na wani irin bugawa,ya riqe kanta sosai a tsakiyar qirjinsa.
Wani irin gigitaccen kuka ta saki,iya bugun da zuciyarsa takeyi ya isa ya amsa mata tambayarta,iya shurunsa ya isa ya gaya mata ya sani....an gaya masa bappi ya mutu,saita sanya hannunta da suke rawa gaba daya ta cukuikuye rigarsa.
"Haisam......bappina.....bappi na ya mutu" Ta sake maimaitawa da madaukakin sauti.
Cak numfashinta ya dauke daga gangar jikinta,dukka wani qarfi ko garkuwa ta jikinta ta soma kakkaryewa.....qafafunta suka lanqwashe suka gaza daukarta saboda tsaiwar numfashi da kuma wani abu me kama da ficewar ruhi daga gangar jikinta.
A razane ya mata wani irin kyakkyawan ruqo cikin jikinsa yadda ba zata fadi ba. Karon farko da wani abu ya sanya gabansa faduwa......wani tsoro kadan ya shigeshi,yadda jikinta gaba daya da tafukan hannayenta sukayi wani irin sanyi.
Fuskarta ya riqe da sauri cikin hannunsa,girgizata yakeyi sosai muryarsa tana sauyawa completely.
"Babe" Ya fada muryarsa tana rawa. Wani rauni yana bayyana sosai cikin muryarsa sosai,kamar wanda yake hangen zai rasata shima adan qanqanin lokaci irin wannan
"Akhnan" Ya sake kiranta yana tattaba fuskarta sosai,saidai ba wani alamun motsi sam a tattare da ita.
Da wani irin sauri ya sureta gaba daya,ya soma komawa da ita ciki. Ya tsaya hannunsa yana rawa ya kira security service.
"Call the doctor......now!" Ya fada da wani irin murya da tayi amsa kuwa a dukka sassan suite din.
Yama manta yana da wani training gaba daya akan irin taimakon gaggawar.....ya manta kansa......ya kuma manta wayeshi.
Gaba daya suite din ya shiga motsawa,su shehnaz aisa dake kuka,da sauran ma'aikatan dake sauri saurin hada mata abinda zai taimakawa numfashinta. Idanunsa dukka suna kanta,ko sau daya bai daukesu daga kanta ba,yana ganin kamar idan yayi hakan zai waiwayo ne ya tsinci gawarta.
Tana jikinsa....har zuwa sanda likitar ta kammala bata dukkan taimakon da zata bata din.
"Zata tashi in sha Allah" Haka kawai yakejin kamar bata fadi gaskiya ba,haka kawai yakejin kamar ba tashi zatayi ba. Komai ya kwance masa,ji yakeyi kaman ba gangar jikinsa bace a jikinsa.
A tausashe ya gyara mata zama cikin jikinsa. Bakinsa saitin kunnenta ya kirata.
"Khadeejah.......my princess" Sai muryarsa ta sake karyewa
"Wake up" Ya fada kamar wanda yake roqonta akan ta bude idanunta. Ganin idanunta a rufe sake karya masa duk wani qwarin gwiwa yake,ganin idanunta a rufe yana sawa yaji kaman duk duniya ta kulle masa qofofinta gaba daya.
Karon farko cikin lokaci mai tsawo tsoro ya bayyana sarai a idanunsa,wani abu guda daya daba wanda zaice ya taba gani tattare dashi.
Shafa kanta yayi,muryarsa na rawa cike da damuwa.
"I'm here....." Sai muryarsa ta sake rauni cikin yanayi na roqo da magiya.
"Akhnaann". Kamar taji kiran,kamar sunanta daya ambata yakai har cikin qwaqwalwarta da zuciyarta dake shirin tsaiwa da aiki,saita motsa yatsunta sannan idanunta suka fara motsawa suna yunqurin bude kansu.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*