← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 176

Sashe 103

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanunta ya sauka akan mutanen dake tsaye suna jiran saukowarsa. Hotel representatives.....business officials.....security chiefs da personal staff's wadanda kowanne shigarsa ta bayyana matsayinsa.

Bayansa kadan ya sanyata,kamar wanda ke boyonta kada a kalle masa ita,cikin madaidaicin takunsa ya soma sauka,me cike da ginshira da qasaita. Tana biye dashi,still hannunsa bai zame daga nata ba.

Haka kawai wannan karon tsaiwar tarbar tasa yaji ta takureshi. Gani yake kaman kowa ita yake kalla,kaman ita daya tayi saura halittar diya mace a duniya. Musamman abayar dake jikinta yanzu,royal silk ne me asalin tsada da kauri da kuma daukar idanu. Shi da kansa data kammala shiryawa ta fito sai daya jima zaune,ya sanyata tana tsaye a gabansa yana qare mata kallo,ya fusgi kalmar

"Ma sha Allah" Da wani sanyin jiki da kasala da kallonta kawai yake saukar masa dashi.

A hankali ta lura da wata kalar girmamawa daga dukkan wanda yake gurin. Duk wanda haisam ya isa gabansa sai taga ya sunkuyar da kansa kadan kafin ya bawa haisam hannunsa suyi musabaha. Cikin ladabi dukkansu suke kiransa.

"Welcome back mr aba jifar" Sunan daya tsayawa akhnan sosai a ranta. Ba wai don yau ta fara jinsa ba.....aah,sai don yadda take ganin dacewar sunan dame shi.

"Thank you" Yake amsa musu dashi,saidai saman fuskarsa akwai murmushin daya rage miskilancin saman fuskarsa.

Kaman yasan ta shiga wani tunani na daban,ya matsa yatsunta a hankali kamar yana tuna mata cewa yana tare da ita ne.

"Don't look so startled.....they're only being polite" Ya fada calmly.

"Only being polite?" Ta maimaita kalmar a cikin kanta. Wasa yakeso ya mata da hankali kenan kamar yadda ya saba?. Ta sake maimaita kalmar.....alhali mutanen suna kallonsa da irin girmamawar da akewa sarakuna. Yarima ne shi ta sani....ba wani sauran abinda zai boye mata.....sai sauran abinda bata sani ba.

Wani daga cikin mutanen ne ya matso,hannunsa dauke da tablet

"The palace district has been informed of your arrival sir" Kadan taji numfashinta ya tsaya

"Palace district?" Ta sake maimaitawa qasan zuciyarta.

"And everything has been prepared..." Ya qarasa maganan yana miqa masa tablet din.

"Good" Haisam yace kawai yana riqe tablet din cikin hannunsa,mutumin ya gyada kai kamar wanda aka bawa lambar yabo yana matsawa a gurin.

Sake riqeta yayi a hankali tana daga bayanshi suna takawa. Idanunta na cikin airport din zuwa motocin da suke dosa,amma kunnuwanta suna jiye mata sautin haisam. Sautinsa ne.....saidai a yau din da wani yare da wani harshe da bata taba ji yayi magana dashi ba. Harshen larabci....mafificin harshen da a duniya shine yare na daya da take matuqar son taga ta iya.

Yana mata wani irin dadi.......tana jin wata nutsuwa a duk sanda ake yaren,koda kuwa bata fahimtar komai a cikinsa.

Duk da tarin mutanen dake neman yabawarsu wajen girmamashi......amma hakan bai hanashi barinsu ba,ya matsa a nutse ya bude mata qofar Royce rolls din yana duban idanunta da girmamawa.

Takawa tayi a nutse zuwa cikin motar,saidai idanunta a kansa. Kowacce rana sake bata mamaki yake,kowacce rana bayyana mata kanshi yakeyi ba tare da yayi magana da bakinsa ba.

Dangerous calm smile dinsa ya sakar mata,sannan ya zagaya a nutse daya daga cikin guards dinsa suna bude masa tasa qofar.

"Wane irin mutum ne wannan?,And how much of him have I yet to discover?" Ta yiwa kanta tambayar sanda convoy din motocin ke motsawa a hankali suna barin harabar airport din.

Bata sake sanin cewa ta shiga duniyar mutumin da take tunanin kawai ta sanshi bane.....bata sake sanin a yanzun bane zata fara sanin.....zata kuma fara ganinsa da gaske ba sai sanda suka isa harabar hotel din.

"Ya salam ya Allah" Ta fada can qasan maqoshinta lokacin da motocinsu ke qoqarin sanya kansu farfajiyar hotel din.

*_Turqashi!!!.....haisam ne akhnan......akwai saura.....baki gama shan mamakinsa.....ki adana mamakin nan kada ya qare.....ba akhnan ba.....ko ni da naga hotel din an gama tashin kaina 🧐🧐,mu hade gobe in sha Allah with scene view na hotel din in sha Allah kaman yadda muka saba_*

*_INA FATA BAKU MANTA BA....WANNAN WEEK DIN NA DABANNE NACE KO IN SHA ALLAH_*

*HUGUMANKU CE*🙌🏽🙌🏽🙌🏽

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 92*
__________________________
https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee*
_________________________

*_ATLANTISTHEROYAL_*

.......Hotel mafi tsada a dukka hotels na duniya. Hotel din da bata taba kawowa a kanta zata shigeshi ba. Dream hotel dinta.....ba ita kadai ba,hatta da aisa shehnaz dama duk wanda ta sani suna tafiye tafiyen yawon bude idanu.

Yanzun kam kai tsaye take kallon haisam. Tana ganin ta gama saninsa,tunda tasan cewa shi din yarima ne,dan sarkin jimma. Tana tunanin ta gama saninsa tunda tasan family dinsa......amma saidai a yanzun ta fara qaryata wannan.

Bai kula da kallon da take masa bane.....ko basarwar daya saba ne cikin jininsa oho,bai waiwaya ba har zuwa sanda motar ta gsayata qawatacce kuma tsararren gurin adana motoci,ya sanya hannunsa ya bude side dinsa. Ta glass din tana iya kallon yadda yake sallama da mutananen da suka masa rakiya. Da wannan yanayin da zai gaya maka tabbas an haifeshi ne a cikin IKO.....ba kuma shike neman ikon da girma ba,sune suke bibiyarsa.

Takunsa a nutse.....wannan royal walking din ya qaraso gaban motar,ya sanya hannu ya bude mata hana dubanta a tausashe.

"Bismillah.....my princess" Idanunta ta lumshe a kansu,sannan ta budesu lokaci daya.

"Bazan iya saukowa ba......alhalin har yanzu ban gama sanin waye kai ba" Idanu ya zaro gaba daya mamaki yana bayyana saman fuskarsa,kafin kuma a hankali ya maye gurbin mamakin da murmushi.

Matsowa yayi gaba kadan zai riqe hannunta amma ta janye

"Is okay....." Ya fadi shima yana maida hannunsa ya hade tafukan hannayen nasa yana murzasu guri daya.

"Kiyi haquri....."

"Nayi.....kuma zanyi,bazan matsa maka ka gayamin komai ba,har sai sanda ka shirya......amma zuwa yanzu.....duk abinda na gani na tambayeka lallai zaka bani amsarsa.....wannan shine sharadin shigata ciki" Ta fada tana dan bin ginin hotel din da kallo.

Shuru ya danyi,kamar yana nazarin wani abu,sai kuma a hankali ya gyada kansa yana lanqwasar da kansa cikin yanayi na girmamawa.

"Accepted your royal highness" Ya furta yana saka tafin hannunsa a qirjinsa.

Cikin jikinsa ya riqeta sosai,yana jin kamar zata bace masa ne. Idanunta a hankali suke qarewa hotel din kallo,zuwanta na farko kenan saidai gani a hoto da videos. Wasu irin palm trees masu haske da qyalli da suka qawata shi a jere gefe da gefensa. A zahirinsa yafi mata kyau,yafi kama da modern palace.

Qofar main entrance na hotel din,doormen din suka matsa cikin girmamawa,matsawar tasu ya bashi daman ganin wadanda ke tsaye suna jiransa.

Security da managers ne na hotel din,wani irin fountain light. Crystal reflection tako ina,ga wani irin fresh oud scents dake yawo a cikin iskar gurin.

"Welcome back sir" Managers din ke fada cikin girmamawa.

"Welcome back" Ta sake maimaitawa. Hakan na nufin ya saba.....ya riga ya saba da zama kenan a gurin?..

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Larabcinsa dasu yaci gaba da shiga kanta,ta sake lumshe idanunta tana jin tarin tambayoyi a kansa suna cika mata kwanya. Yanayin accent dinsa ya fita daban da nasu,ta kasa tantance a cikinsu waye yaren yafi zama da dadi akan harshensa?. Zata iya cewa SHI duk da hakan zai zama kamar wani son kai ne tayi,saidai kam zata zabeshi ta sake zabinsa saboda. Husky voice dinsa da take zama very calm da wani irin soft tone yadda take fita yasha banban da nasu,ta saba jin hakan,muryarsa daban....da wani irin banbanci da muryar kowanne d'a namiji a duniya.

"Your penthouse was ready" Muryar daya daga cikin staff din ta fada. Godiya ya masa kaman yadda ta lura dabi'arsa ce ga duk wanda ya masa hidima,sannan kowa ya qyaleshi da ma'aikatan hotel din biyu da security din data kasa ganewa nasa ne tun asali ko a nan yayi hiring nasu?.

Penthouse kawai ke yawo cikin kanta,idanunta kuma suna son gane mata zahirin abinda kunnuwanta sukaji mata.

Private elevator suka shiga,iya shi da ita kadai,sauran suka shiga wata don su tarar dasu a building din da zasu sauka.

Ya matsa ya bawa elevator din number building din,tayi tsaye a bayansa tana kallon yadda yake tsaye. Cikin nutsuwa da kamewa,da wani kalan hali da dabi'ar da bazaka taba zaton ya taka irin wannan matsayin ba a rayuwarsa.

*_Mr aba jifar hallway_*

Abinda ta gani kenan a rubuce jikin wani arrow na silver bayan fitarsu daga elevator din. Mamaki yana sake kasheta,private floor?,dama akwai private floor a hotel?. Residence guda take gani a rubuce,bawai suit da suka saba sauka ba?.
Chapter 103 · 0% Book details