← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 176

Sashe 139

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa ameen*
____________________________

Qarya take.....ta sani itama qarya take,a yanzun a duniya akwai wani abu da zai sanyata ta qishi?. Anya kuwa?,koda ranta ya dauka kuwa tunda har ya bawa sultane wata sabuwar rayuwa?. Ya fiddasu kuma daga makauniyar rayuwar da suke ciki.

Bai barta ba bai kuma matsa mata ba.....amma da wani irin salo sai daya tabbatar ya sanyata bacci saboda zuciyarta ta huta,jikinta kuma ya karbi treatment din da aka bata. Ba bacci bane burinta ko muradinta ba.....muradinta taga sultane,amma sai gashi haisam din ya maidata duniyar baccin da bata shirya ba.

★★ Ta sake d'aga idanunta a hankali ta kalli babban royal agogon dake kafe a bango,kafin ta saukesu a nutse akan haisam.

Haisam din dake zaune saman sofa.....gabansa table ne d'an madaidaici a ajiye,samansa kuma laptop ne wayoyinsa da tarin takardun da yaketa fama cikewa tun dazu.

Idanunta suma sauka nutse akan fuskarsa,bata iya ganinta sosai,amma tar take ganin dogayen eyelashes dinsa da yake kallon takardun gabansa dasu,sai sukayi kaman sun hade da juna saboda tsahonsu,kamar kuma a lumshe idanun suke maimakon a hade.

Juriyarta ce take qarewa......haqurinta yana gazawa tana dai daurewa ne kawai. Daga d'azu da abun ya faru har zuwa yanzu haisam ya hanata fita ko ina. Ya kira mata sultane ta wayar falaak ya saka ta a handfree,kuma sultane din ya gaya mata.

"Ki zauna.....karki fita ko ina,har yanzu masarauta a hargitse take,zuwa dare....idan komai ya lafa zan shigo" Da wannan alqawarin na sultane.....da wannan idanun na haisam da yaketa tsareta dasu.....da nauyinsa na kalar hidimar da yaketayi da ita ya sanyata jan bakinta tayi shuru tana jiran lokacin da sultane yace zai shigo.

Komai dare... Komai tsahon lokaci kuwa ba zata kwanta ba. Zata yita jiransa.

Idanunsa ya daga a hankali sai suka hada idanu,ta janye kallonta daga kansa tana basarwa.

Qarin hujjarsa......tana buqatar hutu,tana buqatar nutsuwa. doctors sun hana mata stress.

Amma ita,tasan akwai wani abu daban. Tun safe yake fita yana dawowa. Long calls. Meetings. Guards daketa shigowa suna fita,duk da bata ganinsu amma tana jin motsinsu.
Kuma duk lokacin data tambaya yaushe zata fita?.

"Later" Kawai yake ce mata.

Ya hana ta fita ko ina. Ya hana ta shiga council chamber. Ya hana kowa kawo mata details ya gargadi su birra sosai.
Kamar yana kareta daga duniya.
Ko yana boyeta daga dukkan komai.

Yanzun daya kamata tana satar kallonshi,saita zame idanunta tana maidashi akan cup din tea din dake hannunta,wanda tuni cup tea din ya riga ya huce.

Tana jin zurfin kallonsa a kanta,kallon da batasan yau adadin sau nawa ya mata shi ba.

"You’re ignoring me again?” ya furta a hankali da wannan tarin calmness din nasa. Bata amsa ba,sai kawai ta shanye tea dinta a hankali,duk da ya riga yayi sanyi ba tare data kalli haisam din ba.

Murmushi kadan ya saki.....wannan miskilancin ya motsa.....wannan izzar ta motsa......wannan jan ajin ya tashi wanda bayajin bayan mutuwa akwai wani abu da zai rabata dashi.

"learned from the best.”

Siririn murmushi ya subuce masa,ya ajiye file din hannunsa yana qare mata kallo a nutse,wannan jin kan nata yana burgeshi.

Still taqi kallonsa,sai yaji kaman ana fusgarsa zuwa gareta,ya ture gami da tattara dukkanin takardun gabansa a hankali ya miqe ya isa gabanta,takunsa masu nauyi na amsawa cikin dakin. saidai akwai tazara daya bayar tsakaninsu.

Ya sunkuya a hankali yana qoqarin kamo idanunta. Hanya qwara daya tak da zai karya alkadarin wannan rigimar.

"habibti" Ya fada a tausashe har tana jin saukar muryar a kowanne sashe na jikinta,saidai still bata amsa ba

"Kina fushi dani.....saboda naqi barinki fita waje?" Sai a sannan taso kallonsa amma ta kasa,hawaye ya taru a idanunta. Ta qagu ta sake ganin sultane,ta qagu,gani take kaman za'a sake ce mata ya sake mutuwa....gani take ban bada gaske bane shine.

"Kaine ka kulleni a nan.....kowa yaga sultane ya qara.....kowa yana samun amsoshin abinda ke faruwa a cikin gida amma bandani".

"Kina buqatar hutu" Ya motsa labbansa da wata kalar izzarsa daya saba da ita.

"No....you needed control" Wani siririn murmushi ya bayyana a labbansa.

"And if i did?" Ta zaro ido kafin ta narke fuska.

"Haisam" Ta fada a shagwabe. Takowa ya sakeyi yana sake rage tazarar dake tsakaninsu.

"Kin samu a hannuna....."

"......You think I’d let you walk into another emotional storm immediately after that?” ya qarasa fada yana dage mata dukka girarsa biyun.

Ta bude baki zatayi magana,amma sai kuma ta kasa. Cikin muryarsa akwai wani abu.....wani abu me nauyi dake bata tabbacin da dukkanin zuciyarsa yake magana. Idanunta ta sauke qasa a hankali.

"Sultane nakeson gani...."

"Zaki ganshi.....zaizo"

"You keep deciding things for me.”

"Only when I’m terrified of losing you.” Sai ya yi shiru na second biyu. Kamar yana tunanin wani abu na daban. Da alama har yanzu batasan girman matsayinta a zuciyarsa ba.....har yanzu....fake death na sultane ya karya wasu tsarukansa da yawa. Wasu shirye shiryensa. Ya shirya shayar da ita kalar soyayyar da ko cikin finafinai da litattafai bata taba cin karo da ita ba. A dubai......yaso kafa abubuwa da dama,yaso shirya abubuwa masu yawan gaske wannan issue din ya taso.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Zuciyarta ta buga da amsarsa daya bata. Duk lokacin da yake bud'e mata wani bangaren zuciyarsa,sai ta kasa ci gaba da fushi sosai dashi kaman yadda take tsarawa a bayan idanunsa.

Ya bude lumsassun idanunsa a kanta,suka hada ido,wani irin shuru ya ratsa tsakaninsu,wadannan tsumammun idanun nasa.....a hankali suka sanya jikinta ya mutu. Wani irin tsumammen kallo,kamar ita kadai ce abinda yake iya gani a duniya.

Ba zata iya jura ba,don haka ta janye idanun nata. Murmushi me sanyi ya kubce masa.

"There she is" Ya fada da wani yanayi na tsokana a cikin muryarsa.

"Who?" Ta tambaya da wani yanayi akan fuskarta. Takawa ya sakeyi yana hade tazarar dake tsakaninsu. Ya aza fuskarsa akan kafadarta,ya sanya bakinsa saitin kunnenta,muryarsa can qasan maqoshinsa da wani irin shauqi yace.

"My stubborn wife" Kusan daukewa cak numfashinta yayi. Sai daga baya ta samu ta jashi da wani irin qarfi tana saukeshi a hankali,kafin tace ko shi yace komai aka sanarmusu

"Sultane ya iso" Abinda ya sanyata miqewa cak kenan. Hannunta ya kama softly yana zaunar da ita.

"Relax" Ya fada yana duban tsakiyar idanunta,saita dakata tana kallonsa har zuwa sanda ya ta ka ya bude qofa wa sultane.

Daga bakin qofar bayyana.....yana tsaye kyam,wadannan kamannin nasa na cikakken ba'abzine tana bayyana. Giant tsaho da murjewar jikin da a yanzu akhnan taga kaman ya sake qiba ne,jikinsa ya sake yin kyau da murjewa,ya sakeyi fadi kamar wanda yaje hutu wani guri ya dawo.

Shi daya ne.....shi kadai......yana me amsa sunan MAHAIFI bawai SARKI ba. Ba shigar sake nuna saraura ko mulki. Ba guard ko daya,hakanan ba komai sai farar jallabiyyar data nuna kyans,falaak na biye dashi qafa da qafa,kamar wadda akace mata itama zai sake ba'acewa rayuwarsu. Akhnan tayi sak tana dubansa,idanunta suka cika sosai da hawaye tana kallonsa

"Zan iya shigowa?" Ya furta cikin salon neman izini,abinda ya azawa haisam kunyarsa. Girmansa yana sake qaruwa a idanunsa. Sarki ne.....amma yana neman izini ga d'iya da surukinsa.

Baya haisam yaja,yana bashi hanya cikin girmamawa. Ya soma takowa a nutse idanunsa akan akhnan. Kasa jurewa tayi ya iso gareta,sai taji kaman yayi nisa tazarar dake tsakaninsu,ta miqe cak,ta kuma kwasa da wani irin gudu da ya sanya haisam sadda kansa,quruciyarta sosai tana bayyana.

Juyawa haisam yayi ya soma takawa don ficewa da zummar basu space,saidai sultane dake rungume da akhnan a jikinsa bayan sun zauna ya dakatar dashi.

"Koma ka zauna...".

Dakin yayi shuru na wasu mintuna,bayan sultane ya kammala warware mata komai. Kuka take da wani irin laushi karyewar zuciya da nadamar irin rayuwarta ta baya. Tsanar mammina.....dama tsanar komai daya shafeta yana sake ratsata. Wanne abune yafi wannan ciwo da muni?,maqiyinka ya girmar dakai?,ya dinga bin rayuwarka yana rusata d'aya bayan daya?. Har yanzu zuciyarta bata gama amincewa da wai sultane bane raye a gabanta. Wani abu da tasan koda tafi kowa qaunar sultane a duk duniya ba zata sameshi ba,wato dawo dashi daga mutuwa,sai gashi wata babbar almara ta rayar dashi daga mutuwar da akewa shirin yiwa sadakar arba'in a jibi.

Ta kasa d'auke idanunta a kansa......idan ta tuna duka abinda mammina tayi.....ta kuma juya ta kalli sultane dinta a raye.....sai taji komai yana kwaranyewa daga zuciyarta.

"Ki yimin afuwa da barinki kika shiga wahala haka da yawa" Sultane ya fada cikin kulawa. Tabbas kowanne d'a da irin son da Allah ya azawa iyayensa a kansa,ita kam akhnan wannan tabbaci ne na cikin 'ya'yansa soyayyarta tafi ta kowa tasiri a ransa.

"Kada kace haka bappi.....bansan me zan kwantata wannan yanayin ba......na binneka.....na soma koyon yadda zanyi rayuwa babu kai....sai kuma gaka?,me yafi wannan dadi a gurina." Murmushi ya saki,ya waiwaya yana duban falaak. Shigen abinda tace dashi kenan sanda ya zauna dasu bayan sakin morsa safiyya ta dawo gida. Morsa safiyyan da har yanzu ta kasa cewa komai. Shima ya hanata cewan,yace ta huta....ta huta daga dukkan abinda ta fuskanta.
Chapter 139 · 0% Book details