← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 176

Sashe 109

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yadda taga ya yaba kawai ya sanyata jin wani irin dadi. Take zuciyarta taji tana mararin ci gaba da ganin wannan yabawar.....wannan jin dadin saman fuskarsa.

"Komai da komai......ya kamata na koya" Taji zuciyarta tana sake qarfafarta.

Tayi qoqarin serving nasa.....zata sake zubawa a wani plate din ya janye,ya saka musu spoon biyu a dukka plate din.

"Oya....bismillah" Ya fada yana tattare hannun rigarsa gami da janye nasa spoon din gefe.

Bata gasgata da hannu zaici abincin ba sai da taga yayi bismillah yakai abincin bakinsa ya sake wata lomar.

"Ya salamm" Ta fada qasan ranta. Komai nashi simple ne?,mutum irinsa amma ya tattare hannu yana cin abinci da hannunsa?.

Idanunsa ya aje a kanta yana tauna lomar a hankali,sai daya hadiye sannan yayi magana,komai nasa akwai tsari da ilimi a ciki. Yanason qure rashin cin abincinta a yau,bai taba ganin cin abincinta ba tunda suke.

"Eat properly"

"I'm eating" Ta amsa masa a hankali.

"No" Ya fada da calmness sosai cikin muryarsa.

"You’re moving food around the plate dai princess" . Lips dinta ta cije kadan cikin kunya,duk sanda ya kirata princess sai taji ya aza mata nauyi saman kanta.

"You noticed too much" Ta furta can qasan maqoshinta.

"I noticed only you". Kasa amsa masa tayi,sai wani irin shuru ya gilma,irin shurun dake nuna sabo dakeson kutsowa sosai tsakanin mutum biyun da wata alaqa me girma ta gifta tsakaninsu.

Da wani irin yanayi najin nauyi take gyara blanket din,daidai sanda ya miqa hannu ya qarasa kashe fitilar data rage ta gefan gado.

Duhu ya mamaye dakin,shuru ya sake gilmawa kafin ta jiyo muryarsa cikin duhun.

"Akhnan...."

"Uhmmm" Ta amsashi gangar jikinta na kwadayi da fatan samun kusanci dashi,saidai wannan izzar dake cikin jinin kowacce diya mace ya hana ta nuna hakan koda a fuskarta.

"I liked today" Ya fadi kansa tsaye da zahirin abinda yake cikin zuciyarsa.

".....coming back to you afterward" Ya qarasa bude mata maganan.

Wani irin laushi zuciyarta taji tanayi sanda ta tsinci dumin tattausan jikinsa yana mamaye duk ilahirin jikinta,ya ilahi....batasan sai yaushe zai qyale zuciyarta ta huta ba. Bata sani ba.....qila ko sai sanda ta soma yawo layi layi tana gaya musu haukan son prince haisam aba jifar takeyi?.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

*NANAY*

Cikin qanqani lokaci ta tashi hankalin sassanta dama gidan gaba daya wajen neman inda akhnan ta shiga. Kusan duk wata hadima a tsaye take wajen bincika cikin gidan,maganan yaje har kunnen motii sai gashi da kansa a sassan.

"Kina tunanin wani mummunan abu ya isa ya shigo ya shallake kowa yayi gaba da ita?" Motii dake boye dariyarsa ya fada yana duban nanay wadda tashin hankalinta ya bayyana muraran.

Kai ta girgiza da sauri.

"Nifa ban gamsu ba.....ba inda giiftii zata sanya qafa ta fita ba tare da sanin kowa bafa". Dariyarsa ya sake kalmashewa sosai yana duban qwayar idanunta. Har yanzu duk data girma amma yana iya ganin wannan zallar quruciyartata da yasha fama da ita a shekarun baya saman fuskarta.

"Shikenan.....a sake dubawa wataqila a dace ko tayi bacci a wnai gurin" Ya fada yana gyara zamansa kawai.

Daidai lokacin rumaisa ke shigowa gurin. Bayanta baiwarta ce obsa,rungume da 'yar magen rumaisa din fara qal wadda ke da wani irin kwantaccen gashi me taushi dake gwada irin kulawar data samu.

Idanunta akan nanay,don tun sassafe ta fita makaranta,sai kuma yanzu take shigowa gida.

"Lafiya nanay?,me yake faruwa?" Ta tamabaya adan rude ganin yadda kowa yayi carko carko.

"Giiftii ce ba'a gani ba rumaisa" Fuska tadan tsuke kadan,da alamun mamaki saman fuskarta.

"Ba'a ganta ba?,tunda yaushe?,kunyi breakfast ne tare?"

"Aah....tunda sassafe fa?" Dariyarta take qoqari dannewa kadan,sannan ta sassauta fuskarta.

"Nifa naga obbo haisam din dazu" Waiwaya nanay tayi sosai tana duban rumaisa.

"A ina?"

"ta private exists.....kuma kamar giiftii din ce tare dashi,don mun hadu tana fita ina shigowa" Rumaisa ta qarasa fada kamar zata qyalqyale da dariya ganin kallon da nanay take mata dukka idanunta a waje. Data sauke idanunta akan motii kuma sai ta juya fuskarta saboda shima fuskarsa ta nuna dariya yakeson yiwa nanay din

"Subhanallahi" Tace a hankali saboda gaba daya ta rasa abun fada. Gurin ya dauki shuru,kafin kuma ta sake cewa komai Aanani dake zaune gefe da wayar nanay din a hannunta tace.

"Obbo haisam.....ya turo saqo nanay,kamar ma tun jiya.....kinji abinda yace" Ba tare data jira cewar nanay ba ta fara karantawa a fili.

_"Assalamu alaikum_ _Nanay._

_Ki yafe min rashin sanar dake da wuri._

_Na tafi da Akhnan Dubai tare da ni._

_Na san hakan ba shine tsarin da ya_ _dace ba,amma na yi _missing matata fiye da yadda zan iya_ _jurewa._

_I promise tana cikin_ _kulawa da aminci,zan riqe alqawari_

_Ki yi hakuri da ni_ _Nanay_

Wani shuru ya sake wanzuwa a falon,motii ya tattara dukkan jarumtarsa ya cinye dariyarsa yana yiwa rumaisa sign na su fita,sai itama ta baiwa kowa dake gurin umarnin hakan.

Sannu a hankali gurin ya zamana ba kowa sai shi da nanay din. Ya sake kallonta sosai yadda ta zama speechless gaba daya.

"Kin manta waye d'anki.....haisam baya hayaniya,.....but idan ya yanke abu......yana aikatashi,musamman abinda ya tabbatar yana kan daidai ne,bai kuma sabawa Allah ba" Yayi shuru still yana qoqarin danne dariyarsa kada ta tunzura.

"Amma fisabilillahi ya saceta har cikin daki kamar wani qaramin yaro?" Ta fada tana kwabe fuska kamar wadda ta rasa uwa da uba. Dole a wannan karon yabar dariyarsa kadan ta fita.

"Ya dauki matarsa ne,ba wata yarinya a waje ba...sannan ma kada ki azawa yarona duka laifin,da qafafunta ta fita itama fa,tabbacin tanaso kenan tabi mijinta,kara kawai take miki"

"Ya yaudareta dai.....dama ku maza kun iya yaudara" Ta fada a karon farko tana dan harararsa,irin wasan da suka saba can baya.

Murmushi ya sakeyi

"Tun farko dama na gaya miki,kada kice zaki tsananta tsakanin lamarin miji da mata....."

".....kaima dai kana goyon bayansa ne dama tun farko" Dariyarsa gaba daya ta subuce masa,royal father laugh dake kama da nutsuwar dake tattare akan fuskarsa.

"Dama dariya kakeso kayi ai na lura tun dazu,to kayita dariya" Ta fada tana miqewa. Hannu yasa ya riqota yana fadin

"Zo mana.....haba hadeezata" Ya jawota ta koma ta zauna a inda ta tashi.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 98*

*DU B A I*

Lallausar safiyar da wani siririn haske da iska me dadi ke kadawa sosai tsakanin kowacce qofa da window na penthouse din nasu dake cikin Atlantis the royal.

Saman tsararren dining din dake shiyya ta musamman cikin residence din,dining din da aka cika da kalolin breakfast iri iri,tamkar mutane da yawa ne zasuci,bawai iya khadeeja da muhammad ba.

Yarima haisam ne zaune kan kujerar dake opposite na akhnan

Sanye yake da pure white Tom Ford shirt da charcoal trouser,hadin color din daya fidda wani launi me kyau,irin launin da zai gaya maka ansan ainihin hada colors su bada ma'ana me kyau. Hannunsa sanye yake da black Patek Philippe watch wanda ya kwanta saman kyakkyawar fatarsa da gargasa ta yiwa ado me daukan idanu. Sanda yake fitowa,idanunta sun sauka akan berluti shoes din dake qafarsa,wanda yake bayyana asalin tsada da dukiya,saidai bada murya me amo ba,don zaka dauka gama garin takalmi ne,amma kuna sananne ne a idanun wadanda ke rayuwa daidai ko kusa da mizanin nasa arziqin.

A nutse yake sipping coffee din nasa,yana qare mata kallo cikin wata doguwar riga midnight blue data haskata kamar zaka saceta ka gudu. Shi ya zabi rigar da safiyar nan,yace ita yake buqatar gani a jikinta,zai kuma zabi shigar da zata masa da dare idan ya dawo.

Bata iya zama haka ba,sai data dora qaramin farin baby hijab daya nuna fuskarta a tsakiya da wani irin kyau da kwarjini. Ya sani,ta masa rowa,don ta rufe abinda yake matuqar mararin kalla wato albarkatun qirjinta

A zahiri suna zaune ne cikin shuru,saidai a badini wata hira ce akeyi tsakanin idanuwa da zukata,wannan karon baki baida rawar takawa ko abun fada.

Karo na hudu ya sake sauke idanunsa akan qirjinta daya ciko fam ta rigar,amma ta hanashi ganin komai banda wannan tudun. Kasa jurewa yayi,ya miqa hannunsa a hankali dake daure da agogon,yasa yatsunsa don hanye inda hijab din ya rufe. Da sauri ta riqe hannunsa caraf zuciyarta tana bugawa. Har yanzu ta kasa goge abinda ya faru daren jiya,bai mata komai ba.....amma ya fidda dukka maitarsa da soyayyarsa da gurin,har yanzu kuma tana jin kowanne feelings a jikinta.

"No" Ya fada can qasan maqoshinsa yana sarqe idanunta cikin nasa.

"It's my halal,karki hanani kalla.....kinaso idan na fita na kalla na wasu a waje?" Ya fada yana langabar da wuyansa kamar marayan dake neman tallafi.

A hankali ta sakar masa hannun,NA WASU A WAJE daya fada sai taji kamar ya dauki mashi ya caka mata a qahon zuciyarta......sai taji zuciyarta tana mata nauyi da wani irin kishi.

Idanunta suka dan sauya kadan tana kallonsa. Kamar yanzu ne ta fara fahimtar cewa......Haisam mutum ne da mata zasu kalla. kuma duniya cike take da irin kallon da take masa yanzu.

"Kada ka qara fada.....don Allah....banaso". Wani irin abu me sanyi yaji yana ratsa dukka jikinsa.

"Kishi.....kishi na take?" Ya fadawa kansa da kansa. Wannan dabi'artata ta masa,bata iya boyen komai,muddin dai ta daukeshi da muhimmanci.

Hannunsa ya miqe a nutse ya kamo yatsunta cikin tashi ya saka a nasa hannun yana murzawa softly. Kai ta dauke taqi kallonsa,ya sake sakin murmushi dan kadan

"Hey..." Ya furta softly yanason sake ganin wadannan blue eyes din.

"I was joking" Ya fada a nutse. Kallonsa tayi saita sake kauda idanunta. Da gaske taji zafi,wani irin zafi da batasan zuciya na iya jinsa ba,kuma har yanzu zafin takeji

"Ni banason jin kana kallon wata" Ta motsa labbanta a hankali ta fada kamar zuciyarta tana karyewa.
Chapter 109 · 0% Book details