← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 176

Sashe 74

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya salam" A hankali yana jin yadda juriyarsa take zagwanyewa....a hankali yana jin yadda dauriyarsa take raguwa. Anya zai iya?....zai iya ci gaba a haka?,alhalin tana gefansa?......zai.iya ci gaba da qaryata kansa?......alhalin komai yana bayyana gaskiyar abinda yakeji?.

Cikin cikakkiyar nutsuwa mutumin yayi sallama. Dogo ne baqi me murjajjen jiki,wanda asalin fatarsa ta nuna qabilar Ethiopia ne na gaske shi din.

"Allah ya taimakeka....na kammala"

"Madalla Dr jamaal.....ina saurarenka" Motii ya fadi,bayan ya baiwa Dr jamaal hankalinsa.

Takardar hannunsa ya bude yana sake kallonta,sannan ya rufeta a hankali,ya maida dubansa ga haisam dake zaune,da Akhnan dake gefansa,sannan ya maida dubansa ga motii.

"Ranka ya dade.....kaman yallabai yayi aure ko?" Ya fada cikin girmamawa da d'ari d'ari,kasancewar sarai yasan halin haisam.

Tambayar kuwa ta sauka saman zuciyar haisam din,sai yaji kaman duk duniya Akhnan din yake kalla tun daga shigowarsa. A nutse ya matsa yatsunsa,muryarsa can qasa taji ya furta.

"Tashi ki shiga ciki" Daga kanta tayi a nutse,cikin yanayi na rashin fahimta,saidai ba tare daya kalleta ba ya sake maimaitawa.

"Jeki giiftii" Nanay ta furta a nutse.

Miqewa tayi a hankali,tana jin wata kunya na dabaibayeta. Mene zaice ta wuce ciki?,bedroom dinsa fa kenan?,a gabansu?,bayajin nauyi ne?,ita bataga dr din ya kalleta ba kwata kwata,yaushe ma yaga hakan shi?.

Shuru parlor din ya dauka har zuwa sanda Akhnan ta bace cikin dogon corridor din da zai sadata da lafiyayyun royal master bedrooms dinsa guda hudu.

"Me ya faru.......muna jinka" Motii ya fada yana duban Dr jamaal.

Dan shafa kansa kadan Dr jamaal yayi,akwai wani kwarjini da motii din yake masa,duk da kasancewarsa kusan uba a gurinsa,saboda shi din yayan mahaifiyarsa ne.

"Irin dai wancan ciwon da yakeyi lokaci bayan lokaci.....so zuwa yanzu ya kamata ace ya rabu dashi,tunda akwai aure a......" Kasa qarasawa Dr jamaal din yayi,saboda wani kallo da haisam ya watsa masa.

Sosai yake qunshe dariyarsa ta yadda motii bazai gaji ba,da idanu kuma yakewa haisam din maganar

"Taimakonka nayi". Shuru ya wanzu a falon yana hadewa da sauran maganae Dr jamaal data maqale bai iya qarasata ba.

" Na fahimta.....na fahimta " Motii kawai ya maimaita har sau biyu yana gyada kai. Ba shiri Dr jamaal ya miqe yana shafa kansa.

"Ga magungunan da zaiyi amfani dasu nan,saidai su din relief kawai zasu bashi......Allah ya qara lafiya" Ya fadi yana karkatawa inda haisam ke zaune,nauyin motii da nanay yana narkar da shi. Bai amsawa jamaal din ba,sai tsarabar harara daya sake aike masa,yana boye da dariyarsa ya fara takawa yana fita motii da nanay na masa ya gaida gida.

Kaman jira motii yake jamaal din ya fita,sai shima ya miqe tsam yana fadin.

"Kinga yanzun ai sai ki bashi matarsa ko?"

"Zatayi jinyarsa ne yasha magungunansa motii,kwana hudu ya rage mu kammala a rakata gidanta.......ko zuwa da safe kaji qwarin jikinka......zan karbeta mu qarasa aikinmu" Ta fada tana dan duban haisam din. Saidai itama ta kasa duban cikin idanunsa.....ta daure fuska kawai tana rattaba bayani.

Murmushi kawai motii yayi yana takawa zuwa bakin qofar da zata fiddashi daga parlor din ba tare daya sake cewa komai ba. Ita dinma saita zabura tabi bayan mijinta,saidai tana sake jaddadawa haisam aron Akhnan din ta bashi.

Can qasan ran motii dariya kawai yayi,

"wanne irin qarfin hali ne wannan khadeeja?,mutum da matarsa sannan ace aro aka bashi?"

"Eh.....shi akewa gatan ai,kuma me yaci kwana uku?,kwana kin al'ada basu cika ba"

"K'nnnnn,to Allah ya taimaka" Abinda motii ya fadi kawai kenan,can qasan ransa yana sake jinjinawa halin mata,lallai halin mata daban yake dana maza,amma zaibar nanay din ta gani ganin idanunta,shidai zaiga ta yadda zata saka shinge tsakanin lafiyayyen yaronsa da halalinsa.

Yaron da kallon mata ma bai iya ba ballantana doguwar magana.....yanzun ga maganinsa ta saka dokar sai bayan kwana uku?.

*_to masu karatu.....nima dai nacw maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta😂,dama ana bawa kura ajiyar nama?,to qila sheikh dinmu na mutunci dai yasan darajar abun aro,zai kuma riqeshi da kyau.....mu hadu daku a ranar litinin in sha Allah_*

*_har kullum_*
*_Hugumanku ce_*🙌🏽

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 67*

A hankali take daga qafafuwanta tana sauke qafafunta saman tattausan carpet din dake malale cikin dakin. Idanunta take watsawa a hankali zuwa ga kowanne sashe dake dakin wanda yake fidda wani irin tattausan qamshi da wani sanyi da yanayinsa yasha banban dana parlor din data fito. A hankali zuciyarta ke bugawa a qirjinta qamshin da nutsatsen yanayin da dakin yake fiddawa yana ratsa zuciyarta da gangar jikinta gaba daya.

Idan tace iyakar rayuwarta.....iyara adadin yadda ta rayu a duniyarta bata ganin daki me tsari da daukan hankali irin wannan ba batayi qarya ba.

Cak ta tsaya tana tsoron wani abu,tsoron qauyanci......tana ji a hankali kaman tana neman daburcewa da rasa dukkan wayewar da take da ita.

Uwa uba wani baqunta takeji sosai a jikinta,ta sake zuqar iska sosai zuwa hunhunta wadda ta kasance wata irin sassanyar iska dake cakude da qamshin turarennan nasa da batajin har abada zata daina sonshi......turaren data shafe a mayafinta tun ranar da aka shigo da ita cikin gidan,ya kuma zame mata wani abu daban na debe kewa..

Bayan wannan qamshin,wani launin qamshi ne daban da bazata iya banbanceshi ba suka cakuda suka bada wani kalar launin qamshi me saukar da wani irin yanayi daban ga zuciya da gangar jiki.

"Komai nasa.....komai nasa me sanyi ne....komai nasa na dabanne.....komai nasa yana fadin cewa shi din......" Saita kasa qarasawa tana bude idanunta a hankali,wani nau'in tuhuma yana fitowa daga qasan zuciyarta.

"Me yasa yake tsayemin har haka a zuciyata?,me yasa komai nasa yake burgeni?.....me yasa komai nasa yakemin nauyi da kuma kwarjini?" Ta tambayi kanta tana komawa da baya a hankali ta zauna saman lafiyayyar sofa din dake ajiye wani sashe daban na dakin,wadda tayi matuqar dacewa da launin dakin da tsarinsa.

Idanunta suka sauka a hankali akwan wani sashe dake dakin. Akwai wani dan ado da qawata gurin,darduma qur'ani carbi da wasu launikan fitilu masu kyau maqale agurin,wasu kuma a ajjiye a qasa,sai litattafai 'yan tsiraru da basu da yawa.

Tattausan murmushi ya subuce mata,batasan wacce irin soyayya bace tsakaninsa da karance karance na addini ba. Zai wahala ya wanzu a guri bakaga tasirin wani abu daya shafi addini a tare dashi ko litattafan addinin ba.

Tayi kaman zata miqe don isa ga litattafan ta duba wanne iri ne,don tun daga sanda ta karanta tarihin manzan Allah take nutsawa da kadan kadan cikin litattafan addini na tarihin annabi da sahabbansa,saboda wani irin nishadi take samu qarin ilimi da dawo mata da wata rayuwa ta shekaru dubunnai da bata wanze a doron duniya zuwa gabanta.

*N A N A Y*

Cikin wani irin yanayi,wani irin tattaki da dama sun riga sun saba lokaci lokaci sukanyi tsakaninta da motii cikin masarautar suke takawa zuwa ga sashen nanay din dake manne dana motii din. Shuru Nanay ta samu kanta dayi,ba kuma don tsokanarta da motii kawai yakeyi ba.....aah,hankalinta ne taji a hankali yana kaiwa kan maganganun motii din.

"Zanga yadda wannan rigimar zata qare khadeeja,haka akeyi tsakani da Allah?,yaro da matarsa?,mema kuke jira?". Can qasan ranta tana jin akhnan din tamkar daya daga cikinsu balqees ko hasnaaa ce. Akwai wani irin narkakken tausayin yarinyar da takeji yana danqare qasan ranta. Duk da har yanzu basu samu zama haisam ya fede mata meye da meye ya faru da safiyya da safeena ba......amma tana ji a jikinta akwai abubuwa masu tsananin nauyi.....akwai abubuwa masu tarin yawa da sukazo suka dinga faruwa suna shudewa.

Akwai abubuwa da yawa.....da dama masu tarin gaske da take karanta tattare da akhnan din. Har cikin jininta take qaunarta,irin qaunar nan dai da takewa safiyya da safeena. Tana tsananin son safeena......tana tsananin son safiyya,hakanan a yanzu take shauqin son ganin safiyyan data rage mata,saidai batasan dalilin da yasa haisam din daya kawo mata su ya debi wani lokaci da zai sadata da safiyyan ba.

Amma koma meye ta sani,haisam din wani irin nutsatsen yaro ne me tsari,kyauta daga Allah daya zame mata abun alfahari,ba'a gareta kawai ba,har a gurin danginsa na uwa da uba dama 'yan uwansa gaba daya,ta tabbatar akwai babban dalilin daya sanyashi haka.

Can qasan ranta takejin wani abu me kama da tausayin akhnan,haisam d'anta ne....d'a mafi soyuwa a gareta,zataso ya samu dukkan nutsuwa daga gurin mace ta gari,zataso ya samu dukkan kwanciyar hankali irin wanda kowanne d'a namiji daya dace yake samu,wannan shine babban dalilin daya sanya takarkatar da dukka wadannan kwanakin gurin koyawa akhnan din basic abubuwa da zata kula da mijinta da kanta.

Ta lura akwai abubuwa da yawa da bata iya ba,baata saba ba,batasan ma yadda zata yiwa kanta ba ballantana waninta. Ta sani su irin wadannan abubuwan mace ko ke wace,duk gatanki....duk matsayinki inde zaman aure zakiyi baki da wata daraja idan baki sansu ba,baki da wata daraja idan baki koyesu ba,baki da wata daraja idan baki iyasu ba.

A yanayi rayuwar akhnan din,ta karanci akwai gibi da yawa. Ita karan kanta taimaka mata ake gurin kula da kanta,batasan yadda zata yiwa kanta hidima ba bare waninta. Ta kwashe dukkan lokacinta,ta bata wuninta da dararenta wajen mata wasu karatuttuka,tana kuma fata ko yaya su amfaneta.

Ta sauke ajiyar zuciya tausayinta yana sake ratsata. Indai har haisam ya gaza jurewa ya taba akhnan din,ta sani ba zataji da dadi ba. Tayi imanin zataji a jikinta ainun. Tafi kowa sanin waye yaronta.....tafi kuma kowa sanin yaqin data shiga shima ya shiga gurin kare kansa da mutuncinsa.
Chapter 74 · 0% Book details