← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 176

Sashe 140

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 126*

Bawai ta wahala bane.....hasalima kulawa ta musamman da kebantattun dakuna cikin estate guda da haisam ya ware yake ajiye duk wanda yaso daga cikin jama'ar dake da gaskiya da mammina ke kora a nan suke. Estate din da ya ajiye mutane masu yawan gaske,ciki harda su yalwan da yake jiran randa zaa wuce da mammina Ethiopia ya fitar dasu gaba daya suma. A ware masu gaskiya.....irin yalwa wadda amfani akayi da ita,ita kuma tayi amfani da son zuciyarta ta zauna da mammina din a matsayin uwar d'akinta.

"Wait" Akhnan ta fada tana miqewa ta zauna sosai tana duban sultane din. Yadda tayin yaja hankulansu gaba daya.

"Bappi.....waye ya shirya wannan fake death din?". Shuru sultane yayi na sakanni,sai kuma ya saki murmushi a hankali. Ya daga idanunsa a nutse yana duban haisam.

Da sauri tabi kallon sultane din,sai nata idanun suka mata jagora zuwa ga haisam. Kansa ya kawar kad'an daga idanun akhnan din kamar wanda aka kama.

"Kai?,kaine ko?" Ta fada fuskarta tana narkewa a kansa.

Sultane dariya yayi,haisam na boye murmushinsa. Ya sani akwai abinda zai biyo baya duk ranar data karanci wannan gaskiyar.

"Shi ya tsara komai.....the hiding place....devices da ake komai kamar ina gurin,koda tari ko motsi daga masarautata.....the timing,muhammad haisam.....the silent one......alsaamit" Idanu ta zaro a hankali,saita juya inda haisam ke zaune gaba daya tana kallonsa.

"You!"

"YOU DID THIS TO ME?" Ta tambayeshi tana sake shiga mamaki. Yadda ya gudanar da komai......yadda yayi kaman da gaske sultane ya mutu alhali yasan yana raye. Yadda darare da yawa ya hana idanunsa bacci saboda ya bata comfort na gangar jiki dana zuci. Yadda yayi haquri da komai daga gareta. Duka wannan?....duka wannan kuma bayan yasan sultane yana raye ne?.

Ajiyar zuciya ya sauke quietly..... Already yasan wannan reaction din nata yana zuwa. Sunne kai kawai falaak keyi. Batasan sau nawa komai nasu zai dinga burgeta ba. Ita da maleek.....suna burge mutane da yawa......amma ita akhnan da haisam ne suke burgeta,duk da wanzuwarsu tare ba na wani lokaci me tsaho bane,amma ko na minti daya inde zasu kasance a guri daya sai taga wani abu daya tafi da ita.

"Akhnan" Ya kirata da ainihin sunanta murya qasa qasa saboda sultane dake gurin.

"No" Ta fada tana maqale kafada gami da d'aukan pillow ta jefa masa. Hannu yasa ya cafe.....wannan kallon tuhumar da take masa ya sanya ya kusa manta waye a gurin ya marairaice mata.

Tari sultane ya danyi,wanda ke cakude da dariya,kusanma don ya boye dariyar tasa ya saki tarin kadan.

"A idanunka na dinga kuka.....a idanunka na dinga jin zafin rasa sultane kana kallo......na suma duk don saboda kai?" Ta sake fada tana marairaicewa idanunta suna sake hada hawaye.

"You knew every single thing!”

"And you kept looking at me like nothing was happening!” ta qarashe fada da jefa masa harara.

Sultane dai yana gefe......still yana qoqarin adana dariyarsa bayaso ta fito. Ya lura rigima ce take jinta sosai,wadda shikam bazai iya sasancinta ba,da alama tafi qarfinsa.

"If I told you....."

"I WOULD HAVE HELPED!” ta tari numfashinsa. Wani siririn murmushi ya subuce haisam din Shima. Rigimammiya ce ya sani......amma yau a gaban bappinta take gwada masa rigimarta ta farko.

"That’s exactly why I couldn’t tell you.”

"You can’t lie to save your life.” wannan karon daga falaak har sultane dariyarsu sai data fito.

Juyawa akhnan tayi da ragowar hawayenta tana duban sultane da falaak.

"Bappi....you're supporting him?" Ta tambaya da french.

"I'm enjoying this" Ya fada abinsa a nutse.

Juyawa tayi tana sake harara haisam,hararar da take qara mata kyau ita da blue eyes dinta gaba daya.

"I was dying from grief!”

“And you kept saying mysterious things like ‘trust me a little longer’!” MITA?. Ya tambayi kansa yana matse tasa dariyar,yaushe kuma ta koyi mita?.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Giiftii....did you survive?" Ya tambaya a nutse,tambayar data saka falaak cusa kanta a pillow kaman wadda ta kwanta kawai,saidai dariyar ta take cinyewa. Baki akhnan ta bude cikin mamaki tana dubansa da idanunta dukka a waje.

"That's not the point wallahi" Ta fada hawayenta suna gangarowa. Tuhumarsa take a baki.....amma kimarsa ce take ninkuwa a zuciyarta. Da qyar sultane ya saita dariyarsa.

"Haisam...." Ya kirashi.

"Ka cancanci fushin nan fa"

"Na sani bappi.....na sani" Ya fada da sauri.

Ta lura kaman shi da sultane abu daya ne.... Bakinsu daya,sai ta hade hannayenta a qirji tana duban haisam.

“I’m not talking to you.”

Sai ya d'an sunkuya kusa da ita.

“You said that yesterday too.” yana jin kamar ana fusgarsa cikin wannan sabuwar character din tata.

“And I mean it today.”

“Habibti…” ya kirata.

“If I could choose between you hating me…”

“…or losing you to Mammina’s plans…”

“…I would hide it all over again.”

Kasa magana tayi,har na kusan second uku,saboda duk da haushinta—
zuciyarta ta kasa qin fahimtar dalilinsa. Komai ya furta sai taji ya samu gurbi.....ya samu kyakkyawan muhalli a zuciyarta.

Kauda kanta tayi.....tana pretending fushi dashi.

“I’m still angry.” wani murmushi me cike da nutsuwa da kwanciyar hankali ya sauke. Ya sani.....komai da take pretending ne. Zuciyarta a tafin hannunsa take. Bayan a tafin hannun nasa ma......a bude kamar budadden faifai. Lokaci kawai yake jira isashe ya fara dura mata duk abinda yakeso.....ya sake maidata yadda yakeso ta kasance.

“Good.” kawai yace,bayaso aci gaba.....zai iya sauka hanya a gaban bappinta.

“What’s good about that?!” ta tambayeshi tana dan tsuke qaramin bakin nan nata.

“It means you finally have the strength to fight with me again.”

"Sai da safenku" Suka tsinci muryar falaak tana fada.....sai a sannan suka lura sultane ma shi tuni ya kusa bakin qofa abinsa. Kunya tadan kamasu.....amma sultane kamar baiga komai ba ya dakatar da haisam dake shirin masa rakiya.

"Ka zunguro sama da kara.....ka koma ka kashe wannan sabuwar qurar data tashi kuma" Maganan ya sakashi sakin sassanyan murmushi,yayi qasa da kansa yana fadin.

"A sauka lafiya" Ya maida qofar ya rufe yana durfafo akhnan din idanunsa a kanta,yanason tantance meye dalilin sabuwar rigima da sabuwar tsiwar data koyo?.

★★★Asubahin washegari......Sanda yake takowa a nutse zuwa dakin bayan fitowarsa daga sallar asuba.

Sanye yake da baqar baqar silk throb data dace da hasken fatarnan tasa ta qabilar oromo,wani irin fari me kyan gani wanda ya cakuda da hutu da kula da kai da jikinsa da yakeyi.

Itace abu na farko da idanunsa suka fara sauka akai bayan shigowarsa dakin. Tana zaune sosai saman green din abun sallah,kamar yadda tufafin jikinta suke da wannan kalar. Qur'ani ne riqe a hannunta,hasken safiya dake hudowa yana sauka a hankali saman fuskarta.

Calmly ya zauna ba tare da yayi sallama ba ganin karatu take. Karon farko da ya fara jin sautin muryarta a fili cikin karatun qur'ani.

"Ma sha Allah" Yake maimaitawa saboda yadda muryar ta masa dadi,da kuma yadda yaga dabi'unsa sun fara nasarta.

Tana bacci ya fita,ya sanya mata alarm ne kawai,tun cikin dare suna tare da sultane anata shawarwari da qoqarin gyara b'arnar da mammina tayi.

Takai ayar qarshe,idanunsa yana kanta,ta rufe qur'anin a hankali ta ajiyeshi.

"Barka da asuba.....ina kwana" Ta hada dukka ta fada tana dubansa da idanuntan nan da suka rusuna suke nuna alamun bacci bai isheta ba.

Bai amsa ba,saici gaba da yayi da kallonta.

"You’re staring again.” ta fada da murmushi a fuskarta tana tuna daren jiya yadda ya gama rudata da saqonninsa ya kuma janye jikinsa ba tare daya mata komai ba. Karo na biyu kenan..... Abun sai taji kawai ya tsaye mata kadan a wuya.....zuciyarta kuma na zolayarta da YAUSHE KIKASAN DADINSA NE?. Saidai zancan gaskiya.....a jiyan abun ya tsaye mata sosai....ta zurma da yawa.....bata kuma zaci zai barta ba saboda yadda taga shima ya fita hayyacinsa.

"You’re peaceful when you read Qur’an.”

"I like watching that" Ya qarasa fada yana motsa labban nan nasa da suka fusgi hankalinta. Labban sa muddin zai azasu saman nata......sai taji komai na duniya yana kwance mata.

Sauke idanunta tayi cikin wata siririyar kunya da yaga ta mata kyau sosai. Kaman ba ita bace a daren jiya ta nemi fita daga akhnan dinta ba zuwa cikakkiyar matar aure me buqatar kasancewa da mijinta ba. Saidai wannan little izzar ita ta taimaketa ta dawo saitinta.

"Call birra.....ta taimaka miki kiyi packing abun buqatarki daya zama necessary ki dauka" Ya fada yana lumshe idanunsa a hankali. Yana tuna wayar da sukayi da nanay a daren jiya can cikin dare. Yau zata iso agadez.....zatazo taga safiyyanta. Ta gaya masa tunda aikinsa ya kammalu......tanaso taga safiyyanta kada taje ajali ya raba ganawarsu. Ta fada masa.....zasu taho da dukka yaran......balqess ce kawai ba zata samu zuwa ba..

Ta kuma sake gaya masa zasuyi daukan amarya ne.....zasu dauki akhnan idan sun gama kwanakinsu,zasu wuce da ita gidanta Kai tsaye idan suka sauka a jimma ta tare a can.

Duk jikinsa yaji yayi laushi,shi bazai sake bari wani abu ya shiga tsakaninsa da matar sa har ya rabasu ba. A yanzu bayajin yana da wannan kunyar......wannan karar tasa dukka babu ita. Yana mazewa ne kawai bayason tabata a agadez.....kada ayi abun kunya.....amma yanzu da komai ya qare......yanaso ya nuna mata zahirin RAYUWA. Yanason ta sake sanin WAYESHI?. Yana kuma son idanunta su bude sosai.

Yanason soyayya da matuqar qurewar da tun kafin yayi aure yakejin zai iya haqura da komai idan matarsa bata iya ba.....amma banda soyayya. Soyayya ta gaske.....bawai intimacy ba.....ba kwanciyar auren kawai da rungume rungume ba. Soyayya me dafa zuciya.....wadda ana iya rayuwa da abokin rayuwa da kowacce naqasa da sai samu. Saboda ZUCIYAR ta dahu da soyayyar...... ZUCIYAR kuma ita akeso.

"Me yasa?" Ta tambayeshi a nutse. Kasa daurewa yayi,sai dayakai hannunsa ya shafi gefan fuskarta.

"Because I’m taking my wife somewhere.”
Chapter 140 · 0% Book details