← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 176

Sashe 108

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"You waited awake......thank you" Ya fada yana cire agogon hannunsa idanunsa a kanta.

Kasa amsawa tayi,don har yanzu zuciyarta tana processing komai a kansa. Taku biyu ya qara ya matso kusa da ita.

"What's it?" Ya furta yana shafa gefan fuskarta da lallausan tafin hannunsa.

"Wadanne mutane ne wadancan na daxun?" Wani faint smile ya taba lips dinsa. Kamar ya fahimci inda tunaninta ya dosa

"Business associates" Ya amsa mata a hankali.

"No" Ta fada har cikin ranta,haka kawai taji bata gamsu da amsarsa ba.

"....people don’t look at ordinary businessmen like that.”. Magananta ya sauka kunnensa a hankali,shuru ya ratsa na wasu sakanni,sai ya sake takowa yana sake riga tazarar dake tsakaninsu sosai da wani irin kusanci,don har yanzu bai shirya bata license na sanin waye haisam in full details ba. Da wani irin low voice ya kalleta.

"And yet....." Ya fada yana kulle idanunta cikin nasa.

"…you still look at me like I’m only Haisam.” kasa magana tayi,yana sake dora mata kunyarsa. Batasan adadin yadda take kallonsa ba,ita kanta kamar idanunta sun rasa control haka takeji.

Murmushi ya sake mata dan kadan,saidai zurfinsa a zuciyarta yana da yawan gaske. Yakai hannunsa yana dan janye mata gashin kanta daya sauko kaman zari rufe mata ido.

"I think that’s my favorite thing about you.”

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Tanaso ta tsaida kallonsa haka,amma abubuwan mamaki yake bata episode episode. Tayi tsam da ranta tana duban inuwarsa ta gefe kamar tana qoqarin hada mutum biyu guri guda.

Haisam din dake mata magana cikin laushi......karyar da kai da karya matsayinsa. Haisam din dake iya roqonta.....haisam din dake iya bata haquri.....haisam din dake koma mata tamkar qaramin yaro. Da kuma mutumin da manyan mutane ke rusunawa.....mutumin da manyan mutane ke biye dashi a baya.......mutumin da manyan mutanen ke rakashi har bakin mota cikin girmamawa.

Baya ya janye mata kadan,ya saka hannu yana cire cufflinks dinsa a nutse yana ajiyewa saman table.

"Ban sanka sani na haqiqa ba" Ta fada a sanyaye,tana tsoron fadawa inda aka girmi matsayinta da Nisan tazarar da zata wafce dukka kimarta

"Really?" Ya furta yana dage dukka girarsa gaba daya idanunsa suna rusunawa sosai kaman wanda yasha wani abun maye. Idanunta ta sake zarewa a hankali,da gaske takeso ya dauki abinda take gaya masa.

"Kullum saina gano sabon abu game dakai....." Saita dakata.

".....me girma" Ta dora da fadi numfashinta yana sauyawa. Yadda numfashinta ya canza hakan yaji ya tabashi sosai. Ta yaya zai iya jurewa ci gaba da jinyarta ne?,tana juyewa da wani salo da baisanta dashi a baya ba. Sai shima yaja da baya yana jingina da table din dake kusa dashi don ya bashi support. Idanunsa baibar fuskarta ba

"And does that scare you?". Ta fahimci wasa da kuma tsokana kawai yakeson maida zancan. Amma gaskiya ne.....kadan kadan abubuwan suna bata tsoro.

"......A little" Ta yanke shawarar fadin gaskiyar abinda yake ranta.

Wani siririn murmushi ya taba lips dinsa,murmushin fahimtar gaskiyarta da take fada,murmushin fahimtar bata iya boye abinda yake ranta sosai ba.

"Na fahimta......zaizo ya wuce,kema zaki fahimci komai...amma" Ya fadi yana dakatawa.

"You missed me after only a few hours right?" Idanu ta waro sosai tana sake jin mamakinsa da tsoronsa.

"Bance haka ba" Ta fadi da yanayin son karya hasashensa. Can qasa yayi dariya irin wacce ba kasafai yake yinta ba.

Idanunsa sun sake rusunawa sosai sanda yake takowa yana dawowa gabanta.

"You waited by the window" Ya fada calmly yana sake riqe qugunta da duka hannayensa,kaman wanda ake busawa siririyar sarewa take shiga kunnuwansu a hankali.

"You watched for my cars...." Ya sake fada muryarsa tana sakeyin qasa.

"......And your heartbeat changed the second I walked in.” ya fadi da muryar rada wadda ta raunata dukkan jinta da gangar jikinta.

Kunya.....wata irin kunya ta sake lullubeta

"Haisam....." Ta furta da wata kalan kasalalliyar murya. Sai ya sake matseta sosai a jikinsa,yasa yatsansa yana daga habarta a hankali.

"Say it" Ya fada cikin rad'a

"Me....." Ta fada muryarta tana sake zuqewa itama

"That you missed me...." Ya qarasa maganansa ta farko. Da sauri ta girgiza kai,sai ya saki wani kasalallen murmushi......wannan dangerous calm smile din.

"Liar" Ya furta a hankali. Zame fuskarta tayi saboda yadda taji dukka jikinta yana amsawa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 97*
_________________________
https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee*
__________________________

Maganansa ya sanya ta kasa hana qaramin murmushin dake fuskarta fitowa. Sai ta juya zata wuce,still ya kamo yatsuntsa a hankali

"Relax mana....." Ya ha fada yana kashe mata idanunsa.

"I'm teasing you...."sai ya sakar mata hannun a hankali yana sassauta tie din wuyansa idanunsa a kanta still.

" Na gaji" Ta sakejin ya fada sanda shuru ke shirin musu kutse. Daga kai tayi a hankali ta kalleshi. Yadda ya fadi kalmar ne ya sanya ta lura da gajiyar dake boye a muryarsa.

"Duk da wannam composure din......ashe ya gaji sosai" Ta furta can qasa ranta.

"Sannu" Ta furta kalmar da tarin kulawa cikin sautinta da kuma idanunta,abinda yaji ya masa dadi sosai,musamman sanda ta dora da fadin.

"Da alama yau me wahala ce" Idanunsa ya lumshe har kamar bazai bude ba. 'Yar qaramar kulawarta tana nufin abubuwa da dama cikin ranshi dama darensa na yau. Sai kuma ya saki numfashi a hankali yana warware cuff din hannunsa

"Meetings.....investors....royal approval......" Ya sake lumshe idanunsa yana dorawa

".....and too many people talking at once....." fada a hankali duk da ba amsar da yayi niyyar bata ba kenan,amma sai yaga ko yaya.....ko yaya ta cancanci taji wani abu koda kadanne da zai kwantar mata da hankali.

Maganarsa ta qarshe ta kusa sanyata tuntsurewa da dariua,ta kuma shafe abinda ya kamata ace hankalinta yakai kai. Wato kaman itane.....a duk sanda tayi calling for meeting a sahel couture ba'a cika lokacin ake tashi. Batason hayaniya da dogon magana,amma shi da alama ya fita.

Ta murmusa cike da burgewa sannan tace.

"Amma ka iya handling komai calmly" Maganan ya qwace daga bakinta,don ba'a zahiri taso furta hakan ba,zuciyarta taso barwa.

Idanunsa ya sake dai lumshewar yana budesu dukka a kanta kaman ya qara musu girma yanason ganinta sosai.

"Wannan calmness din.....yana disappearing sometimes around you my princess" Bugawa zuciyarta tayi a hankali,ta buga da wani yanayi daya isa har kunnenta ya kuma sanya numfashinta nauyi cikin qirjinta.

Suits dinsa na saman ya zare a nutse,kai tsaye kuma ya miqa mata,kamar wanda ya saba yin hakan tunda dadewa.

"Zanje nayi wanka na dawo before you start over thinking life again". Rusunawa tayi tana karbar rigar daga hannunsa,wani yanayi daya tilasta masa binta da kallo sanda take juyawa tana wucewa daki da rigar.

A hankali idanunsa suka sauka akan qugunta,yadda yake juyawa kaman wanda ke karbar umarni daga wani guri,sai ya samu kansa da miqa hannu kaman zai kamota,sai kuma a hankali ya maida hannun nasa ya dunqule,murmushi yana qwace masa,ya taka a nutse yana bin bayanta.

Haka kurum tunaninta yayi nisa sanda takejin motsin saukar ruwa a bathroom din. Me ya kamata tayi?,yace ya gaji.

Samun kanta tayi da duba menu dinnan da nanay ta aiko mata a gida a wancan lokacin,ta kammala dubawa tas,sai ta saki qaramin murmushi tana cije lips dinta,ta ajiye wayar tana miqewa,a hankali kuma ta furta

"Suruka ta gari".

Mintuna kusan arba'in ya dauka,sannan ya fito parlor din sanye da black silk trouser da farar t-shirt me laushi. Sassalkar sumar nan me santsi da ragowar damshi a cikinta. Qamshin fresh oud da sandalwood na biye dashi qafa da qafa. Yau wani qamshi na daban takeji a tare dashi,baqon qamshin da tunda suke sai yau ta fara jinsa a tattare dashi.

Sauyin qamshin ne yaja hankalinta. A nutse ta daga kanta daga amsa messages na falaak da takeyi ta zube kallonta a kansa. Ya mata kyau....wani irin sassanyan kyau,ko don bata saba ganinsa cikin qananun kaya haka bane?. Data tuna a gaban wa take kuma saita sauke kanta da sauri.

"You're staring"

"Ban kalla ba" Ta amsa da sauri,wata tattausar dariya ya sake.

"Another lie". Kai ta dauke tana sake jin nauyinsa,yayin da shi kuma ya aza idanunsa akan gurin.

Wani irin luxury setup ne.....da warmlight ne a gurin me kwantar da zuciya.

" Wow......ma sha Allah" Ya fada yana qarasawa. An ajiye pillows masu laushi qananu qananu wadanda yafi jin dadin zama a cikinsu yaci abinci duk sanda ya gaji irin haka.

"Waye ya baki satar amsa?" Ya tambayeta kai tsaye bayan ya zauna yana dubanta murmushi yana qin barin fuskarsa.
Chapter 108 · 0% Book details