Sashe 68
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mammina......kusanci da mammina" Zuciyarta ta bata amsa kai tsaye,amsar data tsaya cak cikin kanta tare da riqo hannunta da haisam din yayi cikin nasa yana fadin.
"Muje" Tadan kalleshi kadan,suka hada idanu sai ta basar. Ta fahimci kamar ya soma sabawa kansa da wasu abubuwa game da ita,kaman riqe hannunta,yana nema yayi normalizing din abu gaba daya.
Kanta ta daga cike da wani hargitsi sanda nanay ke fitowa,ta dauka zata gansu su ukune,shi nanay din da matar tashi,saidai ganin nanay ita kadai ya sanyata kafe nanay da idanu,maimakon tarin tambayoyin da su noorah suka baibayeta dashi,
Murmushi ta sakar musu tana zama tsakiyarsu.
"Ba iya surukata kawai haisam ya kawomin ba......harda tsohon mafarkina.....tsohon burina dukka ya tattara ya kawomin,diyata haisam ya shiga duniya ya nemo min.....bazan gaya muku wace ba,zanga waye zai iya gane me nake nufi bayan ta fito" Ta fada tana murmushi.
Cecekuce suka fara a tsakaninsu,kowa yana son canka,kowa yana son fadin albarkacin bakinsa,saidai ga saamee kuwa,wani qarin firgicin ta sake shiga,
Wacce diya ce ta nanay bayan su dinnan dake gabanta?,wacce diyace haka data samarwa nanay wani irin launin farinciki daga shigarta gurinta wanda ta dade ita bata gani ba a tare da ita?.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Kacamewar da sukayi da magana sai ya hadu da tunanin qwaqwalwarta kwanyarta ta soma nauyi,nauyin da bata fahimci me girma bane sai sanda idanunta suka sauka kan farar qafar haisam data fara shigowa wanda ke sa ye cikin lallausan baqin takalmi na fata.
A hautsine tayi gaba kadan da idanunnata,suka sauketa kan qafafun akhnan din dake dauke da zara zaran yatsunta da suke da alamun ragowar lalle a rabin kowanne farce.
Da wata nutsuwa data tilastawa kanta,da wani matsanancin bugun zuciya take daga idanunta don isa ga fuskar akhnan da take bala'in dokin son ganinta. Wacece ita?,me zata gwada mata?,dame ta fita?.
Daidai sanda idanunta suka kai kan fuskartata,daidai sanda akhnan din ke daga kanta a hankali tana laluben fuskar noorah. Ta riqe muryar yarinyar da tayi kiransu har sau biyu a dazu,shi yasa a yanzun data sake jin muryarta dab da ita ta daga kanta don ganinta.
Wani sashe ne na zuciyarta taji ya zaftare daga qirjinta yana neman hanyar da zai fado. Wani tsoro shock da wani irin razani ya mamaye ruhinta zuciyarta gangar jikinta dama b'argonta gaba daya.
"Ya Allahu.....ya Allahu" Ta fada can qasan zuciyarta bakinta yana rawa,kaman yadda hannuwanta da qafafunta dukka suke rawa.
Takawa takeyi a hankali,idanunta har yanzu a qasa kadan,hannuwan noorah cikin nata ta riqesu da kyau cikin siraran yatsunta.
Ta dauka zata ganta macace kamar kowacce mace,amma sai take ganin wata TAFISU....wata mace da sunan macen kawai tayi tarayya dashi da sauran mata.....amma komai nata na dabanne. Komai nata yana nuna ainihin ma'anar kalmar KYAU.....yanayinta zubinta gaba daya yana nuna asalin abinda IZZA da qasaita ke nufi. Bata zauna da ita koda na minti.uku ba,amma daga nan inda take zaune abubuwa take hanga tattare da ita masu nauyi. Idanunta yakai kan blue eyes dinnan nata,wani nau'in kalar blue eyes da bata taba ganin irinshi ba. Wata irin fuska da aka azurtata da sassanyan kyan da ko ita ta sani KYAKKYAWA ce,duk yadda takeji a lokacin bata isa ta qaryata wannan ba.....hasalima yana daya daga cikin abu mafi daga hankali da birkitata a yanyanzun
Wata irin tafiya take majestically,natural grace,blue eyes dinta ta sake kalla,ba irin wanda ta sani bane,ba kuma irin wanda ta saba gani bane. Wannan kalan blue din me wani irin kyau ne da wani haske me daukan hankali a cikinsa.
"Ta yaya zai iya tsallake idanuwansa daga kan wannan halittar?" Wata zuciyar ta rada mata a hankali,saita maida idanunta ta lumshe tana jin haushin gaskiyar da zuciyartata ta gaya mata,tana jin yadda bugun zuciyartata ke sake ninkuwa,yana kuma sake tsananta da wani irin mahaukacin kishi.
"Ta fini.....ta fini tako ina na yarda.....amma na fita kusanci dashi,na fita kusanci da nanay,na fita kusanci da sanin komai da yakeso,don haka ina da nawa quality din,ina da sauran quality din da zan karbeshi" Ta fadawa kanta a hautsine tana sake bude idanunta tarwai a kansu.
Wannan karon daya hannun nata dake cikin na haisam idanunta suka sauka. Yatsunsa cikin nata ya sarqafesu sosai kaman wanda ke tsoron zata subuce masa. Karo na farko.....lokaci na farko a rayuwarta da taga hannunsa cikin na wata d'iya mace. Wadannan zara zaran yatsun nasa da suka jima suna burgeta,wannan yatsun nasa da takan jima tana kallonsu musamman idan yana rubutu da wani irin salon burgewa dake jan hankalinta. Wani abu ne zafi ya sake matse zuciyarta.
"Zo nan d'iyata" Kalmar nanay ta sanya kowa ya koma cikin nutsuwarsa,ta fada ne saboda tayi saving akhnan kan yadda rumaisa Aanani da noorah suka baibayeta kowa yanason ta fara bashi kulawarta.
Da idanun nan nata take kallonsu.....wani irin kallo daya motsa asalin farinciki daga zuciyarta. Murmushi ne kwance saman fuskarta ba tare data sani ba,dukkaninsu burgeta sukeyi,burgeta sukeyi da wani irin yanayi da bata taba sanin akwaishi ba. Family guda....ahali guda.....iyali guda,wasu na kama da wasu a cikinsu,nutsuwa da tarin kamewa da qaunar da take gani tasu a idanunta. Me ta musu data cancanci wannan soyayyar da kulawar?.
Kama hannunta nanay tayi,ta zaunar da ita saman kujerar data tashi. Idanu saamee ta lumshe nauyin qirjinta yana neman rinjayarta. Wata kalar girmamawa take gani daga gurin mama oromo.....mama oromo me tarin girma da kuma matsayin da ita kanta tasan ba qarami bane. Ita take tashi daga muhalli sannan ta zaunar da wata?,wani babban alama na qarshen girmamawa a al'adarsu.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 62*
"Waye zai iya gayamin.....diyata ta wanne bangarene?....ni kuma na bashi kyautar da bazai manta da ita ba" Ta fada tana murmushi tana kuma rarraba dubanta tsakanin fuskokinsu gaba daya.
Murmushin dole saamee ta qirqiro sanda idanun nanay ya sauka akan fuskarta. Ta motsa bakinta kadan,saidai wani abu daya dunqule mata a wuya ya hanata cewa komai.
"Ina ganin kamanni nanay,saidai banason fada na daga miki hankali" Balqess ta furta a hankali idanunta akan akhnan wadda kanta yake qasa har yanxu,hannuwan noorah kuma suna cikin nata.
Yarinyar taqi yarda sam ta matsa daga kusa da itama,tana jinta a yau a yanzu kamar tana cikin family dinta,kamar tana cikin ahalinta,wani irin sakewa da wani farinciki dake huda zuciyarta. Daga sanda ta biyoshi kawai ta dauka ta rasa komai nata......amma a yanzu da take ganin abubuwa tamkar musanye akayi mata zuwa mataki na gaba.
Daga shehnaz da aisa kawai take samun irin wannan abun da sakewar,amma a yanzun saiga ninkinsu a gabanta kowa na qoqarin nuna mata kulawa.
"Safeena nanay.....momma safeena idan zan iya tunawa daidai" Balqess ta fadi tana kasa jiran amsar nanay to umarninta na fadin abinda ke zuciyarta.
Sunan ya daki zuciyar saamee,ba ita kadai ba,indai zaka zauna da nanay na kwanaki uku saika san da wadannan mutanen guda biyu. Safiyya da safeena,tana jin bugun zuciyarta har cikin kunnenta,ta daga idanunta a hankali tana saukewa kan fuskar akhnan kafin ta janye,kunnuwanta na jiye mata sanda nanay ke bada tabbaci.
"Itace.......jinin safeena ce ta dawo,saidai mun rasa safeena.....amma alhamdulillah,safiyya tana raye". Ko na second daya ba zata iya sake zama a gurin ba haka taji,saita motsa qafafunta da takejin kamar sun mace,ko kuma basa iya amfani a jikinta,ta miqe tana sulalewa gami da nufar qofar fita a parlour din. Kawai tana jin tata ta qare......tana bata da wani sauran hope akan wai soyayyar nanay zata buda mata.hanya a zuciyar haisam,don koda wasa ba zata hada soyayyar safeena da tata soyayyar a zuciyarta ba.
Yadda kowacce ke sake mamakin abun ya ajiye wani abu me girma game da mutanen a zuciyar akhnan. Sai taji ta matsu ta sake samun cikakken haske.....da cikakken tarihin alaqar mamminta da wadannan ahalin.
"Ya akayi yasan da wannan alaqar wai?" Ta fadi tana satar kallonsa ta can qasan idanunta sanda yake tsaye hannayensa goye a qirjinsa,lokacin da aka gama shirya kyautukan mama oromo hajiya khadeeja yunnus jallata a gabanta.
Abinda ya sake bata mamaki,yadda kowa a cikin su ya shiga bada umarni ana shigowa da tasa kyautar.....kowa ciki harda auta noorah.
Wani abu da taji ya burgeta,wani abu daya alamta mata tabbas akwai qauna da shaquwa me girma a tsakaninsu,tasa hannu ta tallafi akwatin da noorah ta bata na tata kyautar. Ta kasa budeshi tana juyashi kawai a kunyace.
"Kyautar maraba daga iyalin motii aba jifar ne wannan" Zenebu ta fadi tana rusunawa a gaban akhnan.
"Na gode.....na gode qwarai" Ta fada da harshen turanci wanda kusan dashi suketa magana,don har yanzu ba cikakken communication a tsakaninsu. Kadan kadan take tsintar yaren oromo din,wanda shima bai wuce gaisuwa ba irinsu akkam jirta da sauransu,hakanan suma basu iya French ba hakanan basu iya yaren Tuareg ba,hausarsu da qyar take fita,abinda zai alamta maka basa mu'amala da masu yaren.
"Bazan tafi nabar diyata ba......tuntuni na aike masarauta anyi shela,qafata qafarta,wannan rainon.....wannan tarbiyyar nice da kaina zan qarasa dasata" Nanay ta fadi tana kallon agogo wanda yake nuna yammaci na gabatowa.
Kadan ya murmusa,yana zare hannuwansa daga aljihun wandonsa,yadan saci kallon akhnan din sannan ya dauke kanshi.
"Duk yadda kikace haka za'ayi in sha Allah".
Awa daya tak tasa a dauke duk wani abu daya shafi akhnan daga gidan,tasa aka qara motoci aka kuma shirya komai bisa tsari,suka fara gaba,sannan sukayi sallah tare da cin abincin dare,sa'annan suka wuce zuwa aba jifar palace.
Duk wannan abun tana qarqashin kulawa da soyayya ta 'yan uwan haisam,kowa kaffa kaffa yake da motsinta da bata wani irin kulawa. Noorah kuwa tana maqale da ita,kamar wannan matsayin na haisam dukka ta tattara ta maidashi ga akhnan din.