← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 176

Sashe 90

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuciyarta ta buga,a rayuwa batasan sau nawa zai kasheta ba.....batasan sau nawa yakeso ta mace a kansa ba. Ko har sai tayi hauka?,ko har sai ta fito tana gayawa duk wanda ta sani dama duk wanda ta gamu dashi?.

"I....." Ta soma fadi,amma sai ya girgiza kansa a hankali yana qulle idanunsa cikin nata.

"Noo" Da wata muryar me zurfi da yake zarcewa tana komawa cikin maqoshinsa.

"Say my name" .

Ji take kaman zata sume,saita lumshe idonta na daqiqa daya,sannan ta sake budesu slowly.

"Haisaamm" Kalmar ta fito da wani irin taushi da amo,sannan ta zarce tana gauraya da shurun cikin dakin.

A hankali ya daga yatsansa ya aza saman lips dinta,ya fara zagayasu a hankali,wani irin lallausan qaramin murmushi na gefan baki tana subuce masa. Idanunta ta maida tana sakeyin luuu kamar wadda zata tafi ta suma,saidai ba suman bane.....ita daya tasan irin bala'in da abinda yakeyi yake saukar mata cikin jikinta,ya tayar da kowacce tsiga ta jikinta har tana jin tana tsuma sosai.

"Be careful Akhnan......I’m becoming addicted to that voice.” ya fadi yana qarasa hade tazarar dake tsakaninsu ta hanyar manneta a jikinsa.

" Ko sau dubu nawa.....ko sau miliyan nawa nake buqatar naji.....don Allah...karkiyi rowar fada" Ya qarasa maganan yana manne fuskarsa jikin dogon wuyanta dake fidda qamshin skin product dinsa. Qamshin da tunda yake amfani dasu sai a yanzun ya soma jin dadinsa.....saman fatarta,lallausar fatar da bai taba zaton akwai jikin wani dan adam da za'a samu da laushi da santsi irin haka ba.

Wani numfashi taja sosai tana damqe kafadunsa da duka hannayenta,tana jin kamar yana fusgar wani abu cikin kanta da gangar jikin ta gaba daya. A gefe guda kuma tana jin zazaabin dake jikinsa,zazzabin data dauka ya gayawa nanay ne kawai.....da gaske shine cikin jikinsa.

"......my healer.....bani da lafiya" Ya fada yana sake narke mata gaba daya a jiki,kamar duniyarsa batasan komai ba bayan jikin nata.

".....Muje ki bani magunguna na nasha" Ya furta yana daga kansa daga wuyan nata zuwa ga fuskarta ya hade fuskokinsu guri daya. Kalmar MAGUNGUNA daya fadi da kuma zazzabin da taji a jikinsa shine ya cire mata tunanin komai a ranta,cikin rawa murya da neman mafitar samun tazara a tsakaninsu kan yadda ya manne mata da yawa ba tare da tunanin komai ba tace.

"Muje". Wani boyayyeb murmushi ya saki ganin bata gane ba,rashin wayonta muraran yana fita,yana jin yana qara raina shekarunta tare da hango kusakurai a ainihin shekarunta. Abinda yafi aminta dashi,ta fara makaranta da wuri,ta kammala da wuri,wannan ya bata iya experience na kasuwanci da iya riqe kamfani kawai........ya dauke hankalinta daga sanin rayuwa da mu'amala. Don ta rayu ita kadai ne ba cikin jama'a ba. Ta rayu cikin kebantacciyar rayuwa ita daya.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

D'ai d'ai yayi saman gadon yana qare mata kallo sanda take kai kawo kawo tray na maganin da sauran dosage cap din dake ajiye guri daban.

Cikin ransa yakejin inama zai iya haqura ya barta ta huta sosai kaman yadda ya tsara......saidai shi kansa yasan a yanxin ba shine yake da control da kansa ba.

Zama tayi sosai tana zubawa tana miqa masa. Baiyi musu ba wannan karon ya dinga karba yana shanyewa. Saidai a duk sanda zata d'aga kanta ta kalleshi idanunta cikin nasa suke fadawa.

Sanda ta kammala tana daukewa kiran sallah ya ruskesu,sai ya miqe zuwa bathroom ya daura alwala,ya fito idonsa a kanta yana ware hannun rigarsa.

"Zaki bani maganin dare?" Ya tambaya idanunsa suna raunana. Still bata kawo komai ba ta gyada kanta a hankali sai ya juya ya fice yana murmushi.

Haka kawai ta samu kanta cikin kallon agogo,haka kawai ta samu kanta da liasafa yawan dadewarsa a waje bai shigo ciki ba.

Tana cikin lallausan duvet din data lullube har kanta,saboda sanyin Ac dake ratsata daya soma yi mata yawa.

Tsoro takeji sosai,zuciyarta kuma a raunane take,don tun bayan sallar isha'i ta soma jin rugugun hadari daya fara hade sararin samaniya.

Ba kowa a kusa,batasan inda wayarta take ba ballantana ta kira birra ta kasance a kusa da ita,ko ina akwai.haske tarwai,amma cikin zuciyarta tana jin kamar ita kadai ce ta rage,don haka sai kawai ta shiga toilet tayi wanka taci abinci,sannan ta koma tayi brush ta dawo dakin ji yadda iska ke daga manyan curtains din dake zagaye da dukkan wasu windows da doors na sashen.

Cikin sleepwear me kauri ta shirya data zaqulota da qyar a qarshen suitcase dinta. Saidai abun haushin wandon marabarsa da pant kadanne,don duka duka ya tsaye a cinyoyinta. Gwara rigar sakkiya ce me gajeran hannu,round neck ne bata da zip ko button ko daya,wannan shine abinda ya bata nutsuwa da kwanciyar hankali.

Bude jakar da nanay ta bata dazu tayi na turaren wutan shuwa incense(+234 704 229 3387),qamshin ya sauka a hancinta da wani irin laushi da taji ya dace da yanayi garin na yanzu.

Samun kanta tayi da takawa zuwa ga babbar burner din dake tsaye daidai musallah area na dakin,ta debi turaren wutan ta zuba,abinda bata taba yiba,aiki ne na hadimanta,sunsan yadda takeso guri koda yaushe ya zamana cikin qamshi.

Gaban madubin ta koma tana bude khumras din. Kowacce ta shanshana sai taji tayi mata,sai ta dinga budesu daya bayan daya tana zubawa a tafin hannunta ta soma mulke jikinta dasu. Body milk,humra misk,humra sandal,sannan ta hada genani da kulaccam ta sake mulke fatarta dasu.

Murmushi kawai takeyi tana jin yadda qamshin ya hadu dana turaren wutar yana gauraye dakin,yana kuma bada wani irin qamshi me saukar da farinciki da nutsuwa a zukata.

"Ya salam" Ta fada sanda ta nutse cikin duvet din,dukka qamshin suna ratsata da wani irin yanayi,saidai bata jima ba wani irin kewa da tuninsa suka cika mata zuciya,abinda ya sanyata wannan dubawar da lissafa lokacin,har zuciyarta tayi wani irin shuru kawai yana sauraren yayyafin dake daba glasses din dakunan dake lullube da curtains.

Har lullumshewa idanuwansa suke sanda ya fito daga wankan,wankan da yayishi saboda ya samu sassaucin zazzabin da yake d'anji.

Wasu sauqaqan silk pyjamas ya sanya marasa nauyi me gajeran wando,saboda gudun saka kaya masu nauyi da zasu sake tunzura zazzabin.

A nutse ya tura qofar dakin da wani irin kasala da mutuwar jiki da zazzabi yake saukarwa. Sai ya maida qofar dakin ya rufe a hankali,yanayin da yaga dakin da wani irin dim light yasa ya sanya a ransa tayi bacci.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 81*
____________________________
https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee*
__________________________

Yana takowa a hankali idanunsa suka sauka kan magungunansa na dazu,kaman ya biya yasha amma sai wannan kasalar tasa da sakalcin daya saba yiwa nanay ya hanashi,ya yanke gwara kawai ya kwanta a hakan. Remote na Ac din ya dauka ya kasheshi gaba daya,ya matsa ga windows din yana budesu yadda fresh air din zata samu daman shigowa.

Bai sani ba.....amma yana ganin kamar batasa muhimmanci fresh air ba,ba abinda yakeso a rayuwarsa sama da fresh air.

Yanayin dakin ya gauraya da tatacciyar iskar,sai ya sake maida dakin da wani yanayi na daban me sanyaya zuciya.

A hankali cikin nutsuwar nan tasa data dace da kowanne yanayi ya taka zuwa gaban gadon,kai tsaye ya sanya hannunsa ya janye duvet din data rufe har saman kanta dashi.

Wannan cute and innocent face din nata ya soma gani,qananun gashin kanta data daure tsakiyar kanta wasu duk sau hauro saman idanunta suna sajewa da wannan zara zaran gashin idanun nata da suka zama tamkar wani fure cikin shukoki a saman fuskartata. Yakai hannunsa a hankali ya shafasu yana janyewa gudun kada ya tadata.

"Akhnan" Ya furta can qasan maqoshinsa yana qarewa fuskarta kallo..

Wannan fuskar data riga ta kafe kanta cikin zuciyarsa da wani irin kafewa me matuqar tsaro da qarfi.....wannan fuskar data zama ta farko a duniya gaba daya daya soma yayewa hijabinsa......wannan fuskar data shiga da fita cikin kowanne tunaninsa take hanashi sukuni gaba daya. Fuskar nan dai da a duniya idan ka dauke nanay akwai fuskar data kaita daraja a idanunsa.

A hankali ya sunkuya ya bata forehead kiss da tausasan labbansa,sannan ya daidaita mata duvet din ta yadda zata samu numfashi me kyau.

Remote ya dauka yana sake rage kaifin dim light din dake fita ta ceiling din dakin,ya maida ya ajiye yana haurawa gadon a nutse.
Chapter 90 · 0% Book details