← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 176

Sashe 92

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ku nememu kai tsaye a wannan number don GYARA DA MAGANCE MATSALOLIN FATARKU*
0806 299 1549

*MG'S ORGANIC SOAPS*
*_takenmu (MAIDA TSOHUWA YARINYA....A SABUNTA YARINYA ZUWA SABUWAR HALITTA)_*
_________________________

Sai daya maidata jikinsa ya mata kyakkyawan riqo da zummar su koma bacci,sannan hawaye suka balle mata.

Dama.dalilin da yasa ya daukota daga gaban sultane?,ya kawota nan?,ya qirqiri ciwo kuma saboda ya azabtar da ita?.

Yayi tunanin ya barta ta rage hawayen saboda zuciyarta tayi sanyi amma sai ya kasa. Ci masa zuciya yakejin ana masa da wani irin yanayi me nauyi. Hannu ya miqa,ya dauki remote ya qara haske kadan na dakin,zuwa sannan ruwan sama ya kece sosai,abu daya daya hana akhnan ce masa yabar mata saman gadon.

"Giiftii" Ya kirata da sunan da zuwa yanzu ta fara jin girmansa. Bata amsa ba,dama kuma bai sanya ran amsawar ba,wani yanayi ne daya shirya tunkarar kowanne hukunci ta shirya yi.

"I'm so sorry please" Ya furta da muryar da take sirri ce tsakaninsa da ita kawai. Ta bude baki zata kira sunansa da nufin gaya masa ya barta ya qyaleta,amma sai ya girgiza kai.

"Ki barni na gama magana...."

"Bankai matsayin na zama wanda zai saki kuka ba......ina neman afuwa dana sanya gimbiyar agadez kuka" Ya fada yana kwantar da kansa a hankali saman kanta kamar wanda zuciyarsa ta karye. Ya bawa shuru dama na wasu daqiqu sannan yace.

"Na yi kuskure… I should have been more careful.” sai ya dakata.

"More gentle.......more patient" Sai ya daga kan nasa ya saka hannunsa yana dagowa da fuskarta. Idanunta a runtse suke alamun batason kallonsa.

"Ki sani… ba na jin dadi idan na ga hawaye a idon mace." Muryarsa ta sake wani laushi da zurfi.

"Kuma idan har nine dalilinsu....." Sai ya sake dakatawa kamar me zaben kalmomin.

"To nafi kowa jin zafi".

Wani kyakkyawan sauka kalamansa suke mata saman zuciyarta tamkar saukar fiffike. Taja wata ajiyar zuciya 'yar siririya wadda ta alamtawa haisam zuciyarta ta fara samun nutsuwa da sassauci.

"Ki gafarceni....." Shuru

"Ba saboda in tilasta miki ba....ko don ke kanki" Ya sauke idanunsa qasan labbanta a hankali.

"Because you deserve peace… not confusion.”

Tass ta lalubi duk wani fushi daga qasan zuciyarta ta rasa. Kamar yayi amfani da hypo ya wanke farin tufafin da suka baci da datti.

"Naji" Ta samu kanta da furtawa a hankali. Murmushi ya saki me taushi,a yau yaga wani other side din nata. Saurin yafiya.....afuwa da zuciya me taushi.

"Zonan" Ya fada kaman wata tazara ce me yawa a tsakaninsu yana sake jawota cikin jikinsa.

"I'm here now.....just for you....just for your comfort...." Ya sauke numfashi

"Kukan ya isa haka.....ki huta" Ya qarasa fada yana sauke mata tattausan kiss dinnan da take jinsa har tsakiyar zuciyarta duk sanda ya sakar mata shi.

Wani irin bacci sukayi shi da ita,wani ni'imtaccen bacci daya kusa waftarsa ya kusa wuce lokacin daya kamata ya fita sallah.

Wani abune daya manta a rayuwarsa wato ranar daya makara sallar asuba.

Dakinsa ya wuce ya sake wanka,don bayajin zai dawo da wuri daga masallaci. Akwai wani issue daya taso da yakeso daga masallacin ya wuce don yayi ya kammala ya dawo da wuri yayi jinyar b'arnarsa. Dan qaramin bincike ne a wajensa da yake ganin awa hudu zuwa biyar sun isheshi ya kammala,dalilin dadewarsa kenan a jiya,ziyarar sirri ne da gwamanan jimma ya kawo masa akan issue.

Koda yace awa hudu ko biyar zai kammala,sun yarda dashi,saboda sun san wayeshi. Maye ne kuma qwararre kan aikinsa da wata irin qwarewa ta samu gindin zama a wajensa. Hakanan idan abu zai yuwu zai yuwu,idan baze yuwu ba zai fadi,kai tsaye.....kaifi daya da baya sauya zance.

Cikin qatar thobe ya shirya ruwan zuma data color din tayi kama zata saje da launin fatarsa,saidai hakan bai hana bayyanar kyan data masa ba.

Har sanda ya dawo dakin yana zuba wannan sassanyan qamshin nasa bacci take. Bayaso ya tadata tun yanzu,kuma bayaso ta rasa sallar asuba,sai ya dauki wayarta ya gyara alarm din da kwanaki ya cire ya qara mata mintunan da zai tasheta yadda lokaci bazai qwace mata ba,lokacin sallar bazai wuce ba. Ya ajiye mata daga saitin kanta kusa da bedside lamp,ya sunkuya softly yayi kissing goshinta yana ja da baya.

Wani soyayyarta ce take hudashi da wani irin yanayi dashi kansa baisanshi ba. Wani irin shigarsa take a hankali. A halin yanzu.....a yadda yakejinsa koda quda me cutarwa bayajin zai iya qyaleshi ya sauka a kanta. RAYUWARSA ce muraran yake kalla tsakanin fuskarta,walwalarsa ce.....da DUNIYARSA gaba daya.

Yaso ace kafin ya fita ya tattare zanin gadon ya sauya da wani,to amma dole ya barshi,saboda inde zai sauyashi zai tasheta ne abinda baya so,tunda tana da ragowar lokacin da zata iya qara baccinta hankali kwance. Sai daya tsaya ya sake waiwayowa kaman wanda akace masa idan ya fita bazai sake dawowa ya sameta ba,yaja qofar a hankali yana furta.

"Fi amanillah"

A hankali ta bude idanunta sanda alarm din ke kadawa da tattausan kiran sallar nan daga bakin zaqaqurin ladanin nan,limamin masallacin harami dake makkah.

Ba iya siririn hasken da dakin ke dashi kawai ta gani ba,aah......harda lallausan qamshin nan nasa da taji ya cika mata hancinta.

Waiwayawa tayi kaman me neman wani abu,ba kowa.....baya kusa da ita,sai pillows da duvet daya barta dashi,sai taji kamar gadon yayi fadi da yawa.

Fuskarta ta yamutsa tana jin yadda kanta yayi mata nauyi,dukkanin jikinta babu dadi,yanayi na zazzabi yana son saukar mata,ta miqa hannu ta jawo wayar don katse alarm din,amma saita samu ta hado da wata takarda. Alarm din ta kashe,sannan ta juya takardar tana qarewa rubutun jiki da aka yishi da faransanci kallo.

My Healer,

_I did not want you to wake up and find silence where reassurance should be._

_Ki yi hakuri da ni._

_Last night is still heavy on my mind._

_Rest today._

_Don’t overthink anything… especially us._

_And my giiftii_

_don’t cry because of me again._

*_Haisam_*

Sai wani kyakkyawan Royal sign daga gaban sunansa kadan daya sake janye hankalinta da matuqar burgeta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Duk da tarin gajiya da zazzabin da takejinsa har cikin idanunta amma hakan bai hanata rungume takardar a qirjinta ba tana ajiye numfashi a hankali.

Tana jin da dukka kalamansa kamar ya zare komai da takeji. Wannan shine abinda ya bata qwarin gwiwa,ta sauka a hankali cikin takatsantsan ta wuce bandaki. Saidai kafin ta kammala sallar tuni zazzabin da ciwon kai ya dawo ya rufeta,dole ta rarrafa ta koma saman gadon ta rufa ruf har kanta.

*_NANAY_*

A nutse take takowa zuwa babban parlor din da take sauraren baqi al'umma da sauran mutanen data sahalewa su ganta kowacce safiya. Cikin shigar kamala me daukar hankali gami da nuna zallar dattakonta da haiba kwarjini da kamalarta.

Haka kawai tun jiya hankalinta yake kan yarinyar. Duk bayan wasu mintuna sai tunaninta ya fado mata.

Cikin girmamawa take sauraren baqin nata gami da sallamarsu,har zuwa sanda kowa ya tafi,ya rage mata ita da zulaihat wadda ta kirata saboda wani kaya da takeso a qarasa qawata sassan akhnan na asalin mansion din haisam da duka kwana hudu suka rage a rakata.

Hankalinta ya koma kan obsa,hadimar rumaisa wadda ta qaraso cikin girmamawa.

"Ya akayi obsa?" Ta tambayeta hankalinta yana kanta.

"Ranki ya dade......yarima haisam ya fita tun safe....suna kyautata zaton sai ita daya......to amma sun yita aike saqo ba amsa daga bangaren nasa da dukka wayoyin dakunan". Idanunta ta qanqantar ciki.

"Karfa wani abu yasamu yarinyar nan" Ta fada can qasan ranta,saboda yadda tunaninta yake yawan zuwa mata rai sai takejin kamar ba lafiya ba.

"Muje na duba da kaina.....zulahat....ki jirayeni" Ta fada tana miqewa

"An gama ranki ya dade" Ta amsa mata sanda nanay ta miqe tana gyara lullubin farin mayafi jikinta.

D'aya bayan daya take wuce falukansa tana dosar sassan dakunan baccinsa,abinda ta jima rabonta da tayi,a hankali har qafafunta sukakai qofar dakin.

Knocking tayi har sau uku amma taji shuru,sai kawai ta murda handle din tana tura qofar dakin ta sanya qafafunta.

Haka kawai yau takejin nauyin shiga dakin a sassan jikinta gaba daya,duk da ta sani baya nan kamar yadda suka mata,amma yau sai take jin kamar wani baqon guri wanda ba muhallinta bane take shiga.

Ko ina na dakin fes,yana fidda wannan qamshin nasa. Ta sani dama ko a baya,matsayinsa sam bai sanyashi qazanta ko sakin komai a yadda yaga dama ba. Bama shi kansa ba,har ita yakan kama wasu abubuwan da hadimai ne ya dace suyi amma yayi shi.

Saman gado ta hango mutum kwance,kuma ta gane akhnan ce saboda wani sashe na gashinta days bullo ta saman duvet din.

Haka kawai take jin akwai wani abu,ta soma nufar gadon a hankali tana dan kiran sunanta,saidai bata motsa ba har zuwa sanda ta isa bakin gadon.

A gefe ta zauna,ta saka hannu tana janye duvet din cikin mamakin wacce irin rufa ce haka har saman kai?. Saidai hucin zazzabin daya fito yabi ta iska da hanyar daya samu shine ya bata amsar komai.

A dan rikice ta sake kiran sunanta a yanzun dab da ita tana dora hannunta a wuyanta,wannan sanyin hannun nata ya sanya akhnan motsawa a hankali bakinta yana furta.

"Hh.....haisammm" Cikin muryar dake dauke da mayen bacci dana zazzabi.

Sak nanay ta danyi,sai kuma ta sake kiran sunan nata a tausashe tana hadawa da fadin.

"Nanay ce.....momminki" Maganar ya dawo da ita kadan daga duniyar da take ciki. Ta bude blue eyes dinta a hankali wadanda suka sauya kala akan nanay din,saitayi qoqarin daidaita kanta daga baccin wahalar dame fusgarta.

"Me yasa zaki kwanta haka ki lulluba gaba daya?,bakyajin irin zazzabin da yake jikinki?,ina shi haisam din ya fita ya barki?" Ta fada tana fada gami da qoqarin cire mata duvet din gaba daya saboda ta samu wadatacciyar iska kada zafin yakai temperature di da ba'aso.

"Da yasan ya warware.....me yasa ya kasa maidomin ke kaman yadda mukayi alqaw......." Saita gaza qarasawa saboda sauka da idanunta yayi akan farkn duvet din wanda yabar stain na jini gurare daban daba.....jinin da akhnan din kanta batasan dashi ba ta dawo ta sake kwanciya samansa abunta.

*_To kedai nanay ki gani kiyi kamar baki gani ba shine kawai_*🫣🫣🫣

*_Wai yaya labarin sultane ne?,ya yake ciki?_*

*_uhmmmm.....akwai kwantacciya a qasa fa.....amma dai....bazan baku satar amsa ba_*
Chapter 92 · 0% Book details