← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 176

Sashe 165

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata taba ganin irin wannan fuskar tasa ba. Fuskar dake shimfide da wani sabon farin ciki tsantsarsa.

Sai ya lumshe idanunsa na dan lokaci,kamar yana godewa Allah a ransa.

Da ya sake bude su....suka hadu da na akhnan.

Kasa magana yayi,don yaji kawai ba'a buqatar kalmomi. Sai ya daga hannunta ya sumbaci bayan tafin hannun a hankali,sannan cikin murya mai rauni da ba ta taba ji daga gare shi ba yace

"Thank you,akhnan." Hawayen da take qoqarin hanawa suka zubo jin wani sabon kukan bayan wancan daidai sanda haisam ya gama kissing hannun ta yabar mata wani abu me taba zuciya.

Ta yi murmushi a hankali a lokaci guda,saboda a wannan lokacin....ta san cewa ko bayan shekaru masu yawa ne.....idan ta tuna wannan rana. Abin da zata fi tunawa ba tsoro ba ne. Sai yadda haisam ya kalleta.....kamar ita ce kyauta mafi girma da Allah ya taba yi masa a kaf rayuwarsa.

"Wait." Muryar likitar ta ratsa dakin. Dukkansu suka tsaya kafin a hankali daya daga cikinsu ya kalli monitor.

"Doctor..." Ya kirata
Wani irin shiru ya ratsa dakin. Kamar ita kanta ba ta yarda ba likitar dake duba cikin akhnan din.

"I think..."

"...there's another baby." Miqewa tsaye kawai haisam yayi,har yanzun dai bai saki hannun akhnan ba,amma mamakin da yaji yana juyashi sam sai yaji bazai iya zama ba.

"There's another baby." Ta sake maimaitawa sanda ta tabbatar.

Zaro ido akhnan tayi
"Another baby?!"

"We were told twins." Haisam ya fada yana jin yau duka kaman jarumtarsa ta qare.

"So were we." Likitan ta fadi itama.

Har yanzu yana tsaye,kamar an dakatar da tunaninsa,har zuwa sanda daya daga cikin nurses ta zagayo ta kawo masa daya daga cikin jariran da aka gama gyarawa.

A hankali ya karbe shi......ya karbeshi da hannayen nan nasa. Hannayen da suke riqe na'urori domin binciken tabbatar da gaskiya. Hannayen da suka rattaba manyan yarjejeniyoyi. Yanzu kuma... Sune suke riqe da jariri.

"All yours." Nurse din ta fada tana nuna masa bangaren da guda biyun ke kwance ana gyarasu suna sake rikita dakin da kuka.

A nutse idanunsa suka koma kansu.
Na farko.
Na biyu.
Na uku.
Sai ya yi wata irin murmushi me sauti qasa-qasa. Wannan murmushin da akhnan bata taba ji daga gare shi ba.

Idanunsa ya maida kan yaron a hankali. Kyakkyawar halittar me wani irin kyau da shiga zuciya. Komai nasa qanana masu kyau da daukan hankali,da kamannin da baisan da baisan na waye ba shimfide saman fuskarsa. Shi ko akhnan. Wata irin qaunarsa ta farat daya ta soma shiga zuciyarsa,qaunar daya tabbatar ashe sanda yana cikin akhnan qaunar bogi ce yayi musu,yanzunne yake ta haqiqa da gasken gaske take shiga.

Da kansa ya taka ya kawo matashi saitin fuskarta.

"Twins ko?" Ta fada tana son samun tabbaci. Haisam ya sauke idanunsa a kanta,sai ya girgiza kai a hankali.

"Apparently not." Ta yi dariya cikin hawaye tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da qaunarsa shi da abinda yake riqe dashi da sauran 'yan uwan da bata gani ba.

Shi ma yayi murmushi. Sai ya matsa kusa da ita,ya sumbaci goshinta,sannan ya rada mata

"Akhnan..."

"Mm?"

"Next time..." Ta daga gira,sai ya kalli jariran uku.

"...we're discussing this with Allah first." A wannan karon har likitocin suka yi dariya. Yadda komai nasa ke cike da nutsuwa.....komai nasa ke cike da addinin nan da kowa ya sanshi dashi. Wani miji na daban suma suke gani,wanda ya sanya sukayi wata irin tiyata me sauqin da basu taba irinta ba.💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 152*

Ya tayasu sun mantar da matarsa a inda take ba tare da allurar bacci ba. Kallo kulawasa kaffa kaffa dake cikin idanunsa a kanta na dabanne,ba irin wanda suka saba gani a idanun kowanne magidanci bane.

A gurin....sun sake ganin wata fuska tashi ta daban,da duniya bata san da ita ba. Wani sassauqan yarima.....wanda farincikin iyalinsa.....kulawa dasu ya sanyasu sama da komai nasa.

Akhnan kuwa ta kasa daina murmushi,idan ta tuna ba twins ba ne. Ba kuma daya ba ne......Allah ya ba su fiye da abin da suka yi tsammani,sai taji kamar sa'arta ta kere ta kiwa a rayuwa.

A wajen theatre dukkaninsu sultane jira sukeyi. Sanda qofar ta bude nurse din ta fito don ta musu albishir dukkaninsu sukayo kanta.

"Ya suke?" Dariya tayi cikin nishadi.

"They're fine."

"They?" Hussam ya fada yana matsowa kusa da imda nurse din take tsaye.

"All three of them.."

"Three?" Morsa safiyya ta fadi da wani irin tarin mamaki a fuskarta.

"Three?!" Noorah itama ta sake fadi tana sakin qaramin ihu.

"THREE?!" Hussam ya sake fada yana qara fidda ido sosai.

"Three healthy boys" Nurse din ta sake jaddada musu albishir dinta na farko.

Morsa safiyya ta fashe da kuka. A wannan karon ba ta iya tsayawa ba.

"Alhamdulillah..." Kusan dukka bakunansu ke furtawa.

Sultane ne ya janyeta yana lallashinta,kafin ta nutsu ta zauna. Tana kuka tana dariya lokaci guda,wanda bata taba sanin ana hakan ba sai a kanta.....a kanta a yanzun.

A cikin dakin kuwa an gama komai. An shirya akhnan da duka yaran zuwa dakin hutu. Sannan aka kawo yaran kusa da ita.

Ta waiwaya a hankali tana duban qananan fuskoki uku. Qananan hannaye uku.

Ta kasa magana,kawai kallonsu takeyi,sai ta waigo ta kalli haisam,nan ma ta tarar shima kallon yaran yakeyi kamar wanda aka cire masa numfashi.

"Haisam."
Bai amsa ba.

"Haisam." Ta sake kiransa.

A hankali ya kalleta,Idanunsa sun sauya launi da yanayin dake nuna yanayin ya taba jikinsa sosai.

"Yan uku." Ya maimaita a hankali

"Three." Ta sake maimaita masa,sai ya yi murmushin da ba kasafai ake gani ba. Murmushin farin cikin da ya fito daga zuciya.

"Allah has a sense of humor." Sai ya kama hannunta. Ya sumbaci bayan hannun.

"You gave me a kingdom." Ya fada da wata murya me kama da rad'a.

Lallausan murmushi tayi cikin hawaye,tana jin wata falala da ni'ima daga Allah tana lullubeta.

A ranar ba kamfanoni ba ne. Ba dukiya ba ce. Ba sarauta ba ce. Abin da ya fi komai muhimmanci ga haisam shi ne matarsa da kuma qananan yaransa uku da Allah ya ba shi lokaci guda. Kyautar da baiyi zato ba.

Daya bayan daya ya daukesu,yayi musu huduba kaman yadda addinin musulunci ya tanada. Tana daga kwance bacci yanason kwasarta,amma shine a idanunta. Shi da yaranta. Shi dasu kewaye a gabansa yana daukarsu daya bayan daya.

Ko sanda zai gama musu hudubar bacci yayi awon gaba da ita. Ya taka zuwa gabanta a nutse ya tsaya murmushi yana fita daga fuskarsa. Ya dora hannunsa saman sassalkan gashinta me tsaho da santsi da hular dake kanta ta zame saboda santsin gashin. Ya tsugunna a hankali yayi kissing goshinta.

"Allah yayi miki albarka" Ya maimaita har sau biyu yana jin yadda soyayyarta take ratsa zuciyarsa da wani sabon babi da muhalli na daban.

Yinin ranar gaba daya asibitin ya zama wani guri na zirga zirgar jama'a. Familyn motii aba jifar gaba daya a hautsine yake da murnar samun yara uku lokaci guda. Yaranma wadanda suka fito ta tsatson yarima muhammad haisam.

Batasan gata suna ya tara ba sai yanzu.....batasan gara a rayuwa hawan hawa bane sai bayan data haifi yaran.

Zamanta a asibitin ya sanya ta gane a baya qaryar gata take. Zamanta a asibitin ya sanya ta gane tsananin zurfin son da haisam yake mata wanda a baya bata gama fahimtarsa ba ashe kwata kwata.

A zaman asibitin ta sake yarda dashi da dukka komai nata. A zaman asibitin taga other side dinsa cikin kwanaki uku kacal. Baya kunyar kowa a kanta,baya shakka ko kowanton nuna mata kulawa. Baya barin kowa da hidimarta. Komai shike mata,abinda ya sanya ta sake tsinkewa da lamarin. Idan ka ganshi zakayi tunanin ba shine wannan yariman ba.....ba shine mamallakin manyan kamfanunuwan turare......fitaccen malamin nan.....jinin sarauta daya tara dimbin ilimin addini dana boko ba.

Hatta da saka drip allura bada magani dake wuyan nurses ya azawa kansa shi. Kome yake idan lokaci yayi zaka ganshi ya iso asibitin ya shigo dakin. Ko a gaban waye zai dauki yaransa ya rungumesu,ya gaya musu yayi missing dinsu. Zai matsa gaban gadon,zai riqe hannuwanta,zai gaya mata yayi kewarta,zai kuma tambayeta dame dame tayi sanda baya nan?. Dame dame take buqata a yanzun?.

Cikin yaran waye yayi kuka?,wayi yayi bacci sosai?. Bame zazzabi?,bame wata damuwa?,idan kaga yadda yake tambayar komai daki daki sai ka dauka ya jima basa tare,kaman tazarar kwanaki ne suka raba tsakaninsu ba 'yan qananun awanni ba. Yawancin lokuta yana shigowa dakin kowa ke fita ya basu guri. Cikin kwanakin wani abu daban take gani a qwayar idanunsa da ya ninka wanda take gani a baya.

Kwana uku kawai.....amma ya zame mata wata duniya ta daban. Ya bar mata tarin memories da har abada ba zasu taba shafewa daga rayuwarta ba.

Batasan adadin mutanen data gani ba masu zuwa marabtar yaran.....a hakanma asibitin da haisam sun iyakance adadin masu ziyara a kullum.

Har a ranar da suka cika kwana ukun bataji komai game da sunan yaran ba. A ranar ne kuma group na 'yan shidansa suka iso asibitin dukkaninsu a tare don ganin yaran.

Yana dakin a sannan,yana zaune a gabanta,ya tsirata da idanun nan nasa yana bata magani tana karba tana sha da qyar. Ya rasa wanne irin rashin jituwa ne tsakaninta da magani,ita kuma ya mata kwarjinin nan nasa da bazata iya musa masa ba. Allah ya taimaketa daya daga cikin yaran ya farka,ya tashi kuwa kuka sosai dake alamta yunwa yakeji.

Tsam ya miqe zuwa gadajensu,wani irin gado me kyau hade da rumfar da bazai bawa ko qura daman shiga ba bare wani abu na daban.

Da murmushi a fuskarsa ya ciroshi yana rarashinsa kamar me magana da babba. Daya daga cikin abubuwan da idan yanayi yake sanyata tattara hankalinta gaba daya tayita kallonsa riqe da yaran.

Ya qaraso gabanta,ya tsaya dab da ita har tana jin saukar wannan lallausan qamshin nasa. Sai daya tabbatar da nutsuwar yaron sannan ya daga idanunsa ya sauke a nata.

"Gyara ki feeding nasa" Idanu ta fiddo tayi narai narai. Ta yaya zata fara haka a gabansa?..

Yaci gaba da kallonta yana karantar reaction dinta.
Chapter 165 · 0% Book details