← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 176

Sashe 168

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Out" Dariya ta sake mamaye dakin,wata irin dariya dake cike da nutsuwa ba hayaniya sam a ciki. Sun tafi da alqawarin shehnaz da aisa din duka zasuzo suna,kuma kwana zasuyi,magana data mata dadi sosai,har taji jiran kwanakin kawai takeyi.

A wannan ranar akhnan ta fahimci cewa....yaranta basuzo cikin iyali kawai ba.....sunzo cikin wani babban da'irar mutane da suka riga suka shirya sonsu tun kafin susan sunayensu.....tun kafin susan kansu.

Kyaututtukan su maleek sai ya zamana kamar bude qofa kawai sukayi.....don kafin subar asibitin wanda sukayi kwana biyar saida haisam ya hana shiga ganinsu,sai kebantattun mutane kawai.

Wasu irin kyautuka ta dinga samu naban girma,wasu ma batasan su waye suka aiko da ita ba. Cikin kyautukan harda minister Agaichata Wadda ta aiko da set uku na akwati na kayan babies 'yan gaske. Sai wani handmade memory chest da zata iya ajiyar komai daya shafi yaran idan mamarsu naso. Domin adana tarihinsu da kaman kayan farko da aka fara saka musu. Hoton farko da aka fara yi musu,da sauran abubuwansu na farko da aka fara musu amfani dashi.

Da kanta tayi tattaki tazo,duk da an aike mata itama da katin gayyatar bikin suna da za'ayi sati biyu da haihuwar yaran.

"Nasan watarana zaki bude wannan.....ki tuna ranar da kika zama uwa" Agaichata ta fada tana murmushi hannunta akan handmade memory chest din,wanda ita kanta akhnan din ya bala'in burgeta ya tafi da ita.

*NAMING CEREMONY DAY*

Rana ce ta musamman......ta musamman din data adanawa akhnan wani tarihi babba cikin dukkan abubuwan da takejin ba zata taba mantawa dasu a rayuwarta ba.

Ba ga iya gidan sarautar aba jifar kawai ba....aah,gaba daya jimma ce ta motsa. Jimma ce tayi wani motsi da ranar bikin sunan 'yan ukun jikokin masarautar aba jifar,sannan jinin masarautar gumma asalin salsalar yunnus jallata!.

Tun ana ya gobe sunan yanayin garin ya sauya gaba daya. Akwai baqi manya mahalarta da suka dinga shigowa saboda halartar bikin. Masu iko mulki da madafun iko daban daban daga qasashe da garuruwa daban daban. Abun yaso ya girgiza akhnan,ya sake nuna mata kuma irin kyakkyawar alaqar da haisam ke da ita da mutane masu matsayi da madafan iko dama wadanda basa dashi.

Agadez cif take gani a jimma,don kusan kowa da take buqatar yazo yazo din. Falaak,hairaan,nannie,shehnaz,morsa safiyya dama wasu daga cikin ahalin diory hamani yan uwan mahaifiyarta kenan.

Ranar da suka iso jimma gaba daya rasa gane kanta tayi saboda murna da farinciki. Tana tsakiyarsu ana hira irin wadda ta shafi 'yan uwan da alaqa me kyau me qarfi ta shiga tsakaninsu.

Shehnaz an wani sake nutsuwa,dukkaninsu ita da aisa din idan ka kallesu zakasan khadeem da mutallab sun iya riqo. Hakanan dazun da rumaisa ta shigo tayita tsokanarta,don sosai agadez ta karbeta,ta sake wani girma ta zama babbar mace sosai. Anaani kam dama kusan da ita aketa zirga zirgar haihuwar tunda ita 'yar qasa ce. Ita dinma wata nutsuwa tazo mata sosai,tana jin balqees na fadin.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 155*
_________________________
*_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________

"Dama akwai ranar da zaki daina shegen rawar kai Aanani?" Bata amsa mata ba,sai murmushi kawai data saki cikin jin kunya.

Kayan da morsa safiyya ta kawo mata ko zata buqata take budewa,abinda yafi jan hankalinta daddadan turaren shuwa incense and more daya sanyata lumshe idanunta. +234 704 229 3387.

Bata iya daurewa qamshin ba,sai data kira birra tace ta dauki dukka night wear dinta ta mata kabbasarsu.

"Matar nan bala'ice a turare,raina kama kaga gayya kenan,saika turara sannan zaka fahimci inda maganar take" Hairaan ta fada tana juya kwalba daya.

"Shi yasa duk sanda na samu chance,ko bame zuwa nake saka order akaimin airport zuwa gumma" Falaak ta fada tana shinshina wani body milk dake cikin set din turarukan.

"Inajin na fiku sanin muhimmamcin turaren nan" Akhnan ta fada wadda hannunta da yasha wani irin jan lalle ke ajiye saman bayan daya daga cikin jaririn data gama shayarwa yanzun tana so yayi bacci. Hada idanu sukayi da falaak,ita tasan dawan garin,don haka murmushi kawai suka sakarwa juna.

Shigowar muhammad da sultane ahmad almaz shine abinda ya qarawa hirar armashi. Dukkaninsu a nan zasu kwana,gobe ayi walima dasu su wuce. Shikam ahmad ma sultane ne ya riqe masa agadez din kafin ya dawo,koda yazo nan sai ya ajiye sarautar ya koma ahmad dinsa sak.

Hira suke sosai,yana basu labarin zamansa a Ethiopia wanda mammina ta tailasta masa zama dan qasar tun yana yaro ba tare da zabinsa ko kasan ba. Wani guri suyi dariya.....wani guri su dakata dukkansu saboda jimami.

Ganin zaman labarin zai tabasu morsa safiyya ta yankeshi ta hanyar fadin.

"Nikam kwanciya zanje nayi,don idan na zauna bazan samu zama hira da 'yar uwata ba bayan sallar asuba(nanay wadda bata jima da fita daga gurinsu ba).

Amma saidai kafin takai ga miqewar qamshinsa ya fara yiwa parlor din maraba. Sau daya tak taja iska zuciya kwanya da kuma gangar jikinta suka gaya mata HAISAM ne. Ta lumshe idanunta tana jin yadda zuciyarta raje harbawa da qaunarsa. Missing dinsa da tayi tun safe yana saukowa ya lullubeta.

A nutse yake takowa kamar baya karance da kowa a parlor din,saidai dukkan wata jijiya ta jikinsa dake harba jini zuwa zuciyarsa tana gaya masa akhnan.....da yaransa da suka kasance duniyarsa suna gurin.

Ta janye idanunta a hankali sanda yake isowa gaban morsa safiyya daketa maraba dashi,yayi wani irin sassanyan kyau cikin Moroccan jallabiyya dake jikinsa dark green sosai data fidda asalin lafiyayyar fatarsa.

"Barka da dare" Ya fada cikin girmamawa yana zama sosai gami da gaidata ita da nannie. Cikin kulawa morsa ta amsa.....nannie kuma cikin surukuta,don suna gama gaisawa ma ta miqe ta fara yin gaba.

Hannu ya bawa muhammad da sultane ahmad suka gaisa. Wani girma suke bashi dukkaninsu,kowanensu idan ya kalleshi makomar rayuwarsa yake kalla a jikin haisam din. Allah ne ya qwacesu....haisam din shine sila.

"Yaya gajiyar tafiya?" Yace da morsa safiyya yana maida hankalinsa kanta.

"Alhamdulillah." Ta yi murmushi,duk sanda ta tuna d'an khaddu dinta Allah ya hada aure da diyar safeena tana jin duk duniya ba abinda yakai mata wannan nishadin a rayuwa. Tana kuma sake girmama hukuncin Allah da alqawarinsa da baya tashi idan ya tsara hakan.

"Amma ba ni ka zo dubawa ba." Morsa safiyya ta fada cikin 'yar tsokana da tsakanin uwa da d'anta. Murmushi ya saki a nutse yana shafa lallausar sumarsa,sannan ya saci kallon akhnan din da wani yanayi na qwarewa,don ya kasa jurewa ya basar da ita din.

Dariyar ahmad da muhammad ta tashi,haisam ya yi kamar bai ji ba. Amma idanunsa sun riga sun sauka kan Akhnan.

Itama tayi kaman bata lura ba,don tasan kadan shehnaz da aisa ke jira tayi misbehaving su samu na tsokana.

Sai ta zarce da gyara blanket din daya daga cikin yaran. Motsi ya fara yi,alamun yunwa ce ta tasheshi.

"Feeder dinsa yana bedroom." Ta fada tana miqewa da yaron a kafadarta tana takawa a hankali. So take ta gujewa idanun haisam daketa hukuntata da idanuwansa masu nauyin miqewa morsa safiyya tayi abinta,dom ta gama karantar abinda ya shigo dashi. Matarsa ce,kuma tasan idan tana gurin zaiji nauyinta ba lallai yayi abinda ya kawoshin a zahirance ba.

"Sai da safenku" Ta fada,kusan a tare suka furta

"Mu kwana lafiya.....Allah ya tashemu lafiya".

Kaman hakan yake jira kuwa ya miqe a nutse,ya zube hannuwansa a aljihun rigarsa ya soma wucewa zuwa bedroom din. Da idanu suka dinga gulmarsa har ya bacewa ganinsu.

Wani qaramin ihu suka saki suna dariya. Zai wahala ka zauna kusa da rayuwar haisam da akhnan baka raina kalar taka soyayyar ba.. Yana da wahala ka zauna tare dasu irin kulawa da soyayyar da suke nunawa juna da wadda ke cikin idanunsu bata burgeka ba.

Tana cikin dakin tana neman feeder a drawer. Duk da fiye da rabin hankalinta yana parlor din inda haisam din yake.

Ba ta lura da shigowarsa ba. Sai kawai ta ji an rufe qofar a hankali. Da sauri ta waigo,idaunta cikin nasa.

Sunyi wani irin laushi idanun nasa....sun rusuna sosai da yanayi na gajiya sosai a tattare dashi.

"Haisamm" Ta kirashi da yanayin da tasan yana kewa. Ya tsaya cak kawai,ya jingine da qofar,hannuwansa a hade a qirjinsa,fuskarsa a nutse da wannan nutsuwar tasa.....amma idanunsa qunshe suke da wani irin kallo.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Ta masa kyau ainun,fatarta glowing kawai takeyi,ta dan cika kadan irin ta masu jego,saidai qiba tayi ba. Ta murmure sosai,qirjinta ya cika fam ya zauna daidai da shape din jikinta. Wannna cikin ya shafe ya koma cikin sati biyun,abun har mamaki ya dinga bashi,shape dintan nan ya fito. Fatar cikin ta batabar wani alamu me yawa ba,saboda wani hadi da nanay tayi mata traditionally daya batar da duk wani tattarewa da fatar cikin tayi ta kuma taimaka wajen fidda shape dinta sosai.

"Na zo in ga ko kina tuna cewa kina da miji." Ya fada da gajiyayyar muryarsa.

Kasa riqe murmushinta tayi sam.

"Ta yaya zan manta da rabin zuciyata?"

"Da kyau." Haisam ya fada yana lumshe idanunsa.

"Me ya hanaki nema na?" Ya fada da tuhuma sosai a muryarsa.

"Family dina ne fa suka zo."

"Na gani."

"Sun zo daga nesa."

"Na sani."

"To me na yi?" Ta fada a shagwabe tana dan buga qafarta kadan a qasa. Hakan da tayi kaman ta tsokanoshi ne,sai ya matso kadan.
Chapter 168 · 0% Book details