← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 176

Sashe 172

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse haisam ya sumbaci goshin akhnan din,sai yusa ta kalleshi,ta kuma tura masa tata fuskar. Dariya suka sanya dukansu ita dashi,yayi kissing nata itama,saita qanqame wuyansa tana murna,abinda ya sake basu dariya gaba daya.

"Kawota.....kaje ka dawo.....zaka samemu cikin aminci da yardar Allah". Girarsa dukka biyun ya dage.

" Are you sure?" Kai ta daga masa a tausashe. Ya miqa mata yusra,amma saita maqale kafada.

"Ba zata yarda ba...."

"...muje na rakaka sai na karbeta a bakin motar"

"Kina nufin da ba zaki rakani ba yau?" Ya tambaya yana bata fuska,ta saki murmushi kawai. Kasala take fada da ita kwanan nan duk safiya,batason gaya masa yanzun nan zai rasa nutsuwar sa,sannan uwa uba ma zarginta yafi qarfafarta akan ciki ne,don duka alamunsa sun nuna mata.

Tare suke takawa da wani irin yanayi me dadi inda jerin motocinsa ke jiransa. Dab da zasu fita yaran na shigowa. Dukkaninsu suna maqaleshi,hakanan ya sunkuya ya dauki yumna itama,su ahsan suka riqeshi ta gefe da gefe suna zuba masa surutu,duk da yadda akhnan ke fadin kada su bata masa kaya sam bai damu ba,don pyjamas ne duk a jikinsu,yau ba wanda yayi wankan safe,sannan duk yashin gefan pool na gurin ya bata hannuwansu da qafafunsu.

Akhnan na kallonsu tana girgiza kai. Wannan abu na yaran idan haisam zai fita bai taba canzawa ba.

Ko da yaushe sai sun yi masa rakiya,indai suna gidan,indai idanunsu biyu.

"Abbee,ka kalli kayanka." Akhnan ta fada sanda daya daga cikin amintattun guard dinsa ya bude masa qofar motar ya kuma zura jikinsa. Ta nuna farin shirt dinsa da yanzu yatsun yumna suka bar masa alamar yashi.

"Meeting zaka je fa." Sai ya kalli rigar.
Sannan ya kalli yaran.

"So?" Ya furta yana dage mata dukka girarsa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"So?" Ta maimaita tana dariya.

"Ba su ne suka bata min ba." Ya fada yana kade gurin da wani dan farin handkerchief me kyan gaske da guard dinsa ya miqa masa a girmame.

Ajiyeshi yayi,ya sake jawo yumna da yusra ya dan rungume su. Ya miqa musu kuncinsa,sai kowacce ta bashi kiss guda daya.

"Sun qara mata kyau ma rigar." Dariya ta kubce mata daidai sanda Yumna ta sa qananan hannayenta biyu ta riqe fuskarsa.

"Abbee..."

"Na'am, princess?" Ya amsa yana shafa sassalkar sumarta me tsaho da santsi data gada daga buzuwar babarta.

"Kar ka dade." Nan take zuciyar Akhnan ta yi wani irin laushi. Yarinyar nada wani irin wayo na daban,har yanzu idan zai tafi sai sun gaya masa hakan.

Sunkuyo da kansa yayi ya sumbaci goshinta.

"I won't."

"You said that yesterday." Ahsan ya fada,akhnan ta rufe bakinta tana dariya.

Da dariya a fuskar haisam ya juya ya kalli ahsan.

"Whose side are you on?"

"Mama's." Ya fada yana tsalle da dariya.

"Me too." Ajmal ma ya fada yana dariya.

"Me three." Yumna ma ta fadi tana daga yatsunta uku duk da bata gama fahimtar akan abinda ake maganar ba.

Sai kawai ya girgiza kai kamar wanda aka ci nasara a kansa a yaqi.

"Traitors." Yaran suka fashe da dariya.

Dariyar itama ta danyi,saidai kuma ta ji wani jiri sama sama ya ratsa ta.

Ta dafe gefen motar a hankali tana kiran sunan Allah. Ba wanda ya lura sai haisam. Nan take murmushinsa ya dusashe.

"Akhnan." Kirata da kulawa. Ta dago kanta a nutse.

"Hmm?" Idanunsa suka tsaya a kanta.
Na dan lokaci kamar yana qoqarin karanta wani abu.

"Are you alright?"

"Of course." Ta amsa masa da confidence.

"You're tired." Yace yana zare seat belt dinsa da sauri.

"Just a little." Ta fadi tana daga masa hannu gami da dakatar dashi,saboda ta fuskanci fitowa yakeso yayi,kuma taga yadda hussam keta kiransa,da alama abune me muhimmanci. Dakatawar yayi amma sai ya ci gaba da kallonta kamar bai nutsu da yanayinta ba.

Wancan kallon dake mata nauyi,don idan ya fara yi mata shi.....yana ganin abubuwan da take son boyewa fes cikin idanunta.

"Kinci abinci?" Ya sake tambaya.

"Eh naci,ka shigo ka ganni da cup ba?"

"Properly?"

"Muhammad." Ta fada tana yarfe hannunta kamar yarinya irinsu yumna.

"Akhnan." Ya kirata shima don bazaije ko ina ba sai ya tabbatar lafiyarta qalau.

Yaran suka fara kallon iyayensu.
Saboda sun san wannan yanayin. Tsananin kulawa da junansu da baya boyuwa ko a gaban waye.

Haisam ya ci gaba da kallonta,sai kuma ya sauke ajiyar zuciya.

"Rest today." Ya fada daga qarshe.

"I will." Ta amsa masa.

"Banda shiga kitchen yau duka.....ba girki na auroki kiyimin ba" Qaramin murmushin da bata shirya ba ya qwace mata. Dole sunan NA MUSAMMAN batasan sanda zata sauke masa shi ba. Abubuwan da maza da yawa suka daukakesu,suka kuma daukesu da zafi shi basu dameshi ba. Kawai shi ta zamana cikin qoshin lafiya,ta kula da tarbiyyar yara,sannan ta kula da buqatunsa a shimfida,komai ba dole bane a wajensa idan ya wuce wadannan.

"Promise?" Ya tambayeta. Sai ta gyada kai.

"Take care of yourself......" Yayi maganan yana miqa mata hannunsa kaman yadda ya saba duk sadda zai fita suyi musabaha. Bashi tattausan tafin hannunta tayi,wanda take kula da taushinsa sosai tun daga sanda ta gane yana daya daga cikin abinda yakeso a jikinta. Baya rabo da riqe hannunta muddin suna tare.

"......For me." Ya qarasa maganan daya fada din dazu.

Akhnan ta ji wani irin murmushi ya subuce mata.

Sai ta kalli yaran da ke maqale da mahaifinsu. Ta kalli haisam.......tana tunanin yadda zai kasance idan ya gano abin da take zargi.

Ta san abu daya kawai..... Idan ya tabbata...mutumin nan ba zai sake samun nutsuwa ba kwata-kwata sai sanda ta haifa abinda ke cikinta din.

"Am....amma nace zamu samu jet?,nasan ka manta" Ta fada sanda take dab da rufe masa qofar motar. Kai ya daga yana dubanta ba tare da yayi magana ba.

"Zamuje agadez....duba sultane.....baya jin dadi,aisa ma ta sakeyin miscarriage tana gida".

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 159*
__________________________
https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa ameen*
___________________________

"I know,ina sane,ta yaya zan manta da duk wanda ke rayuwa cikin gidan nan?.....zansa su shirya jet din,ko gobe da safe sai muje. Sahel couture new branch ma yana buqatar sanya idanunki.....kamar akwai gyararraki daya kamata kiyi".

" Yes sir" Ta fada tana saluting nasa. Abinda ya sanyashi sakin murmushi kenan,ta rufe masa qofar a hankali sannan taja baya,ya sauke window din kamar yadda ya saba ta tsaya sosai ta masa addu'a kamar kowacce rana idan ta rakoshi zai fita. Suka shafa addu'an tare.

"Allah yayi miki albarka" Ya fada sanda ya bawa driver umarnin tayar da motar,

"Ameen....."

"Fi amanillah" Ya furta lafazinsa na qarshe kaman yadda ya saba fada kowanne lokaci.

★★★

*_TSAKANIN HARSHE DA HAQORI_*

Gagarumin sauyi da sabbin tsare-tsare ne suka fara bayyana a tsakanin masarautar Agadez da ta Jimma qarqashin jagorancin Prince Sheikh Muhammad Haisam Aba Jifar.

A cikin yan shekarun da suka biyo bayan aurensa da Khadeeja Sultane Muhammad Hammud,an samu qulla manyan alaqoqin kasuwanci, ilimi da al'adu tsakanin masarautun guda biyu. Abubuwan da a baya suke daukar watanni kafin a cimma matsaya a kansu, yanzu cikin sauqu suke samun sahalewa da cikakken goyon baya daga bangarorin biyu.

Dangantakar da ta fara ne ta hanyar aure da haduwar jini, ta rikide zuwa wata gada mai qarfi da ta hada al'ummomi daban-daban, tare da qara kusantar da zukatan jama'ar qasashen biyu.

An fara shirye-shiryen musayar dalibai,qwararru da yan kasuwa. Haka kuma an ƙ
Qarfafa harkokin yawon bude ido da ayyukan raya al'umma, wanda ya sanya sunan Agadez da Jimma ya fara karadewa a idon duniya.

Sai dai cikin dukkan sababbin abubuwan da Haisam ya aiwatar, babu wanda ya ja hankalin jama'a kamar shirin Hawan Daba na Jimma.

Tun lokacin da ya halarci wasu bukukuwa a Arewacin Najeriya, ya kasance yana sha'awar yadda sarakuna ke fita cikin jama'a domin sada zumunci da talakawansu. Wannan al'ada ta burge shi qwarai.

Ya yi imani cewa shugaba bai kamata ya kasance a bayan katanga koyaushe ba. Saboda haka ya gabatar da sabon tsari da zai bawa motii damar kusantar jama'arsa,musamman wadanda ke zaune a yankuna masu nisa kuma ba sa samun damar zuwa Aba Jifar Palace domin ganinsa.

Daga sanda aka sanar da ranar hawan, Jimma ta sauya gaba daya. Baqi suka fara kwarara daga sassa daban-daban na Ethiopia, har ma daga qasashe makwabta.

Masana tarihi suna son ganin yadda za a hada tsohuwar al'adar Habasha da salon hawan sarakunan Hausa.

Masu yawon bude ido suna son zama shaidun wani sabon tarihi.
Chapter 172 · 0% Book details