← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 176

Sashe 131

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Mu tafi?.” ya tambaya kamar me mata rad'a. Sai taji zuciyarta ta harba tana skipping na wasu sakanni daga aikinta.

“Ba zan barki a nan ba.” ya bata tabbaci yana sake gyara mata hijabinta daya sake fdda wannan marainiyar fuskartata.

Sai ya riqe hannunta cikin nasa. Ba kamar yadda yake yi kullum ba. A yau.....riqon nasa ya sake zama na musamman. Tamkar yana gayawa duniya da ita dashi kansa cewa. NINE GARKUWARTA NA HAR ABADA.

Ita dinma Ta kasa sakin hannunsa ko da sau d'aya. Kamar idan ta sake shi,zata sake fad'uwa ne....faduwar da ba ranar sake tashinta.

Da kansa haisam ya bud'e kofar. Ya jima da tsaida da kima dakatar da wata hidima duka data shafi akhnan din. Komai......kusan komai dasu birra ke mata shi yakeyi yanzun. Yayi tasa yayi nata. Takanji nauyinsa idan ta ganshi kitchen......yana dafa mata tea ko madara. Batasan wanne baiwa Allaj ya mata ba.....wacce irin nau'in kyauta Allah ya mata daya bata irin wannan LU'U LU'U da yafi komai tsada cikin nau'in kadara. Billionaire irin wannan......ita diyar muhammad hammud tayi sanadin shigarsa kitchen yana mata hidima?. Mutumin da idan yaso inda kuma yana da ra'ayi.....cook kowanne iri ne zai iya hiring ya kawoshi kawai don ya masa girki.

Yana lura da hakan,akwai kuma sanda ya rutsata da narkakkun idanun nan nasa,ya sanyata a tsakiya yana tareta da hannunsa ta hanyar dafe cabinet din kitchen din da hannuwansa.

"Kin dauka da wasa ne......idan nace miki ina karantaki ta idanunki?" Kai take qoqarin kawarwa saboda yadda kwarjinin nan nasa ke bugunta.

"A duniya babu wanda yakai muhammadurrasulillah daraja......duk duniya sun shaida haka ne?" Ya fada yana d'age girarsa. Kai ta gyada a hankali.

"Amna yana tsayawa a gidansa,ya taya matansa hidima". Maganan ta sauka a kunnenta da wani irin ma'ana da cikakken nutsuwa. Daga ranar.....daga lokacin wani girmansa ya sake ninkuwa a ranta da idanunta. Ko a labari.....ta jima bataga mutum me matsayi irin nasa ba,amma kuma bai dauki kansa a bakin komai ba.

Ya shigar da ita ciki yana kaffa kaffa da ita. Dakin yayi duhu mai laushi,nutsuwa.......da wata irin kwanciyar rai a cikinsa.

Ya sake matsawa ciki,sai ya cire alkyabbarsa ya aje gefe. Ya juya gareta. Har yanzu tana tsaye kusa da qofa kamar bata san me zatayi ba. Kyawawan farare kuma blue eyes dinnan jajur da alamun kuka.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 119*
________________________
✨ AMINTACCEN GURIN SIYAN THRIFT ABAYAS ✨
Ingantattun Thrift Abayas masu kyau da tsari akan farashi mai sauƙi da araha.
Muna kawo sababbin kaya akai-akai tare da rangwame na musamman.
🤍 Dukka sai a MK ABAYA BOUTIQUE 🤍
Duniyar Thrift Abayas masu kyau, masu tsari, da salo iri-iri domin kowane lokaci da kowane irin event.
Abayas masu inganci, masu salo, masu araha, kuma na zamani ga mata masu son ƙawata kamanninsu cikin kamala da kamun kai.
Karki bari a ba ki labari... Leƙo ki ga yadda MK ABAYA BOUTIQUE kullum ke cike da kyawawan Thrift Abayas akan farashi mai kama da kyauta.
'YAN SARI, 'YAN REPOSTING, DA MASU SIYA DON AMFANIN KANSU... DUKA INA MUKU MARABA! 🤝🤍
📱 WhatsApp: 07064399623
📞 Call: 08036027448
🔗 Join our Wholesalers Group:
https://chat.whatsapp.com/JBg80RmA47v7GoqvWdgLJT?s=cl&p=a&mlu=3
__________________________

A hankali ya qaraso kusa da ita. Ya dago hannunsa ya sake gyara mata hijab din daya dan zame cikin kulawa.

“Kin ci wani abu yau?”
Ta girgiza kai.

“Bani jin zan iya…”

“Zaki iya.” ya amsata calmly

“Ko kad'an ne.” sai ta sauke idanunta.

“Bana jin cin komai yanzu…” Sai ya d'an yi shiru yana kallonta da wani irin taushi mai nauyi a idanunsa

“Then borrow my strength tonight.” Ta d'ago idanunta gare shi a hankali.

“Har sai naki ya dawo." Ya furta yana lumshe idanunsa gami da budesu a cikin nata.

Wannan kalaman nasa,suka sake karyata. Yana da wasu irin kalamai....a idanunsa da harshensa wasu irin dafi ne da ba wanda zai gane sai wadda ta jarabtu dashi......sai wanda yake tare dashi. Tarin hikimar zance me laushi da nutsuwa.....wanda ke iya sanyaka ko ya hanaka abinda duk kayi niyyar yi.

Sai ya ja ta zuwa sofa gently ya zaunar da ita. Ruwa ya miqe ya dauko da kansa,ya dawo ya tsugunna gabanta yana zuba ruwan da kansa. Ta bishi da kallo......yana sake shiga zuciyarta da wani irin qarfi da shi kansa bai sani ba.

"Madalla da miji na gari" Ta fada tana sake jin kamar zuciyarta zata karye sanda ta tuna sultane shine tsanin samun wannan lu'u lu'un me tsada a gareta. Wanda ya yarda yayi kuka tare da ita.....suyi dariya tare. Wanda ya yarda ya tsaya a gefanta ba tare daya durqushe ko ya tsuguna ba.

"Take it" Ya fada yana miqa mata tambulan na glass cike da ruwan idanunsa masu sanyin nan cikin nata.

Ya jira har ta sha kad'an. Ya karba ya ajiye,sai taga ya jawo plate din abinci da bata lura da sanda ya zubashi ba. Kai ta langabe sai shima ya mata yadda ya saba,yadda yakewa nanay dinsa,dole ta sauke nata makamin duk da ranta baya so. Cikin nutsuwa har ta ci spoon uku. Cikin bata kulawa kamar yana kula da abu mai rauni da zai iya karyewa.

Shi ya tsaya tayi wanka.....shi ya tsaya ta sauya kaya,ta zauna gefen gadon cikin shiru......shurun da ya dauketa ya cillata wata duniyar tunani da mamakin da har yanzu bai saketa ba.
.
Kamar zuciyarta ta gaji da kuka haka takeji. A nutse haisam ya zauna kusa da ita,sanye da lausasan pyjamas da kyansu ya sake fitowa saboda daddadan qamshin nan nasa dake kadawa. Qamshin kuwa yayi nasarar isa zuwa ga hancinta kai tsaye,ya kuma aike mata da wannan nutsuwar da ya saba aje mata a dukka sassan jikinta.

Na d'an lokaci babu wanda yayi magana,sai shuru daya wanzu tsakaninsu,suka barwa zukatansu saqe saqensu.

Sai ya d'ago hannu ya kamo nata da wani irin taushi da nutsuwa. Ya miqa dogayen yatsunnan nasa yana shafa bayan tafin hannunta a hankali.

Numfashinta taki yayi nauyi......taji ya soma saukar mata da wata irin tsumammiyar kasala a dukka gangar jikinta. Tadan saci kallonsa,idanunsa suka d'an gutsira mata wani abu daban.

"Kinga d'a namiji.....bashi da haquri a fagen mu'amalar aure......musammanidan yana samun dukkan yadda yakeso....kuma idan har ya d'an d'ana yaju yadda abun yake......bazanji kunyarki ba.....zan fada miki.....mijinki da dukkan yaqini zai iya kasancewa a wannan sahun" Ta tuna wata magana da nanay ta taba gaya mata,wadda sai da taji inama ace qasa ta tsage ta shige?.

“Ki kwanta.” muryarsa ta sauka a kunnenta softly. Idanunta ta bude a hankali,ba wannan maganan ta dauka zataji daga bakinsa ba,akwa abubuwa masu nauyi danqare data hanga cikin idanun nasa......amma me yasa ya zabi gaya mata iya wannan?,koda ba zata magance masa da komai ba.

kai ta girgiza kai kad'an,tana jin tausayinsa yana saukar mata a hankali. Yayi kawaici.....ya kauda kai akan komai......bayan tasan can qasan ransa yana da buqatuwa zuwa gareta.....wacce irin sadaukarwa ce wannan?.

“Idan na rufe idona…” muryarta tayi rauni,tana jin zata fada masa ne don shi kadai ya rage mata a duniya.

“…zan sake jin muryarta.” Wani irin abu ya motsa a zuciyar Haisam me ciwo,sai ya matsa kusa da ita kad'an. Ya d'ago hannunsa ya shafi gefen kanta.

“To kada ki yi yaqi da tunanin.” ya fadi calmly

“Kiyi tunaninki gwargwadon yadda zai ishi kwanyarki ta bari ya wuce.” sai ya dakata yana kallon fuskarta da kullum kwanan duniya sai yaga abinda ya burgeshi.....sai yaga abinda ya masa kyau.

“And every time it hurts…” ya saka hannu yana share wani sabon hawaye

“…look at me.” Sai ya ja ta jikinsa a hankali. Da wani irin rauni ta kwantar da kanta a kafad'arsa shi kuma yana riqe da ita cikin nutsuwa.

Mutsuka tafin hannunta yaci gaba dayi,ta daidai gurin da yake da connection da idanuwa da sanya bacci. Batasan me yakeyi ba,tasan dai tana jin dadin wadannan tafukan hannayen cikin nata. Sannu a hankali kasala ta fara saukar mata,idanunta suka fara nauyi.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Kwanta" Ya fada yana gyara mata pillow. Ba musu ta kwanta,yaja mata comforter yana lullubeta sosai. Idanunta a lumshe sanda yake shafeta da addu'a. Taja numfashi sosai,tana jin yadda hannuwansa suka yita son sauya akala da tsaiwa a wasu gurare da yawa a jikinta,abinda ya haifar mata da kasala kenan,ya kuma so tayar mata da nata tsumin daya tsuma mata a ranarsu ta qarshe a dubai.

Ta dauka zai fita ne yayi uzurinsa bayan ya gama mata addu'ar.....amma maimakon haka sai taga ya jawo abin sallarsa bakin gadon ya zauna akai kamar wanda aka bawa gadinta. Bai matsa mata da magana ko yawan kallo ba.....ya bata space sosai yana raba hankalinsa tsakaninta da littafin hannunsa.

A haka ya zauna da ita tsawon dare.
Yana shafa kanta lokaci zuwa lokaci. Yana duba yanayin baccinta. Yana gyara mata gashi idan ya rufe mata fuska. Yana lallashinta idan hawaye suka sake kufce mata.
Kamar duk aikinsa na daren nan guda d'aya ne....... Tabbatar da cewa Akhnan bata ji ita kad'ai bace a duniya ba!

*_Nima a nan nace MADALLAH DA MIJI NA GARI IRIN HAISAM_*

★★★Tun bayan kalaman mammina zuciyar Akhnan ta kasa samun sukuni.

Duk sanda ta rufe idonta,sai ta ji muryarta tana dawo mata kamar a sannan take fada.

“Ban tab'a kallonki a matsayin d'iya ba…”

Amma abin da ya fi kashe mata zuciya ba wannan kadai bane. A’a. Yanzu ta fara tuna yadda aka rabata da morsa safiyya tun tana yarinya. Yadda aka sanya aka kuma maidata me tsananin yi mata rashin kunya. Yadda aka cusa mata qarya shekaru masu yawan gaske,ta kuma girma cikin wannan qaryar.

D'aya bayan daya abubuwan da suka faru a shekarun suka fara dawowa mata. Tana qin zuwa sashenta. Tana jin haushinta ba tare da dalili ba.
Chapter 131 · 0% Book details