Sashe 81
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
".....kece maganin.....na fada miki" Ta katse maganna nata yana lumshe mata idanunsa hannunsa harde a qirjinsa,kamar yadda yake kwance a miqe sambal daga can qasa kuma ya harde qafafunsa suma.
".....kasha wannan din....zan baka wancan maganin duk inda yake za'a nemoshi nayi alqawari" Wani sanyi yaji yana ratsashi,ya sake bude idanunsa sosai a kanta.
"Indai zaki bani wancan maganin......zansha wannan......amma ba yanzu ba......sai anjima".
Kai ta jinjina a hankali,don ta gagara magana,ya gama kashe mata jiki gaba daya. Wannan kusancin ita kadai tasan me takeji a cikinsa..
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Shuru ya ratsa dakin na wasu mintuna,ta dauka bacci yakeyi,sai kuma taji muryarsa a hankali da wata irin nutsuwa.
"Khadeeja bint kuwailid" Ya furta da wasu nutsatstsun kalmomi. Bai sake bata daman yin magana ta biyu ba ya sake furta.
"Kin taba jin tarihin me sunanki?....khadeeja bint kuwailid,matar manzo ta farko?" Ya qarasa fada yana bude idanunsa fes a kanta.
"Aah" Ta amsa masa a nutse,can qasan ranta wani abu yana motsa mata game da son jin tarihin.
Numfashi ya sauke a hankali,ya koma ya kwanta saman cinyarta kaman dazun,yana jin wata irin nutsuwa da bai taba samun makamanciyarta koda zai kwanta akan katifar da tafi kowacce katifa tsada a duniya.
"Soyayyar da bata da makamanciya har yanzu a tarihin duniya......soyayyar khadeeja bint kuwailid da manzon Allah S A W" Ta kama masa kalmar qarshe suka maimaita tare,wanda bata sake bari ta kubce mata ba tun daga randa ta karanta a tarihinsa falalar yin salati a gareshi a duk sanda aka ambaci sunansa.
"Itace mace me daraja...mai qarfin kudi dana iko.....'yar kasuwa irinta ta farko a tarihin musulunci....amma bata daga kanta ga soyayya ba...." Ya furta a nutse kamar me maida numfashi.
".....lokacin da taga abinda takeso" Sai ya sake dakatawa.
"......ta zabeshi cikin nutsuwa.....ba hayaniya......ba matsawa"
"Kuma bai manta da ita ba ko bayan ta rasu......ya qare rayuwarsa yana ambatonta har a gaban macen da yace yafiso wato nana aisha RA.....ya maimaita mata yana son khadeeja.....ya sake maimaita mata Allah bai musanya masa da wadda ta fita ba......kinsan duk dalilin me yasa ta samu wannan darajar?". Kai ta girgiza a hankali,kwadayinta da son jin cikakken labarin yana ratsata.
Idanunsa ya bude sosai a kanta yana dubanta,
"Ta soshi sanda kowa ya qishi,ta sadaukar masa sanda kowa ya hanashi......ta rungumeshi sanda kowa ya juya masa baya......ta gasgatashi a sanda kowa ya qaryatashi......ta zabeshi a sanda ta fishi dukiya......ta fishi shekaru......itace kuma uwar 'ya'yansa gaba daya banda guda daya tal a ciki". Sai yayi shuru yana duban cikin idanunta. Shuru ya biyo amma yana iya ganin yadda ta kalleshi har sau biyu.
Tanaso tace ya bata cikakken tarihin.....amma kamar mejin nauyin hakan. Murmushi ya saki
"In baki tarihin......ke kuma me zaki bani?" Ya tambaya da wani irin coolness idanunsa kamar namejin bacci. Batasan sanda murmushi ya subuce mata ba,.....a karo na biyu ba tare data kawo komai a ranta ba tace.
"Komai.....komai da kakeso" Kai ya jinjina sosai,sannan ya gyara kwanciyarsa cikin jikinta. A nutse kuma ya fara warware mata tarihin tun daga farkonsa har qarshe.
Tarihin yazo qarshe da kiran sallar magariba dake kwararowa daga babban masallaci zuwa cikin gidan. Sai shuru ya ratsa dakin sai sautin kira sallar. Zuciyarta tayi wani irin sanyi.......wani irin yanayi takeji yana saukar mata.
"Khadeeja da muhammad S A W" Ta lumshe idanunta tarihin yana qawatar da ita. Sunan kuma yana sake mata yawo cikin kanta.
"Kamar sunana da nasa?" Ta tsinci kanta da tambayar kanta da kanta,saita ware idanunta wani murmushi yana subuce mata.
Tunda take kallace kallecenta......tunda take karance karancenta bata taba cin karo da tarihin soyayya me qayatarwa irin wannan ba.
Ya miqe a hankali yana jin yadda zazzabinsa yake sake yawa da kadan da kadan.
"Zanyi tattaki inje masallaci".
" A dawo lafiya" Ta samu kanta da furtawa a nutse.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 73*
Da wani irin yanayi ya tafi ya barta,wani irin sanyi takeji a zuciyarta. Wani wasai takejin zuciyarta,kamar wadda aka bawa kyautar wani abu.
Haka kawai takejin wata walwala ta musamman tattare da ita. Tayi sallah saita shiga wanka. Tunda ta shiga toilet din kansa burgeta yakeyi,wani irin gini da har yanzu idan ta kalleshi,ta kuma hadashi da ginin gidan data baro na koyon al'adu mamaki takeyi. Wadanne irin qwararrun engineers ne dasu haka?. Masu wata irin fasaha?.
Wanne irin iko ne haka masarautar suke dashi?. Ko ina idan ta waiwaya ba abinda take gani sai luxury. Wasu abubuwan da yawa saita dinga hangen yadda aka narka gold muraran akayi abun ado na cikin parlor da dakin gaba daya.
Riga ta saka mara nauyi,tayi magariba tayi isha'i. Har zuwa sannan bataji alamun shigowarsa ba. Taga tex dinsa bayan sallar isha'in.
"My doctor....ina tare da baqi 'yan dubiya" Kalmar ta dinga maimaitawa. Yaushe har ta zama likitanshi? Wanne kulawa ma ta bashi?. Ajiye wayar tana sakin ajiyar zuciya,siririn murmushi yana subuce mata. Sai taji tanason bashi kulawa din sama da yadda ya zata daga gareta.
"Don ramuwa ga kyautatawarsa.....don godiya ga soyayyar nanay a gareni" Ta fadawa kanta da kanta murmushi yana sake wanzuwa akan fuskarta.
Rabonta da abinci tunda rana,wannan ya sanya ta zauna ta debi kadan daga cikin abinda zata iya ci.
Sake duba agogo tayi,bata gaji da zama ba.....amma sai takejin kamar tana cikin kewa....kamar akwai wani abu daba daidai ba tattare da ita,sannan kamar akwai abinda zuciyarta take buqata.
Ta sauke qafafunta kenan da zummar miqewa don ta wuce daki ta sauya kaya kira ya shigo wayarta. Tadam fidda ido tana mamaki,shehnaz ce.....a wannan lokacin?,saita sauke murmushi ta koma ta zauna tana daga wayar.
"Matar nan,nan gaba sai mun fara cika foam Allah sheikh zai bari mu kiraki bama ganinki ba" Idanu akhnan ta fidda kadan,kewar 'yar uwarta yana kamata. Tayi missing rigimar shehnaz......da komai nata. Fadansu da aisa kawai ke iya rabawa.
"Ni matsalata dake ko.....sharrinki baya sallah" Dariya sosai shehnaz ta sauke.
"Da gaske nake miki......ba kowa ke iya kiran wayarki ya samu ba,kin zama wata ta daban......irin matar eh....." Bata qarasa ba ta sanyasu dariya gaba daya ita akhnan din,irin dariyar data kwana biyu batayi ba.
Zama.tayi sosai tana tambayar masarauta dama kowa da kowa,duk da zai wahala rana ta fito ta fadi momma bata kirata ba.
Wani lokacin takanji kamar ta yiwa morsa safiyya tambaya akan nanay,amma saita tuna alqawarin data yiwa nanay din,ba zatayi maganarta da morsa din ba har sai lokaci yayi.
Hira suke sosai,irin wadda suka jima basuyi irinta ba.
"Ina fushi da aisa da gaske shehnaz".
"Ki yiwa aisa uzuri......ta shiga wani aiki ne,amma komai idan ya kammala na tabbatar da kanta zata nemeki,ko waya bata riqewa yanzun". Mamaki ya kama akhnan,duk qaunar aisa da waya?,
" Wanne irin aiki ne wannan?"
"Banace ba....ni kaina batamin cikakken bayani ba". Shuru alkhnan tayi na wasu daqiqu sannan a hankali ta furta.
" Allah ya taimaka" Can qasan ranta tana tuna case din sahel couture,abu daya data sani sultane ya gaya mata ta nutsu ta kwantar da hankalinta,shi zai kula da komai,shi yasa bata sake maganarsa ba.
"Ya ake ciki mutuniyar?" Shehnaz ta fadi da salon tsokana.
"Shehnaz......zaki fara ko?" Ta fada a narke,don ta sani indai shehnaz ta fara magana da irin wannan yanayin,ba shakka saita tuburaka da tsokana.
"Na shigesu.....akhnan wacce irin murya ce wannan?.....sak muryar mutumin daya fara soyayya" Ta fadi tana dariya. Karon farko dariya ta qwacewa akhnan,shehnaz nada tsokana da sharri kala kala......amma sau tari tana da saurin dago abubuwa a zahirin ma'anarsu.
"Banason iskanci shehnaz"
"Tsaya....to me ya faru?don Allah ki gayamin,tsakanina dake akwai Amana fa" Yadda ta marairaice mata ya bawa akhnan dariya wannan karon sosai.
"Babu komai magulmaciya"
"Na sanki ciki da bai.....nafi tsoronki idan kikace ba komai,har gwara kicemin akwai kuma kiqi cewa komai din.....inaso ko yaya naji wani abu game da sheikh......wannan zuciyar......yayi nasarar sace mana ita?" Har tsakiyar ranta taji maganar shehnaz,wani sirri ne dake danqare a zuciyarta,ko yaya kuma tana buqatar wanda zata fitarwa dashi....ko yaya tanason wanda zasu tattuna tare.
"Nace miki fa ba komai......shi baida lafiya ma.....nanay ta bani jinya" Dariya sosai shehnaz takeso tayi,tana sake yarda da maganar nannie da tace dukkaninsu sun girmi akhnan din. Quruciyarta ta dabance a cikinsu.
"Aah.....kice kin zama likita kenan,ko kuma dai zuciyarsa kike gyarawa?" Ta fadi tana dariya. Murmushi tayi itama,tana tuna kalmar daya kirata da ita kenan dazu. Kenan likitar daya kirata......tana iya daukar ma'anar LIKITAR ZUCIYA?.
Kai ta girgiza da sauri,ta yaya?......bai taba gwada furta mata komai da yayi kamaceceniya da wannan ba,bataga komai da yake alamta mata wannan ma'anar yake nufi ba. Tabbas kulawa......dukkan wani nau'i na kulawa ta sameshi. Kalar kulawar data sanyata ta fara jin kanta daban.....kalan kulawar data sanya ta fara gane girmanta yana sama da yadda ta zata yake a baya.
"Bansan me yake nufi ba shehnaz" Ta furta da wani sauti daya tabbatarwa shehnaz har cikin zuciyarta abinda ta fada. Tashi shehnaz tayi ta zauna sosai tana maida yanayinta na nutsuwa.
"Bani labari biftuuu.....ba wani abu daya sauya?,bakya jin komai har yanxu game dashi?......kinsan kalar mijin da kike aure akhnan?.....prince ne.....yariman da yake cikin jerin sahun yarima guda goma da sukafi kowanne yarima gata ilimi kyau da qarfin iko na sarauta a duniya......baki taba googling ba?" Mamaki sosai ya kama akhnan,tadan fidda idanu waje kadan. Dama shehnaz ta sani?,tasan wayeshi amma bata taba gaya mata ba?.
"Ya akayi kika sani?,me yasa baki gayamin ba?". Kai shehnaz ta girgiza.