← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 176

Sashe 56

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_Ina amfani da wannan damar na shaida ma masu fidda mana pages ta kowacce hanya cewa,zanta gayawa Allah inde ban taba satar miki komai ba....ban taba cutar miki da komai ba......to Allah ubangijin al'arshi yayi min sakayya Allah ya isana duk wadda ta fitarmin da pages ta kowacce fuska kuwa,Allah ya sakamin_*

*_Yadda muka killace haqqinmu kayanmu,kuka watsawa duniya UBANGIJI KA BANKADE SIRRINTA DA TAKE ALKINTAWA A IDANUN DUNIYA,ALLAH KARKA SUTURTATA HAR ABADA_*

*_Na gode da jumurin bina da kuke,kuma in sha Allah next time labarinmu zai zamana pages saba'in tamanin kamar yadda aka saba book a baya ayi a qarqareshi_*

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 51

Sosai ta narke cikin duvet din tana dora wayar saman kunnenta. Ba zatace ga yanayin data ji ba sanda muryar nan tasa me zurfi take sauka cikin kunnuwanta ba,saidai da qyar ta qwaci kalmomin amsa sallamarsa hotonsa data gama kalla yanzu yana dawo mata cikin kanta.

Ta cikin wayar yakejin kamar yana sauraron bugawar zuciyarta,shurun nata yana wani irin qonashi tare da yunqurin binne dukka jarumtarsa. Yana jin kamar da gayya tayi shurun.....kamar tasan abinda yake muradi....

"Me ya samu muryarki haka?" Yayi maganan da wani irin taushi cikin amonsa yana sake jin kamar ana tunzurashi zuwa wancan yanayin.

Idanunta ta lumshe,kamar dai dazun muryar na sake shigewa wani gurbi me girma a zuciyarta......kamar ba daga waya yayi maganar ba,kamar gashi gata haka takejin tasirin muryar a cikin jikinta.

tana jin yadda yake matsowa kusa da ita sosai,ba da jikinsa ba.......da muryarsa,da wannan yanayin yanayin kulawar tasa da take jin kanta ya kumbura sosai a duk sanda ya nuna mata ita.

"Gajiya ce kawai" Ta fada softly da wani yanayi da batasan tayi magana dashi ba.

Har cikin qasusuwansa yaji sound din......ya sake matsa recording dinsa yana sauke wata boyayyar ajiyar zuciya.

Bai gamsu da maganan data fada ba.....yanayin muryarta kawai akwai wani tasiri me banbancin tsakanin kiran farko da yayi mata da wannan,duk da tsakanin kiran bai dauki lokaci me tsaho ba.

"Biftuuu" Ya sake kiranta da sautin daya sanyata taji kaman zata shide. Bata iya amsa masa ba,saboda ta sani,abune me wahala,muryarta ta fita yadda ya kamata,wataqila yaji rauni a muryarta sama da yadda yaji a dazu......wataqila ya gano wani abu da taketa gujewa take avoiding nasa.

"Akwai wani abu da baki fadamin ba" Ya fadi da kwantacciyar muryarsa yana jin yadda jikinsa gaba daya yake sake saki. Sosai maganan yazo mata a bazata,ta ware lumsassun idanunta sosai zuciyarta tana bugawa. Akwai nisan tazara a tsakaninsu.....amma me yasa yake iya sansano wani abu?.

"Me?" Ta furta a hankali.

"Eh" Shima ya bata amsa da wannan husky voice din nasa da kasala ta cikashi fal. Ci gaba da bugawa zuciyarta ta dinga yi,tsoronsa yana cikata. Bata shirya ba sam.....bata shirya karba da fuskantar komai ba a yanzun. Me yasa yake iya gane komai ne?,wanne irin mutum ne shi?.

"Me kika boyemin?" Ya tambaya yana cize lips dinsa na qasa saboda tsigar jikinsa data sake tashi sakamakon fitar numfashinta da yaji a hankali ta cikin wayar. Kai ta girgiza da sauri da dukkan qoqarin ta nason binne koma meye takeji a kansa.

"Ba komai,me yasa zan boye wani abu?,akwai wani abune a tsakaninmu?" Murmushi me sanyi ya kubce masa wannan karon,murmushin da sautinsa yakai har kunnuwanta ya kuma sake kashe mata jiki gaba daya. Yadda tayi maganan da sauri da salo iri na son kare kai shine abinda ya d'arsa masa wani abu a ranshi,amma a yanzun bayan buqatar jin muryarta so yake hirar tayi tsaho koda kadanne......ya fara samun wani relief yanzu haka.

"Eh akwai......akwai biftuuu" Ya furta sunanta a qarshe da wani yanayi dake illata mata zuciya,saita haqura da qoqarin komai ta maida kanta ta sake kwantarwa tana sauke numfashi a hankali. Fargaba takeyi......meye a tsakaninsu?,me ya gano game da ita?,yanayinta ko muryarta?.

"Akwai akhnaaan........kewata kike" Ya fadi kai tsaye yana sake fadin sunanta a tausashe.

Idanunta ta runtse sosai,kamar wadda taga wani abun tsoro,bugun zuciyarta yana ninkuwa fiye dana dazu.

"Waye kai?,don Allah waye kai?" Ta samu kanta da jefa masa tambayar da asalinta adane take a zuciyarta,bata kuma shirya furta masa ita a yanzu ba.

Shuru na sakanni,sannan ya saki murmushi kadan.

"Wani bawa ne ni......wanda ya sanya bauta a gaba".

"Bawa?"

"Eh" Ya amsa mata kai tsaye yana son karantar komai daga muryarta.

"Bakayi kama da bawa ba" Ta fadi kanta tsaye a wannan karon tana jin takai maqura nason sanin wayeshi.

"Bakiyi kama da wadda bata kewata ba......kaman dai na fara cin nasara ko?" Maganarsa ta yanzun ta maida kwadayin son jin amsar tambayar da tayi masa.

"Kinji kewata da gaske?" Ya fada muryarsa na sake yin qasa sosai.

"Aah" Ta amsa da sauri,saurin da yake sanyashi wani siririn murmushi. A komai tana qoqarin nuna tsayayya ce jajirtacciya ce......saidai a wannan fagen.....a wannan fannin,a wannan bangaren kamar dai bata da wayo.

"Shikenan......inzo zaki sake fadi a gaba na?". Idanunta ta soma warewa sosai tana kallon duhun daya mamaye dakin. Inde da gaske zuwan zaiyi a yadda takeji zuciyarta ta narke da kowanne bugu.......a yadda takejin zuciyarta a yau kamar tana shirin fin qarfinta,zuciyarta kamar tana son d'arsa mata wani abu da takejin bai kamata da zuciyarta da rayuwarta ba.......komai zai iya karanta daga idanuwanta,wanda a yanzun sam bata shiryawa hakan ba.

Maimakon ta amsa sai kawai ta zabi kashe wayar ta cusata qasan pillow,sannan itama tabi wayar qasan pillow din tana qanqameshi sosai tana kuma jin yadda zuciyarta taci gaba da bugawa.

Wayar ya zare daga kunnensa a hankali,wani murmushi da baisan me ya haddasashi saman fuskarsa ba yana subucewa. Ya maida idanunsa saman wayar,yana juyata a hankali a hannunsa.

"Wannan shine rauninta" Abinda ya fadi kenan a hankali can qasa maqoshinsa yana motsa labbansa. Yaja iska sosai ta hancinsa yana fitarwa ta bakinsa,yana jin yadda ya samu sassauci sosai,yana kuma jin yadda jikinsa yake sakewa sosai,wata kasala tana baibayeshi.

Tunda yake a duniyarshi ba wani sauti ko murya na wata d'iya mace daya taba sanyashi a irin wannan yanayin.......baima tsaya ya saurara ba ballanta ya dasa masa komai cikin kanshi. Amma ita fa?,da sauti kawai?,da dan qaramin kusancin da baiyi zurfin da zai shiga rayuwarsa can ciki ba?,saidai kusancin yana neman masa illa da baisan iyakar inda zai tsaya ba?.

"Me yasa?" Ya tambayi kansa sanda ya sauke wata qatotuwar ajiyar zuciya yana jin yadda wankansa ya baci gaba daya. Me yasa qanqanin abu a kanta yake masa tasiri?. Me yasa yakejinta kusa dashi sosai?,bai taba jin irin wannan kusancin ba. Ta tsaya masa a tunaninsa.....itace mace ta farko da zai kalli idanunta yaji wani abu. Itace mace ta farko da zaiji muryarta yaji wani yanayi na daban tattare da shi,itace mace ta farko da zai kalli jikinta yaji tamkar ana fusgarshi.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Kiran ahmad muhammad hammud almaz shine ya katse masa tunaninsa,ya shafa wayar yana amsa kiran. Da wannan tarin girmamawar suka gaisa da ahmad,girmamawar da almaz bai banbanceta data mahaifinsa ba.

"Bani minti goma zan kiraka yanzun" Yace da ahmad.

"To in sha Allah" Ya amsa masa a girmame. Wayar ya katse,sannan ya miqe a nutse ya wuce bathroom,ya tsarkake kansa ya hado da alwala ya dawo,ya tsane jikinsa sosai,wannan gargasar data lullube ko ina na jikinsa. Ya shirya kansa cikin silk Moroccan jubah,fara qal me adon golden din zare. Wani irin kyau yayi.....ajiyayyen kyau da zaka dauka wani ado yayi bawai jallabiyya bace a jikinsa. Ya sani nanay yanzu haka tana can tana jiransa,don haka ya zura flip-flops masu taushi farare ya dauki wayarsa ya soma fita a dakin,qamshinsa yana tsayawa a duk inda ya gifta tamkar bai wuce ba. Kan hanya ya kira ahmad,yana tafiya da nutsuwar nan dake sake nuna kwarjininsa.

"Ya yanayin sultane?.....ya komai yake tafiya a masarauta?" Haisam ya fadi yana bada hankalinsa ga ahmad.

"Jikinsa yana nan kamar yadda yake......ba wani ci gaba a yanayin farfadowarsa da kuma komawarsa dogon baccinsa". Kai haisam ya gyada a nutse.

"Ka nutsu ahmad da kyau......karka karkata damuwarka da sanya idanunka akan ciwon sultane kadai.....a yanzu tarkon da kake ciki yafi wanda sultane yake ciki......ba wanda ya isa ya yiwa sultane komai a yanxu.....kai din kaine abun hari......kaine abu mafi sauqin da za'a cimma,tabaka kawai yana nufin taba ran sultane ne gaba daya"

"Bani shawara....." Ahmad ya furta. A duk sanda zaiyi magana da haisam,duk yadda yakai ga sarewa,duk yadda yakai ga mutuwar jiki da rasa fata da buri......maganganun haisam kawai suna gina wannan da gini me qarko a zuciyarsa. Yana gina masa JARUMTA.......yana gina masa YAQINI har sama da yadda yake dashi a baya.

"Banason tasan komai......banason tasan rashin lafiyarsa.....duk wanda zai iya gaya mata inaso ka shaida masa abinda nace"

"Idan da bamu hadu dakai a rayuwa ba......da yanzun a wanne mataki.muke?" Ahmad ya fada a sanyaye da wani yanayi daya sanya wani irin tausayinsa shida Akhnan samun muhallin zama na sosai cikin zuciyarsa.

"Ba azzalumai bane ku,koda babu ni Allah bazai bari ku tozarta ba" Yayi furucin da wani yanayi daya sake sanyawa ahmad nutsuwa me tarin yawa a zuciyarsa.

~Dukkanin magungunan da tasha da allurai bata ji ko guda daya da yayi mata aiki ba. Bata kuma saka ran zaiyi mata aikin,saboda ba maganin daya kamata su bata kenan ba.
Chapter 56 · 0% Book details