← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 176

Sashe 102

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zan kaiki wajen da hayaniyar duniya ba zata samemu ba......" Shuru

"Wajen da babu kowa da zai rabamin ke" Shuru

"Wajen da ba wanda zai sake daukemin ke" Shuru.

"Khadeejaaah" Ya kira sunanta da wannan unique accent din da daga bakinsa kawai take jinsa.

"Na gaji da sharing attention dinki da kowa" Ya qarasa fada yana ciro tarin ma'anoni daga qwayar idanun nan nata dake masa haske koda kuwa cikin duhu ne.

"Me zamuyi a duniyar nan ko?" Ya fada yana dage mata dukka girarsa biyun sama. Idanunta ta kawar tana jin kansa sosai har cikin naman cinyarta,tana jin sauti sa muryarsa kallonsa da idanunsa dukka suna sake narkar mata da zuciya lokaci guda a tare.

"We'll breathe" Ya dakata a tausashe har yanzu hannunsa yana shafa fatar fuskarta da ya sakeji ta masa wani irin fitinannen laushi.

"We'll rest" Ya sake dakatawa a kasalance

"And may be......" Ya sake tsayawa

"......finally learn each other properly" Idanunta ta lumshe a hankali. Yadda yake maganan a rarrabe kanshi wani abu yake saukar mata. Tamkar dai yana zaben kalmomin da yakeso yayi maganan ne dasu,ko yana qoqarin kiyaye abinda tafiso cikin dukka jimlolinsa.

Hannu ya miqa a hankali yana shafa kwantaccen gashin dake gefan kunnenta,wanda a baya yake kira da sajen mata. Daya daga cikin wasu abubuwa da yakeso matuqa a fuskar diya mace.

"Inaso wajen da idan na kalleki....." Sai ya sake dakatawa,muryarsa kuma ta sakeyin qasa fiye da dazu kamar me tsoron wani zai iya jinsa.

".......bazan riqa jin lokaci yana gudu daga gareni ba"

"Kana magana kamar a mafarki?" Ta fadi ba tare data shiryawa fadin hakan ba,sai don abinda yake kai kawo kenan a ranta. Wanne guri ne wannan?,wanne abu ya shirya mata?.

"No...." Ya fada da murmushi ne dan sauti Yana laluben qwayar idanunta yanason ya riqeta sosai cikin tasa,saboda yana son ta dauki duk abinda zaice mata seriously.

"I'm talking like a man who finally found peace......" Ya sake sauke wani numfashin,ya juya ya koma rub da ciki yana qanqame cinyoyinta sosai.

".......and is terrified of to losing it".

Wani irin shuru ya ratsa tsakaninsu,wani irin shuru da bugun zuciya kawai ya bari a tsakaninsu.

Bayan kowanne second sake kasheta yakeyi da kalamansa......da ayyukansa dama shigarsa gaba daya. Kalamansa zata iya rantsuwa da Allah bata taba jin masu zaqi irinsu ba.....bata taba jin zababbun kalamai irin nasa ba,wai dama haka malaman suke?,ko shine na daban?,ko shine ya fita daban a cikinsu da cikin maza gaba daya?.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 91*
_______________________
DEA’S MODEST ARTISTRY ✨
Aminataccen wajen samun
✔️ Abaya masu kyau
✔️ Lifaya & Veils masu tsari
✔️ Handmade paint work
✔️ Shadda designs
✔️ Elegant modest wears
✔️ Accessories masu kyau da inganci
Muna kawo muku kaya masu kyau, tsafta da araha domin kowane irin event 💫
Ko na daily wear, outing, wedding ko special occasions —
DEA’S MODEST ARTISTRY na tare da ke 🖤
📍Quality first
📍Affordable prices
📍Neat finishing
📍Classy & Modest styles
Ki kasance cikin kyau da nutsuwa ba tare da tsada ba ✨

https://chat.whatsapp.com/IZGMwJXP8Oa5qUc4sDSKZv?s=cl&p=a&mlu=3
_________________________

Hannunsa ya miqa mata a hankali sanda yaji alamun motar ta tsaya. Ba don baya da ikon kamosu ba

"Akhnan....." Ya kirata softly,yana kan cinyarta,har yanzu a rub da ciki,idanunsa kuma a kulle kaman bai shirya su sauka a motar ba.

"......come with me please,na miki alqawarin baki duk kalan space din da kikeso......ba takura.....ba matsantawa.....just ni dake kawai,mu raini soyayyarmu....." Ya qarasa fada yana juyowa rigingine hadi da bude qwayar idanunsa dukka a kanta.

Batasan me yajata ba,batasan yaushe ba. Ita dai ta miqa masa hannunta a hankali,ya riqe cikin nasa da murmushi.

"Bazan saki kiyi regretting ba har abada.....but.....kafin na sauke qafafuna qasa,kice kina sona.....ko sau daya ne.....don Allah" Ya fada yana langabe kai.....ya fada da kalar wannan sakalcin da taga yana yiwa nanay.

Wata kunya ce ta dabibayeta,ta maida idanunta ta kulle a hankali. Ta yaya zata iya......

"Pleeeeeeeeaaaaaaseeeeeeeeeeee....."

"I love you" Ta fada da sauri labbanta suna rawa saboda yadda ya gigitata da sautin da ya yiwa sound din wani mugun ja.

Idanunta kawai ta kalmashe sanda suke takawa hannunta cikin nasa. Wani takun girma,royal walking suke dake bayyana iko ba tare da hayaniya ko qaqarin nuna kai ba. Komai da kowa yasan girmansa ba tare da yace komai ko yayi wani motsi ba.

Dukkan ma’aikatan private terminal ɗin, manya da qanana, suna sunkuyar da kai cikin girmamawa yayin da suke wucewa.

Kyakkyawan private jet din da suke tunkara,idanunta cike da tarin tambayayoyin data gaza hadiyesu sanda suke step na qarshe na jirgin.

"Ina zamuje?" Ta tambaya tana langabe kanta a wannan karon. Ta gaji da tarin mamakin da yake bata,ta fahimci shi din wani allo ne da har yanzu bata kammala karantarsa ba.

"Dubai" Ya amsa mata a taqaice yana gyara mata gefan hijabinta cikin kulawa.

"Dubai?" Ta fada da mamaki fal muryarta idanunta suna dan fita waje kadan.

"Eh...." Ya amsa yana satar kallon reaction dinta.

"Ina neman na abinci ne a wani kamfani,sai suka gayyaceni wani taro da zasuyi" Shuru tayi bawai don ta gamsu da hujjar daya bata ba dari bisa dari. Saidai tayi shurun saboda tasan ba zata fahimci komai ba sai idan shi yaso ta fahimta din.

Abu daya kawa daya sanyata mutsu mutsu,ta dinga jin kamar ta roqeshi.amma ta kasa,kasancewar bata saba neman alfarma akan kowa game da komai ba.

"Me yake faruwa?" Ya yambayeta tana dubanta da lumsassun idanunsa.

"Akwai wani bikin bude company branch na favourite perfume dina.....a dubai ne.....date din saura kwana biyar.......don Allah.....zaka barni naje?" Ta fada da wani salo da yanayin daya qarasa karyashi gaba daya.

"Ya salaammm" Ya fada yana duban qwayar idanunta. Ashe ta iya magiya?,ashe ta iya karyar dakai har haka?,wanne irin so takewa kamfanin da turaren haka.

"Sun iya turare......best perfume brand ever" Ta sake fadi duk a qoqarinta nason amintar dashi. Yadda take magana yana burgeshi,yadda idanunta ke budewa sosai,take sakewa tana magana dashi tafiya yakeyi dashi. Bayason wannan yanayin ya yanke da sauri haka,don haka bai amsa mata ba,sai yaci gaba da kallonta kawai.

"Don Allah.....zan aike musu email na neman invitation din. Nasan zasu bani indai sukaji daga agadez ne. Ko ban samu shiga ba,zan tsaya na jira ganin founder na company din".

" Zakije....zaki shiga.....in sha Allah".

"Na gode" Ta fada da wani irin murna har tana rungumarsa bata lura ba. Sai kuma tayi yunqurin janyewa da sauri,saidai ya rigata da zafin namansa,ya jawota zuwa cikin jikinsa yana cewa.

"Good girl,wannan shine lada na ai,ya zakimin rowa?" Murmushi ya qwace mata a kunyace,ta saka fuskarta tsakanin qirjinsa,ta lumshe idanunta tana jin sassanyan qamshin dake fita daga tsakiyar gurin

"Ya Allah......Wani irin qamshi ne wannan?..…Too elegant for one man.” saita sauke numfashin a hankali tana zame jikinta,ya saketa a nutse ba tare daya qalubalanci hakan ba.

*_DUBAI INTERNATIONAL AIRPORT_*

A hankali private jet dinsu ya sauka akan runaway cikin tsari,ba'a babban airport na gama garin jama'a ba,aah...cikin private Royal terminal . Guri ne da luxury jets kawai ke sauka ta nan,gwamnoni....sarakuna....da kuma manyan billionaire's.

A hankali ya sauke idanunta ta cikin window din tana kallon qasa,jerin motoci ne baqaqe dake sheqi da daukan idanu a jere cikin tsari suna jira. Luxury SUVs. Rolls-Royce Phantom. Sai security convoy..

Da idanun ba kuma tare data sauka ba ta fahimci yadda komai na gurin ke dauke da nutsuwa da wani irin tsari ba tare da hayaniya ba. Irin tsarin da zai gaya maka akwai mutum me daraja da girma da ake jiran isowarsa a gurin.

Ya miqe tsaye daga kujerarsa cikin nutsuwa. Cuff din hannunsa ya gyara,sannan ya dauki agogonsa yana qoqarin maidawa tsintsiyar hannunsa.

A sace ta kalleshi,komai nasa yana nuna old money discipline,ba hayaniya.....ba nuna kai,saidai a jikinka kana iya jin presence nasa saboda kwarjinin da Allah yayi masa. Komai nasa cikin nutsuwa da sanin girma kai,yana komai cikin yanayin da zai gaya maka nutsatsen mutum ne shi da bai taba gaggawa ba a komai.

"Ready?" Taji ya furta a hankali,abinda ya sanyata saurin janye idanunta daga kanshi kenan ta sake maidawa ga window din zuciyarta tana wani irin bugawa.

Kada dai ace yaga yadda take qare masa kallo?. Ya yanke mata tunaninta sanda yake sunkuyowa inda take,ya sanya hannuwansa gaba daya yana dagata tsaye,sassanyar iskar hancinsa tana dukan fuskarta wadda ke cakude da turarensa dan amana.

"I'm your halal.....dukkanina khadeejah....halal dinki ne,ki kalleni as much as you can.....ba laifi...." Sai ya dakata kaman yadda maganansa yake a tsare. Yatsansa ya daga yana nuna saitin qirjinta dashi.

"Kibar wannan mallakin tawa ta huta....ki daina razanata haka kina sanyata tana gudun wuce kima". Tsit tayi tana kasa hada idanu dashi,gaba daya ya qarasa qona mata ruwan kai,ta fahimci al'adarsa ce.....yana da basarwa,ya gani yayi kaman bai gani ba.....yaji yayi kaman baiji ba,haka tayita gasa masa magana akan French language,amma yanzu ta zama tamake 'yar koyo a gabansa,har ba komai takeson tayi magana akai da yaren ba.

"Ready again?" Ya sake fada yana tsaronta kayarsa da qwayar idanunnan nasa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Kalma daya.....amma daya fadeta sai taji kamar umarni ne da zuciyarta ta riga ta yarda dashi kafin karan kanta.

Hannunsa ya sake miqa mata,a yanzun ma ba wani haufi ta saka nata a ciki. Matseshi yayi softly yana duban blue eyes dinta. Bada qarfi ba,amma kuma kaman yanason ya tabbatar mata da ownership dinsa ce ita me cike da kariya daga garesa.

Daya bayan daya suke takawa har zuwa bakin jet din. Royal walking,wata irin nutsuwa me bayyana girman da basai an fada ba.

Daddadar iskar dubai ta soma sauka saman fuskarta,warm elegant dauke da wani qamshin alfarma.
Chapter 102 · 0% Book details