← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 176

Sashe 137

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake takawa yayi zuwa gabanta,idanunsa dauke da wani zuzzurfan kallo. Ba irin kallon mata da miji ba.....ba irin kallon dake dauke da taushi qauna ko bege ba.....aah....

Kallo ne da wanda akaci amana yakewa wanda yaci amanar tasa. Kallo ne irin na wanda soyayya ta juye masa zuwa zazzafar qiyayya.

"Kinyi mamakin dawowata ko?" Ya fada yana sake jin wata matsananciyar qiyayyarta tana hudashi.

"Ka saurareni!" Ta qwato kalaman da qyar tana jin yadda harshenta da maqoshinta gaba daya suka bushe,ba wani digon yawu,tana ji kuma a ranta da zuciyarta cewa.....komai bazai tafi a haka ba.....komai zai daidaita. Hargitsin na wani d'an lokaci ne kawai.

"Shuru!" Ya fada cikin daka tsawar data sanya kowa sunkuyar da kansa cikin ladabi bawai iya mammina kawai ba. Sabon abune wanda basu taba ganin irinsa ba. Sultane yayi magana da hadimai da irin sigar nan bama ballantana kuma matarsa.....matar tasa ma kuma GIWA.

"AKHNAN!" Ya kira sunanta a kausashe.

"Yarinyace da aka rasa uwarta" Sai muryarsa ta karye.

"Na dorata a hannunki"

"Amma maimakon ki zame mata mafaka......sai kika mayar da rayuwarta filin yaqinki" Motsawa baya kadan mammina tayi,komai yana gwada mata duk abinda ke faruwar nan da gaske ne yake faruwar.

"Kin rabata da danginta....."

".....kin cusa mata qiyayya"

"Kinci amanar gidan nan" Ya dakata yana jan numfashi da qyar idanunsa suna sauya launi.

".....amma abinda yafi karyani....."

".....ashe duk tsahon shekarun nan jiran mutuwata kike ki tarwatsa iyalina....ki tarwatsa ahalina.....ki shafe komai nawa daga duniya".

" Wallahi ina sonka" Ta fada tana girgiza kai,tana jin kamar kwanyarta na shirin fara aiki ba daidai ba.

Ji yayi kaman ta dauki guduma ta doka masa a tsakiyar kansa.

"Kina dai son nasara.....kinason nasararki,kuma kin shirya yinta ta kowacce hanya. Kansa ya dauke,don baya qaunar ganinta ko yaya,ya waiwaya ga tarin guard din dake tsaye.

"Ku saki Ahmed.....ku fitomin da safiyyatah!.....sannan ku tabbatar.....duk wanda aka tsare bisa zalunci a sakeshi bisa yardar yarima haisam" Ya fada maganan da wani amo.

"Kinsan me yasa ban bayyana tun farko ba?" Ya sake juyawa gareta sanda guard din ke fita da sassarfa don cika umarnin adalin sarkinsu.

"Saboda inaso naga iya duhun da zuciyarki ke dashi.....a kwanciyar da nayi da sunan ciwo.....ba ciwo bane.....hutu ne da haisam ya yanke bawa gangar jikina.....na huta,na karanci wasu abubuwa da xirga zirgar mulki.....kula da jama'an dake wuyana......da makircin masu makirci da idanuwana basa iya gani....."

".....ina kwance.....amma ina iyaji.....ina kwance amma ina gani......naji!.....na gani....tun daga sanda kika fara saka guba cikin fankoki da ac da pillow din da zan dora kaina a kai......daga sannan haisam ya fara shirin yadda zan mutu a idanun duniya kafin ki sakani nayi mutuwar gaske." Wani irin shock ya sake shigan kowa. Mamakin wannan idea ta yarima sheikh muhammad haisam yana sake shigarsu.

"Nasan wacece ke zaituna......gudajjiyar me laifi daga Ethiopia......wadda ta biyo safeena......ta biyo dukiyar ajani.....wadda ta shigo ahalina.....saidai wani abu daya...." Ya fada yana hadiye yawu da qyar.

"Shi Allah......adalin sarki ne.....ya hanani sanin wacece ke......bayan inacan ina damuwa don baki haihu ba.....ashe ya hanani....bani kadai ba.....ya hanaki haihuwa da dukkan mazan da kika aura saboda bamu da haqqinki......saboda ke din GUBA ce.....saboda baki cancanci zama UWA BA!"

"Ba hukuncin agadez kawai ke jiranki ba,.....zaki isa Ethiopia......zaki kuma amsa nasu tuhumar qarqashin jagoranci da binciken sheikh muhammad haisam"

"Haisam kuma?" Ta fada tana dauke idanunta daga kan handcuffs din da ake maqala mata. Da farki kafin ya kira sunan haisam.....sanda ake maqala mata ankwar.....tana dubanta ne.....tana jin cewa itace mafi girman tozarci a gareta......amma yanzun da yake shaida mata cewa.....zata fuskanci tuhuma daga wajen hukumomin Ethiopia.....kuma qarqashin sheikh haisam......sai taji wannan tozarcin yafi na maqala mata handcuffs din sau dubun dubata.

Bai amsa mata ba.....amma yaga meye cikin idanunta. Nadama yakeso ya gani me zurfi,duk da hakan bazai qaresu da komai ba shi da ita.....amma sai yake hangen akasin hakan daga idanunta. Kansa ya sake daukewa,sai ya waiwaya ga al'ummar dake gurin.

"Ba ita kadai ba.....duk wanda ya taimaka wajen qulla dukkanin wannan sharrin......to xa'a bincikeshi shima". Ya juya yana nuna mammina da yatsarsa.

"Amma ita......ta rasa matsayinta da komanta a wannan masarauta daga yau!". Daidai sanda guard din suka fara janta. Wani irin fusga me cike da rashin girmamawa.

"Muhammad!!!......don Allah!!!.....ka tsaya ka saurareni!!!,sharrin maqiya ne.......abinda kazo yanzun ka tarar yana faruwa!....."

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Abinda ke faruwa yanzu?.....wansa ya faru a baya fa?.......ko alfashar da kikaso yi da hadiminki da kika saka aka qulle da sunan d'an tawaye saboda bai baki had'in kai ba shima yansu ya faru?!!!......zaituna!.....Ki kirani da matsayina.....ba da sunan mijin da kikaci amana ba....sunana na gaske yabar bakinki da bashi da tsarki!." Ya fadi yana jin zuciyarsa kamar zata tsinke daga qirjinsa ta fado.

Dif wuta ta daukewa mammina.....bama ita kadai ba.....kowa dake gurin.

"Ka yafemin" Ta fada wani irin kukan baqincikin tona mata asiri da rashin mafita da bata hango ba ya qwace mata.

Idanunsa ya lumshe yana jin jininsa kamar gashi yana hawa. Ya lumshesu na second daya yana jin kamar ya binne wadancan shekarun gaba daya.

"Da ace laifin a iya kaina ni kadai yake......"

".....wataqila na iya yafewa" Sai ya bude idanunsa da suka sauya zuwa kalar ja,wani yanayi daba wanda ya taba ganin sultane a cikinsa. Wani yanayi daya sanya kowa sadda kansa qasa.

"Amma kin cutar da marayi.....ba daya ba ba biyu ba.....uku!.....dukka jinina.....akhnan.....mahmud.....da jinjirin ajani......kinso hada haramtaccen aure a tsakanin jini daya......saboda SAFEENA KAWAI?". Mummunar kaduwa ta sakeyi.....dukka wannan.....dama sauran sirrikanta......haisam ya sani?,haisam ya gaya masa?.

"Ka yafemim....bazai sake faruwa ba.....ka dakatar dasu mu fahimci juna.....zan gyara kura kuraina.....zan gyara komai" Ta fada tana jin wata masifa da bala'i suna tsarga mata. Daga waje.....ta hangi tarin 'yan jaridu kafe da cameras da takardu abubuwan rubutu da abubuwan nadar sauti.....ta tabbatar kuma jiran fiddo da ita kawai suke.....kaman yadda kura ke jiran shigowar nama dakinta.

Murmushi me ciwo.....shine abinda ya subucewa sultane....irin ciwon da wanda ke nesa ma sai daya hangoshi. Mamakin rashin kunyar mammina.....mamakin qarfin halinta.

"Matata?" Ya tambaya kaman yana tantama. Ya daga idanunsa yana kallon dattawan da kyau.

"A cikinku.....a nan na tabbatar akwai wadanda suka shaida daurin aurena da zaituna shekarun da suka wuce......to a yanzun a gabanku inaso ku shaida....." Sai ya kalli magatakarda.

"Dakai da mataimakanka.....dukkaninku ku ukun ku rubuta.....ni muhammad hammud........sultane na agadez......na saki matata......"

"Sultaaannne!!!......don Allah!!!!" Ta fada tana turjewa guard din sanda suke dab da fita kuma take jiyo kalaman bakinsa.

Abu na qarshe da zai mata da yafi komai ciwo cikin abinda yayi ko yace kenan......ya rabata da aurensa....auren daya bata kariya......ya bata garkuwa......ya bata abubuwa da yawa da bata isa ta mallakeshi ba. Koda da amsa sunan MATARSA kawai wata alfarma da martaba ce a tattare da ita.

"......na saki matata zaituna saki daya"

".......ya isa sultane.....don Allah!!!" Ta fada tana hada hannayenta biyu guri daya daga inda take tsaye.

"Na saketa saki biyu"

"Na roqeka sultane don Allah!!!" Ta sake fada da mahaukacin sautin daba wanda ya taba jinsa a tattare da ita.

"Na saketa saki uku!" Ya qarasa fada da wani sauti da amon daya ratsa gurin,shuru kuma ya maye gurbinsa.

"Ku ninke ku bata dukkanin takardun uku ta fita dasu......don wannan ce fitarta ta qarshe a gidan nan......" Ya fada cikin umarni.

Sauri sauri suka ninke.....suka kuma miqawa guard din suka karbar mata.

"A tabbatar a yau.....basai gobe ba.....an kwashe komai daya danganci zeenatu anbar gidan nan dashi" Yayi magana ta qarshe yana fita ta qofar baya,qaramar qofar daya shigo a dazu.

Waiwayawa tayi tana duban tafisu. Ta yaya zata bari a tafi da ita haka a qasqance ba tare da tafisu ba?. Ta rasa kowa amma ba zata rasata ba....a duk inda zata fuskanci hukunci tasan zata taimaketa.

"Tafisu.....tana daya daga cin...."

"Karki kuskura ki qarasa" Tafisun ta fada tana dagawa mammina yatsa,abinda ya kusan sumar da ita kenan da wani irin d'an banzan mamaki.

"Kin dauka nima shashace maciyar amana irinki?. Aduk shekarun da muka dauka....kin dauka ina aiki a qarashinki ne?,ina aiki saboda ke ne?" Ta mata tambayar data sanya mammina taji jinin jikinta yana qafewa.

Kai ta girgiza tana dubanta idanunta fal da hawaye.

"Ni 'yar halak ce.....ina zaune dake ne saboda AKHNAN......bazan taba manta halascin safeena a gareni ba...." Ta fadi muryarta tana katsewa da wani irin kuka me cin rai.

"Mutuniyar kirki kenan...baiwar Allah....Allah ya rahmsheta" Sautikan mutane daban daban na yabon safeena ya dinga shiga kunneta. Da qarfi ta runtse idanunta,tana fatan ta daina jin wadannan muryoyin masu yabon safeena a gabanta.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 124*
__________________________
*_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________
Chapter 137 · 0% Book details