Sashe 122
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mammina ce mutum ta farko data fara shigowa,cikin black royal tufafi dake bayyana ikon da take neman daukakawa. Daga bayanta kuwa bayine da hadimai masu kula da tsaro na sasannin sultane......'yan sanda harda sojoji a cikinsu.
Tsakiyar hall din ta iso,idanunta a bude tarwai
"A dakatar da wannan nadin!" Ta furta da madaukakiyar murya tamkar ba macen dake cikin takaba ba. Ta maida idanunta kan jami'an tsaro sannan ta aza akan ahmad dake tsaye.
"Hajiya zaituna" Muryar wazeer ta fada a rude tana dubanta.
"Dakata!......." Ta fada cikin fusata tana daga masa hannu.
".......Ba za’a dora wanda ake tuhuma da kashe Sultane akan kujerarsa ba!.” a hankali haisam ya lumshe idanunsa sannan ya budesu tar kan fuskar mammina. Yanaso ya gane a wanne jinsi zai sanyata?,yanaso ya fahimci mutum ce ita ko wata halittar dabbar ta daban?.
Wani irin girgiza ilahirin hall din yayi,dukkan wasu manyan fada dake gurin suka soma kallon kallo cike da zallar mamaki,qananun surutai suka fara tashi kadan kadan.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Nannie take fada a birkice idanunta dukka a waje. Rawa kawai ilahirin jikinta yake,mammina take kalla,kwanyarta a yanzun tana komawa shekaru talatin baya. So take ta dauko maga wacece wannan mamminan?,....wannan mamminan da suka qyamaci aurenta?.....wannan mamminan da magabatansu suka hana sultane aurenta.....wannan mamminan da ita kanta asali bata sonta.....amma kirkinta ya rinjayeta.....ya rinjayesu gaba daya suka manta da duk wani qishin qishin din bincike a kanta. Maida dubanta tayi ga morsa safiyya,idanunta a lumshe suke tamkar batason taga kowa da komai dake faruwa a gurin,saidai can qasan zuciyarta
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Astagfirullah" Take fadi a hankali tana maimaitawa.
Daya daga cikin dattawan masu zartawa ya dakatar da yamutsewar gurin,ya miqe yana duban mammina din.
"A dakata jama'a.......a saurara"
"Ku kamashi!" Ta furta gaba gadi kai tsaye.
"Me kike fada?,kin rasa hankalinki ne?" Ahmad ya furta yana takawa gabanta. Dukkanin idanunsa a bude suke tarwai,kamanninsa yana son komawa na wannan almaz din data raina a baya. Murmushi ta saki a nutse tana dubansa.
"Koda ka qaraso gurina.....ba abinda zaka iyayimin...." Ta fada tana jin zafin yadda daren jiya duka ta sanya a nemo mata shi,su bugar dashi da kayan mayen daya daina sha,ya sanya mata hannu a wadannan takardun sannan a yau ya tashi cikin maye a gaban kowa,saidai sama ko qasa ba ahmad din ba dalilinsa,abinda ya sanya ta qarfafa zarginta akan lallai akwai wanda ya sanar masa da wani abun,wanda babu wanda tafi maida hankalinta a kanshi irin HAISAM ALSAAMIT.
"......ko kunsan tsohon mashayi aka dauko a matsayin yaron sarkinku!" Wani irin hautsinewa gurin ya sakeyi
"Ku kamashi!" Ta sake fada saboda duk qaruwar minti daya tana jin kamar delay take jawo mata. Tanaso kafin sultane ya cika kwanaki bakwai a kabarinsa ita ta gama nata aikin. Tanaso kwanakin bakwai din suzo daidai da sanda zata gama hargitsa masarautar kuma ta tashi.daga wannan duniyar data dade qulle a cikinta. Ba wata duniya data taba dadewa haka zaune a cikinta tana jiran wani abu irin wannan duniyar.
"Ba zamu bari ku kamashi haka kai tsaye ba" Daya daga cikin dattawan ya fada.
".....akwai hujjojin da suka bayyana qarara suka kuma nuna yarima ahmad yana da hannu a mutuwar marigayi sultane" Wani d'an tittirnan mutum dauke da kaya irin na lawyers da tarin files a hannunsa ya matso gaba yana fadi gami da soma bude wani babban file cikin files din hannunsa.
"Wacce hujja kuma?" Morsa safiyya ta furta cikin ba zata tana bude idanunta tarwai a kansu. Idanu mammina ta aza mata......tanaso ko sau daya,ko sau daya wannan fuskar......wannan halittar RAZANI TSORO da FIRGICI ya nuna saman fuskarta. Saidai har a yanzun da take shirin fara yiwa iyalinta d'auki d'ai d'ai ba wannan alamun a tattare da ita.
"Rahotannin masu tsaro guda biyu..." Ya sake fada mutumin yana daidaita takardun hannunsa.
"An samu tabbacin cewa,a daren da sultane ya rasu,kaine mutum na qarshe daga shiga gurinsa,ka kuma fito da mintuna masu qarancin tazara Allah yayi masa rasuwa" Kallon kallo aka fara yi,kafin mutumin ya dora.
"Kuma masu tsaron sashen sultane guda biyu,mafi kusa da dakunansu sun shaida cewa.....sunji sabani tsakaninku kwanaki kafin mutuwarsa"
"Wannan qarya ce!" Ahmad ya fada cikin fusata yana motsawa kaman zai kaiwa me karanto bayanan duka.
"Ka nutsu.....nan fa ba mashaya bace" Mammina ta fada tana sakin murmushi.
"Tabbas haka ne" Muryar hadimin ta ratsa gurin yana matsowa tsakiya. Mahadi.....daya daga cikin mafi kusanci kuma amintattun da aka yarda sukai kusa da dakunan sultane.
"Naji sultane yana cewa bazai yarda da wasu abubuwan da yarima Ahmad yakeso ba......shi kuma yana fadin babu wanda ya isa ya masa shamaki da tsarikansa da abinda yakeso" Ya fada da yanayin da ba tsoro ko shakka a tattare dashi.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Akhnan ta fada a hankali tana lumshe idanunta,tana jin kamar bugun zuciyarta zai dakata daga aiki. Hannunsa ya sake matsewa cikin nata zuciyarsa na bugawa sosai. Yana kallon yadda matar ta shirya qarya ha'inci yaudara da cin amana,takeso ta gamsar da kowa cikin salo me burgewa. Koda dukka jikinsa kunne ne......ba yadda za'ayi ya amince ahmad zai iya kashe sultane.....to ta yaya ma?,yaron da sultane din kawai ya sani?,shine duniyarsa?,shine kadai ya rage masa?.
"An kuma samu wannan" Mutumin yaci gaba da rattabo bayanai yana matsowa kusa.
"Menene?" Daya daga cikin dattawan ya fada.
"Guba ce......gubar da aka sameta a sassan yarima ahmad,bayan an samu ragowar irinta a matse matsin gadon sultane" Shock kowa ya shiga,wasu suka waiwaya suna kallon ahmad din,ciki harda akhnan da falaak.
Ba don sun yarda ba.....sai don yadda hujjojin sukayi hatsari da yawa....yadda hujjojin zasu iya shigar da shakka da kokwanto a zuciyar al'ummar agadez.
"Ahmad?....ahmad fa" Akhnan ta fada ita da kanta wannan karon tana matse hannun haisam a nata.
"Masarautar azbin tana da dokoki!!!" Mammina ta fada tana dukan table din dake kusa da ita. Shuru ya sake wanzuwa......ta juya tana karbar wata tsohuwar takarda daga hannun daya daga cikin masanan doka na masarautar.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 110*
".....Doka ta goma sha bakwai....."
“…ta bayyana cewa......duk magajin da ake zargi da hannu cikin mutuwar Sultane......”
“…za’a dakatar da nadinsa har sai an gama bincike.”
Wani irin shuru hall din ya dauka......shurun da kowa ke da tabbaci akan dokar. Kowa ya sani,haka dokar take a rubuce,kuma har yau har kwanan gobe ba abinda ya sauyata akanta masarautar take aiki.
"Kuma idan zargin ya shafi cin amanar jini…” ta fada tana dora idanunta akan ahmad dake tsaye dukka jinin jikinsa a daskare.
"…masarauta na da ikon tsare wanda ake zargi ba tare da jiran nadin sarauta ba.”
"Qwarai kuwa....haka yake a rubuce cikin doka" Daya daga zaune cikin dattawan fada ya fada saboda tsegungumi da suka fara tashi gurin. Doka haka yake a rubuce......amma kuma zukatan wasu basu kwanta da ita ba.
"Wannan ba tsari bane......bai kamata ba.....abune da hankali bazai dauka ba" Wazeer ya fada yana dubanta,jikinsa yana rawa saboda tashin hankali ga shekaru,idanunsa akan mammina. Waiwayowa tayi ta kalleshi,ta dade tana jin haushin mutumin,ta dade tana zarginsa akan hana ma ruwanta gudu sosai,tsakaninta da sultane ko kuma cikin fadar,yanzu ya jefa kansa cikin issue din da asali babu shi a tsarin
"Duk wanda zai hana a kama Ahmad......tabbas zai shiga sahun wadanda za'a iya tuhuma da hadin bakinsa......ku kama WAZEER......sannan ku kama Ahmad ku tsaresu dukkaninsu". Ta fada tana jin wata power.
Fara tattaki sukayi da wani irin energy,kamar wadanda zasu kama wani zaki.
"Aah.....bazai yuwu ba!" Falaak data kasa jurewa ta miqe tana fada dukka jikinta yana rawa.
Tsam morsa safiyya ta miqe.....ta damqe hannunta falaak cikin nata tana zaunar da ita.
"Ki nutsu falaak.....ki nutsu....me laifi shike tsoron kamu.....kamun Allah kawai muke shakka,don duk wani kamu na duniya ya biyo bayan na sarkin sarakuna!!!" Morsa safiyya tayi maganan da dakakkiyar muryarta da ba tsoro ko shakka a ciki.
"Ahmad jinin safeena ne.....jinin safeena ba tsoro a cikinsa.....jinin safeena halastaccen jini ne da ba abinda ya isa ya batashi ko ya gurbatashi......tana tsarkakakkiyar haihuwar da ba wanda ya isa ya taba wannan nasabar!!" Ta sake fada da muryarta data amsa a kowanne sashe na hall din. Saqonta yakai.....saqonta ya isa zuwa duk inda takeso ya isa. Ahmad da mammina,mamminan da ambatar suna safeena yaje ya mata tsaiwar mashi a zuciya.
"Dole na haramta kiran wannan sunan a gidan nan.....dole na shafeta har a bakinsu" Ahmad kuma maganganun sun sake daukan hankalinsa zuwa ga morsa dinne.
"Haisam......" Akhnan da bata fahimtar komai ta fada tana matse hannunsa da qarfi. Ahmad kawai take gani.....kuma ahmad ne kawai bataso a tafi dashi yanzu......wannan kawai shine matsalarta ba komai da ake tattaunawa ba.
"Pleeeaseee" Ta furta tana juyowa gareshi,fitar kalmar ya hade da fitar hawayen idanunta. Shi kadai ne take da hope.....shi kadai ne take da fatan yana magana komai zai canza.
Idanunsa ya daga a hankali ya zubewa ahmad su. Wani irin kallon kallo a tsakaninsu na tsahon wasu sakanni.
"The investigation should continue......and the low should proceed". Ji tayi kaman ya sanya hannu ya zabga mata mari.
" What?" Ta fada a gigice kunnuwanta suna kasa yarda da abinda taji. Kai ya gyada mata a hankali ba tare daya kalli cikin idanunta ba,don bazai iya kallon idanun nata ba.
"Idan har shi bame laifi bane.....gaskiya zata wankeshi" Ya fada Kai tsaye da wannan tarin nutsuwar tasa.
Yayi maganan ne idanunsa akan mammina.....yayin data sakar masa wani murmushi. Murmushin da zuciyarta ke yaudararta tana gaya mata ta fara nasara.....kuma itace da nasara har abada. Taku suka sakeyi guard din don isa gareshi dauke da handcuff.
"Ku dakata!" Morsa safiyya ta furta cikin wani irin zafi.