← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 138

Sashe 97

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya ya sauke ya dago dubansa ya dora saman AMMI, a sanyaye ya ce" *SHIN LAFIA UMANI AKA RIKEN MATA YAU KWANA HUDU BATA ZO INDA NAKE BA?*

Ammi ta kale shi da sauri tana kara jin dirara magangannunsa a kunnayenta, UMMU kuwa sai ta kaida kanta a kasan zuciyarta tana murmushi, AMMI na kallonsa da kulawa ta ce"

*SAKON GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI ZUWA GAREKU A DUK INDA KUKE, NA SAN KUN SAN DALILIN SHIRUNMU BAKI DAYA YAN NIGER, ALHAMDULILAH MAY BE KOMAI YA DAIDAITA, SOSAI NA TARAR DA SAKWANI MASU MATUKAR YAWA YAN UWA DA AMINAN ARZIKI, DA YAWA NA NUNA TASHIN HANKALIN RASHIN JI NA, DA YAWA NA NUNA KULAWARSU DA SAKON GAISUWA, NA GODE ALLAH YA BIYA ALLAH YA SAKA MAKU DA ALKHAIRI YA BAR KAUNA, HAKAMA WA'INDA SUKA RINGA SAKWONNINSU NA KYAUTATAWAR DA SUKA YI NIYAR YI MIN DAN JIN DADIN WANNAN NOVEL NAWA SAKWANNINSU SUN SHIGO KUMA AN SHAIDA MIN ALLAH YA KARA ARZIKI YA BIYA, MASOYA, A DUK INDA KUKE SAKON GAISUWATA ZUWA GAREKU, ALHAMDULILAH GRUP MAGE BANI DA TAMKARKU, ALLAH YA BIYA YA KARA DANKON ZUMUNCI, GASU FA, KADAN NE....AMAN IN SHA ALLAHU MUN DAWO BAKIN AIKI😅😅😅😅, daga taku ce SAJIDA*🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

50

Cike da basarwa AMMI ta ce" eh ta dan yi rashin lafia ne"

Idannuwansa masu girma da ladaftar da mutun ya zubawa mahaifiyarsa yana kallonta, bai ce komai ba aman a yannayin kallon da ya kurawa fuskarta ya fasara irin tarin tambayoyi ko nace tarin son karin hasken da yake,

Cire kanta ta yi daga dubansa ta maida wajen tanfatsetsiyar tV din dake jikin bango wace ke kashe tana dan girgiza kafarta daya ta dora da fadin" idan kuwa ita dinma gaba za'a yi da ita a hanna min ganninta sai na ji karin bayani "

Dan murmushi ya yi yana sauraron Nusaiba na tambayar ya saka mata Game a wayarsa bayan shi ko kwaya babu a cikin wayar, ya maida dubansa wajen UMMU,
Cikin yannayin wadatacen murmushin fuskarsa ya ce" UMANI, me ke damun kawarki ne daga farin ciki sai na ga kamar kawarki zata bata ranta fa ko menene?"

Itama dubansa ta yi, ta yi dan murmushin zata bashi amsa Mardiya ta fito daga dakinta,
Karar rufe kofar da dan karfi ya saka UMMU yin shiru bata ce komai ba

Niyar Mardiya ta fice ta karasa diner, ta gaishe da Ammi kawai, sai dai hango wani mutun mai girman jiki, kyakyawan gaske, uwa uba tarin tarin kwarjinin dake fita daga jikinsa, tarin haske da lamari mai girman dake hanna tunkararsa kai tsaye, irin tarin hasken Azhkar da salar asuba, da tarin nafilfillu dake dakushe du wani karamin tsagera, sai ko wadinnan idannuwa nasa masu zabgawa tsagera mari da suka hadu suka sakata rage saurin da ta kwaso da niyar shigewa

Da dan mamaki ya yi mata kallo daya ya cire idannuwansa a kanta, domin kuwa ya ganeta matar Abih ce, sai dai abinda ya bashi mamaki irin shigar dake jikinta da kuma ganninta kamar wace ke zaune daram dakam haka a gidan?

Tana karasowa ta dan rage tsayinta ta gaishe da Ammi

Ammi ta amsata da kulawa ta ce" Mardiya, mijin NAJEEBA ne ai ku gaisa"

Da wani irin firgici da mamaki ta dago dubanta ta yi niyar kara kallon fuskarsa, duda ba ita yake kallo ba sai ta kasa yin hakan ta tsinci kanta da saurin sada kanta idannuwanta na kara zazarowa tamkar zasu balo su fito waje, what? Mijin wa? Idan bata manta ba SULTAN SHAHEED ne ya auri Najeeba, Sultan din da take tunanin wani margayaye ne bayan rawanin nan dake kansa koda taushe, da yawa a cikin gari na tunanin wai ko dai wata kama ce da fuskarsa dake sakashi kin son bude fuskarsa ko ya ringa yin sasaukan rawani irin na sarakan zamani komai zafi? Bata taba jin du abinda take aikin banza bane irin na yau, ashe haka yake? Tana gannin ta samu galaba a kanta tunda ta aurar mata uba hakan na nufin ta rama rabata da saurayinta da ta yi, sai kuma a yau ta ga wannan bawan Allah da bata san da wani sunna zata sufanta shi ba ace shine SULTAN?

Muryarta na rawa rawa ciki ciki ta kai gaisuwarta kafin ta mike ta juya da sauri ta nufi ciki , wato ta koma tama fasa zuwa table din, sam bata da karfin iya cin wani abu, kwata kwata bata da karfin hakan, a yanzun jin zuciyarta take tamkar zata fashe, ji take tamkar zata hadiyi zuciya ta mutu, bata taba kawowa kanta Najeeba zata samu irin wannan mijin ba, bata taba tunanin zata kasance a irin wannan ranar ba, itafa bata da makiyiya sai Najeeba da uwarta, wayarta ta warto tana sintiri tana tunanin me ya dace ta yi? Wa ya kamata ta yi kira? Ko dai shawarar bin bokayen take dauka ta fara ne? Domin kuwa a da ta yiwa kanta alkawarin ba ita ba harkar boka ba dan komai ba sai dan ta kawo rantsuwa ta gita kamar yanda Najeeba ta ce da ita ba boka ba malan zata yo andani da lamarinta na mace ta zartar da hukunci ta hanyar haramta mata soyaya da saurayinta, itama ta kawo rantsuwar ba boka ba malan ita kuwa sai ta auro ubanta kuma sai ta hanna mata kwonciyar hankali karshe sai ta yi sanadiyar da ubanta ya kore ta! ,
Sai dai kash, a yau sai ta fara tunani cikin daya biyu.......anya kuwa zata iya ci gaba da gogaya da Najeeba da Uwarta ba tare da ta bi ta kasan kasa ba?

Wayarsa ce ta dauki kuka a hannun Nusaiba

Amsa ya yi ya kara a kunnensa, a tausashe ya amsa gaisuwarsa

Abih dake tsaye kofar dakin ya ce" Allah ya taimakeka, na shigo ne tanzun zamu gaisa da su Bilkissu, shine nace yau ko zaka fita fada ne? Zancen aminin nan nawa dake kwonce wanda nake maka bayanin matarsa ta tashi hankalinta bisa maganar da ta ji makocinsu na yi a waya tsakiyar dare wanda ya saka mata tsantsamta da saka hannunsa kan rashin lafiar mijinta, shine na ce ina so da kanka ka yi shara'ar nan, walahi ciwo gaba yake ya ki ci yaki cinyewa gashi asibiti basu ga komai ba, ana ta na hausa wannan ya ce matabiya ce, wancen ya ce jifa ne, kai dai ka san lamuran kwashe kwashen mutanenmu, shine nace dan Allah a shigar mana lamarin nan"

SHAHEED ya dan gyada kansa, a hankali ya ce" ABIH yau ba zan fita fada ba, ama ka saka a fada masu gobe in sha Allah mu yi zaman karfe tara a cikin gida "

Godiya Abih ke ta yi har ya sanyo kansa falon, sai kuma ya dan yi turus da mamakin Gannin wai da gaske SHAHEED din ne yake ganni a zaune tsakanin UMMU da BILKISSU ba RAWANI??

Murmushi ne ya fadada a fuskarsa kafin ya karaso shima yana kara kallonsa da kallo mai nuni da yannayin farin cikin da ya tsinci kansa a ciki ya mika masa hannu suka gaisa kafin ya samu waje ya zauna yaran du suka shiga dane shi sunna gaishe shi da murna da ihun fadin ABIH ne ABIH ne

Wannan abin shi ya saka Mardiya zabura ta ajiye wayar da suke da kanwarta fitinaniya wace a yanzu haka ta kai wajen da bama a gida take ba ta tafiarta Maradi wajen wani Alhajinta da ya kama mata gida, sam bata ji yarinyar ko a lokacin da mahaifinsu nada rai, da adu'a kawai yake binta , a yanzu da kasa ta birni idannuwansa sai da ta yi bikin bayana cewar ta zama rikakiyar yar bariki sannan ta faso gari da lasisinta take fantamawarta hankali kwonce

Da sauro ta warto hijab dinta maroon ta saka ta bude kofar ta fito

Daidai ta kusa karasowa UMMU ta ajiye masa ruwan da ta zuba masa a cikin copin glass mai dan tsayi mai sanyi ta koma wajenta ta zauna duda tunda ya zo ba wani magana da ta hada su daga gaisuwa sai ruwan da ta dauko masa ta ajiye masa

Du irin yanda Sultan ya cika wajen bai hanna Mardiya karasawa ta dauke kofin ruwan ta je saman table ta ajiye a ranta kuwa fadi take 'karya ne walahi , ba zaki zauna kina gwada min bariki a wajen da mijina yake ba '

Tana dawowa ba ko dar sai ta samu waje dan kusa da Abih kadan ta zauna, ita bata gaishe shi ba, ita bata bar wajen ba, sai binsa take da kallo , sai kawai take ga kamar wanda ya cencara kwaliya domin ya sha sabuwar shada ne ya hade abin dai ba'a cewa komai, hakan ya sa ko dan datijantakar tasa ke son boyewa sai yan tsirakun furfurar dake jikin gemunsa dake iya shaidawa da ya dan kwana biyu da kuma fuska irin ta baba daban take da ta yaro

Sai da ya ajiye wayarsa ya dan matso da zamansa ya hade hannayensa biyu ya dora gwuiwoyin hannayen nasa saman rigar shadarsa da ya dan ja baya kadan yanna kallon Abih, muryarsa a dake kadan tamkar ba sirikinsa ba, ya dauko muryarsa da yake magana da ita a kausashe a wajen shara'a ya ce" *Meye anfanin zaman iyalinka a gidan nan bayan ba wata sabga ake ba ABIH?*

ABIH ya kale shi, sai ya maida dubansa kan Mardiya da sai da ajiyar zuciya ta kwace mata jin abinda SHAHEED ya fada, dama hanya take nema ido rufe dan haka ta samu nauyin da zuciyarta ta yi mata ta fara ragewa

Abih ya maida dubansa kan SHAHEED, a hankali ya ce" gata ai SHAHEED ka tambayeta"
Chapter 97 · 0% Book details