← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 138

Sashe 50

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A saman gashinta ta totse abin caje kan, sannan abin tsagawar daya a kan matar daya kuwa a cikin gashinta domin gashin nata hade shi ne ta yi ta kame shi a sama

Hira suke da Nadia tana yar daria
NADIA ta ce" NAJEEBA, ni da yau na maki abinda bakya so, Najeeba Huzaifa ya matsa min walahi, kin ga ko yau da sasafe shi ya tasheni a baci ya rantse cewar ba zai iya hakuri ba
Najeeba meye laifin Huzaifa ne? Idan kudin ne ke kin san waye HUZAIFA a damagaram, yaro ne mai kudin balaki
Idan kyan ne meye laifinsa?
Gashi baki ne kamar yanda kike so mijinki ya kasance me ya sa ba zaki amsa shi ba? Shi fa a shirye yake da yau kika ce ya fito zai fito

Tsaga wani kitson ta yi ta dauka sannan ta dubeta ta ce" numberna kika bashi hajia ko me kika min?

Nadia ta dan kebe bakinta ta ce" walahi na bashi numberki, na fada masa inda kike bi, na fada masa harda da food din dake birke ki

Najeeba ta ringa gyada kanta tana idasa kitse jelar kitson matar, domin har karshe take kitse mata shi ya kwonta yar yar da shi shi yasa matar ke masifar son ta zo saloon din, bata barinsa sai an yanyara mata kitso da kunshi an wanke mata kafarta sannan ta sayi dadadan turarukansu masu birge mijinta ainun

Najeeba ta ce" kin san meye, ya cika daria wa kowa ne,
Nadia ina son namiji mai wasa da yawan yin daria aman fa ni kadai nake so ya ringa washewa hakora ba kowace mace ba haka kawai

Kwonkwasa wajen da ake ne ya sakata kai dubanta kofar

Gabza gabzan dogarai har biyun da aka hadata da su ne suka tarewa wanda ake maganarsa hanya

Saurayi ne jikake, ya jiku har ya jike da cefa ga iya kwaliya
Yana da kyakyawan nasaba, gashi da fara'a
HUZAIFA dan kasuwa ne sannan yana karatunsa wanda ya fi baiwa kasuwancinsa karfi domin karatun mamansa ce ke matsa masa aman ya malaki abubuwan rayuwar da ba shi ba ko wani masa ya huta

A duniyarsa yana son mace mai irin halayen Najeeba,
Ya santa ne dalilin cousine dinsa Nadia,
NAJEEBA na kashe shi, shagwabarta na haukata shi, idannuwanta na tsuma shi, uwa uba tafkeke kugunta mai kara masa yardar cewa yes shi namiji ne sakamakon idan ya ganta yakan rasa nutsuwarsa ke kara haukata shi da son malakarta ta kasance tasa
Yakan je wajen da take buga basket ball ya zauna a motarsa yana hangen yanda take wasanta ransa na tafarfasa da kishin mazan wajen
Yakan sakin murmushi idan ya ji wajen manya manyan maza irin ana hirar yan mata an yi katari wani ya sako zancen babyn
Irin yanda take wawusar aljihu na kashe shi hakan ya saka yake so ta shigo nasa aljihun domin yana kara kaimin nemansa dan ya bude mata bakin aljihun nan ta shiga ta yi burgima ta yi jina jina ta wanke kafa ta fito

Sai dai abinda ke damunsa ta kasa bashi dama

Ta raina shekarunsa, ta kuma raina yannayinsa
Ya kwatanta tashi daya amsar da ta bashi shi je" murmushin sangarta kafin ta dora da fadin" aman tsokanana kake ko? Ka dai san koda ka girme min bai fi da shekara biyu ba, gaka mai arhar daria a kowa, yaya kake so na maka wayo ka hada ni da hukuma??????

Happy weekend people💓🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

28

Bata motsa daga yanda take ba tana dai kitson tana kallon yanda yake iya yinsa dan gannin sun barshi ya shigo wajen

Kasancewar saloon dinta, sun kwana da sannin maza kan shiga ya saka ba wace ta wani damu dan sun hangi namiji na son shigowa domin akoy mazan dake zuwa takanas a yi masu manyan kitson nan na irin samarin nan na zamani
Wasun kuwa sukan rako yan matansu ne wasu kuwa su kawo matayensu

Nadia ta mike tana daukan dan kwalinta ta ce" a gaskiya wannan sabon tsari na tare mutun a waje ba zai haifa mana d'a da ido ba, ni banma san a kan wani dalili zaki yarda da irin lamarin nan ke da bakya so

Ita dai bata ce komai ba sai dan sauran gashin da ya yi saura take son idasa kitsewa

Fita ta yi ta shiga kokarin gannin an barshi ya shigo, sai dai dogarin nan na buda baki ya ce da ita" MAI MARTABA YA FADA MANA CEWAR BA WAJEN SHIGAR MAZA BANE DAN HAKA BA ZAI SHIGA NAN BA

Da mamaki ta koma ba tare da ta yi gardama ba jin ashe mai martaba ne ya saka dokar hakan a kan kannensa?

Najeeba bata ce da ita komai ba bayan ta shaida mata, sai da ta gama kitson nan sannan matar na murnar an gama mata ta cire jika ashirin ta mikawa Najeebar tana ta godiya kudin kunshi ne da kitso da gyaran faratuna da gashin ido tamkar wace aka yiwa kyauta

Itama Najeebar cike da fara'a sukai salama matar ta tafi

Gurin da take wanke hannaye ta je ta wanke hannayenta tas tas tana murmushin jin darun wata budurwa dake fadin ita gaskiya ita zata yi mata gyaran gashinta idan ya bushe yarenta kuwa sunna fadin ba kananun aiki take yi ba, zasu iya yi mata ko wani kala take so domin ta koya masu kuma sun kware sosai
Sai dai ta kiya ta ce ko nawa ne zata biya ita dai NAjeebar take so ta yi mata

Hijab dinta mai ruwan ash color ta saka mai hannaye sannan ta kara fesa turare ta juya ta fita daga shagon kafarta sanye da takalmi mai ruwan hijab din aman kafa ciki ne mai dan tsini a kasansa

Tana fitowa suka shiga bun bayanta hakan ya sa da mamaki ta dakata ta juyo tana kallon su
Du kawunansu a kasa a lokacin da ta juyo sannan sunna fadin" Allah ya ja da ranki, Allah ya huci zuciyarki

Bata iya basu amsa ba sai karasawa da ta inda ya kafeta da ido kamar ya dauketa da idannuwansa yana kallonta fuskarsa dauke da wani irin murmushi mai girman gaske

Tana isawa ta dan harde hannayenta tana kallonsa
A sanyaye ta ce" menene?

Murmushi ya yi yana shafa kansa daga gaba zuwa baya, a hankali shima ya furta" kauna ce, dan Allah ki bani dama

Motar da ya zo da ita ta kalla, motar nan zata yi kudin hudun tata gata baka sidik mai shegen kyan tsiya

Bakinta ta dan tabe kafin ta ce da shi" mu je

Tare suka juyi suka nufi cikin saloon din

Da sauri baban dogarin ya ce" Allah ya taimake ki, an hanna maza shiga ciki

Dakatawa ta yi ta juyo tana jin uwa ta ce da shi da ubanwa suka yi tarayar siyan wajen da har zai ringa shiga sabgar da ba tasa ba? Sai dai kasancewar kwakwaran gargadin da ta samu daga wajen Anmy a lokacin da ta nuna ba wanda zai bita ya saka ta cire dubanta daga kansa ta furta" harda mijin da zan aura?

Da sauri ya girgiza kai yana bashi hanya, shi kuwa wani mahaukacin dadi ya saka shi saurin cin mata suka jera suka shige saloon din tare

Sunna shiga sanyin Ac din dake busa saloon din ya dake shi, kanshin turaran wuta fa kuma tarin turarukansu na siyarwa dake cikin wani katon waje mai dauke da madubai ya hade ya saka shagon zama cikin wani kamshi unik da sansanyan sanyi

Juyowa ta yi tana kallonsa a hankali ta ce" ina fatan baka dauki maganar da na fada da mahinmanci ba domin dan ka samu shigowa na fadeta

Matsota ya yi yana kallonta kafin ya furta" zan tabatar da ita ne, domin ba wanda ya cencenci amsa kiran sunnan mijin princss sai ni

Irin yanda ya yi maganar ya sakata dan juya idannuwanta sannan ta idasa shiga tana mai cire hijab dinta dan itafa idan tana ciki tana aiki gaskiya bata saka komai a kanta

Waje ya samu ya zauna kusa da Nadia saman kayataciyar kujerar zaman mutun hudu kafin ya shiga binta da kallo

Budurwar nan ce ta hau saman kujera Nan NAJEEBA ta karasa ta shiga ciro atash din da za'a saka mata a boye cikin gashin kanta ya zama tamkar gashinta
Sak sak irin gashinta ta ciro maroon mai duhu sosai, sannan yannayin santsintama ya zama irin na gashin matar
Col (gam, wannan abin dai mai danne atach din )
Ta fitar sabo ta ajiye

Sai da ta kara busar da gashin sosai sannan ta shiga fitar da wadatacen da zai boye atach din baki daya zagayen kan budurwar

Cikin nutsuwa ta warware atach din nan ta wari daidai misali ta tsaga wanda zata hadewa ta hade sauran ta soke da yar wukar kitson sannan ta shiga shafa col din nan a jikin atach din
Sai da ta shafa ta dan hura da bakinta ya dan sha iska sannan ta daidaita ta dora shi gaba kadan da tsagar sannan daidai tsiron gashin kafin ta hade da gashin cen kasa ya kasance ya zauna das da shi ta kuma tsaga wani
Nan da nan ta idasa sakawa shi kuwa ya wani irin kura mata ido tamkar zai cinyeta yar uwarsa tun tana masa magana har ta yi shiru ta rafka tagumi ta zubawa sarautar Allah ido

Wanda ta ware din nan ta kunce ta hade su , mai ta lakato ta shafa sama sama dan col din baya son mai sannan ta saka abin cajewa ta ringa caje gashin har ya hade da atack din ya hade sosai da sosai kafin ta dago daga bayan matar hakan ya kasance ta baiwa su Nadia baya kennan

Da sauri ya koma saman kujerar yana daga hannayensa ya dora saman kansa ya kara zubawa kugunta ido kafin ya cire dubansa da sauri a fili ya furta" takwarankwatsa sonta nake kuma sai na aureta
Chapter 50 · 0% Book details