← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 138

Sashe 103

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan salar isha, GIMBIYAR garin Agadez ce zaune da waya kage a kunnenta tana sauraron kalaman kamilin mijinta, a sanyaye yake maganar sai dai abinda ke neman kasheta shine irin kashedin da ya yi da irin alwashin da ya ci a kanta, bata gama farfadowa ba ya dora da fadin" ban san yaushe zaki yi hankali ba, abinda na sani shi ne ni ba tsohon banza bane, na zuba maki ido na zata zaki yi tunani? Sai na ga kin kara bani mamaki a karo na ba adadi a lokacin da kika tare a gidan sirikinki da sunnan kina jinya, shin ina iyayensa? Ina yan uwansa? Ko ba su shi kansa bai isa ya kula da matarsa ba? Ki sani na san me ke damunku ku duka, daga ke har Zinaria idan baku farka ba zan saka maku hukunci mai tsananin da zai firgita du wani mai kaunarku, idan a gobe baki biyo jirgin da zai fito daga garin Niamey ya yo damagaram daga nan ya yo Agadez ba komai na iya faruwa da mulkinki, idan nace maki komai ina nufin komai!"

Kitt ya kashe kiran da ya sakata zabura har hannayenta na rawa tana kallon screen din tanfatsetsiyar wayarta
Ta kasa yarda cewar shi ne, yau ita ce mai martaba ya yiwa magana a haka? Ita ce ya yiwa fada a haka? Sosai kanta ya dauki hayaki ta cika ta batse, ina ai dole ta je ta ganshi gashi ga ita ya maimaita magangannun nan, zata je kuwa ko dan ta gani da idannuwanta abinda ke shirin samunta ita kanta, me hakan ke nufi? Shin yarinyar nan bayan yarta har ita sun gama da ita ko meye?

Da sauri ta mike ta yi dakin Zinaria dake kwonce har ta fara baci bayan ko salar isha bata yi ba wai ta gaji dan kawai an mata wankin kafa bama ita ta yi da kanta ba gannin tana baci ya sakata fitowa ta shiga kiran number babar yarta, ina ba zai yiwu ba, walahi ba'a yi su ba!

....... . . .. . ...........................

Tarin gajiyar da ya dawo da ita a yau ta hanna masa tunanin komai, yana gama dukan abinda ya zame masa jiki, ya gama waya da lauyan da ya dora kan binciken abubuwan da suka tsaye masa a rai, domin shi dai ba lauya bane, irin halin tsantsamtun da ya shiga ya hanna masa fita neman bayanan da kansa, domin a yanzun fitarsa sai idan ta zamo dole ne, ya daina fitar daren da yake ya dakatar har komai ya warware masa

Yana gamawa bayan ya gama nafilarsa sai kawai ya nemi waje ya kwonta dan samun hutu,
Sosai shara'ar da ya yi a yau ta caza masa kwakwaluwa, ya hadu da mutane ne masu matukar taurin kai dan kuwa du yanda ya so a gama shara'ar cikin masalaha da junna sai da suka saka shi mikewa da kansa ya kawo kur'anin da sam baya son yawan saka shi a garinsa ya ajiye a gabansu kan su rantse domin mutun ne kwonce ba ta yada yake, sai bin mutane da ido, bayaj a da shi din shi ake so da gani sai gashi a yanzu komai sai an masa, ga mata ga y'aya, rayuwa dai tai masu zafi sai hamdallah....cikin fadawa Allahn da ake ne matarsa ta tashi tsakiyar dare dan dauro alwallah sai ta ga babu ruwa baya zuwa, niyarta ta zagaya baya dan samun ruwan a butar makiciyarta, sai dai a nan ne ta ringa jin magangannunsa kan lalurar mijinta
Sosai aka yi rigima domin Abih kansa ya ja ya tsaya kan sai sun fadi komai idan kuwa ba haka ba kur'ani ya ci su

Ajiyar zuciya ya shiga saukewa a hankali wanda ke nuni da ya samu baci kennan

(Asuba ta gari SULTAN)

a yau ne ya kama ranar da iyayenta sukai mata alkawarin zata koma bakin aikinta zata je ta fara gabatar da aikin da ta fi kwarewa a shi wato harkar saloon

Shiri ta yi na mamaki, domin ta sha wata rantsatsiyar shada ne doguwar riga sannan da kanta ta aminta ta dora alkyabar nan dan ta san ba za'a bata lafia ta yi tafiaarta haka ba

Daurin da ya fi fitar da sirrin kyanta ta kafa a saman kanta simple sai jelar gashinta dake dan yawo a gadon bayanta wanda ta saka masa biboudi sai nanadewa yake a gadon bayan nata masha Allah
Takalmi ta kafa mai dan tsini, sannan kafa ciki bayan ta saka safa suka yada zango a falo sunna jiran yaya DAYABU su karasa wajen sannan daga cen su yi salama da Zahrau wace ta sha wani irin rantsatsen mak'up itama sai kyali take daidai da kalar fatar jikinta

Yana zuwa cikin shigarsa ta Gizner ya gaisar da iyayensa sannan suka tashi dan karasawa bayan sun yi masu adu'a

Cike da nutsuwa suke tafia, hakan ya sa du hankali ya yi kansu
Du inda suka zo sai an duka an kawo masu gaisuwa, sannan kowa so yake ya bambance wacece amaryar sarkinsu? Aman a yau sun kasa bambancewa dan irin kamar da y'ayan Abih suke, gashi sun saka Alkyaba ne su dukansu, haka kuma tafiarsu cikin tsari

Yaya Dayabu ne ya hango tarin takalma a kofar wajen hakan ya saka shi dan zaro idannuwansa ya ce" ke NAJEEBA hala mutanen nan du sunna cikin wajen cen?"

Najeeba dake sakin murmushi gannin irin yanda aka kawata wajen ta ce" yaya, sunna ciki, to aman bana gannin abubuwan hawansu fa?"

Yaya DAYABU ya ce" ai a kofar shigowa aka umarcesu ajiyewa, akoy dogarai dake baiwa abin hawan mutane tsaro, kema yaya za'a yi kowama ya shigo gidan nan da mota sai kace wani karamin gida?"

Murmushi ta kuma yi, lokaci daya droon din SULTAN ya ringa yawo a wajen, du kawunansu suka daga suka bi shi da kallo, haka kawai ta ji a jikinta kamar ana kallonsu ne, sai dai gannin yan uwanta basu damu ba sai itama bata damun ba

Karshe dai yaya Dayabu kasa shiga ya yi domin tun daga waje zaka gane fa yau sun hadu, mata ne birjik a wajen baba da babarta

Ita kanta ta yi mamakin wasu fuskokin mutanen da ta gani a wajen nan, ba dan komai ba sai dan da yawansu irinnan san junnan nan ne aman gaisuwa kawai ke hadawa, da yawansu irin sunna yiwa mutun kallon sun fi karfinsan nan ne, ciki kuwa harda matar ambasador da ta rangada guda lokaci daya tana fadin" gata fa ta shigo, Allah ya yi mana maganinta, Allah mun gode maka, yanzun kam sai dai a je a karata da Zinaria, Zinaria kuwa ta ci dubu sai ceto, zamu ga wa zai fadi a wasan"

Da mamaki Zahrau ke kallonta gannin irin yanda wajen ya bada kala daban daban, a ranta ta furta 'To fah, kar dai a dora daga inda aka tsata'

NAJEEBA na murmushi tana kara bin kowa da kallo, masu tafe dan taya murna ta gane haka kuma masu son ganewa idannuwansu komai a bayane yake dan haka sai ta cire alkyabar dake kanta, baki daya ta idasa cirera a jikinta hakan ya sa Hadimarta da sauri ta amsa ta yi dakin da aka ware dan hutunta ta kilace ta fito tana risinawa da tambayarta inda zata fara zaunawa dan hutawa

Murmushi ta yi mata bata ce da ita komai ba, ta shiga bin bakinta daya bayan daya tana gaisawa da su tanai masu lalle marhabin

Bayan ta gama ta umarci su Aida kan su bubude kayan aiki a fara aiki, aman aikin yau ba za'a amshi kudin kowa ba, sai dai zuwa gaba

Ai kuwa wajen ya idasa rikicewa da murna da gudar mata

Sai a lokacin ta ga Habu dan daudu, sai da ta zaro ido dan mamakin yaushe ya shigo,
Idannuwansa ya yiwa far far ya tafa hannu ya ce" ci ubansu kawata, takawarki lafia mata a wajen mai damagaram, karya ne a tankawa uwar dakina na kyale ko a gaban dubu sai nai motsi sai dai a dinken baki, kin san wanda ya gama tsorata da maciji ko igiya ya gani firgita yake, kin jijiga matan gwamnoni, kin tarwatsa zuciyar dakakiyar macen da take gannin ita mace ce, kin zaburar da yan mata, kin watsa kannanun kwari kin mike kin mana raf da wuyan MAI DAMAGARAM uban gidan ZINARIA, tabas ke din sai sarauta, domin manyan kaya kike janye da su da mai tuka su sai OGA, sitiyarin kan motarki ba kowani hannu zai iya juya shi ba, dole ki firgita mana fara mai takama da hakan, da Allah muka dogara ba da uban wani ba, mun tabara mun sha yasin mun motsa da adu'ar iyaye dan alkur'ani makiyanmu fadawanmu"

Ihun aka kuma sakawa hakan ya bata ran wa'inda akaiwa habaicin, ciki kuwa harda matar doctor wace itaka ta zo tataki ne yau dan ta ga wannan NAJEEBAR sannan ta san Habu farin sani ta ce" kai Habu habaici kake mana ne?"

Habu ya kuma juya ido ya ce" kar ki ce min kin ji kamar da ke nake?"

Zahrau ta girgiza kai tana kallon yanda wajen yake, ita ta rantse da Allah har a cikin zuciyarta baki daya ta tsorata, aman cikin ikon Allah NAJEEBA a tsaye take hannayenta sake fuskarta bata nuna alamun mamaki ko tsoro saima bin kowa da take da kallo daya bayan daya, ko shewar nan da ake du masu yi tana bin su da kallo, ga uban jus jus da ake rarabawa inda su Ummu ne suka ja ragamar rabe raben da sauransu,

A sanyaye ZAHRAU ta ce" ni dai dan Allah a bar wannan abubuwan haka, wai shin kaima kitson ka zo ne?"
Chapter 103 · 0% Book details