Sashe 113
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da zafi zafi AMMI ta ce" wato har yanzu baki ga ilar tarbiyarki da mashawarantarki da son zuciyarki ba har kike furta kalaman nan? Wato har yanzu baki gane alfarmar kin amsa kiran sunnan matarsa ya saka ba'a saka maki ankwa an fita da ke a gaban talakawanki ba? Wato har yanzu baki gane kina cikin matsala mai girman gaske dan kuwa ke kanki baki san irin abinda yake bakin ko na menene ba har sai sun gama bincikensu a kanki sun gano irin girman laifinki shin ya cencenta a barki a hora ki a sirri ko kuwa dole a fitar da sirrin ba? Ke baki gane cewar alfarmar mahaifinki kika ci ba?, Baki gane cewar a yau, a yanzu ke din nan ba kowa bace sai sakaryar macen da ta kasa yin hakatacen kishi ta tafka kuskure wa rayuwarta ta wulakanta kanta ba? Baki ji daga bakin wanda kika yi mugun abun dan ki malake shi naki ke kadai din kin cenza sunna daga ZINARIA zuwa Zulaihat ba?, kaicon ki ZULAIHAT, kaicon ki, ke kau kin shiga uku, ki rasa wanda zaki ci amana sai mijinki?, kishi ai ba hauka bane ZULAIHAT! Ke yau koda an samo gaskiyar lamarin cewa babu hannunki a maganar kisan nan kina tunanin SHAHEED zai sauko da wuri wuri ya dube ki ne? Zaki samu irin darajar da ya baki a da ta kasancewarki matar da ya fara aura, wace ya fara haihuwa da ita ne? Zaki yi asara ta yardar da mijinki ya baki, zaki yi asara ta irin gannin girmanki da kimarki da yake, zaki gani a aikace ke din ba wanda kika fi, zaki fahimci halayanka sune limamin dake jan ragamar rayuwar da zaka iya fuskanta da mutane tun a nan gidan duniya! Kin san kina son sa kika yarda aka aura maki SULTAN? Inace y'ayan zamani akoy gungiyar dake kare hakin ku, koda kuwa mahaifinki ne sai su hanna shi yi maki auren dole, ita mahaifiyar take da ta kasance babar banza ta isa ta hanna kanta zama da kishiyar ne? Yaya bata iya hanna komai da nata rayuwar gidan mijin ke kike gannin ta isar maki? Dan ta haife ki shikenan komai halayanta sai aka ce ki yi mata biyaya? Ke din sakarai ce da baki san abinda ya dace da rayuwarki bayan haihuwa guda da bari uku da yanzu y'ayanki hudu a gidan nan, da a gabansu zaki amshi hukuncin cin amana wa abihnsu? Yaya zaku yi auren gidan sarauta ku yi tunanin zaku kasance ku kadai jal?, ke a zamanin nan ko talakan da bashi da ko sisi ya samu damar jera mata hudu jera sun zai abinsa koda kuwa bashi da abinda zai ciyar da su ne, bale wanda Allah ya horewa? ke da kina da hankali, ko da kina tare da magaya masu nazari da sun nusar da ke cewar idan akoy mai dama a wajen mijinku ke ce, ke kika fi kowa sanninsa kafin wata, ke ce mai dauke da lakanin da zaki iya zuwa kai tsaye gare shi kafin wata, ke din nan da kin koya masa yanda a duniya koda ya so wata fiye da ke to fa tsananin girmanki, darajarki, kauna ta zaman tare zai hanna masa wulakanta ki, an fada maki matar farko abin wasa ce a zuciyar mijinta? Idan kin ga namiji yana abun kirkin da a da ba haka yake ba sai bayan aurensa tabata harda gudunmuwar matarsa, idan aka ce lalacewa halayansa suka yi tabata wace ta ja hakan ita ne, menene burinki? *MULKI, ARZIKI, KI KADAICE SHI IYA KE* dan kar KAWAYE SU ZAGE KI, ko a gazawarki? Sai gashi ina mai cike da tsoron kar a je kin rasa komai.......AMMI ta karashe tana mai share hawayenta sosai
Dubanta ta mayar wajen mahaifiyar Nadia da Nadiar kanta dake zaune kawunnansu a kasa ta ce " Ku yi hakuri, a yanzu ba zai iya bayar da hakuri ba, ku tashi a raka ku bangarenta ta huta "
Da sauri Nadia ta ringa girgiza kanta, a tsorace ta ce" AMMI, dan Allah aa, akoy maciji a cen "
AMMI ta dam sauke ajiyar zuciya ta ce " to ku tashi ku je bangarena, nima gani nan zuwa "
Ai kuwa mikewar suka yi ita ta yima mamanta jagora hanyar bangaren AMMI suka bi suka shige
Dubanta ta kai wajen UMMU a sanyaye ta ce" idan yaya ya dawo zamu yi shawara da shi kan maganar wannan ware waren turakar, bana jin zan iya kuma barin hakan ta faru"
Ita dai kai ta gyada kawai, domin baki daya jikinta ba karfi, harma mamakin irin karfin zuciyar AMMI din take, duda takan share hawaye lokaci zuwa lokaci aman sai kokarin gannin ta daidaita komai take
Wayarta ta ajiye, tana kara taba jikin NAJEEBA
Cen sai ga tsohuwar JAKADIYAR dake kula da kebantacen wajen da ake kebe ahalain gidan da wani abin ya ritsa da su
Sosai ZINARIA ta fashe da wani irin kuka tamkar zata side a lokacin da suka kamata suka mikar da ita
A kausashe Jakadiyar ta furta" Hatara dai Zulaihat, sasauta muryarki a falon mai damagaram kike "
Ai kuwa ta yi kitttt tana ji tana ganni suka fice da ita duda an bi ta sirri da ita aman ina ta tabata wannan magana har ta gama yada fada, ita kam ina zata saka ranta? Ina zata tsoma ranta? A irin yanda take da wulakanci, yanda ta dauki masu yi mata hidima da sauransu tamkar wasu bayinta, sam ba maganar mutuntawa sai tarin wulakanci da tozarci, dan ta tofa maka yawu ta kireka dan talakawa bawanta ba wani abu bane, dan ta saka a yi maka bulaka ba wani abu bane, tana jin dadi idan tana wulakanci, takan ji kwonciyar hankali da nutsuwa a zuciyarta idan tana wulakanci, a ganninta wannan shi ne bambancinta da sauran, wannan shi ne bambancinta da talaka, sai gashi yau zata je kebantacen wuri, wajen da ba rasa ci, sha , sutura zaka yi ba, bambancin shine bata da wata alfarma a wajen sarki, bata da damar ganawa da shi, bata da damar dora doka ko taka wani, tana da yan hidima sai dai bata da damar wulakanta su domin inci ne da su, suma sunna wajem da suke fada a ji ne, zata je duniyar mahidimta ne, wajen da suke nasu sarauta ne, y'aya da jikoki ne, bata da damar sakawa ko hannawa sai abinda hali ya bada ne, hakan ya matukar razanata, ya hanna mata sukuni har aka karasa da ita fadi take a bata wata
Basu hanna mata ba, suka bata wayar , nan da nan ta yi kiran mahaifiyarta ta shaida mata wannan labari da ya kusan saka maman nata jin zuciyarta zata tsaya
Itama hankali tashe ta nemi gannin sarki a kusancin magaribar nan wanda a yau bangaren Zahrau yake, sai dai amsar da aka bata cewar ba zata samu ganninsa ba ya sakata yin zaman yan bori, a nan kasa inda kuyanginta suka rikice harda yar kazaginta wace ta fece da gudu bangaren Yarima dan kai masa labarin halin da mahaifiyarsa ke ciki
Wannan kennan
Sai da AMMI ta ja numfashi ya fi a irga sannan ta kara shafa kan NAJEEBA a hankali ta ce" tashi Najeebana "
Da taimakonta da na UMMU ta mike tsaye
Ammi ta kama hannunta da niyar tafia da ita bangarenta , duda ba haka take so a kasan zuciyarta ba sai dai gannin kamar NAJEEBAR nada bukatar taimako sai ta kasa barinta a nan din
A hankali UMMU ta ce" AMMI, me zai hanna ita a barta a nan? Mai yiwuwa ta taimaka masa da wani abin?"
Sai da ajiyar zuciya ta kwacewa Ammi, aman sai ta kada furta komai ta ja ta tsaya tana kallon yannayin NAJEEBAR
Gannin kanta a kasa tana ta wasa da yar yatsarta sai AMMI ta lumshe idannuwanta ta juya a hankali ta yi gagawar kama hanyar tafia, kwarai tana son ya samu kadaicewa da mace koda kuwa ba abinda zai shiga tsakaninsa da ita, koda kuwa ba zai yi maganar abinda ke damunsa ba, koda kuwa ba zai kulata ba, tana son wani ya kasance a kusa da shi, shima fa mutun ne, mai rauni, mai tare da damuwa, mai son idan yana cikin damuwa ya samu mai taya shi, mai bashi shawara, mai nutsar da zuciyarsa
UMMU ta kama hannun nata da take wasa da shi, a sanyaye ta ce" ki shiga ruwa masu zafi ki jima a ciki sosai, sannan ki sha ibuprofen"
NAJEEBA ta dan gyada kanta tana hadiyar yawu masu zafi a makogwaronta cike da yannayin damuwa
UMMU ta dago habarta a sanyaye ta ce" my BEEBA? "
Najeeba ta kaleta jin wani sunna da ta fada
Ummu ta yi dan murmushi ta ce" SHAHEED ne yake ce maki MY BEEBA, a lokacin da ake kawo ki wuni wajen AMMI din ki "
Da mamaki a fuskarta, muryarta a sanyaye ta ce" Dama yana min magana ina karama? "
Murmushi UMMU ta yi ta ce" yana son yara kananu, burinsa AMMI ta haifa masa kani shima, ganninki a wajenta sai ya samu abin nishadi idan ya baro fada da wajen horo da hawa doki, yakan yada zango a bangaren da aka zuba maki kayan wasa da masu kula da ke, sukan bara maku wajen shi kuwa ya ringa saka ki tatata kamar yanda kike tafiarki a hankali sai ya ce *ZO NAN MY BEEBA* , tun baki iya sunnansa ba, irin yanda yake zuwa da ke wajen mai martaba shi kuwa yana kama sunnansa ne kai tsaye har kika iya da maganar yara sai ki ce " JAHITT, wai SHAHEED "
Wani murmushi ne ya dan subuce mata , sai kuma ta kalli UMMU ta ce" to me ya da daga baya ya tsane ni? Me ya sa daga baya na kasance babar makiyiyarsa? Kaf cikin yan uwana na dawo ni ya fi tsana? "
Ummu ta lumshe idannuwanta, a hankali ta ce" ni kaina ina son sani, ko zaki yi kokari ki samo mana amsar nan?"
.............hi............
[3/31, 11:36 PM] BAK'A CE: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
57