← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 138

Sashe 10

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunna zuwa gida tun a hanya ya yi waya cewar a kawo masu Burger adadin da ya san zasu koshi kafin ya karasa shiga da motar

Talabeta ya yi a jikinsa har suka karasa shiga cikin falonsu sai kara kwontawa take tana raki tana rigima shi kuwa sai sannu yake mata tamkar ya fashe da kuka

Sunna shiga hankalin yan uwanta dake zaune ga abinci da yawa sun kasa ci sakamakon jin shiru yayunsu uku basu dawo ba wato DAYABU, NAJEEBA, DA ZAHRAU

Gannin Najeeba langwabe tana kara sakin kukan tabara ya saka su tashi a firgice sunna rige rigen karasowa wajensu

Hankalinsu tashe suke tambayar me ya sameta, ahin ko accident ta yi? Ita kuwa sai kara lafewa take a saman kujera baba ta ki amsawa

Abincin da aka kawo ya kalla
Bakinsa ya tabe ya tambayi ummu kamar haka" ke ummu wa ya kawo abincin nan?

Sai da ta tabe bakinta itama ta ce" mai gidan ce ta kawo

Bai ce komai ba sai zama da ya yi ya shiga balo maganin Najeeba ya amshi ruwan da Bilkissu ta dauko ya bale ya mika mata

Fuskarta ta yiwa takwaf takwaf hakan ya saka shi fadin" Najee, kin ga ki amshi magannin nan walahi idan kuwa ba haka ba zan dura maki shi katuwar banza kina yin amai kuma zan kara maki wani

Rauda ta ce" ya wai me ya sameta ne? Ko ciwon cikin ne? Na ga kuma ai ba karshen wata bane

Yayansu ya ce" a wajen basket aka daketa ta summa

Ido du suka zaro kafin karaminsu mai shekara bakwai ya bushe da daria ya ce" yaya an rama min dungure min kan da ta yi a school

Hararansa ta yi ta ce" NAJEEB zan wanka maka mari

Da tausayi kulsumu ta zauna gefenta tana dafa gefen wuyanta ta ce" wani dan iskan ne ya dakar min ke bayan ba'a dukan min kanwata

Langwabewa ta yi a jikinta ta saki shashekar kuka ta ce" bako ne, kuma walahi na daku baki ji yanda har yanzu nake juwa ba, ya kashe min kwayayen haihuwa

Khairy ta kai hannunta ta buge mata baki ta ce" shegiyar banza mai mugun fata, idan ya kashe maki kwayayen haihuwa ni ba sai na rike mar makogwaro ba?

Yayansu da ya shigo da manyan ledojin burger ya ajiye inda yaran suka fara tsale, sufa a dasha dan du idan manyan sukai fushi haka ake koda yaushe zasu ringa cin dadi ne, duda na gidansuma mai dadin ne aman kun san irin gashin nan na waje mai tonka akoy motsa kunne (aminiya kawar arziki maman jaririna ga kaza🤣🤣🤣)

Dubansa ya kai wajen magannin gannin bata sha ba ya saka shi yin wajen da sauri da niyar dauka ya dura matan

Sai dai bai kai ga karasawa ba Zahrau ta shigo da gudu tana kuka sama sama tamkar ranta zai fita

NAJEEBA dake langwabewa tana kamar ba zata iya tafia ba tana raki ita ta fara zabura ta yi wajenta hankali tashe

Baki daya suka zagayeta sunna tambayarta meye ita da, wa ya mutu, me aka yi take kuka?

Cikin wani irin kuka tamkar zata sike ta budi bakinta ta ce" *wai wai wai an fasa aurena*

Ta karsashe tana mai kife kanta a kirjin NAJEEBAR da ta fara karasowa sannan ta fi kusanci da ita a durkuahen da take

Shin kuna so? Idan kuna so ina comment ne mai nunan kuna bi? Free ne mutanena ku zagine mu je tare 😄😄😄😄😄
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

7

A hankali NAJEEBA ke shafa lallausan gashin yayar nata da dan kwalinta ya fadi sakamakon kukan da take shekawa

Du a firgice suke, aman sun rasa wace irin tambaya zasu yi mata

Hannunsa ya saka ya janyeta daga jikin NAJEEBA ya jata saman kujera ya zaunar da ita sannan ya shiga sintiri

Baki dayansu suka koma suka zazauna

Yar budurwar cikinsu mai shekaru goma sha biyu ta ce" shikenan yanzu anko din shada da lesh da komai din da akai mana an fasa auren?

Hararanta Bilkissu ta yi hakan ya sa ta yi shiru ta rafka tagumi cike da zulumin an fasa aure shikenan ba zasu yi sabga a gidansu ba

Hannayensa da yake hadewa yana kara budewa ya kuma hadewa ya ce" wani irin ya fasa aurenki? Wani abu kikai masa?

Tana kukan dai ta ce" aa, dazu ne da ya zo yake tambayana wai me ya kaimu gidan sarki ne? Sai nace masa ziyara
Shine ya ce min" Zahrau karya kike, ashe abinda momy ke fada min gaskiya ne? Ku dangin jaraba ne baku da aiki sai masifa da fada? A gaskiya zahrau ba zan iya auren macen da ta kai karar ubanta aka bashi laya ba, kuma a gaban mutane kanwarki ta mari matar ubanku maimakun ku horata sai kuka tare mata fada, to gaskiya wace kika shakar nan aminiyar momy ce kud da kud, da ita aka kawo kayanki ita ta je tana kuka ta zayanewa momy komai ashe ku dai dangin jaraba ne?

Ummulkhair ta zabura ta mike ta rike kugunta ta ce" mu ne dangin jarabar?

DAYABU ya harareta hakan ya sa ta koma ta zauna tana gunguni

ZAHRAU cikin sanyinta ta ce" nima nace da shi ya yi hakuri, abinda ya kai mu gidan sarki sirrin cikin gidanmu ne, kuma fadan nan da aka yi suna da yawa fa suka rufawa NAJEEBA ita kadai, ta yaya yake so na kyale ina kallo a dakar min kanwata?

Shine shine.....sai ta fashe da kuka tana kara dora kanta a kirjin NAJEEBA wace du ta manta ciwonta jikinta sai rawa yake dan walahi a duniya sun rayu da rayuwar jin ciwon dan uwansu a cikin jinnin jikinsu
Ana fadin maganar dan ubanci a duniya, su basu san da wannan kalmar ba
Sunna fada tsakaninsu fa, aman idan kana son ka ga hadin kai da tsantsar soyaya wani abu ya samu dayansu

DAYABU da hankalinsa ya kara kololuwar tashi ya ce" shi ne me?

Dagowa ta yi tana kallonsa ta ce" shine ya kara kiranmu da jarababu harma yake ikirarin ko Abanna zai bashi hakuri ba zai hakura ya iya zabawa y'ayansa uwa irina ba dan sam ban samu tarbiya ba bare na tarbiyantar da yaransa

Nima raina ya baci shi ne shi ne.....

Kara tsareta ya yi da ido ya ce" shine me ZAHRA?

Ta sada kanta kasa ta ce" shine nima nace masa mu ai du da sauki, shi da yake shege wanda uwarsa ta haifa ba aure bayansama ta haifi uku kannensa baki daya su ba'a zage su ba sai mune zai saka gaba yana ta zagi

Idannuwansa baki daya ya rurubo lokaci daya ya tafa hannayensa ya ce" MAHAMADU rasululahi salalahu alaihi wa salam

Da wani karfi karfi UMMULKHAIR ta ce" kin min daidai, ai walahi da kika kai karshe baki fada min ke kuwa me kika ce masa a kan irin zaginmu da ya saka ki a gaba yana yi ba da sai na dauke ki da mari walahi, dama sam bai min ba mutun ne sai shegen taurin hannu idan zai maki kyauta sai kaf danginsa sun sani

Namijin dake buga gem kuma yana kallonsu a wayar yayansu wato Najeeb ya ce" lalala, ba yaya ya hana karami yace zai daki baba ba?

Yayansu kam dake salalami dubanta ya yi ransa bace ya ce" sau nawa zan maku magana kan koda ranku ya baci ku ringa tauna magana kafin ku fadeta? Yaya zaki masa gori Zahra dan ya zage ki? Ke baki da bakin rama zagin da ya maki koma wani kala ne aman banda irin wannan gori? Shin shi ya saka mahaifiyarsa haihuwarsa haka ko me? Ko ke kina tunanin an maki albishiri din zaki gama da duniya lafiya ba tare da wata jarabawar da zaki ringa jin kunyar kanki ta same ki ba? Ina gannin kece mai hankalin cikinsu aman sai ki bani mamaki har haka? Na tabata da Najeeba ce da ake gannin ta fi ku rashin hakuri ba zata yi haka ba sai dai ta cire masa bakinsa dan gobe kar ya kuma

Sanyi ya yi gannin du sun zuba masa ido shi kuwa yana fada sama sama

Yatsarsa ya dago ya shiga nuna su daya bayan daya ya ce" ku yi kokarin gannin kun rufe naku sirrin,
Ku sanni, bana so, bana son ku kasance masu izgili da kuma son daga fitina a duniya
Domin kunada baban tabo
Kuna tare da baban tabon da mai tabon kansa bai san na san yanada tabon ba
Bana son abinda zai taba min nasabarku
Bana son a fara da haka a kanku cewa ana fasa aurenku
Bana so abin ya yi nisa

Wata iska mai zafi ya furzar yana kallonta ya ce " to in ba rashin hankali irin na dan fari a wajen uwa ba me ya kaiki buda baki ki yi wannan shirmen?

Ita dai kukanta ne ya tsaya a lokacin da yake bayannin suma sunnada sirri, tabo! Wannan kalmar sau uku kennan tana jinta daga bakinsa idan ta tsare shi sai ya nuna sam shi ba wani abu yake nufi ba yana nufin dai ita mace ce ya dace ta kasance mai taka tsantsan

Baki Najeeba ta tabe tana hade mata gashinta
Ta riga ta shaka, ta shaka iya wuya hakan ya sa ta kasa kida tofa ufan ne sai irin yanda take ayanna yanda zata yi da shi
Chapter 10 · 0% Book details