Sashe 6
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana kokarin saka farar rigarsa ta likitoci ya bata damar shigowa domin a tunaninsa nurse din da zata kawo masa liste din mutanen da zai duba ne yau
Kamshin turaranta ya saka shi juyowa da sauri
Lokaci daya fuslarsa ta fadada murmushi yana kallonta
Gannin fuskarta ba murmushi da alamun baci bacin rai ya saka shi saurin kara juyowa yana kallonta ya ce" oh angel, waye ya taba min ke da safe haka na ga fuskar ki a hade kamar wace aka batawa ko baki da lafia ne?
Jakar hannunta ta ajiye saman fararan takardun table din tana kara yatsina fuskarta ta ja dan kwalinta baya gashinta ya kara bayana ta sauke ajiyar zuciya ta kale shi
Sai da ta ja wata yar shasheka sai kawai hawaye ya shiga bin kuncinta
Lokaci daya ya rikice, ya bi ya daburce, ya kai hannunsa da niyar kama hannunta sau uku yana fasawa sannin da ya yi cewa a duniya ta tsani a taba jikinta, du irin yanda take da iya wankar samari kana yin wannan kokarin na kwatanta zaka tabata zaku bata , batawa kuwa wace ba zaku shirya ba
Kansa ya dafe yana jin zuciyarsa na bugawa, a duniya yana son yarinyar nan, idan kuwa ya ga ranta bace yakan fita a hayacinsa, bai san wani irin so ne yake mata mai tsanani haka ba, dalilinta ya sa ya daina fade fade a garin domin tana da kawaye kai bama maganar kawaye ba saloon dinta du wata mai ji da kanta a cen take gyaran kai ne, gyaran jiki ne, ko kunshi, ko mak up shi yasa ya nemi biye biyen matan da yake ya ajiye gefe, matarsa kanta yana kiyayewa kar ta san yanada aure domin shifa a kanta yana iya sakin matar tasa,
Baban burinsa ya sameta, ya cin mata ta aure ko ba aure, sai yana gannin abu ne mai wuya ba auren domin har yanzu baban abinda ya fi bashi mamaki a kanta du irin wayewarta da tarin shagwabarta ko soyayar shan minti ba'a yi da ita, mutane da yawa na mata muguwar fasara, shi dake tare da ita shi ya san wacece ita
Agogon hannunta ta dan kunce tana kallonsa ta ce" kudin jakana sun kare shine hankalina ya tashi domin yau ba zan bude saloon ba kai kuwa ka san inada kashin kudi shine na zo
Kabsa ya dafe cike da kulawa ya ce" Angel, kuma shine sai kin taso? Haba baby idan kika yi kirana ko ina ne sai na zo na kawo maki aman shine zaki taso har ki zubar min da tsadadun hawayenki?
Mikewa ya yi yana maganar ya dauko jakarsa ta laptop ya buda bayanta ya ciro kudi masu kauron gaske ya buda jakarta ya zuba mata
Catin Airtel ya ciro ya buda jakar nata ya kuma saka mata sannan ya dubeta ya ce" kin karya?
Idannuwanta ta juya masa cikin yannayi na lumshe su kafin ta dan cije lebenta na kasa ta kuma sake shi
Jin an kuma buga office din ya saka ta tashi ta dauki jakar nata ta sakar masa murmushin da ya saka saman kuncinta cen sama kamar kusan idannuwanta lotsawa kadan wanda hakan ke kashe masu begenta, ta kara yi masa wani warwar da idannuwanta sannan ta kuma gyara tsayuwarta ta ce" jarumina, ka kula da kanka, sai mun hadu
Bai iya amsawa ba sai wani irin sakai da ya yi da bakinsa ya rakata da kallo tamkar ya janyota ya maidota ya rukunkumeta a jikinsa yake ji har ta fice a office din
Wata wawuyar ajiyar zuciya ya saki a fili ya furta" dole na malaki babyn nan, tawa ce ta ni kadai!
Ita kuwa daga nanma direct shagonta ta nufa, wato saloon dinta
Motarta ta parker ta sauka bayan ta ciro gilas dinta pink coler mai yannayin heart ta dora ta dauki jakarta ta nufi cikin wajen da tun daga kofar take hangen da alama sunna da mutane sosai yau bayan ta hana a dauki mutane da yawa yau sakamakon amaryar da zata shirya
Tana shiga wajen ya dauki ihu, domin kawarta ce bahija da kuma Ramlat suka kawo mata ziyara, kai ziyarar tafe take da son jin abinda ake cicirawa a gari wai sun kai mahaifinsu kara gidan sarki
Itama da murna ta karasa wajensu ta zauna tana kallonsu
Sai da suka gaisa, masu aikinta suka kawo mata jus da ruwa, da sauri dayar ta je ciki dan gyara mata abin kari ita kuwa ta sakarwa Bahija murmushi ta ce" bahija ina zuwa bara na cenza kaya
Bahijarma murmushin ta sakar mata sannan ta dauki Iphone dinta ta danna kira
Shiga ciki ta yi ta cire abayar nata ta dauko wata doguwar riga marar nauyi ta saka mai dan gajeran hannu
Gashin kanta ta hade ta yi sama da shi ta saka masa dan karamin ribom ta daure shi hakan ya sa yake ta reto da cikarsa da kuma tsayinsa ga bakinsa
Tana fitowa gaban madubi ta je ta shiga bin aiyukan da akaiwa mutanen,
Biyu ne atach din da aka saka masu bai yi mata ba domin ya yi tudu da yawa dan haka ta sa a kunce ta shiga hada zare a jikin katuwar allura ta harhada da yawa su kuwa suka shiga sauke masu sai da aka gama na fari ta kama cike da kwarewa da kaunar aikinta ta gyara masu ya yi tsaf tsaf da shi ya kwonta kafin ta caje masu ta masu yanda suke so da shi
Sai da suka gama suka biya kudin da aka yanke masu na aikinsu cike da farin cikin samun biyan bukata suka tafi
Sai da saloon ya rage mace daya ta maida hankali ta saka mata gashin ido ta gyara mata girarta sannan ta saka mata akaifun nan da ake kira natural masu tsadar nan ta gyara mata su sukai wani iri kamar nata domin an rage tsayinsu sosai da sosai sun bada kala
Itama biya ta yi ta tafi cike da farin cikin sakin fuskar NAJEEBA
Sai da suka gama tafia ta je jikin madubin ta juya takardar dake nuna a bude suke zuwa a rufe suke ta dawo wajen ma'aikatan nata
Fuska tamke ta ce" Nadia yaushe kika zama uwar gidana?
Nadia da ta san ta yi laifi ta ce" aunty dan Allah ki yi hakuri, walahi tun jiya suka tambayeni yau zasu zo a masu aiki, kuma ke baki ce min kar na bude ba sai dazu a lokacin tuni sun zo na yi na yi na ce da su su tafi suka kiya, clients dinmu ne aunty ke ke hana mu wulakanta clients dinmu
Wani huci ta sauke ta ce" to maza maza a gyara wajen a tatare komai a tsaftace, minister ya yi amarya nan za'a kawota nan da awa biyu, ku tanadi komai domin tun daga kurkun zamu silleta dan uban mama zata gani ba tace ba za'ai mata kishiya ba?
Daria kawarta ta fashe da shi tana kallonta ta ce" NAJEEBA, wai waye ya taba ki yau du kike hawa uwa fulawa?
Murmushi ta sakar mata kafin ta gyara zama kusa da ita ta dauko gashin idon da zata sakawa kanta bayan natama masu tsayin gaske ne da baki, aman da yake tana da bako yau za'q kara firgita shi
Abin sakawar ta dauka bayan ta saka masa col ta shiga dan hura shi tana kallon yanda Ramlat ta huda hancinta
Murmushi ta yi ta ce" Ramlat idan na kale ki hanci a huje kamar saniya
Ramlat ta hade fuska ta harareta ta ce" bana son wulakanci NAJEEBA
ke dake son a huda maki gwfen lebenki fa, nan har cewa kika yi a huda maki harshenki kina tsoron kanwar dad ne ya sa kika fasa wancen aman ai jira kike a kawo maki dan kunnen zinarin da kika saka a maki a huda maki lebe uwa wata yar hannu
Idannuwanta ta jujuya tana dan rawa da kanta ta kalli madubin ta dago shi sosai a hannunta tana kallo ta kasa kasa ta daidaita ta dora na gefen dama
Dayan ta dago shima ta shiga dan matsa masa kadan a sama ta shiga yarfe shi dan ya sha iska kafin ta dora, kunnayenta ne suka jiyo mata muryar bahija na cewa" wai me kuka je yi fada yau ne?
NAJEEBA ta dan saci kallonta ta daga kafadunta ta ce" matsalar cikin gida ne
Baki ta tabe ta ce" ku dai cikin gidanku kulun matsala, to Allah ya sawaka, aman yaya kuka kwashe da mai damagaram yau?
Sai da ta kuma gyarawa ta dora ta daidaita da kyau, tana dago idannuwan nata sun kara wani irin girma da fuzga ta sauke su samanta ta ce" yau na ji jaraba wai ke ina ruwanki da son sannin abinda ke tafe a gidanmu? Kar ki manta kowa da sirrinsa wanda yake gannin sirri ne haba!
Da sauri ta ce" aa, Allah ya baki hakuri, ni ba wani abin ya sa nake tambayarki ba gani na yi ke ke zaginsa kice ya damu mutane a kasa ya hanna mana rawar gaban hantsi ya tsane ki
Allurar da ta dauko tana kara daidaita kashin idon dan ya yo das kar a ga col din da ta saka da shi ta shiga aiki da shi cikin kwarewa ta ce" ba zaki gane ba, ni ina iya zagin ahalina! Aman ke ya haramta a gareki
Ramlat ce ta yi gagawar cenza zancen ta hanyar sako wani, daidai lokacin kuma yayanta ya yi kiranta cewa gimbiya na nemansu bayan salar isha'i
Sai da gabanta ya fadi, lokaci daya ta shiga aiki cikin rashin kuzari gashi aiki ne jajir a gabanta shirya matar minister guda amarya wace kuma ta yiwa kanta alkawarin sai ta mata kwaliyar da zata firgita uwar gidan domin uwar gidan ce abokiyar gabanta wace suke fada da ita
Ba ita ta bar saloon ba sai da magariba ta shige sosai, bayan ta yi sallah ta kama hanyar gidansu da wani irin gudu
Tana zuwa a kofa ta bar motarta ta yi bangarensu da gudu tana lalubar kys din dakinta
Budewa ta yi ta afka bayi ta shiga wanka da wani irin sauri