← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 138

Sashe 73

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karin chek din shine karin da suka yi, sai maganar a ja jari da suka d'ora wace sarai magana ce cikin hikima.

Murmushi Anmy ta yi kafin yayar Zinaria ta dauka ta je gaban Anmy ta tsuguna ta ajiye sak'on ta k'ara gaishe da Anmy din sannan ta koma mazauninta.

Dubansa ya kai wajen su Nadia,
Sai kici kici Aunty take da jaka ita batama san inda ta zuba chek din da ya bada Jakadiya ta kawo masu ba, sarai ya san a wannan wajen za'a so nuna hali na wulakanci shi ya sa ya bada chek biyu wanda ya tabata wannan uwar handamar ba zata taba iya ciro kudi irin haka ba.

A lokacin da ta fitar da takardun sai da ya lumshe idannuwansa sannan ya ci gaba da kallo

Sai a lokacin ta kalli takardar, sai da ta zaro ido tsabar kad'uwa har da yan yatsunta ta kara irga ziro din dan tabatarwa.

Ajiyar zuciya ta sauke ta nufi wajen itama

Tana inda inda ta ce" NADIA na godiya, sannan ta bada kyauta a baiwa kishiyoyinta kamar haka, million muraran million har million ashirin ashirin... *su ja jari* (kar ku manta ita ba sannin me ake fad'a ta yi ba, kokari ta yi ta kamanta)

Itama ta nufi wajen su Anmy, sai da ta duk'a da hannu biyu ta mik'a masu sannan ta mik'e ta nufi wajen Nadia da baki d'aya ta zaro idanuwanta da mamakin kud'in, kan ubancen kaya sa, wani abin sai manya, wani abin sai kishi, yo ita uban wa zai bata wannan kud'in ta yi wasa da su? Ko hauka take, ba dai dan ta birge kishiya ba walahi, kai, inama inama daga ita sai Zinaria ne suka shigo? Inama inama hakan ne?

Kwarai gwuiwar Zahrau ta yi sanyi a lokacin da ta tuna kudaden da suka zo da su kwata kwata million hudu hudu ne, suma Anmy ce ta bada chek din tana fadin akoy tadar nan, suma zamaninsu an yi, idan an kawo amarya kowa na yiwa kowa kyauta, sai dai su nasu da sauki domin zamaninsu idan ka bada million dayama ka yi kokari bare har sama, su kam ba ta nan suka zuba kishi ba, aman sai ga wani tashin hankali kiri kiri ana wasa da kudi kamar jaraba yanzu haka kowace iya abinda gareta ne ta kakabe dan kawai kar a rainata?

Anmy dake yaki da zuciyarta kan ita zata je wani duban ta kuma kaiwa wajen Sultan
Ta sani, farin sani cewar shi ya bada kudin Nadia

Aman why ya yi haka? Shin tsana ce mai tsanani tsakaninsa da Najeebanta har ta kai haka ko me?

So take ta shiga idan ya so sun dade basu ce ta zabi Najeeba a kansu ba! Sam ba zata iya bari a shiga da yan kudaden nan ba, lalle yau ta yarda yanzu irin tadar nan ta zama hauka, gaskiya mahaifiyar zinaria bata son zaman lafia , a kan me zata bada irin hanyar nan? Sai kuma shi kansa dole sai ta tuhume shi da kudaden nan idan kiwa shi ya bayar sai ya ba sauranma!

A hankali ta ajiye ambulope din ta dan mizguta zata tashi

Hannun da ya mayar da ita ne ta bi da kallo

Murmushi ta sakar mata kafin ta idasa mikewa gaba dayanta
Ina sam ba zaka ce matar nan ta haifi najeeba ba,
Doguwar riga ce a jikinta ta shada an mata makeba wace ake fitar da wuya kawai
Rigar ta sha handwork mai tsadar nan irin wanda ake yi a dubai
Rigar ta hadu, ita kadai abin kallo ce sannan aka yi mata dauri das irin na zara buhari a saman kanta
Ashe itama gashi ne da ita?, hakan ya sa daurin ya kawata sosai a kanta
Sam babu irin cikar nan irin tumbi daban mama daban, rigar ta bi shafafen cikinta sannan mamanta ta saka bra das sun zauna a muhalinsu

Kafarta kuwa sanye take da takalmi mai tudun gaske baki sidik wanda ya haska fatar kafar tata, Ummu ba baka bace tana da hasken fata aman kuma ba fara bace

Hannunta dauke da yar poss dinta ba kudi ba abin kudi ko daya a hannunta

Sai da ta tsaya a tsakiya kafin cikin harshenta wanda larabci ya kwonta muraran ta furta" Asalamu alaikum

Idannuwansa ya lumshe cike da jin kunyar wace ta fito mata, Ummu uwa ce a wajensa, ya so Zahra ta shigo dan ya kula da motsin son shigowarta, sannan ya ga Anmy ta so shigowa duda ya yi niyar dakatar da Anmy din domin a nan a yanzu ba a matsayin maman Najeeba take ba, aa , a matsayin mamansu su duka take, sai ya ga Ummu ta fito

Amsawar da suka yi sunna kallonta ya saka ta yi murmushi a hankali bayan ta daga idannuwanta da ta saka masu karin gashin idon da ya zame mata jiki ko a yanzu da ta baiwa shekaru arba'in baya sam bata sake da gyare gyare ko dan ta yi zaman saudiya ne? Ita dai bata sake
Cike da sanyin murya, dauke da tsararen murmushi har hakoran makarta biyu na azurfa suka bayana kansu ta furta" Alhamdulilah
Godiya ta tabata a gareku adalan yan uwa
Allah ya saka da alkhairi da kyauta masu girma da tsari

A hankali ta kai dubanta wajen Sultan.

Sai da ta k'ara sakin murmushi sannan ta ce" Allah ya taimakeka, kyautar *GIMBIYA NAJEEBA* zuwa ga yan uwanta su ne tagwayen gida da kuma shop place."

Shi da kansa sai da ya k'ara kallonta da kallo irin na *DA GASKE KIKE?*

Tagwayen gida dai, gidaje ne da ahalin sarauta suka kashe k'atuwar anguwa suke tanfatsa gidaje kala daban daban a ciki, mahaifiyar Najeeba ta yi dank'ara dank'aran gidajenta masu firgitarwa har k'waya bakwai, gidajen sun ginnu, k'asa ta ci kud'i
sannan shop place d'in nan wajen da ake gabatar da kasuwanci ne, shagunna ne a laye har k'waya shida kowane da sunan shop place ba abinda ba'a siyarwa suma malakinta ne.

Idanuwanta ta d'an bud'a masa sannan a hankali ta ce" har abinda ke ciki." (tana nufin kowace gida d'aya da shago d'aya da abinda gidan da shagon suka d'auka).

Lalle ta kai duka
murmushin nasarar da yayar zinaria ke yi na sun ci fadan sai ya ka ciki, ita bak'uwa ce, aman ta san gidajen nan babu na wasan yaro, sannan ta san shop place.

Ai Nadia gaba d'aya ta ji wani girma ya hau kanta, ita ina ruwanta da wani duka, sam bata san mahimmanci hakan ba, ikon Allah take kallo a dan kankanin lokaci ta zama hajia (🤣 k'awata kennan)

Murmushi ya yi daga cikin rawaninsa, tabas iyayensa sun gama magana, wato idan sauran sun bayar da kud'in jari da sarkar kwaliya, su sun bayar da muhali da uwar jari?

Kansa ya ringa dan girgizawa a hankali , du ita d'in nan ce suke tarawa kasa?
Da sun san, ko baki daya garin nan zasu bayar dan k'watar martabarta ita din ta gama zubarwa da basu yi wannan k'ok'arin ba, da sun san sun siyarwa kansu kunya ne kan kunya da basu yi irin wannan lamari ba.

Sai da ya bushi iska yana gannin ta koma wajen Anmy ta zauna, fuskar Anmy ta fad'ad'a da farin ciki da annashuwa ya sauke ajiyar zuciya.

Bayan sallamar nan, dama zai yi shiru ne du su gama gabatar da kyautarsu wa junnansu, idan sun gama mahaifiyarsa zata yi nasiha , sannan ta fad'i wace zata fara zuwa turaka kamar yanda abin yake a tsare.

Anmy ce ta bud'a bakinta cikin sanyin murya, da mulkin dake cikin jinnin jikinta , cike da aji, da aiki da ilimi ta shiga yi masu nasiha.

K'warai ta yi nuni da girman igiyar da ta rataya a kansu a yanzun, sannan ta yi masu nasiha da su yi koyi da kishi tsaftatace domin kuwa kishi halal ne aman idan har bai zarce ka'ida ba, ta yi masu nuni kan kowace ta girmama ta gaba da ita, su wanzar da zaman lafia a zuciyar mijinsu.

A hanki ta dago ta ce" a yau *NAJEEBA* zata fara tarewa bisa k'a'ida, sannan Nadia dake amarya."

A zabure ta d'ago dubanta da kanta dake kasa, ita kanta a cikin hali take na damuwa, tabbas ta lura idan ba da gaske ta yi ba tana cikin tsakiyar tashin hankalin ne da ake kira gaba k'ura baya damisa.

Rabonsu da wani magana ta shiga tsakaninsu tun a bakin titin nan, sai dai irin kallonsa kan isar da sak'on zuciyarsa.

A yau da ya d'auko mata Nadia a matsayin kishiya sam ta k'i aminta cewar soyaya suka yi, sai ta d'ora hakan a matsayin da saninsa, wata hanya ce ta ya nuna mata cewar ita ba kowan kowa bace, abinda take jin haushin kanta irin yanda abin ya mata ciwo, k'warai abin ya daketa harma fiye da kishiyar da take zaune cikakiya k'osashiya, fitinaniya wato Zinaria, Tabbas abin ya daketa, sam bata tab'a kawowa kanta cewar zata wayi gari ta ganta a irin rayuwar nan ba, yau gata ita najeeba zaune ga kud'i ga mulki aman sun kasa sakata kwaso shoki saima cikin tunani kala daban daban, shin tsoronsa nake? Shine tambayar da ta cika yiwa kanta.

Eh ina tsoronsa, domin tamkar dodo haka yake a wajena, ban san kamaninsa ba, ban san zuciyarsa ba, ban san laifina a gareshi ba, idan dan ina kallonsa ne, ba wani abu bane sai son ganin wai kullum shi sai ya saka kwali? Wani sa'in kuwa idan na ga ana ta magana shi bai yi nakan kale shi dan na ga wai yana wajen kuwa? Fad'ana da matarsa bai shafe shi ba, ita dake zagina da munanan kalamai fa? *SHIN ME NA MASA DA YA SAKA YA FI TSANATA DA KOWA A DUNIYA?*, ni nake da abubuwan da zan tsaneka har mutuwarka, ka d'oran karan tsana kana tsargina? Sannan ka haye dukiyar marayu kana wasa da ita? An ce wai kasuwanci yake, yaushe yake fita kasuwar? (Kam Najeeb, kasuwa zai je? To sarkin wasan karan yara ne ba?), an ci an tayar da kai!
Chapter 73 · 0% Book details