Sashe 60
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuma dubansa ta yi a sanyaye ta ce" wannan rigimar cikin gida ce, ni din, bana iya fadin sirrin Ahalina
Tana gama fada ta yi gama cikin wani taku na ban tausayi domin gaba daya jikinta a sake yake hakama tunaninta ba a jikinta yake ba
...........................
Bayan sati daya
Da yamaci ne suka hadu a bangaren mai martaba,
A tsakanin wannan sati dayan baki daya y'ayan sun cika da zulumi da tashin hankalin abinda zai faru
Ko a yau basu san cewa za'a yanke abinda aka yanke shawara ne hakan ya sa suke cen wajen harkokin su, Najeeba na saloon, Ummu na wajen aure
Tun da aka yi maganar nan Dayabu da kansa ya dakatar da Huzaifa kan ya bari zai waiwaye shi idan hakan zata yiwu
Likita kuwa ba'a bashi damar shigowa bama sai dai a waya suna soyewarsu tamkar ba gobe
Abih du suke kallo a lokacin da ya gama adu'a, kafin a sanyaye ya dago dubanza cike da gamsashiyar amsar da zuciyarsa ta bashi, haka kuma malaman da ya rarabawa kan a taimaka suka shaida masa ya budi bakinsa cikin nutsuwa da kamala ya ce" ALHAMDULILAH,
ba wanda ya isa godiya sai Allah
Alhamdulilah da Allah ya dora mu kan amsar da ta tara mu a yau
Dubansa ya kara kaiwa wajen Anmy dake zaune tana sauraro a hankali ya ce" BILKISSU, du wajen wanda na yarda da kamalarsa, da datijantakarsa , da irin shaidar adininsa da na kaiwa maganar nan ya nuna min ya yi abin a cikin kwana shida, ya yi kwana uku da sunnan kowace
Wasun kuwa sunnan Ummu kadai na basu
Wasun kuwa na Najeeba
Tabas Allah ya kawo amsa,
Amasar nan kuwa ita ce
*NAJEEBA*
BALIN BALIN BALI
🤣🤣🤣🤣🤣 wata wakar indiya[2/12, 4:04 PM] Ummu Sadeeq: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
32
Irin yanda yayi wani dum a zuciyarsa na lokaci d'aya ya saka shi rintse idanuwansa da k'arfi.
"Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une! Me ke shirin faruwa a tarihin rayuwarsa? Shi? SHAHEED, shine da auren wannan yarinyar?"
Bud'a idanuwansa da suka rigaya suka cenza kala yayi da niyyar budar bakinsa ya furta masu magana kamar haka" *Aa, ba zan lamunci auren fasik'a ballagazar mace ba, ku yi hak'uri ku nema mata wani*."
Idanuwan nasa ya fara saukewa kan DAYABU
DAYABU kansa na sade ne, ya kasance zuciyarsa ta cika bugawa mai tsananin gaske domin ya tabbata ba zai amshi maganar Najeeba ba
yana da damar k'iyawar, kuma idan ya k'iyan ba abinda za'a yi
sai dai sai ya kasance ya had'e hanayensa biyu dake rawa rawa cike da tsoron amsarsa yana ta adu'a a k'asan zuciyarsa.
A hankali ya kai dubansa wajen Abih
Sai ya ga Abih ba a zaune dangalgal yake ba, shi bai san yar tsamar dake tsakaninsa da yarinyar ba hakan ya saka farin ciki ke kwonce a kan nitsatsiyar fuskarsa amsarsa kawai yake jira.
Dubansa ya maida kan Anmy.
Irin yanda ta bi ta marairaice fuskarta zaka rantse cewar jira take ta ji amsarsa ko ta suma ko dad'i ya sakata kai sujada k'asa, irin kallon da take masa na jiran jin amsarsa ne, hakan ya saka ta d'an langab'e kanta sannan ta k'ura masa ido tana sauraronsa.
Sau biyu yana k'ok'arin gyaran murya dan ya furta abinda ke cikin zuciyarsa cewar ba zai yiwu ba, Alkhairin ta kai shi wajen wani, sai dai ya kasa d'aga ya d'ora dubansa kan mahaifiyarsa sai ya ji du ya tsintsinke.
" *SHAHEED*." Ta fad'a muryarta har tana d'an rawa rawa.
A sanyaye tace "Sai nake ganin jinkirin amsarka tayi yawa SHAHEED, ko dai ba zaka auri yarinyata ba?"
"EH ba zan iya aurenta ba Anmy..." Zuciyarsa ke fad'a a lokacin daya kasa magana.
ANMY ta ta budi baki da d'an k'arfi tace "SHAHEED?"
Idanuwansa ya lumshe kafin ya kuma bud'ewa kansa ya cire daga dubansu da k'yar ya bud'i bakinsa ya b'amb'aro maganar dake ciki ya furta" Allah ya tabatar da alkhairi Anmy."
Ajiyar zuciya ta sauke tana maida dubanta wajen Abih da yanayin farin cikinsa ya fara raguwa.
A hankali ya ce" SHAHEED? Anya kuwa mun yi maka adalci a maganar nan? Ya dace ka fad'i ra'ayinka domin kai dai yanzu ba wani yaro bane da za'a saka ka gaba a tirsasa maka wani abin ba."
Kansa ya d'an girgiza cikin nutsuwa kafin ya ce" Allah ya sanya Alkhairi Abih."
Abih ya sauke ajiyar zuciya ya d'an saci kallon DAYABU ya ga yanzun ya d'ago kansa yana kallon sarkin.
ABIH yace "Yaya maganar d'ayar yarinyar?"
Saida ya d'an jik'a leb'unansa da suka bushe kafin yace "Insha Allahu idan kun tsayar da ranar d'aurin auren ita ma zan gabatar da danginta sai a yi komai a had'e."
Albarka sosai suka sakawa lamarin, Anmy ta k'ara dubansa , a sanyaye ta ce" Alkhairi ne, insha Allah SHAHEED."
Murmushi ya k'ak'aro mata kafin suke mik'ewa su masa sallama.
A baya ya tsaya sai da suka fita ya dawo da sauri.
Wajen da ya tashi ya koma ya zauna.
Kansa sade ya k'ara had'e hannayensa kafin ya d'ago yace "Dan Allah, ka amsheta da zuciya d'aya domin kai d'in mai zuciyar adalai ce, ka zame mata bango, ka zame mata uba, ka zame mata farin ciki ka zamo sanadiyar shiryuwarta, tabbas na san cewar kana yawan tuhumanta kan harda sakin hannuna a yanda take sangartarta, ka yi hak'uri, ka rufa min asiri ka dubi baiwar Allahn nan da idon rahama."
Saida ya gama maganar sannan SHAHEED ya lumshe idanuwansa ya k'ara gyara kwoncinsa a saman kujerar da yake hakan ya saka DAYABU k'ara godiya sannan ya mik'e ya fita.
Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une ya ringa maimaitawa a k'asan zuciyarsa.
Me ke shirin faruwa da rayuwarsa wanda bai tab'a hasashen kawowa a cikin tsarin rayuwar tasa ba? Meye wannan? Yarinyar nan itane zai aura? Waye bai ce yana sonta ba waye bata amsa tana sonsa ba? Waye bata yiwa kwaliya ta yiwa rangwad'a ba? Waye bai ganta da dan wando tana tsalen gudu da ball a hannunta wai ita ta tafi sport? Wani sakarai ne baya son tab'a jikinta? Wani irin zaman aure ne zai yi da ita bayan yana da dar da irin kasancewarta mace marar kamun kai? Aure fa aka ce,
Idannuwansa ya kuma rintsewa yana jin wani irin haushinta a kasan zuciyarsa
Me ya sa kika gama iskancinki zaki kare a gidana?
Har kansa ya ringa sarawa a irin wannan tunani da ya yi.
Kwonciyarsa ya gyara yana mai lumshe idannuwansa da suka yi ja sannan sukai nauyi yana tunanin rayuwa
A yau bama zai je wajen gudu ba dan baya tunanin idan ya fita zai iya aiwatar da wani abu
Tabas Anmy na cikin farin ciki madaukakin farin ciki, hakama yayanta da kuma DAYABU
Sai dai basu cika nunawa ba domin zaune suke sunna kara tsara ta inda zasu hayo mata
Anmy kan ji har gabanta ya fadi idan ta tuna yanda za'a sha fama da ita
Farko, harkar saloon,
Biyu harkar fita
Uku auren kansa da wanda za'a d'aura mata bayan tana tsalen fad'in ai ita ga wanda take so *HUZAIFA*
Abih ya dubi agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa na hagu ya kalli Anmy ya ce" Bilkissu, wai karfe nawa take dawowa ne, na ga lokacin ace ta dawo ya yi gamu dare dare a zaune shiru
Anmy ta kalli agogo itama, mikewa ta yi tana fadin" k'warai, zuwa yanzu ya ci ace sun dawo duba da tun da na dora mata dokar lokaci bata taba kaiwa lokacin bama take dawowa dan wataran har sai ta rigayi Ummukulsum wace ke zuwa wajen lesson da Professor
Wayarta ta gwada kira shiru, hakan yasa ta nemi layin SHAHEED.
Ta jima tana ringin kafin ya d'aga.
Anmy a tausashe ta ce" ALLAH ya taimake ka baci ka yi?"
SULTAN dake zaune saman sallaya ya d'an girgiza kansa yana fitar da hucin zafin dake cikin zuciyarsa ya dan girgiza kai tamkar tana ganninsa sannan ya d'an furta" Ummu."
Anmy ta k'ara tausasa muryarta ta ce "Dama, so nake ka bani number amintacenka, zan yi kiransa ya yi kiran dogarin dake tare da Najeeba, shiru basu dawo ba."
Idannuwansa ya k'ara rintsewa a k'asan zuciyarsa yana fadin" yaya zata yi ta dawo yanzu? Sai ta gama bi kwararo kwararo tana siyen naman bakin titi ta je wajen da ta nasa k'wai ta zauna daga cen kuma idan ta raya mata ai sai ta nufi wani wajen? Yanzu Anmy wannan ce kika zaba min matar aurena?.
Du a k'asan zuciyarsa yake bayaninsa kafin ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya furta "Ina zuwa."
Kashewa ya yi ya mik'a hannu ya d'auko wayarsa mai d'auke da numbobin du wasu dogaran gidan.
Abin layo layo ne,
DOG NAJ ya kamo kafin ya danna kira.
Daga b'angaren da suke cikin tashin hankali kira ya shigo masa sam bai duba ba ya d'aga ya kai kunnnensa a lokacin kuwa d'an uwan nasa na fadin" Bayan nan ina zamu nufa nemanta? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une."
"Hello? Hello?" Ya ringa maimaitawa.
Shaheed kuwa na sauraron irin yanda dayan ke ta ambatar" Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une." Hankali tashe yana fadin "Kuma wajen mai nama bata nan, mun je wajen mai ice cream bata cen, mun je stade bata cen, to wai ko dai tana cikin saloon d'in nata bamu duba da kyau bane."
Shima hankalin nasa a tashe ya ce" ba ka ga suturar da ta fita da ita bace a jikin yar aikin nata? Yaya aka yi ta fita bamu ganeta ba?"
D'ayan ya furta" baka gannin yau abin ya kasance da wani irin cinkoso gashi dare ya yi mutane wasu sai fitowa suke wasu na shiga ta yaya kake so mu ganeta bayan yau ko fitilar kofar saloon din ba'a kunna ba."
" *INA TA SHIGA?*" Ya fad'a a dake wanda sai a lokacin dogarin nan ya ciro wayar daga kunnensa da wani irin fad'uwar gaba ya lek'a sunnan da ya kira shi
" *GURNANIN ZAKI*."
Wayar ce ta sub'uce daga hannunsa yayi wani irin sama da hannayensa kafin ya furta "Mun mutu."