← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 138

Sashe 96

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya saukar a kan fuskarsa kafin ya mamayeta da fara'a ya idasa wajen da UMMU ta bude na zama

Zama ya yi da bismillah sannan ya kara bin mutanen wajen da kallo,
'MASHA ALLAH' yake ayannawa a kasan zuciyarsa, ashe haka yan uwansa suke da yawa da kyan kallo?, yaren du sai suka shige masa idan ka cire daga bakin marar kunyarsa sai namijin sai yar karamar da ta shiga ransa sakamakon wasan da ya ringa yi da ita harma ya rike sunnanta
Ta kasan ido ya saci wajen da ta duke, ganni ya yi sunna yar kiciniya ita da uwar kafin ta dagota tsaye ta dan harareta sai kuma ta waske ta janyota ta zaunar da ita kusa da ita wanda hakan ya zama ta fi kisa da shi a gefensa na dama

A tausashe ya ce" ku zauna mu ci abinci mana "
Du bin umarninsa suka yi, wanda shi kansa ya kula umarninsa ne suke bi kai tsaye domin yar hayaniyar da ya tarar sunna yi sun yi gum sai kallon junna da suke a sace du sun nutsu

Murmushi ya kuma yi, a lokacin da kamar an budi bakinsu da Zahrau ta kawo masa gaisuwa du sai suka ringa yin irin nata sunna fada a tatare

Ba na wace ya amsawa, sai dubansa da ya kai wajen Ammi ya sakar mata murmushi a hankali ya ce" Ammi, y'ayan naki hala makarantar gaisuwa kika saka su? Na ji sai maimaici suke uwa wa'inda suke kawo harda"

Ammi ta yi yar daria a lokacin da ta fahimci ya tsokani yaren ne, hakama UMMU dake ta bubude kayan abincin
Ummu ta ce" aa fa SHAHEED, kar a haskawa my stars "

Shima dan murmushin ya kuma yi,
Ummu ta kai dubanta wajen yan matan da suke serving tare a da, tun daga kan Zahrau har kan Najeeba aman a yau du sun nutsu irin kamar sunna tsoron su motsa su mutun nan

Da kulawa ta ce" yan mata yau ba za'a zuba ba? Oya maza ku tashi ku yi serving dinmu "

Du sai suka kuma mikewa su hudun nan, sai ya kasance sunna hada ido da junna kowace na son fashewa da yar uwarta da kuka

Ammi cikin jin dadi ta ce" Ke NAJEEBA, ki zubawa mijinki "

Gaba daya sai suka waiwaya suka kalleta, hakan ya saka ta dan zaro ido ta kikifta su a kan yan uwan nata da kuma lokaci daya suka dauke dubansu a kanta kafin ta maida kan Ammi,
Ganni ta yi sam bata kuma bi fa kan maganarta ba, gashi shi din kansa ya yi wani irin zama kamar wanda ya lumshe idannuwansa yake barci bayan idannuwan nasa a kanta suke, kare mata kallo yake haka kawai ya tsinci kansa da tambayar kansa 'yanzun da wani ne ya zo gaishe da Ammi haka zata fito a gujen nan da irin shigar nan kanta ba ko dan kwali' (ta hade gashin kan nata cen sama irin idan zaka yi bacin nan ta daure hakan sai ya kawatata sosai)

Korar tunanin ya yi, ya ci gaba da bin yan uwanta da kallo ya ga yanda suka yi serving din kannensu baki daya bayan sun bubude sunna tambayar kowane abinda yake so

Ajiyar plat a gabansa ya saka shi bin hannayenta da kallo, kamar da wasa sai da ta ajiye har hudu wanda hakan ya saka shi bude idannuwan da dan mamaki yana binta da kallo

Komawa ta yi kujerarta tana maida numfashi kamar wada ta yi tsere kafin ta ja nata da Zahrau ta zuba mata da har cokali mai yatsu ta shiga dan cacaka aman sam ta kasa ci

Na gabansa ya kuma bi da kallo, harda gayya wannan lamari sai kace wanda mutun shida ne zasu ci abincin? Du ta zuba iya kokarinta sannan babu abinda bata zuba ba ta ajiye

Ammi da Ummu kam summa cike da farin ciki suka shiga kokarin jan nasu, a sanyaye Ammi ta yi adu'ar cin abinci a bayane wanda hakan ya saka da sauri wa'inda suka sha'afa suka kama aka idasa da su kafin du a fara cin abincin

Ina iya cewa yaren da su Ammi su ke gwagwarmayarsu ta hanyar cin abincinsu hankali kwonce,
Sauran yan matan da suka dan fara tasawa da wa'inda suka tasa din sam sai suka kasa cin wani abin kirki sakamakon irin yanda tarbiyarsu take na kasa cin abu a waje gaban wani bakuwar fuska , hakan sai ya zame masu wani irin cin abinci su din nan gaban SULTAN SHAHEED

Shima a hankali yake tsakurar wanda ya janyo gabansa yana hankalce da yanda NAJEEBA ke ta wasa da spoon din cikin salak zala da aka zuba mata wai ita ba zata ci mai nauyi ta zama katotuwa ba

Hannunsa ya mika a hankali ya dauki yan kunnayen da suke rigama a kansu, hakan ya sa ta dago da ta sauri ta bi hannun nasa da kallo har ya maida kusa da plat dinsa ya ajiye sannan sam baya kallonta kamar bai yi wani abu ba ya gimtse abinsa

Satar kallon su Ammi ta yi, sai ta ga su ta farin cikinsu suke, duda ba mai magana aman sun kasance masu yalwataciyar fara'a a fuskokinsu

Hannunta ta mika ta dora saman yan kunnen, ba zato tana shirin daukewa ta ji nasa a saman nata
A hankali ya shafa saman hannun nata wanda hakan ya sakata zare ido da zare hannun nata da sauri tana kallonsa

Da sauri Zahrau da su UMMU suka kawar da kai cike da mamaki, ita kuwa sai ta harhade fuskarta kamar zata fashe da kuka sannan sunna hada ido ta murguda bakinta gefe tana kara tura bakin haka kuma tana son zare hannun nata aman jin nasa take ya riketa taf

Ido ya zaro gannin rashin kunyar da take masa, sai ya dan yi murmushi yana gannin su Ammi har sun kamala hakan ya saka a hankali ya kara murza bayan hannunta sannan ya yi aiki da yan yatsunsa biyu ya zare yan kunnayen ya mayar gabansa ya ci gaba da dan cin abincin

Baki ta turo gaba sosai ta ringa kallonsa, shi kuwa sam baya kallonta, su Ammi kansu sun kula da yannayinsu aman ba wanda ya nuna ya ga wani abin

Nan da nan kowa ya gama cin abincinsa banda Najeeba da ta yi ta cika tana batsewa

Ammi ta kalleta ta ce" Najeeba, ya haka? Ki ci abincin mana na ga baki ci komai ba"

Najeeba ta kara takwakwafe fuskarta sai kawai ta saki dan kukan shagwaba ta ce " Ammi, yan kunnayena ya dauka bayan da tsada sosai na siye su fa "

Shi kansa da mamaki yake kallon fuskarta da lebunnanta da take hadawa tana kukan tabarar da su, haka kawai ya samu kansa da kara tsare fuskarta da ido yana jin wani irin abu tamkar tabarar tata na birge shi

Dan tissu ya ja yana goge bakinsa ya tabe bakin nasa bai ce komai ba

Ammi ta kale shi, ta ce" eyah yayansu bata abinta mana baka ga itace karama, ai ummuna ta bar mata ko?"

Ummu ta turo baki itama ta ce" Ammi, to tace na bata sai na bata aman ta daina yin karyar wai ita ta siya "

Najeeba ta gala mata harara ta ki yin magana tana kara matsar kwalar dole sannan baki daya ta saki jikinta rigar jikinta bata dameta ba tana ta kara tura bakinta da yannayi na rigima take ji

Dan murmushi ya yi a lokacin da ya mike tsaye, tura yan kunnen ya yi a aljihunsa sannan ya kai dubansa wajen su Nusaiba

Hannunsa ya mika mata a hankali ya ce" Nusaiba zo"

Nusaiba dake kallon fuskarsa da yar dariyarta ta yi wajensa ta kama hannunsa ta rike tana ta kara kallon fuskarsa so take ta tina inda ta sanshi

Murmushi ya kuma yi mata ya dauketa baki dayanta sannan ya yi wajen babar kujerar fallon ya zauna yana ajiyeta gefensa kafin ya shiga yi mata wasa

Da yannayin farin ciki iyayen suka karasa wajensa gannin da gaske zama ne zai yi tare da su du sai suka bar yaren nan zaune

Kasa kasa Bilkissu ta ce" auntyna dan girman Allah wannan shine sarki?"

Ummukulsum ta gyada mata kai tana murmushi

Bilkissu ta ce" wauh, walahi haka yake da kyau? Kuma ashe ba tsoho bane auntu Najeeba ke cewa za'a aura mata tsoho, kuma Aunty ya fita kyauma ko?"

Najeeba ta ringa share fuskarta ita a dole fushi take, kuma Ammi bata amso mata yan kunnen ba, ita haka kawai take son yan kunnayen ba wani na zinari ba karfe ne sak aman an masu tsari ne sosai,

Yar dariya Ummu ta yi tana kallonta ta ce" SORRY sis, ba zan kuma ba na bara maki yan kunnayen kin ji kanwata?"

Zahrau da ta gama amsa waya kasa kasa ta kashe tana binsu da kallo a hankali ta ce" ta ina zamu fita ne? "

Ummulkhair ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsu ta ce" gaskiya gwara ya ringa rufe maku kansa, ina wannan da budewa yake ai da rikicin mai yawa ne, lalle Najeeba baki da kunya wannan ne kike cewa ke bakya son fari waye waye? Tap, yanzu dai Aunty Zahrau tashi mu je kawai kar mu yi da sanyi, walahi mu je, kai ni daga yau na daina jin haushin kishin Zinaria a barta ta yi kishin mijinta walahi"

Su dai kannanun karasawa suka yi suka hadu da shi da su Ummu sunna wasan su

Da yake AMMI ta san da fitar salamarta kawai suka yi suka tafi su uku tare da dogaran da zasu dafe masu baya har mutun hudu

Sai da ta gama zamanta saman table din sannan ta mike bayan ta yiwa yaya DAYABU mesage cewar tana son ya shigo mata da babar waya da layi

Niyarta ta ratsa ta yi shigewarta daki domin yayunta fu sun fice, kannen nata kuwa kowane ya shiga wasansa kafin malamin makarantarsu ta islamiya ya zo

A tausashe, yana sauraran hirar iyayensa da suke bashi labaru kala daban daban ya bi bayanta da kallo kasa kasa har ta bacewa ganninsa
Chapter 96 · 0% Book details