← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 138

Sashe 82

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lamo ta yi saman bed, a hankali take shafa gashin jikin matashin kan dake ajiye
Idannuwanta ta lumshe kafin ta kuma budewa ta kai dubanta saman yan yatsunta
Hawaye ne suka bi gefen idannuwanta a hankali ta furta" *Yau gani da auren farin mutun, mai sarauta, mai takama, mai jin wahalar magana, wanda ya tsane ni, mai mata biyu bayana*
Dan murmushi ta yi tana juyawa cikin bargonta a hankali ta furta" *ABIN DARIA*

A yau da safe da murna Nadia ta bar bangaren Sultan, duda a jiyan ba wani tabata ya yi ba domin haka ya kwonta sukuku da shi , kwata kwatama a zaman da ta yi a bangarensa na sati daya cif sau uku kadai ya zo mata,kwanakin da ta sha matukar wahala a wajen angon nata, domin kuwa ya kasance du idan zai kawo mata ziyara gabanta ke kwonci kwonci ya fadi ita kuwa sai ta kasa rufe bakinta ta yi ta kurma ihu tana neman agaji da neman yanda zata yi ya sauka da wuri

Sannan tabas ta yarda sarauta wani lamari ne na Allah mai girman gaske da wuyar fasara.

Komai da ido, da hannu ko da kansa yake nuni
Sai idan yana son nuna ya ji dadi yakan dan yi wani killer smile

Bayan ta koma bangarenta Aunty ta amsa kiransa
Wani dan akwati ne ya bata a hankali ya furta" Allah ya bamu zaman lafia

Da amen amen ta amsa kafin ta baro bangaren cike da farin ciki da annashuwa, tana tunanin yanda zata yi ta koma gida, itafa walahi ta ga waje

A cikin satin nan ba abinda suke tsakaninta da yan uwanta sai zama sunna debewa junna kewa
Wani irin karfin gwuiwa ta ringa ji yana kara shigarta, wani irin tabacin decision dinta na kara zama a kasan zuciyarta
Bangaren anmy bata daina tsumamata ba wanda hakan har mamaki yake bata, domin akoy lokacin da ta ce" Anmy, shi abin nan yaushe za'a daina shi?

Sai Anmy ta ce" Jannuh, ba za'a taba daina shi ba koda kuwa Allah ya albarkaceki da samun ciki, domin bashi da matsala ga lafia, sai dai ma ya kara maki lafiar, Najeeba, mace ko
me take takama da shi sai da gyara, baki ga yanda yanzu Zahra ke dauka da kanta ta kimtsa kanta ba? Ai sannin darajar abin da ta yi ne

Ita dai murmushi kawai ta yi wai ciki, ciki fa? Da wa? Ko kare mata kallo da ya yi ya shamaceta ne, macuci kawai azalumi mai fuska biyu!,

sam ta fasa gardamar amsar gyara ko shan dadadan nonon rakumin da ake mata hade hade a cikinsa,
Takan maida kai da fata ta karba a ranta kuwa fadi take, tanadin wani ne, domin yana sakina zan maka auren rashin mutunci wanda Damagaram zata girgiza

Mijin zahrau ya kasa hakuri ya shaida masu cewar zai zo su tafi, daka ta shige ta yi kiransa ta kwontar da muryarta, sai da ta gama rarashinsa tamkar wani yaro da dadadan kalamai kafin ta furta masa ya bata kwana uku kawai, in sha Allah zata zo koda bata gama abinda take yi ba

Kwarai ta rike wannan abu a ranta, ta yiwa kanta tambaya....yaya aka yi yake zumudi a kan yayar tata? Gashi dai Gimbiya na nan, rabonsu da ita tun haduwar da aka yi wai tana jinyar Zinaria, sun hadu sun dinke a bangaren Zinariar ita kanta ko barorinta rabonsu da su ganta sati dayan kennan, Anmy da Ummu da su ummu da Zahraun zuwansu biyu aman Gimbiyar kadai suka gani ita din wai baci take.

*Ranar tarewarta*

Zaune suke a falo su biyar, UMMU na kitse kan Zahrau da wasu irin kannanun kitso masu bala'in kyau tana yiwa Anmy Daria
Ba dariar komai bane face irin yanda tun dazu takan dan rafka tagumi sai kuma ta cire ta kai dubanta agogo ta furta" yaya zamu yi da y'ata? Yau ranar zuwanta turaka ne, gashi har an yi magariba."

Wani irin sansanyan kamshi, mai hade da kamshin turaran wuta, da takun takalmin mai dan tsini ne ya saka su dan juyawa.

Ya Subahannalah,
NAJEEBA ce ta bayyana cikin shigar wata abaya bak'a sid'ik mai dan ado fari fari
Tsaf ta zane fuskarta da simple mak'up kafin ta gyara gashin kanta ta yane dan kwalin rigar bak'i mai shara shara.

Irin yanda rigar ta bi shap dinta abin ba'a cewa komai.

Hannunta kuwa dauke da wata jaka mai dan girma fara kal itama wace ta zuba abubuwan buk'atarta.

Wauh, Ummulkhair ta fada tana mikewa da yannayin tsokana ta ce" Najeeba, wannan kwaliyar du ta oga ce?"

Murmushi ta yi ta ajiye jakar tana rufe fuskarta da hannayenta bibiyu.

Wani farin ciki da sanyi ne ya ratsa zuciyar Anmy har ta kasa boyewa, UMMU ta dan cije lebenta na kasa tana murmushi a kasan zuciyarta kuwa mamaki ke son kasheta, ya salam, wannan yarinyar ba abinda ta bari nata ko meye? Bangaren halaya bayan ba tare suka rayu ba?

Farin cikin Anmy ya kasa boyuwa hakan ya sa ta mike da matsanancin farin ciki ta yi cikin dakinta da wayarta, dan zata yi kiran Jakadiya ne, sannan ta dauko dahuwar da UMMU suka yi da ZAHRAU wace da kanta ta shaida masa cewar yau ita zata tura masa abinci, sannan ta nemo Alkyabar da zata hau da irin shigar yarinyar nata.

Cike da Tausayi zahrau ke kallonta, bata san dalilin da ya saka UMMU ta saka maganin nan a cikin abincin da za'a kaiwa SULTAN ba, abinda ta sani shine tana da dalilin son dole dole hakan ta tabata.

Hannunta ta kamo ta janyota kusa da UMMU sosai kafin ta kaleta, muryarta ta sanyaya ta ce" yau tsal, ina so na ji kun yi magana."

Najeeba ta kaleta, aman sai ta dan cure lebunanta masu shegen kyau ta kasa cewa komai.

Ummu ta yi murmushi tana jin tamkar ta ciro zuciyarta ta buda mata ita ta nuna mata irin ilar da soyayarta ta yi mata, shin yaushe zata dubeta? Yaushe zata yafe mata? Sai kuma wani tausayinta da take ji na daren yau wanda ko wace uwa take iya kasancewa, wato cikin zulumi da tsoro da tausayin y'arta,
Ta tabata abinda ta je ta siyo ta zuba a abincin SULTAN ko dokine shi sai ya motsa shi bale mutun dan adam mai rai da lafia tabbas ba zata iya fitowa ta nuna rashin jin dadinta a abinda ya faru da y'ar tata ba, aman ta yiwa kanta alkawarin gyara auren yarinyarta ta kasa
Yanda kowata mace cikin matansa ta samu kulawarsa a lokacin da ya yi niya, to fa zai kalli Najeeba koda bai shiryawa hakan ba
Kwarai bata kulaceshi ba, aman kuma zata saka shi ya fara cire zargin dake damunsa, duda ita kanta bata da tabacin idan har zai cire zargin.

Najeeba na zaune tana kallon yan yatsun UMMU. Tsoro take ta kasa ci gaba da gaba da matar, tsoro take karfin soyayar matar ya yi rinjaye a rayuwarta bayan ta yiwa kanta alkawarin in sha Allahu itama ba zata kulata ba.

D'an d'ago dubanta ta yi sai idanuwansu suka sarke da junna
tsantsar kauna, had'i da yanayin tausasawa take hange a idannuwan matar, da sauri ta cire dubanta.

Ummu ta sauke ajiyar zuciya tana gannin an fara fitowa da kulolin gidan sarautar sababi masu mugun kyau.

Yayunta ne suka amshi kayan, Jakadiya ta rike jakarta
Ta coridor suka bi suka tafi UMMU ta lumshe idannuwanta a kasan zuciyarta tana furta" I'm sorry JANNUH."

Anmy ta zauna a hankali gefenta kafin ta kamo hannunta ta ce" MARIAM, ki kara mata lokaci kadan kin ji? Na tabata ita kanta karfin hali take, shi yasa na daina mata maganar na zuba mata ido, zata zaburo ne a lokacin da bamu yi zato ko tsamani ba.

Murmushi UMMU ta yi ta dora kanta saman cinyar Anmy, a sanyaye ta furta" da na sani, da na zauna komai wahala, da na sani da na zauna komai tashin hankali da bacin rai, Aunty Bilkiss na tafi, yanzun na dawo du irin dukiyata, mutanena, na kasa samun nutsuwar tunanina.

Cike da tausayawa Anmy ke k'ara tausarta.

Dayabu da ya sanyo kai sai ya juya dam ya koma, ba zai shigo ba a irin lokacin nan, dama yau yana da wajen zuwa budurwarsa ta dawo daga karatu zai je su ajiye magana a yita ta kare, dogon karatun nan ya ishe shi haka.

Basu jima wajenta ba suka juyo, su Ummulkhair sai santin falon suke , ita dai Zahrau ta yi gum abinda ke zuciyarta na zuciyarta.

Mikewa ta yi bayan ta cire Alkyabarta a hankali ta nufi dayan dakin da ya saka Nadia wancen lokacin
Hannunta na hagu rike da yar wayarta karama wace rabonta da dubata har ta manta

Jikin kofar ta tsaya tana k'arewa irin kofar kallo.

Bakinta ta yatsina ta saka hannunta a hankali da niyar budewa
Sai dai ta yi ta yi kofar ta ki ta bude
A fili ta furta" Munafurci!

Juyawa ta yi wajen dayar kofar ta karasa
Idannuwanta ta lumshe sakamakon jin wannan turaren du ya cika dakin harta da kofar idan ka rabo sai ka ji shi butu butu

Fasa budewar ta yi ta juyawa kofar baya tana gannin kira na shigowa wayarta

A tsanaki ta daga kiran ta yi salama

Aida ta ringa ihun murnar jin muryar uwar gidan nata a rikice ta ce" Aunty wai dan Allah da gaske yanzu Sultan SHAHEED kike aure? AUNTY wai aure kika yi da gaske? Aunty yaushe zamu zo mu ganki? Aunty shago fa?

Najeeba ta dan dafe goshinta a hankali ta ce" Aida wannan ihun fa, sannan wace kike so na amsa maki cikin tambayoyin?

Sam bata ji budewar kofar ba, sannan bata ji fitowarsa ba, domin Aida ta kasa daina ihunta sai murna take ta ce" Aunty ba zaki gane bane, mutane da yawa sunna zuwa wai a taya su murna kin yi aure, su yanzu so suke su koma yar mutunci da ke kin zama gimbiyar garinmu , wai harda matar Ambasador ta zo gyaran kai fa tace ita so take ta zama mai classs yanda mijinta zai daina fade fade, ta zama client dinmu daga yau tana so a ringa kula da ita a shago
Chapter 82 · 0% Book details