← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 138

Sashe 30

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai mahaifiyarta ta yi kuka ta rungumeta a jikinta ta furta" kamar yanda kika kasance yarinya mai faranta min, mai yi mana biyaya, Allah ya karbe ki da ni'imarsa Bintu, Allah ya yafe maki kurakuranki mu kam mun yafe maki dukan laifinki
Kansa a sade yake yana dauraron irin adu'ar iyayenta a kanta, kwarai ya kara tabatarwa kansa cewa ya yi rashin mace mai daraja, irin yanda du bakin da ya bude tun zuwansa wajen yabonta ne da fatan alkhairi a gareta sai ya ji yana mangarinta, sai ya ji yana mai adu'ar Allah ya sa idan tashi ta riske shi ya samu irin wannan shaidar ta duniya wace itace ta lahira
Mahaifiyarta ta dora kanta a gefen hannun mahaifinta dake dan dadaba bayanta a hankali dan ya rarasheta ta ce"ta rayu da son gannin sarki a rayuwarta, tana son ta ganta gata ga sarki,
Sai gashi yau Bintu gaki ga shi aman baki san yana wajen ba,

Maganar ta kuma dukansa, dan haka sai ya nemi da su je ciki a kaita ciki kawai

Sai da ya gama dukan abinda yake na bincike sannan ya kamata, ya cicibata ya dorata a gadon bayansa dan kuwa ya ki dogarai su kama masa du irin nauyi na gawa ya dorata a bayansa ya nufi bangaren da aka kawata mata

Shinfideta ya yi saman cafet ya zauna a hankali ya cire babar rigarsa

Karatu ya saka ya shiga cire mata takalman kafafuwanta, ya ringa cire mata komai a hankali sai da ya cire mata komai ya dauki sabuwar zanin rufar da ya kawo ya rufa mata shi har kanta

Mikewa ya yi ya je ya yi waya da anmy sannan ya karasa ya bude ya amshi likafanin da ya bukata har an kawo masa, a lokacin yake son shiryata

Dukan abubuwan bukata ya kawo kusa da shi ya shiga binta a hankali a laluma yana lalabata yana yi mata alwallah

Dakatawa ya yi dan dole sai an cire masa abin idannuwan nata da kuma su sarka da yan kunnayen dai da sauransu

Gaba daya jikinta rawa yake, tun da ta dawo ta tardo wannan lamari ta ji gaba daya hankalonta ya gama tashi jikinta kuwa ya kwashi rawa yanda ka san mazari

Bata furta komai ba, tafe dai suke ita da Zahrau har suka shigo falon

Gabanta ne ya yanke ya fadi a lokacin da ta gansa zaune a kasa ya sada kansa gaban gawar yana karatu muryarsa a bayanne aman a hankali kuma a sanyaye
haka kuma bai cire rawanin dake jikinsa ba aman baya dauke da babar rigar
Gaba daya zaka fahimci yana cikin tashin hankali ne idan ka kalli jijiyoyin hannunsa irin yanda suka mimike suka yi wani irin tsanwa da su abinka da farin mutun

Hannun Zahrau ta damka wace ta jata suka karasa baki dayansu

Bai dube su ba, sai hannunsa da ya saka ya bude fuskarta ya kasance fuskar ta bayanna

Irin yanda fuskar ke fitar da annuri dole ka ji hankalinka ya tashi, gata dai kamar wace take bacin gangan

Sai a lokacin ya dago ya dube su
Ya san cewa itace mai iya fitarwar dan haka ya nuna mata kusa da kan Bintun yana nufin ta karaso ta cire mata

Jikinta na ci gaba da rawar ta karasa ta tsugunna
Dan man dake hannunta ta lakuta hannunta na rawa ya kai wajen idannuwan bintun
A hankali ta shafa mata a idonta na dama ya dan dauki dan time ta janye shi ta cire shi a hankali ya biyo hannunta ba saura ko daya a jikin

Dayanma ta saka hannunta ta shafa sai kawai ta ji ta kasa rike kukan nata a wannan karon
Hakan ya sa ta zabura ta mike tsaye da niyar guduwa waje ta ci kukan dake wuyanta, shikenan? Yanzu shikenan? Yarinyar da ta je dazu ta yiwa kwaliya har sunna tsokanarta wajen turara mata turaran wuta itane kwonce haka gawa? Sai an juyata sai an kwontarta?

Hannunta da ta ji an damka ne ya sakata saurin juyowa

Bai bata damar fahimtar komai ba ya risinar da ita kusa da shi sosai har ya kasance sunna gugan jikin junna

Sakin kukan ta yi da karfin gaske hakan ya saka shi janyo kanta shima da karfin ya dora saman kirjinsa ya saka hannunsa ya tare keyarta da shi har yana hade hijab dinta da shi sannan ya shiga girgiza kansa a hankali ya ce" yaya zaki yi irin kukan nan a kan gawa? Kar ki kona min jikin matata

Muryarta cikin kuka ta ce" ta mutu? Shikenan ta mutu? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une

Zahrauma ta janyo kafafuwanta ta hade da gwuiwarta ta fashe da kuka tana mai tausayin kanta da dukan musulmai

Ya zama dole dai sai an mutu? Kowani mai rai mamaci ne , ya zama dole kowa ya dandana zafin mutuwa

Jin ta sasauta kukan ya saka shi cire kanta daga kirjinsa yana yi mata wani kallo mai cike da fasarori irin na jin haushinta, na gannin rashin dacewar ta yi masa ihu a ka ga kuma gawa haka kawai, ya dauki hannunta ya nufi wajen fuskar domin ba idasa cire abubuwan ta yi ba shine zata wani tsere ita ga mai neman balaki!

Hannunta na rawa tana dan cije lebenta na kasa ta idasa cirewa

Gannin ya nuna mata yan kunnayen da sarkar ya sakata zaro idonta

Mikewa ta yi da sauri ta fita da gudu tana kara sakin kukanta

Da ido suka bita daga shi har zahrau, dan haka sai ya nemi da Zahrau ta cire dan shi baima san yaya ake saka abubuwan nan ba

Zahrau ta taimaka masa suka cire yan kunnayen

Sun zo cire na wuyan ne suka ga wani bakin abu ya bushe a wuyan nata

Da sauri ya saka yar auduga a ruwa ya shiga goge wajen
Wasu yan hudoji ne biyu rak suka bayanna a gefen wuyanta

Hannunsa ne ya shiga dan rawa a lokacin da wani tunani ya darsun masa a zuciyarsa dan haka bai yi kasa da gwuiwa ba ya kama wajen ya matse da karfin gaske dan gannin idan har abinda yake zato ne

Irin ruwan da ya fito, kafin wani bakin jinni ya ci gaba da fita ne ya saka shi rintse idannuwansa yana jin wani irin zafi da ciwo a zuciyarsa

Bai ce da ita komai ba sai salamarta da ya yi

Bai yi mata wankan ba sai da ya tabata saran na wani kalar maciji ne sannan ya kimtsata tsaf cikin suturarta ta karshe kafin ya tatare komai ya yiwa malaman dake jira iso suka dukufa suka shiga sauke mata alkur'ani mai girma, sannan liman ya je masalaci ya yi shela da kuma raraba kulhuwalahu dan yi mata shinfida ( ya Allah ka bamu irin gatan nan )

Sai da aka yi saukar fari sannan ya fito ya kara komawa wajen motar nan

Da hasken wayarsa ya kara hahaskawa tare da amintacen dogarinsa
Gaba da baya basu ga komai ba dan haka suka buda boot

A tare suka zabyra sakamakon gannin wani dan saurayi dake daya daga cikin yaran gidan dake gyara wajen dawakai, yaron maraya ne gaba da baya yana aiki ne a gidan sarki a mace shima da kuma macijin nan a raye ya nanade jikinsa sai kansa dake dan gilo a sama kadan

Da sauri amintacen mai martaba ya so matsa mai martaba gefe dan kare shi daga macijin nan

Sai dai ya tare shi ta hanyar bashi wayar hannunsa

Cike da kwarewa ya damki macijin nan ya yi masa rikon nan da ake yiwa makogwaron maciji ya janyo shi inda macijin ke ta fitar da dan harshe yana wani irin kara sssssssssssssss

Yar yatsarsa ya saka bayan ya kara tabe bakinsa sosai ya cire abida ke watsa dafin sannan ya mikawa amintacensa ya maida dubansa wajen yaron

Harbin bindiga ne kansa harbi daya tak wanda ke fasara komai wato yaron ya yi aikin kashe amaryar mai martaba wanda ya saka shi aikin kuwa ya kashe shi

Sai da ya yi kiran asibiti aka tafi da yaron dan aune aunen bulet din da sauransu sannan ya wanke hannayensa ya koma ya har amintacensa da macijin nan inda ya nufi cen cikin fada da shi dan ganno na waye domin akoy yaren dake wasa da macizai a cikin gidan sannan da masu koya masu yanda zasu tafiar da maciji

..........................................

An yi sututar bintu cike da daraja da tarin al'umah
Ta samu adu'a'u, tana cikin samu domin mijinta ya dauri niyar jerota a cikin mutanen dake samun adu'ar nutsuwar kabari har karshen rayuwarsa bayan kuluhin musulmai da yake bi da shi

Gidan ya kuma daukan haramar jama'a, mutane zuwa suke ta kowani gefe ana yiwa sarki da ahalinsa ta'aziya ciki kuwa harda yayunsa da kanwarsa daya kwal dake garin Niamey wajen yayarta

Yana zaman makoki ne hankalinsa a rabe, sosai ya kara sakawa rayuwar gidan ido inda bincike ke tafia ta kasa yana son sannin abinda ya kawo maciji da mai wasansa cikin sabuwar motar da ya ware a boye dan dauko masa matarsa motar da ta kasance mutun shida kawai suka samu ganninta suka san da ita su ne : Sarki, Anmy, amintacen sarki, Zinaria, Abih, sai liman baba

Gidan bai samu sasaucin jama'a ba har sai da aka yi satin Bintu
Daga lokacin gidan ya fara samun daukewar sahu kadan kadan sai masu zuwa ziyara masu zuwa gaishe da sarki daidaiya

Zaune suke kowane da yamutsen zogalensa a cikin plate sun saka Anmy gaba sunna dan ci kadan kadan

Daya daga cikin kawayen matar ambasador ce akayiwa iso tare da mijinta zasu yiwa Anmy gaisuwa duda ita ba sanninsu ta yi ba aman da yake sun saba sai ta umarci a shigo da su
dan

Ajiye nata plate din ta yi sannan ta dan fito daga cikin yaren nata ta zauna inda take karbar baki

Tun da suka shigo suka zube sunna gaishe da Anmy
Mijin nata ba wani tsoho bane, hasalima Ambasador ya girme shi a shekaru

Anmy na amsawa tana mai nuna masu jin dadinta
Chapter 30 · 0% Book details