Sashe 125
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana gama fada ya juya ya shiga takawa, yana jin lokacin da ta kwala wani ihu duda muryarta a shake take ta zube kasa sumamiya, haka suka konkimeta suka sakata a mota, a hanya ne suka yi kokarin gannin ta farfado kafin tale gane komai sun sakata a motar hayar da akai mata shata zata dauki hanyar damagaran zuwa Agadez, hanyar da bata taba bi ba a mota tun da Allah ya haliceta, sai gata yau an sakata da ranar gari zata shiga garin agadez a motar haya, ita kam ko a haka aka barta ta gane rayuwa bale idan ta tuna mahaifinta na jiranta da takardar saki? Ita kam ta kawo abinda ba wanda ya taba kawowa gidansu, aman ta tabata mahaifiyarta zata tare mata (uhum, baki san itama an turata gidan ba😁)
Daga nan bangaren su Nadia ya nufa domin ya yi niyar yau ba zai fita ba
Yana zuwa suka gaisa da iyayenta, sannan ya mata yaya jiki da tambayar ko akoy abinda suke da bukata?, sun bashi gamsashiyar amsa sannan ya fice ya koma falonsa
A nan ya tile, a nan ya kuma bajewa, a nan ya ringa shigar yarinya ta inda bata zato bata tsamani, a nan ya ringa kara yiwa kansa ilah da soyayar yarinyar Ammi, a wajen nan ya ringa baje kolinsa , suka ringa samun kusanci da shakuwar da bai yi da wani mahaluki ba.......
Bayan kwana biyu da daurin auren su UMMU yaya DAYABU ya dawo daga tafiar da ya yi garin Niamey bisa aikinsa
Farin ciki ba irin wanda bai nunawa Ummu ba, sannan ya shigi abin da karfi karfi dan kuwa kiri kiri ya nuna ba zata zauna a wancen gidan ba, dan haka aka shiga gyare gyaren rantsatsen gidan Abih dake anguwar jeune cadre
Tsananin farin cikin da Abih ya shiga ba'a cewa komai, hakan ya sa shima ya shiga gabatar da bincike a kan yarinyar da DAYABUN ke nema, dan kuwa ya shiryawa bikin DAYABU, a duniya DAYABU ya kasance jigon rayuwarsa da ta y'ayansa, kowa dai rigimarsa shi yake zubawa, kowa shi yake kaima, shi kuwa ya dauka ya rungume ya nemi mafita , sam baya wasa da ahalin MUTALAB dan haka shima ya fara dukan lamarinsa da dukan katfinsa, dan kuwa zai masa biki na dan gata.
A cikin sati gudan nan idan fitar SHAHEED ta yi yawa bai fi sau hudu ba, NAJEEBA kam tana ji tana ganni zuwa bangaren AMMI ya gagareta domin Shaheed ya wani irin kasawa ya tsare dukan motsinta a kan idannuwansa, ya zamana idan ka ga an neme shi to abu ne mai girman gaske wanda dole sai ya fita, ko harkar kasauwancinsa da yake yawan operat a dakinsa ya ajiye ya basu dama, ya kasance Najeeba ta gama salamawa zuciyarta da gagarumin abin dake dawainiya da tunaninta
A yanzu kwata kwata ta daina yi masa maganar wani, koda ya yi dan ya nemi fitina takan yi murmushi kawai ta yi masa shiru
Ta yi maganar fita saloon ya fi a kirga, da ta ishe shi ya nuna mata saloon dinta su Aida na aiki , da mutane ba masu wani uban yawa ba domin sai da aka buga bage, idan kana son aiki a wajen zaka ciri tikite ne ka yi jiran rana da lokacin da aka baka,
Ta ji dadin hakan kwarai, harma ta tambaye shi yaushe zata koma bakin aikinta? Sai ya nuna mata zata koma idan ya ji hankalinsa ya kwonta da hakan
A yanzu Najeeba na dawainiya da wani irin kishi a cen kasan zuciyarta, a yanzu take jin haushin du wata mace mai sunnan tasa ko wace suka taba maganar da ta zarce ta yan uwantaka ko ta aikinsa
Ita kanta tana mamakin kanta , basu furtawa junna kalmar so ba, ama sunna wani irin kafa kafa da junna fiye da tunanin mai tunani
Yau suka cika sati guda, kuma a yau ne zata bar aiki Nadia ta kama, haka kawai ta tashi da bacin rai sosai
A cikin ruwan wanka take kwonce ta lumshe idannuwanta, ba komai ke mata yawo a kwakwaluwarta sai irin lamarin da ya wakana tsakaninta da mijinta a daren jiya
Ta kasa cire wannan lamarin a cikin zuciyarta,
A yanzun tsakaninta da shi abu daya ne kwal ya kasa furta mata, wanda zata iya rantsewa zuciyarta na bukatar jin hakan daga bakinsa
Zuciyarta dake tashi ne ya sakata juyar da kanta ta tofar da yawu ta kora da ruwa sannan ta idasa wankanta ta fito tana mai jin wani irin baci
Tana fitowa da gagawa ta karasa wajen kayanta da aka turo mata da su ta shiga kimtsa kanta dan bata son ya tardota har ta yi wanka ta tabata zai nuna bacin ransa ne
Tana gama dora alkyabarta ta karasa gaban madubi da gashin idon da aka sako mata wanda ta sa su Ummu suka sako mata komai ta gyara ta shiga dorawa
Fuskarta ta gyara kadan sannan ta saka jan baki kalar kasa kasa a dukan lebunnanta
Turarensa ta dauka ta shiga fesawa, a haka ya shigo da waya a kunnensa yana amsawa
Bayanta ya kurawa ido, alkyabarta, a hankali ta juyo ya zamanto sunna facing din junna
Murmushi ta sakar masa , wanda shi kuwa fuskarsa ta nuna yannayi na ya shiga halin damuwa a yanzu yanzun
A hankali ta taka har inda yake tsaye , tana zuwa ta shige jikinsa, tana jin muryarsa a sanyaye ya furta" zan tabo ka daga baya "
Bai tsaya ya ji amsa ba ya kashe yana mai sakin wayar nan ya saka hannayensa bibiyu ya rungumeta a jikinsa yanna jin yanda zuciyarsa ke dokawa
A hankali ya ce" Har gagawa kike ki bar ni? Shine har kika yi wankan ki bayan kin saba cuta min bayana? "
Dan murmushi ta yi na karfin hali a ranta tana ayanna ai gara kai idan ba daya da daya, ni fa? A fili kuwa sai ta furta" ango fa kake mijin Nadia, na tabata zata yi maka fiye da hakan "
Bai ce komai ba sai dan murmushi kawai da ya yi ya karasa saman kujera da ita suka zauna yanda suka saba dare dare tana saman cinyarsa
Cikinta yake shafawa, ahi kadai yana adu'ar Allah ya sa kwalonsa ya gama shiga rijiya, yana da burina rayuwarsa, shi ne ya buda ido ya ga cikinta ya tasa, ko zata daina rigima daga ranar?
Sunna nan zaune sai shiririta tafiarta yake, da kyar ta samu ta kubce masa
Ta yi mamakin yan rakiyarta matuka, yayunta ne su biyu da jakadiya da bayi mutanen dai masha Allah
Haka suka sakota tsakiya anai mata wani irin kirarin da ya sakata jin wani irin girma na hawa kanta, a haka har suka karasa bangaren AMMI
AMMI, Yaya Dayabu, Abih, da kannenta ne cike a wajen ana ta hira ana daria
Sai ta ji wata irin kunyar hada ido da su ta kama ta, bata taba jin haka irin na yau ba, ga bacin da take faman ji, ga tunanin barinsa da ya saukar mata da kasala
Basu dai samu yanda suke so da kanwar kuma yarsu ba, dan kuwa sama sama ta tsaya kafin ta shige dakinsu tana sauri
Tana shiga ta tarar da UMMU na ware jigidar nan da Zahrau ta ajiye sauran a saman sif
Da sauri UMMU ta sha murr gannin Najeeba ce, ta idasa fitarwa ta saka a jakarta tana kallon Najeebar dake kallon jakar tara
Daria kawai Najeeba ta yi ta haye bed din a hankali ta yi matashin kai da cinyarta tana mika
Ummu ta yi murmushi ta shiga shafa lalausan kanta, haka kawai ta yi ra'ayin yi mata kitso dan haka sai ta gyara mata kwonciyarta ta dauko kayan kitson ta haye gadon ta gyarata yanda zata ji dadin tsara mata kitson ta shiga yanyara mata shi kannana sosai
Ummulkhair kuwa ta dama masu lale na hausa , Ummukulsum ta je ta kawp skoth ta zauna tana yankawa sunna hirar su har baci ya dauke Najeeba......
YAYA DAYABU kuwa kayan UMMU ya ringa jida yana kaiwa motarsa har ya gama komai ya kulle motar ya dawo dan yana son ganawa da SULTAN yau yau din nan kafin ya kai kayan UMMU a kimtsa mata su dan an gama gyara an zuba kaya an gama jera komai mai dakin kawai ta yi saura, Mardiya kuwa tana wancen gidan na Abih
__________________________
Washe gari ta tashi da rashin kuzari, haka ta yi wanka ta kimtsa kanta suka ci gaba da ayukansu da yan uwanta
Wajen karfe goma suka yi waya da Zahrau da dukan yan uwansu hakan ya sa wayar ta dauki dan lokaci kafin su katse
Garin dan wake suke gyarawa zasu jwfa dan wakensu shelar shigiwar Sultan ta karade wajen
Ai kamar ana wuwurga su suka ringa tserewa kowa na shigewa ciki, hakan ya baiwa NAKEEBA daria har ta dara abinta ta ci gaba da hada garin da kanwa da miyar kuka ko foku
A lokacin da ya shigo sai da ya gama da iyayensa sannan ya karasa wajen da yake hangenta ta dage tana kwaba garin hankali kwonce da muciya
Zama ya yi yana kallonta, a ransa fadi yake hankalinta kwonce, yanzu haka ko tinawa da ni bata yi ba, dama fama take ta dawo ta zuba sangartarta
Gaishe shi ta yi tana dubansa, a lokacin shi kuwa sai ya zame ya zauna saman ledar da suka shinfida dan kar su bata wajen
Daga UMMU har AMMI ido suka zaro daga inda suke zaune da matsanancin mamakin gannin ya zauna a nan ba kan kujera ba, ba cike da takama ba
A hankali ya ce" Na ji, ko ki kiraye ni ko? "
A ranta ta furta'ina ni ina kiranka kana tare da matar so raina ya baci ', a fili kiwa baki ta dan tabe bata ce komai ba
Zamansa ya gyara da niyar yi mata tambayar da ya zo da ita, Allah yana ganni yana matukar mamakin lamarinta, haka kuma bai taba sakawa ransa wai tambayar na iya kawo matsala ba, dan haka hankalo kwonce ya ce" BEEBAH "
Dan dakatawa ta yi da motsawar tana kallonsa, jin ya yi mata irin kiran dake kasheta dan haka ta kura masa idannuwanta masu hadasa masa kasala